Showing 63001 words to 66000 words out of 88726 words
Chapter 22 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt
 kuma shawarar da mummy ta yanke
"hakan shine dai dai, sabit yace baya son cikin don haka Allah ne kaɗai yaan abinda zai yi don ganin ya salwantar da cikin, ki koma can kema hankalin ki zai fi kwanciya, ko kin fi son zama kusa da mijinki ne" 
 "hmmmm wayaga miji indeed"
  Mun daɗe muna hiɗa da ita daga ƙarshe ma itace ta ma ta raka ni na haɗe kayana muka kama hanyar part ɗin mummy duk wannan abun da ake sabit ɗin be ma san anayi ba 
   Ɗaki guda mummy ta bani, amma sam ban ji daɗin yanayin fuskar ta dana gani ba, ran ta a ɓace sai na ɗauka ko don dawowa ta ne part ɗin nata har na fara tunanin gwanda in sabit ya tattara ya tafi in koma wurin mu 
  Sai kusan 12 :00 na rana sannan sabit ya shigo da sallamar sa ina ɗakin da aka bani ina kwance ina jin shi yana ƙwala wa mummy kira 
"kinga yarinyar nan ta tattara kayanta ta gudu ko naje wurin fannah bata nan, yanzu ina zan ganta" 
 "ni nace ta dawo wajena don wallahi baka isa da shegen ra'ayin nan naka ba ka kuma ɓarar min da jika ba, kai ba a haihuwa aka haife ka, saboda tsabar ka raina wa asmaun wayo ma zaka ce wani ta zubar wallahi tallahi wani abu ya sake ya samu cikin nan sai dai ka nemi wata uwar ba ni ba ni, na fara gajiya da halin ka da kuma shegen iyayin ka" 
  "mummy ƙara ta ta kawo ni fa ba cewa nayi baza ta ƙara haihuwa ba ce mata nayi ra bari a kuma yi mata wani dashen kamar na farko, in yaso wannan sai t riƙe, kinga an mata a dalci kenan" 
" ba za a kuma dasa mata ƙwan ko wacce ƴar iskar ba, wallahi don ma ka samu asmaun tana da sauƙin kai ne wallahi da ƴata ce da sai ka gane kuren ka duk da haka wallahi sai na ƙwatar mata ƴancin ta daga gare ka, me kake gudu ba kar matar ka ka gano ka ba sallamamme wai matar sa yake tsoro wallahi kaji kunya ka faɗi ƙasa ba nauyi tiƙ haka ka faɗi" 
   Shiru yayi sam be ɗauka mummyn zata masa haka ba don haka sai ya kwantar da hankalin sa
"haba mummy na ɗan autan ki ne faa, wallahi da an zubar tana watstsakewa za ai mata sabon dashen wannan karon sai ta riƙe"  lallai ma sabit ɗin nan ya wuce duk inda mummy take tunani 
 "jinin asmau me yayi da baza a haihun da ita ba" 
"mummy asmau in ta tashi baƙi zata haifa" 
"to shikenan zan yadda a zubar mata da cikin in ka yadda da sharaɗi na ƙwaya ɗaya"
  Gyara zama yayi ya san halim mummyn sa ai da ya karyar mata da kai zata amince da shi da bishi da yadda so
"idan an zubar da cikin zan je a saka sperm ɗin bature ko balarabe kaga sai ta haifa maka farare tas yadda kake sooo" 
  Zimbir ya miƙe 
"mummy ban gane ba, ya za ayi a sakawa matata sperm ɗin wani kuma ace ɗana ne, wallahi ban yadda ai ba abinda ya haɗa ni da shi"  masifa yai tayi ina ɗaki ina cin dariya ni kaɗai 
"to menene ba de kai kace baza ka yadda ka haihu da ita directly ba ai dashe dashe ne, in har zata yadda a dasa mata ƙwan wata ta ƙyanƙyashe ai kaima baza ka damu ai mata dashen da sperm ɗin wani ba kooo"
  Takaice ne ya ishi sabit yai ta faɗa wai asmaun ce ta jawo shi wallahi ba yanzu yaso ayi wa annur ƙani ba, shi meye da meye 
"yo in anyi wa annur ɗin ƙani kai ne zakai renon ko menene"
  "wallahi mummy in yarinyar nan bata yadda anyi abinda nake sƙ ba wallahi zan tsame hannuna daga lamarinta, kuma wallahi ta sake ta haifa min baƙaƙen ƴaƴa bani ba su" 
 "kar ka samu damuwa kana fita lamarin ta sai in saka daddyn ku ya saka ka ka sallame ta ai ba dole bane ita ma taje ta samu wanda zai yi alfahari da baƙaƙen ƴaƴan natan ba kai me man ta kyauta ba" 
 "mummy kuma me ya kawƙ zancen saki anan"
"kai ka isa ka zauna da yarinya kana muzguna nata ina kallon ka ai an wuce wajen sabit ya ga alamar in ba farkar da kai nayi abin naka sai ya fi haka"
  Ya gama bambamin sa yai waje, yana fita mummy ta shigo 
"kinji yadda mukai da mijin nakin ko, ai kema asmau da naki don kawai yana ganin kina masa sanya ne shi yasa"
  Shiru nayi lallai wannan cikin ya ja mi ƙima a wajen mummy, shawarwa ri ta dinga bani akan yadda zan ƙwatar wa kaina ƴanci in bar zaman da nake yi a wajen sabit 
 Naji daɗin su sosai saɓanin anty fannah ita tana da sanyi bata taɓa cewa yi mai kaza ba ko tace idan yayi kaza in rama amma mummy ƙiri ƙiri ta dinga zayyano min yadda za ƙwatar wa kaina ƴanci kuma kar in sake ko da was in yadda in kuma bashi wani haɗin har sai ya gane kuren sa 
    Tunda yayi fishi ya fice be kuma shigowa, nima naji daɗin hakan dom kuwa sam bana son abinda zai haɗa ni da shi 
   Da yamma sai ga shi da annur, wai yaje gidan su badia ya tarar da yaron yana kuka, mummy ya kawo wa shi wai ta riƙe 
 "kai dai wallahi kaji kunya zanga randa zaka tattara kan iyalen ka ku zauna waje ɗaya lfy ba tare da matsala ba"  
"mummy ni ba komai nake ba kawai ki kular min da shi, ina wannan me hijirar take ne" ya faɗa 
 "oho maka kafin a tambayi me hijira sai an fara tambayar me shirin zubar da cikin matars mara kunya" ta bashi ansa kasancewar ya san dashi take yasa shi be amsa ba sai ya taho directly ɗakin da nake 
   Lallashi na ya dinga yi akan in yadda a zubar da cikin wallahi ana zubar wa zai sa badia ta bada ƙwan natan in yaso idan na haihu sai in riƙe 
    Kallon shi kawai ina ƙarawa 
"asmau bana son kizo ki haifa baƙi in dinga nuna masa bambamci tsakanin abinda kika haifa da annur shi yasa don a aguje wa hakan ya sani son ɗaukar mataki da gayya" 
  Shiru nai masa ya gama soki burutsun sa yai waje daya ga banni da niyyar tanka masa 
 Da daddare sai gashi da fura da nono na kanti me shegen sanyi, har ɗakin da nake ya shigo ya kawo min kamar gaske 
  Ina kwance yace min in tashi inci insha, kallon inda yake banyi ba
"asmau ki tashi ki sha furar nan don ke na siyo ta" 
"bana sha" na bashi amsa, tabbas furar ta shiga raina amma sam bana son bashi fuskar da zai kawo min rainin hankali 
  Faɗa ya hau ni da shi wai yaje ya siyo kuma na baɗa masa ƙasa a ido, yadda naga hankalin sa ya tashi ya nace lallai sai na sha ya na sakawa furar alamar tambaya 
 "sabit ko dai maganin zubar ciki ka saka a cikin furar da ka dage sai na sha" 
  Masifa ya fara ya na rashin mutumcin sa, miƙewa nayi nima na fara balbala masa masifa, 
 "wallahi duk abinka sai na haife abinda ke ciki na"
"to wallahi ki haife zaki ga rashin mutunci tsirarrarsa" 
  Faɗa mukai da shi sosai da sosai faɗan da bamu taɓa yi ba don tun da yake min abu ban taɓa tankawa ba sai yanzu 
  Wai da yake bashi da kunya bayan mun gama faɗan kuma sai yazo wai yana cewa ni fa ayau anan zan kwana, fita nayi naje na faɗawa mummy inda ta zo da kanta ta kore shi 
  Babu irin magiyar da baiyi wa mummy ba akan ta bar shi amma ta ƙeƙashe ƙasa ta hankaɗa ƙeyar sa yayi waje muka kulle 
  Kashegari ya tasa ƙeyar matar sa suka koma ko sallama basuyi mana ba nima sai ya tafi sannan hankali na ya kwanta
[10/05 09:52] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
        *A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*
                    
              🍷🍽🥛
  👩🏽🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽🍳
  🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠
 
       
ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
*HIKIMA WRITERS ASSO.*
   P⃗a⃗g⃗e⃗ 25 🌹
 Da masifar su suka shigo 
"wallahi sai an fito mana da ɗan mu" yayar badia ce hauwa a gaba tana masifa tana ƙarawa 
  A zaune suka ga mummy da sabit sun zuba uban tagumi suna sharɓe kuka 
 "badia wallahi baki sa ar miji ba, ace namiji da kuka ke kuma kiyi me" wannan maganar ta ƙonawa mummy rai sai ta tanka 
 Aikuwa nan da nan aka hau zage zage, mmn badia ce me cewa 
"wallahi sai mun kai yarinyar nan kotu sai alƙali yai mata munmunan hukunci, wallahi sai tayi zaman gidan yari, ku ma baku tsira ba wallahi sai an ƙwatar wa badia ƴancin ta a gidan nan kun mai da ita baiwar ku" 
   Faɗa sosai shi dai sabit yana zaune ya kasa taɓuka komai yana jin yadda ƴan uwan badiar suke ci masa mutumci duk da dai yana ganin laifin su amma asmau ta fi kowa ƙona masa rai 
  Cikin hukuncin Allah sai ga muktar wan sabit shi ya shigo yai musu jan wuya sannan suka haƙura suka tafi akan su jira kiranye daga court 
"kuma wallahi idan court ta karɓar mana ɗan wallahi ya bar gidan nan ke nan har abada tunda dai baku iya kula da shi ba har kukai sake wata yar aiki ta sace shi wallahi annur ya bar hannun ku har abada" 
 Injimn badia ta faɗa tana yin waje
  Sabit kara fashe wa yayi da kuka 
"don Allah mummy ina zanga asmau wallahi yanzu bazan mata komai ba don Allah ta dawo min da ɗana wallahi na yafe mata wallahi na daina yi mata duk abinda nake mata, wallahi ina son annur sosai wallahi bazan iya rabuwa da shi ba"
  "kai sabit wane irin mutum ne kai kamar ba namiji ba ka zauna sai kuka kake tayi, ita kuma mummyn tace me" inji muktar 
 "don Allah muktar kar ka bari a ƙwace min annur wallahi ina son ɗana" ya faɗa yana me riƙe ƙafar muktar ɗin 
 "wai mummy me yasa yarinyar nan ta ɗauke annur ɗin ne, ko faɗa suka yi, in banda abinta ai ko faɗa kuka yi ba kya ɗauki ɗan da ba naki ba" muktar ya tambaya
  Sam mummy sai ta kasa cewa komai don bata ma san ta ina zata fara ba, sabit ma shiru yayi 
******************
 Fannah tana ɗakin ta suna waya da asmaun tana faɗa mata yadda gidan ya rikice, sam ko a jikin ta asmau bata ji komai ba, ita burin ta ma Allah ya sauke ta lfy wallahi ƙarawa gaba zatayi da ƴaƴan ta taje ta nemi dangin uwarta 
 Saboda tasan ko baɗe ko ba jima anty fannah zata iya tona mata asirin inda take 
   Sai da ta kuma jawa fannah kunne akan kar ta sake ta faɗi inda take sannan sukai sallama 
  Tun ana ɓoyewa daddy har yazo magana taje wajen sa, ranar mummy ta sha faɗa sosai kamar ba gobe daddyn yai mata yai wa sabit wanda a yanzu yake kwance saboda zazzaɓi da ya rufe shi 
  Takanas daddy ya saka mutane suka kama hanyar garin su asmai don ganin ko ta je amma ba same ta ba 
  Tas ya tara mutan gidan akan su faɗi ko akwai wanda yasan inda asmau take, amma duk ba wanda yasan inda take 
"har ke fannah don naji ance kullum kuna tare" jikinta ne ya fara rawa don ita fannah Allah yayi ta surutu amma sam bata da zafi sanyi gareta da kuma sanyin hali 
 Amma da ta tuno irin cin kashin da sabit ɗin ya ɗinga yi wa asmaun sai ta dake tace 
"nima ban sani ba" 
"to duk lkcn da ta kira ki ki ce mata ta neme ni koma menene wallahi sai na ƙwatar wa yarinyar nan ƴancin ta tunda dai na lura kamar zaman haƙuri take yi da ku, in ba haka ba tayaya za ayi ace ta ɗauki ɗan da ba nata ba ta gudu an rasa ta ko sama ko ƙasa"
 Ya juyo ga mummy 
"anya fatima ke uwa ce kuwa tayaya za ayi ace wai a gidan ɗan ki ana samun matsala amma sam baki sani ba, wane irin abu ne wannan, kince ke ƴaƴan ki baza suyi nesa da ke ba amma kuma sam ba kya kwaɓar su 
  To wallahi ku sani duk wanda na same shi da laifi a guduwar yarinyar nan sai nayi mugun saɓa masa, kuma ku shirya jibi monday zamu fara shiga court don iyayen badia sun kai ƙara an aiko mana da sammaci sai ku shirya" 
  Sabit da ke zaune kamar mutum mutumi sai ya ƙara narke wa ɗan zazzaɓin da ke jikin sa nan da nan ya kuma hauhawa, shi sam be ma san ya zai yi ba 
  Miƙewa yayi don ya tashi dole duk yadda za ayi ayau sai ya nemo inda asmau take don kuwa wallahi bazai yiwu ace ya yi rashin ɗan sa ba 
 Don kuwa ya san indai suka shiga court ɗin nan da badia sannan suka ci case ɗin dole ne ace ya bata ɗan in kuwa ya bata shi ya zaiyi da rayuwarsa
 Miƙewar nan da zai yi sai jiri ya kwashe shi ya faɗi ƙasa a sume, a guje akayi kansa inda mummy kuma ta fashe da kuka 
  Ruwa aka kawo aka yayyafa masa nan da nan ya farfaɗo jikin sa kamar garwashi saboda zafi 
 Yana farfaɗowa kuka ya saki ya riƙe hannun mahaifin sa 
"daddy don Allah kar ka bari su raba ni da ɗana, ƙila shi kaɗai ne ɗan da zan so a duniyar nan don Allah daddy a nemo min asmau ta bani ɗana a maidawa badia ɗan ta saboda ta barshi a gidan nan" 
   Ko wa a wurin sai da hankalin sa ya tashi, isma'il ne ran shi ya ɓaci ya fara magana 
"wallahi yarinyar nan idan na sake na ganta Allah ko su badia basu kai ta kotu ba ni sai na sa an hora ta wane irin abune wannan"
  Lefi suka dinga ɗaurawa asmaun bayan sam basu san gaskiya suna ta ƙoƙarin cusa wa daddy magana saboda ya ji haushin yarinyar, da fannah ta ga haka sai kawai tace 
 "nasan inda asmau take" 
  Gabaɗaya kowa ya waigo gareta har da daddyn 
"tana ina, suka haɗa baki" 
  Nan da nan fannah ta kwashe inda asmau take ta faɗa musu amma sam bata faɗi dalilin zuwan asmau gidan ba
  Sabit shine a gaba ya fice domin tafiya, daddy ne ya tsai da shi 
 "kai baka da lfy yi zaman ka nida isma'il da ita fannah zamu je mu dawo da ita" inji daddy 
 "ka kira badia a waya su zo nan za a kashe maganar kafin aje court a kashe maganar a gida" 
  Amsawa sabit yayi ya ɗauko wayar sa yana neman number badia wacce tunda abin ya faru ta koma gidan su 
  Bayan ya samu badia ya faɗa mata ne ya zauna  amma ba don ransa ba ya so ace yaje wallahi da sai asmau ta gane bata da wayo 
 
Ina kwance sai jin muryar anty fannah nayi a kaina 
"ki fito da daddy muke"
  Rasa abinda zanyi nayi na ɗauka na ja mata kunne ashe sam bata ji 
"asmau ki tashi mana na ce miki da daddy muke" 
Miƙewa nayi jiki na a sanyaye, na fito na same shi yana zaune a falon gidan da isma'il da kuma wan anty fannah 
  Ina fitowa na gaishe su, daddy da fara'ar sa yace min 
"me yaji munzo mai da ke ɗakinki maza ɗauko kayanki mu tafi" 
  Bazan iya masa musu ba na shiga ɗakin, anty fannah ce ta ɗauko min annur inda ni kuma na kwaso kayana muka fito 
  A mota ba wanda yace min komai sai ma ɗana dana karɓa daga hannun anty fannah na rungume shi duk da ƙaton cikin da ke jikina
 Da sallama muka shiga babban falon gidan wanda yake cike da mutanen gidan harda mutan gidan su badia 
  Tana ganina ta yo kaina da zagi wai in bata ɗan ta 
  Daddy ne ya dakatar da ita inda yace duk a zauna a tattauna me yasa na ɗauke annur ɗin 
 Sai dana zauna sannan daddy ya buƙaci ai masa bayanin abin da ke faruwa, sabit ne ya wangale baki yai masa bayanin, yadda aka samu annur 
  Ba daddy ba hatta ƴan uwan sabit sai da suka jinjina maganar nan, daddy kuwa faɗa ya dinga yi yana ƙarawa sai da yai wa sabit wanki babban bargo sannan daga baya yace 
"sabit wai duk bokon ne ya saka haka ko menene, dashe ka sa akayi wa matar ka saboda ɗayar matar taka ta cire mahaifar ta" 
    Rufe ido daddy yayi ya zage tas shi da badia bayan ya gama sannan kuma ya ɗaura da nasiha akan abinda muka aikata gabaɗayan mu haramun ne 
 









