Showing 75001 words to 78000 words out of 88726 words

Chapter 26 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt

tashi ya za a yi ace ba gan shi ba kuma ba wanda ya damu,


"mummy yanzu baza a duba a sani ko lafiyar shi ƙalau ba" na tambaya


"wannan daddyn ku ne kawai zai iya kuma nasan inna faɗa masa bazai yi ba saboda har yanzu haushin sabit ɗin yake ji akan abinda ya miki"


Kuka na saka mata nidai mummy don Allah ki sa a nemo shi, shekaran jiya ya fita ba a san inda yake ba amma ba wanda ya neme shi yanzu in wani abun ya same shi fa me zance wa ƴaƴana, wallahi duk lalacewar sabit na fi son ganin shi kusa da mu saboda ƴaƴana mummy dƙn Allah ki taimaka kiyi wa daddy magana"


Shiru tayi daga dukkan alamu bata son yin kuka ne yasa ta ƙin yin maganar, wayata ta ɗauko tayi dialing number daddy sai da ta fara ringing sannan ta bani



ringing ɗaya ya ɗauka tare da sallamar sa daga gani bashi da number ta

"daddy asmau ce"

"asmau kina nan lfy ko, ko akwai abinda kuke so ne"


Kuka na saka masa sannan nace

"daddy ba aga sabit ba don Allah ka sa a nemo shi don Allah daddy"


Shiru yayi kamar be ji ba sai da na sake bashi haƙuri na ɗauka ko be haƙura ba ne sannan yace


"asmau lallai ke ƴar halak ce kuma wallahi baza ki taɓa taɓewa ba, ki kwantar da hankalin ki mijinki nanan ƙalau yana lagos ne, wajen aikin sa can ya koma amma in shaa Allah zan koro miki shi"


Kunyar sa naji nai murmushi sannan nace

"ni fa daddy ba ni nake son ganin sa ba, kawai dai ya zƙ yaga babies ɗin ne"


"ato abu ne sauƙi kawai zan sa a aika masa hotunan su kinga shike nan ya huta da zuwa kooo"


"a a daddy don Allah ya dai zo" dariya yayi irin tasu ta manya sannan yace


"shike nan in shaa Allah zan sa a gaya masa"


Mukai sallama sannan na sanar wa da mummy abinda ya faru, ta nuna jin daɗin ta sosai itama tai ta sa min albarka kamar ba gobe



********************



Sabit yana kwance a kan kujerar gidan sa na lagos duk abin duniya ya gama isar sa, sam ya rasa farkn ciki, yana matuƙar kewar asmau daba dan daddy ya kafa masa doka akan zuwa wajen ta ba da tuni ya san yadda zai yi ya taho da ita lagos


Tabbas asmau tana da taurin kai amma kuma zuciyar ta tana da sanyi, shiyasa duk abinda yake mata yasan bata riƙo



Gashi yanzu wallahk yadda yake kewar to ko kaɗan baya kewar badia, wacce sam baya ma son ganin ta, burin shi kawai asmaun sa wacce yanzu aka kafa masa takunkumin ganin ta


Knocking yaji ana yi, agogon bangon parlour ya kalla 11 :20na dare, waye wannan da daren nan yake min knocking



Kamar bazai buɗe ba sai kuma ya tashi yaje bakin ƙofa yayi shahada ya buɗe


Wani yaron daddyn sa bola inda ya faɗa masa wai daddyn yace ya kunna wayar sa matar sa ta haihu


Ai ko sallamar yaron ma baiyi ba ya tafi ciki a guje shi sai a lkcn ma ya tuna da batun wayar sa tun da ya kashe ta lkcn da ya baro abuje



Watsappa ya shiga don yasan ta nan zai ga pics ɗin babyn, aikuwa messages ne sukai ta shigowa kamar ruwan sama


Message ɗin ƴan uwan sa kawai ya shiga dubawa, nan ya ci karo da wasu jarirai kyawawa an turo masa


Duk da dai yaran ba farare bane amma kuma sun masa kyau sosai ashe shima baƙi yana da nashi kyan


Duk da dai ƴaƴan shi baƙaƙe ne amma ya ga kyan ababan sa sosai kamar ba nasa ba, kamar su ɗaya da annur


Miƙewa yayi ya fara haɗa kayan sa dalilin ganin asmau ya kama shi yanzu inyaje gidan ba wanda zaice masa don me


In shaa Allah sai ya samu ya shawo kan asmau kafin a ƙara yi masa get da it don ba ƙaramin wahaltuwa yayi da rashin ta ba barin ma waɗannan ƴan kyawawan ƴaƴan nashin da ta kawo masa duniya


Sai yanzu yai dana sanin zubar mata da ciki da yayi, inda yasan cewar idan asmau ta haifo masa ƴaƴan sa ko da zasu kasance baƙaƙe amma za suyi kyau ai da tun farko be dinga wannan abin da yake ba


A gaskiya ya cuci asmau a rayuwa, sam shi sai yanzu yake jin kunyar kansa ma, yarinyar nan ba abinda tai masa kawai ya kafa mata ƙahon zuƙa



Hawayene su ka sauko daga idon sa da ya tuna irin abubuwan da dinga yi mata, lallai yayi nadama kuma yana fatan ita ma ta yafe masa



Da asuba ya kama hanyar abuja a jirgi inda yayi sa'ar samun flight na ƙarfe 06 :00 na safe, suna sauka diretly gidan da asmaun take ya wuce


Gidan da yake ganin sa kamar na wani shugaban ƙasa saboda tsabar takunkumi da daddy ya saka masa



*******************


Ina kwance ina bacci kawai naji mutum ya kwanta kusa da ni ko ban kalle shi ba nasan sabit ne don nasan duk duniyar nan babu wanda ya isa ya rungume ni sai shi


Da sauri na miƙe tare da haɗe raina

"lfy" na faɗa raina a ɓace, ai na waye yanzu ya za a yi in barshi ya same ni a banza bayan sam be san daraja ta ba


"my asmy godiya zan miki akan wannan kyauta da kika kawo min duniya Allah ne kaɗai zai biyaki"


Baki na taɓe sannan nace

"baka ganin baƙaƙe ne"

"au haba ban lura ba ni kawai kyan ƴaƴana nake gani"


"au ƴaƴan ka ma, ƴaƴan da ka so in zubar su sune yanzu kake kira da naka"


"wai har yanzu ba a yafe min bane"


"sabit ai tuban dole kayi tuban muzuru da kaga na dawo gareka shi ke nan sai a koma gidan jiya"


"ke kuma baza ki min fatan shiryuwa ba"


"wannan kai ta shafa ko da kai ko babu kai zan iya rayuwata"


Duk yadda ya so ya ga na sakar masa jikina sam yaga hakan be samu ba, da ƙwarin gwiwar sa ya shigo ɗakin amma ganin yadda na dage ban yadda da tuban sa ba ya sa jikin sa yin sanyi




Ƙarasawa yayi ya ɗauki ɗaya wacce itace ƙaramar addua ya hau yi mata ina ganin shi yana ƴar ƙwallar sa ko me ya tuno oho


Ganin zai karya min zuciya ya sani miƙewa na fice na bar masa ɗakin parlour na koma na zauna kusa da mummy


Sam bata tanka min ba, ya daɗe sosai sai gashi ya fito

"mummy ni zan wuce gida in ɗan huta, akwai abinda kuke buƙata ne"


Lallai ma sabit ɗin nan dama ba dan mu kazo ba don kazo kaga badia kazo kenan har da wani zaije gida kenan nan daji ne


Harara mummy ta bishi da shi inda ni kuma na miƙe na bar wajen, sam be fahimci manufar mu ba ya ɗauka daga mummyn har ni fushin muke da shi


Sim sim sim yasa kai ya fice shi sam ya ma rasa tudun dafawa wannan shine abinda ake cema rana zafi inuwa ƙuna




Ko da ya koma gidan nan har gidan asmau yafi ni'ima don badia tana ganin sa ta hau shi da zagi da cin mutunci, sam be kula ta ba


Ɗakin sa kawai ya wuce yana shiga ya rufe ƙofar da key kamar ya sani yana juyawa zai shiga toilet yaji bugu kamar za a ɓalla ƙofar


Share ta yayi ya shiga toilet, hmmm lallai badia har yanzu batai hankali ba wai ita har yanzu burin ta sai ya bada sperm ɗin sa sun ka nemo wacce za a sake mata dashen ta haihu ita lallai sai taga ƙwanta a duniya ta nuna wa asmau


Ƙin yadda dan da baiyi ba ne yasa kwanaki sukai fada ta bishi har waje tana ci masa mutuncin sa


In banda ma daddy wallahi da tuni badia ta manta da rayuwa da wani sabit don wallahi in ya tashi katse auren da ke tsakanin su ko duka ba tare ya rage ko igiya ɗaya ba don ya




: "wallahi sabit ka buɗe ƙofar nan ka ɗura min sperm ɗin ka a robar nan in kai asibiti a ɗura wa wacce za tai mana ɗaukar cikin, don baka isa ba kace wai bazan ga ƙwai na a duniya ba, wallahi ba za ta saɓu ba"


Surutai tai tayi wanda suka saka sabit ɗin yin nadama sosai gaskiya ada ya bi son zuciyar sa sosai na cewae shi bazai auri baƙar mace ba balle ya haifi baƙin ɗa amma yanzu in shaa Allah ko ƴaƴa zai dinga haifa kamar baƙaƙen tukunya zai so kayan sa kuma ya basu tarbiyya


Balle baƙin asmau ba me muni bane irin wanda yake da tsadan nan ne wanda bature yake cewa chocolate


Barin ma yanzu da haihu ɗin nan tai wani fresh da ita duk sai ya jishi ya matsu ya jishi a jikin ta tana sarrafa shi kamar yadda take masa idan suna shiri



Wani irin yarrrr yaji a jikin sa lallai akace wani kaya sai amale, asmau tayi wa badia nisa nesa sosai wanda duk abinda badiar zata yi ba lalle ne ta kamo ƙafar asmaun ba



Kai lallai wallahi dole ne ma in dawo da matata wallahi duk abinda za a yi sai na dawo da matata


Yana fitowa daga toilet ya tsiri haɗa kayansa shima gidan zai koma da zama duk yadda za ayi da shi wallahi sai dai ayi amma sam bazai iya rayuwa babu asmau ba



********************



Ina zaune a ɗakina takaici ya ishe ni wai sai yaushe sabit zai fahimci shi wani jigo ne a rayuwa ta da bazan iya cigaba da ita ba face da shi a kusa dani kusan kullum banni da buri daya wuce inga na mallaki mijina a hannuna yai treating ɗina kamar yadda ake wa kowacce mace amma ni sam har yanzu ba samu ba


Ina cikin tunani na naji muryar mummy tana magana


" lfy kai kuma meye haka sai kace me shirin hijara"


"ai mummy duk inda asmau take da yarana ni ma ina nan, zuwa nayi gida ai na kwaso kayana ni ma ayi jegon dani"


Murmushi nayi amma kuma sai na haɗe raina don kar ya shigo ya ganni ya raina ni


Na ɗauka zai shigo ɗakin ko ince naso ya shigo ɗakin amma har na gaji da gyaran fuskar da zan sauke shi da ita na saki fuskata ba shi babu dalilin sa





Sam be shigo ɗakin ba ina jin shi a parlour yata ta zuba cikin mata, kuna duk wacce ta zo sai ya shigo ɗakin ya ɗauke su don kai wa yan barka


Kuma shigowa goma fita goma sak ya min magana, ƙala bana ce masa amma baya gajiya


Haka aka dinga yi da shi ina jin anty fannah tana mai tsiya


"ni na taɓa ganin jego har da namiji"

"kin san ai autar mata ce ta haihu duk abinda take dole ne ai mata, ko da dai bazata yaba ba"



Murmushi kawai nake yi ina cikin ɗaki na


Har azore garin mu mummy ta aika da mota akan idan da masu zuwa suna



ƴan garin mu da yake ba hankali haka suka ciko motar wata akan wata ƴaƴan su da jikokin su, har da me tsohon ciki


Ɗadin abun ma acan gidan mummy akai sunan can muka je saboda kar a ɓata min gida, inda ƴaƴana suka ci sunan

*FATIMA & FATIMA*

sunan mummy da kuma suna mahaifiyata, ɗaya muna ce mata nur ɗayar kuma hoorain amma hoor in short


Hoor da noor sun shaa kaya sosai da kyautuka da kuma hotuna


Tunda aka fara sunan nan har aka gama sabit yana maƙele da ni kamar jaka, duk wani hoton da za ayi tare da shi yana riƙe da baby ɗaya


Wallah tun abin na bani dariya har ya zo ya faɗa bani haushi don kuwa tuni mutan garin mu suka fara magana


"shi mijin mau haka yake abin nasa sam ba kunya"


Ga dukkan kayan da na saka sai shima ya saka, ko kaɗan bansan ya akayi akai mana kaya iri ɗaya ba, ko da yake nasan aikin waye


Na anty fannah ne don kuwa itace akan komai na kayan da zan saka ranar suna,


Mun sha pics sosai da mu da ƴan biyun mu da annur


Suna yai suna haka akai suna aka tashi lfy a daren muka koma gidan mu don gidan mummy babu masaka tsinke

Fatana dai Allah yasa mijina ya shiryu kenan har a bada
[10/05 09:53] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)





*ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN* 🤲🏻🤲🏻





*HIKIMA WRITERS ASSO.*




P⃗a⃗g⃗e⃗ 29🌹







"hiii baby na wallahi na wahala kwana biyu ban jiki ba don Allah my asmy duk abinda zan miki nan gaba kar ki ƙara kashe min waya, a hukun tani ko ta wane hali ne amma don Allah banda hana ni jin muryar ki kinji"

A ɗan shagwaɓe na amsa ƙasa ƙasa

"fannah ta matsa miki ki kira ni koo, shike nan kar ki takura kanki duk lkcn da kika sauko zan jira"


Ya faɗa tausayi ya bani sai nace masa

"ni ba haka bame anty fannah ce tace idan ka haɗu ka matan lagos masu maƙewa namiji zan sani ne"


Murmushi yayi sosai wanda hakan ya ƙara sani ƙuluwa

"haka tace"

"hmmmm" na amsa a takaice

"shike nan rabu da ita in ma zan samo ƴan matan lagos zan samo wacce zata dinga baki arona"


Kuka na saka masa

"wallahi sai dai ka zaɓa ko ni ko ita wallahi bazan kuma zama da wata ba, bayan ga badia kuma ka kuma kawƙ wata wallahi sai na haɗa ka da daddy"


Daɗi ne ya rufe sabit, wanda sam be san ina zai saka kansa ba

"haba baby na daga gani har yanzu baki yadda ba dana ce miki daga ke an zo d end, in shaa Allah ba wata macen da zata kuma ɗaukar hankalina sai ke my asmy, i really love u sooo much"



Hira mukai tayi yana faɗa min kalamai masu ɗumi wasu in mayar masa wasu kuma sai dai inji amma ba bakin mayar wa


Kun kusan awa guda muna waya sannan mukai sallama inda yake gayamin is tooo late daya zo kano


Nuna masa nai ba komai zan ta bin shi da adduar Allah ya kaishi lfy ya kuma dawo da shi lfy sannan mukai sallama





********************


Tun daga lkcn duk wani motsin sa sai ya gaya min sosai muke communicating da shi duk wani motsin sa ko tusa yayi wacce ta canza wari sai ya gayamin ƙarewa kenan


Munyi wata irin shaƙuwa wacce bazan iya fasalta ta ba, ban dai san alaƙar da ke tsakanin shi da badia ba amma ina ji a jikina ko ita bata isa tace sun fi kusa ba




Yara na sun ƙara girma sunyi ɓula ɓula da su kamar kaji kiwon gidan gona


Sam basu damu da shan nono ba ko cikin dare sai dai su sha feeder su don wani lkc ma sai na danne su nayi musu dole sannan suke sha


Itama anty fannah cikin ta na nan ya ƙara girma sosai ya fito haihuwa ko yau ko gobe duk wani siyayya da za ayi na haihuwa munyi shi mun gama jiran ta kawai muke yi



A kwana a tashi ba wuya wajen Allah, har sun gama course ɗin nasu suna ta shirye shiryen dawowa a lkcn ni kuma duk wani gyara nayi shi


Duk wani abunda nasan anace masa mai da tsohuwa yarinya ya daɗe da tsima a jikina buri na kawai mijina ya dawo in nuna masa banbancin da ke tsakanina da badia


Ranar wata alhamis ana sauran kwana biyar sabit ya dawo anty fannah ta tashi da naƙuda inda Allah ya sauke lfy ta samu baby girl ɗin ta itama

Murna a wajen ta kamar ba gode, haka muka haɗu aka cika gidan ana ta murna, kashegari da sassafe ta kama hanyar maid. na so in bita amma sai sabit yace in bari sai ya dawo


Ko da na faɗawa mummy sai tace inyi haƙuri Allah ya dawo da shi ɗin, ban damu ba saboda nasan yana dawowa zai saka ni a gaba mu je maid




Ana gobe zasu dawo da yamma ina zaune na kunna data muna chatting da anty fannah sai naga sabit ya aiko min da messages


Buɗewa nayi me zan gani

Pics ɗinsu ne kala kala shi da badia wasu ba laifi don an yaɗa su amma wasu sam be dace ba


Kala kala sun kusan 20pieces haka aka turomin su wallahi wasu sam ba kyan gani ma, takaicene ya rufe ni


Nasani sarai ba sabit bane ya turo badia ce amma don me ze bata wayar sa har ta shiga ta duba mana sirrin mu


Duk abinda zasu yi bazan hana su ba amma don me zata turo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login