Showing 51001 words to 54000 words out of 88726 words

Chapter 18 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt

office ɗin sa, sallamar mu aka yi muka kama hanyar gida


A ƙofar gida ya ajiye ni, ina shiga ɓangaren anty fannah na nufa tana ganina sai tace min

"naje wajen ku aka ba a san inda kike ba wannan ƴar iskar kishiyar" murmushi nayi yadda anty fannah ta tsani badia ni ban tsane ta ba


"ni albishir ma na zo miki da shi amma kuma kin fara kawo zancen badia" barin abinda take yi tayi sannan ta ƙaraso wajena


"ciki gare ki don ashine kaɗai albishir ɗin da za ki min inji daɗi" murmushi nayi sannan na shafa ciki nace

"wata ɗaya" ina faɗa mata ina murna, rungume ni tayi tana murna nima ina yi, sai da muka gama murnar mu sannan tace min


"asibiti kuka je aka tabbatar" gyaɗa mata kai nayi sannan nace mata


"har allura ma akai min me shegen zafi"

"allura kuma ta mecece" ta tambaya fuskar ta da alamar mamaki


"oho ni ban sani ba, don da muka shiga office ɗin su suke ta abun su banda ni"



"ƙila ko na ƙarawa babyn ƙarfi ne" inji ta muka ci gaba da hirar mu, har anty fannah tana bani shawarar kar in sake in bari badia ta san da cikin sai dai kawai ta ganshi



Hira tai hira muna ta yi can sai naji mara ta ta fara mintsini na, na share, abu wasa wasa tun ina basarwa har na kasa na faɗawa anty fannah ga abinda nake ji faa


"ikon Allah tace ba yanzu kuka je asibiti ba akace muku lfy har da baku magani ba"


Gyaɗa kaina nayi bayan na cije leɓan ƙasa saboda azaba, wani murɗawa da cikin nawa yayi sai kawai naji wani na fita daga jikina kamar fitsari


"anty fannah fitsari nake yi" nace mata

"fitsarin lfy tashi mu gani"


Ina miƙewa ta leƙa inda na zauna wani irin ƙara ta saki sannan ta kama hannun


"asmau zo muje a sibiti kar cikin nan ya zube" jikina ne ya fara rawa ina miƙewa jinin ya cigaba da zuba yana bin ƙafa ta



Har mun kama hanyar fita sai taga ina zubar da jini don haka dole ta raka ni toilet ɗin ta na gyara jikina sannan muka kama hanyar jikina sai rawa yake yi kardai ɓari nayi



Asibitin da suke zuwa ta kaini inda nan da nan aka shigar da ni labour room, ciki ya riga ya gama lalace wa, dƙn haka suka taimaka ya ƙarasa fita sannan suka dinga min tambayoyi akan yadda abin ya faru



Tsab nai musu bayani abinda ya faru anan nurse ɗin ta gane allurar abortion akai min, kuma cikin ya fita sam ba wani matsa, magani kawai aka bani sannan ta ce mu fita tunda dai komai is normal



Anty fannah ce ta bita office inda tai mata bayanin abinda ya faru da ni da kuma asarar cikin ya zube gabaɗaya bashi



Da kuka anty fannah ta fito daga office


"asmau dama sabit allurar zubar da cikin nan ya sa akai miki" ta faɗa tana kuka


Dakewa nayi don bana son taga weakness ɗina


"anty kaɗɗara tace kuma shima babyn Allah dama yayi ba me taka ƙasa bane, don haka babu komai Allah yana kallo kuma zai saka min" kuka ne yaci ƙarfi lallai yau na tabbatar da tsanar da sabit yake min ba kaɗan bace



Sai da muka gama kukan mu sannan muka kama hanyar gida bayan mun sai magani


********************


Sam sabit ya manta ma da wata sai asmau balle har ya tuna da cewar zata ɓari at any moment, hidimar sa kawai yake yi


A yunwace ya ƙarasa gidan yai mamakin da ya shiga ya kan dinning table ɗin ba komai, badia ya kira sannan ya tambayeta me ya faru yau abai girki bane ko mee


"wallahi ban sani ba ni tunda ta fita da yamma ban kuma ganin ta ba" gabansa ne ya faɗi kai dai ace ta san abinda yai mata kuma ta gudu kai ina zata gudu ai har yanzu batta da wannan wayon ƙila tana ɓangaren fannah


Miƙewa yayi ya kama hanyar burin shi yaga asmau acan in bai ganta ba yanzu tayaya za ayi ya fara rayuwa ba ita, ƴar iskar yarinyar duk da dai ba kalar sa bace amma kuma Allah ya bata wani baiwa da duk wanda ya fara sanin ta bazai iya rabuwa da ita



Gudu gudu sauri sauri a haka ya ƙarasa part ɗin fannah, itama a kulle yake bata nan, hankalin sane ya tashi, isma'il ya kira bayan ya ɗauka ne yake tambayar sa fannah


Inda isma'il yake cewa ta cemin suna asibiti ita da matar ka, wani ajiyar zuciya yayi wanda shi kansa bai san zai iya ba Allah ya taimake shi
[10/05 09:52] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




🤲🏻 *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN*🤲🏻




P⃗a⃗g⃗e⃗ 20 🌹




Basu suka dawo ba sai kusan 08 :00pm sannan muka dawo, directly part ɗin anty fannah muka wuce sallah kawai nayi sannan na kwanta sai bacci ya kwashe ni



Sabit yana ɓangaren sa amma ya kasa zaune ya kasa tsaye tunanin sa kar asmau ta faɗawa fannah yai mata allura gaban shi sai faɗuwa yake yi


Sai kusan 09 :00 sannan ya miƙe, badia da ke kusa da shi ta tambaye shi

"sabit ina zaka a daren nan"

"zanje in duba yarinyar nan ne dare yayi a maimakon ta zo ta kwanta" inji sabit


"to meye na damuwa da ita in ta gaji ai dole ne ta samu wurin kwanciya ko, amma ka wani tada hankalin ka sai kace wata matar ka"


Wani kallon banza ya bita da shi sannan ya fice, ɓangaren fannah ya dosa, yana shiga ya tarar da fannahr tana kallo


Sallama sukai shida badia suka shiga, kallo ɗaya fannah tai musu ta kau da kanta gabaɗaya ta dawo daga rakiyar sabit ɗin balle wannan ƴar iskar matar tasa



"fannah don Allah ina asmau take naga har yanzu bata dawo ta kwanta ba" bata kalli inda suke ba ɗakin da asmaun take kawai ta nuna masa da hannu


"amma ta riga tayi bacci don haka zaku iya tafiya da safe in ta tashi ta koma" tsayawa yayi yana kallon fannah kai gaskiya da sake bazai taɓa iya barin asmau ta kwana a wani wajen ba sai da ɗakin ta


"bari inje in taso ta" ya faɗa yana yin hanyar ɗakin, miƙewa ta bi ta sha gaban sa


"baka isa ka tashe ta ba ai matar ka ce indai har ka matsu ta koma ɗakin natan sai dai ka ɗauke ta in kuwa ba haka ba sai da safen"


Nannaɗe hannun rigar sa yayi yana shirin shiga ɗakin, sai badia ta tare shi

" *SD* kar kace min kana son shiga ka ɗauki yarinyar nan da kanka, ka barta mana da safen ta dawo da kanta"


Kallon ta be yi ba ya shige, masifa ta fara yi tana cewa wallahi indai har ka sake ka ɗauke ta wallahi zaka sani don ni kuwa ban yadda in yi sharing miji da wata ƴar aiki ba



Kinkimar asmau yayi yai mata ɗaukar jarirai sannan ya kama hanyar fita da badia a bayan sa tana ta balbala masa bala'i inda shi kuma ko ta kanta be bi ba



Anty fannah ta murmusa dama abinda take som sani kenan da sabit shin anya yana son asmau kuwa ko a a amma ita a ganinta yana son asmaun amma kuma me yasa yake mata haka



Kuma duk wani shawarar da yakamata ya bawa asmaun amma duk da haka sabit ɗin ya kasa sallamawa wannan abun da ɗaure kai yake


Sabit har cikin ɗakin ta ya kai ta badia na biye da shi,

"to tunda ka kawo ta sai ka ajiye ta muje ko" ta faɗa masa kamar wani ɗan yaro, abin nan yai masa ciwo yadda take nuna halin ko in kula da asmaun duk kuwa da yadda asmaun take kular mata da gida



Wani banxan kallo ya bita da shi wanda ya sata jan bakin ta tai shiru, yana son rungume asmau kafin ya fita amma kuma badia ta ƙi barin ɗakin


Haka ya haƙura ya fice bayan ya gyara mata kwanciyar ta sannan ya tafi ɗakin sa badia ce ta shigo tana wani rangwaɗa tsab ya fahinci me take so amma sai ya basar daga baya ma data ishe shi sai ya kore ta ya rufe ɗakin sa




Tinanin asmau ne kawai ya faɗo masa arai yana jin yarinyar sosai a ransa amma gaskiya bazai taɓa barin ta ta haifa masa ƴaƴa ba



Sai da ya tabbatar da badia tayi bacci sannan ya kama hanyar ɗakin asmaun tana ta baccin ta kamar yadda ya kwantar da ita


Kusa da ita ya kwanta sannan ya janyo ta jikin sa ya dinga shafa mata bayanta har bacci shima ya kwashe shi



********************


Na riga shi farkawa ganin yadda yake kwance yana ta sharar baccin sa ya sani zame jikina a hankali na shiga banɗaki tare da ɗauro alwala



Ina fitowa na tarar ashe har ya fice, sallah nayi sannan na kuma kwanciya don kuwa ji nake yi kamar bacci be ishe ni ba



Bacci ne ya kwashe ni, cikin baccin nawa naji muryar badia tana min magana


"sai yaushe zaki tashi ki haɗa mana breakfast gashi lkcn office zai ƙule" miƙe wa nayi sannan ta kalle


"matsayin mu ɗaya a wajen sabit kamar yadda kike tunƙahon mijinki yake haka yake tinƙaho da ni a matsayin matar sa don haka kowacce tata ta fish she ta daga yau na daina bauta wa ko wa kowane ɗan iskan yayi aikin sa an gama wannan wasan"


Sakin baki tayi tana kallo na lallai ma yarinyar nam,
Sabit ta ƙwala wa kira wai yazo ya yi magana


Shigowa yayi shima kamar gaske bayan ya haɗe girar sama data ƙasa


"me yake faruwa ne a ana anga ana ta ƙwala min kira"


" *SD* yarinyar nan taƙi tashi tai mana breakfast nai mata magana tana gayamin maganar banza"

Juyowa yayi ya kalle ni wacce ni kuma idon yake ƙyam akan sa inga irin matakin da zai ɗauka


"ke sai yaushe zaki ki haɗa mana breakfast ne"


"bani da lfy ko kana don ingaya maka abinda yake damuna ne" shiru yayi sannan sai ya juya ga badia sannan yace mata



" Muje mu ƙyale ta tunda tace bata jin daɗi inta warke ta koma duty" ya faɗa yana tura ta don su fita


" a a ku dawo in faɗa muku abinda ke damuna mana ya kuka fita ai kamata yayi kiji ki san me ya same ni" na bita da wannan ina ganin ta juyo shi kuma ya hankaɗa ta tare da riƙe mata hannu yana janta


Ai na dawo daga rakiyar sabit zai sqn ya zubar min da ciki wallahi sai ya gwammaci kiɗa da karatu, wallahi sai ya san asmau ya taɓa bari dai in fita mu haɗu da anty fannah nasan zata bani shawara


Guduwar ma dana ce zan yi na fasa wallahi sai na zauna a gidan nan na haifawa sabit baƙaƙen ƴaƴa sannan hankali zai kwanta in ban haifa masa baƙaƙe ba ban rama wulaƙancin da yai min ba



Wallahi sai ya gane bashi da wayo da asmau yake to nima yanzu lkcn da juya kaina yayi na daina ɗaukar order daga wajen wani nima daga yanzu na zama ogar kaina



********************


Sai da na tabbatar sun fita sannan na tafi ɓangaren anty fannah, tana zaune ta zuba uban tagumi kamar an aiko mata da mala'ikan mutuwa, na shiga da fara'a ta


Tana kallona tace

"lallai yaro be san ciwon kansa ba wai har kin wats tsake kin koma duty"


"wane duty ba abinda nai musu ai yanzu ciwon ido zan zame musu a gidan nan kuma wallahi sabit abinda baya so shine baƙaƙen ƴaƴa ko wallahi anty fannah sai na haifa masa sai na cika wa sabit gida da baƙaƙen ƴaƴan daya baya so" tsayawa tayi tana kallo na


"asmau da niyyata in saka daddy ya ƙwatar miki ƴancin ki, yasa sabit ya sallame ki ke ma kije ki ne mi wanda yake sonki kk aura"


"haba anty fannah ai da kin cuce ni, sabit shi nake son ya kasan uban baƙaƙen ƴaƴana, ko yana so ko baya so wallahi sai na nuna masa shi ƙaramin ƙwaro ne a wajena, abinda ba abinda ban sani ba nashi, wallahi anty fannah cikin sakan ƙalilan zan iga juya sabit, kawai dai yana da taurin kai da tsatstsauran ra'ayi, amma wallahi na ɗau ɗamarar sai na nuna masa banbanci aya da tsakuwa, sai na nuna masa cewar wasu matan ma suna suka tara, wani ƙyalƙyal banza na mace ba lallai ta zama me quality ba"


Tsayawa kawai tayi tana kallona na bata mamaki sosai, yama za a yi in tafi in ƙyale sabit a haka ai ya ci galaba ta wannan yaƙi ne ya soma wallahi sai naga ƙarshen yaƙin nan sai na haifa wa sabit ƴaƴa baƙaƙe mu ga yadda zeyi kuma wallahi ni da sabit ya raina sai na zame masa ciwon ido


"anty fannah kayan gyara nake so" har yanzu bata daina mamaki na ba don haka sai ta jawo ni ta zaunar dani tare da cewa


"asmau ko dai ɓarin nam ne ya juyar miki da ƙwaƙwalwa, naga duk kin rikice kin zama wata ba asmaun da na sani ba"


"wallahi anty fannah nice hankali kawai nayi, kuma nasan ciwon kaina wanda yayi sanadiyyar rasa baby na innace na barshi haka ai banyi ba wallahi sai na ƙun sa masa abinda har abada bazai taɓa mantawa ba amma sai da taimakon ki sai na haifa masa baƙaƙen ƴaƴa iya son raina, goma ma zan haifa masa ko sha biyar"



Tabbas asmau ta zauce inji fannah, zaman dirshen nayi a gaban ta ina ta lissafo mata irin plan ɗin dana ɗauka zan aiwatar akan sabit da matar sa wallahi sai sun san shayi ruwa ne


Tun tana basarwa har tazo ta fara bani tips na mallakar miji a hannun na ada in tana faɗa min yana shiga ne ta kunnen hagu yana fita ta kunnen dama


Amma yanzu tsab nake haddace wa ai yanzu za a fara wasan ada ba komai akayi ba, amma yanzu wasan zai fara


Sai yamma na kama hanyar part ɗin mu abinci na naje na dafa lafiyayye na zuba a cooler na ajiye, na shiga ɗaki na ɗau wanka na sai da na turare jikina da turare na daƙƙo wata fitted gown da mukai da anty fannah na saka



Falo na fito ashe ita uwar gidan ta dawo ma abanji dawowar ta ba, cooler dana ajiye akan dinning table ta buɗe ɗan wake ta ci karo da shi da mai da yaji sai kunun tsamiya


Wani shegen kallo ta bini da shi

"bana cin wannan ki sake ɗaura min wani"

"ai ba naki bane nawa ne, ai na dena yi wa kowa girki duk wanda ya ji yunwa ya shiga kitchen muga in zai iya"


Hannu ta ɗaga zata kwaɗa min mari a dai dai lkcn sabit ya shigo


"ke badia me ya haɗa ku zaki mare ta"


" *SD* wannan yarinyar wai me take taƙama da shi ne, gaskiya na fara gajiya da zama da ita ya kamata a sallame ta"


Juyowa yayi zai min faɗan da yasa wani ƙayataccen murmushi na sakar masa tare da kaɗa masa ido cikin kissa



Tuni ya maida wuƙar tasan sannan yai gyaran murya


"me tayi miki ne da zaki dake ta, bana son hayaniya"


"ni dai kawai na gaji da ganinta" in da inda ya fara ya rasa kalma ɗaya ma da zai ce sai wani kame kame yake



Dining na nufa n zauna na fara cin abinci na ina jinta tama jarabar wai ban kai wannan matsayin ba tana ƙara yi wa sabit maganar ya kore ni ko ita ta barmana gidan


Lallaɓa ta yayi ya hau sama inda ni kuma na zauna ina ta cin abincina, nai mamakin da ya gama kintsawa ya sauko ya ci ɗanwaken


Ita kuma badia tana nan kan bakan ta bazata ci ɗan wake ba sai dai in dafa mata wani abun, iskar da ta ɗauko ta ma ban kalla ba balle ita sabit ɗin ma nai mamaki dana ga sam be ce komai ba
[10/05 09:52] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




🤲🏻 *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN*🤲🏻




P⃗a⃗g⃗e⃗ 21🌹







Tun daga lkcn na zame musu ciwon ido sai haƙuri sai abinda na ga dama nake yi a falon sam sabit sai yayi wani sanyi ashe abun nashi ma iskanci ne



Tuni na ajiye girkin sai abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login