Showing 69001 words to 72000 words out of 88726 words

Chapter 24 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt

ma kanshi annur ɗin ya kuje a goshin sa




Ita kuma ta ciwo a ƙafar ta yana ta jini, tana ganin shi ta fashe masa da kuka


"sabit kaga abinda asmau tai min, wai don kawai na ganta da ciki na tambayeta na waye shi ne tace nata ne wai zuwa tayi ta kashe mu ni da annur tunda yanzu ta kusa haihuwa bata son ƴaƴan ta su samu ɗan uba"


Sam sabit be fahimci abinda badia take cewa ba shidai kawai kallon annur yake wanda yake kwance a yashe goshi na ta jini


Ɗaukar shi yayi ya shiga da shi toilet ya wanke masa sannan ya fito da shi ya gyara masa ciwon ya saka masa plaster sannan ya ajiye shi


Itama badiar first aid box ɗin ya ɗauko ya gyara mata ciwon nata wanda daga gani wuƙa ce ta yanke da ita


Takaici ne ya hana sabit magana, yana gama gyara su ya shirya su sai da ya tabbatar sun kimtsu sannan ya fito daga part ɗin nasan directly part ɗin mummy ya taho a fusace





Ina kwance kawai naji an janyo ni daga kan gadon na faɗo ƙasa sannan ya shaƙe min wuya tare da miƙar da ni sama sannan sauke min yatsun sa guda biyar a kan fuska ta



Tuni na watstsake na ware ina kallon sa

"sabida baki da mutunci har ki shiga part ɗina ki yi mata ta illa sannan ki cutar min da ɗa........


Be gama ba sai ga mummy ta shigo


"wallahi ko ka sake ta ko in ɓata maka rai"




Wancakar da ni yayi ya fice in da mummy ta ɗago ni sannan tace min

" kiyi haƙuri komai me wucewa ne"

Wucewa wallahi an gama da ni haƙuri na ya ƙare anzo wani abu wai shi d end


Miƙewa nayi na wuce part ɗin anty fannah ina mata kukan ta bani aron kuɗi zan tafi ni na gaji da wannan bala'i


Ta so ta lallashe ni amma da ta ga yadda na rufe ido na sai tace min,

"to yanzu in kika tafi ina zaki"


"wallahi ko ina ne ni dai in tafi kuma wallahi bazan bar musu ɗana ba wallahi da abina zan tafi kuma wallahi ko ki taimaka min ko kuma in tafi ko banni da ko ƙwandala"


Jawo ni tayi sannan ta zaunar da ni kusa da ita,

"kwantar da hankalin ki akwai gidan da zan kaiki ki zauna wallahi sai sabit ya gane kuren sa sannan zan dawo da ke"


Wani sanyi naji ya ratsa min zuciya, sannan nace mata

"to yaushe zamu"


"haba so kike a gano ni na fita da ke, ai ke kaɗai zaki fita da annur akan zaki kaishi asibiti nima idan na fita sai ku haɗu, gidan yayana ne shi da matar sa sai kiyi zaman ki a can har sai yadda hali yayi"


Daɗi naji kamar me na kama hanyar part ɗin mummy na fara haɗa kayana



Duk wannan abun da ake yi mummy bata sani ba, sai dana gama haɗa kayan tas sannan na ɗauko su na kawo su part ɗin anty fannah



Itace ta sato min annur sannan muka kama hanyar barin gidan, ƴar tafiya mukai kaɗan sannan muka iso gidan da zamu,



Amaryace ashe na ɗauka ma babba ce kasancewar dare ne yasa san anty fannah bata daɗe ba ta kama hanyar gida


Ɗaki guda aka bani wanka nai wa ɗana sai alkcn naga cieon goshin nasa

"Allah ya saka maka annur"


Sallah kawai nayi na kwanta sai bacci


*******************


Sai sha ɗaya na dare sannan sabit ya dawo gida yana can yana ta fafutukar yadda zai wa asmau rashin mutunci so yake yi tana haihuwa ya kwashe abinda ta haifa ya kai gidan marayu wallahi bazai zauna da baƙaƙen ƴaƴa ba



Yana shigo wa gidan directly ɗakin annur ya shiga yai mamakin daya ga baya nan don haka sai ya ɗauka ko yana tare da badiar ne


Sai da yayi wanka ya gama komai sannan ya shiga ganin shi kafin ya kwanta, badia tana ta sharar baccin ta amma sam be ga annur a kusa da ita ba



"badia badia ina annur yake"

Cikin magagin bacci tace

"yana ɗakin sa da wuri yai bacci na kwantar dashi"

"ban gane ba yanzu daga ɗakin yake sam baya nan"


Miƙewa tayi itama tare da yin hanyar waje domin taje ɗakin annur ɗin amma wayam kamar sabit ɗin ya faɗa



Nan da nan hankalin su ya fara tashi, kafin me wannan tuni gidan ya ɗauka asmau ta ɗauke annur ta gudu


Mummy sabit hankalin su ya fi tashi, fara neman su akai abin takaici ma shine sam ba a san lkcn da ta tafi da su ba


Sabit kamar yai hauka, kasa zama yayi inda ya shuri motar sa ya fice neman annur don ita asmaun sam baya ta tata duk inda taje ai dole wataran ta neme shi ko don abinda take ɗauke da shi


nema aka dinga yi har tsakar dare sannan mummy ta kira sabit ya dawo gida


Da kuka ya dawo mata

"wallahi mummy sai yarinyar nan ta gane bata da wayo, wallahi sai na haɗa ta ƴan sanda ta sace min ɗa na ta gudu"


Kamar zararre haka ya dinga magana lallai sabit ya shiga tashin hankali, ko da mummy ta nemi ya kwanta ƙin kwanciya yayi a haka ya kwana yana ta trying number ta


Da asussuba ya miƙe ya nufi part ɗin sa yana zuwa ya tarar badia itama ta shirya


"wallahi sabit sai mun shiga kotu da yarinyar nan sai ta gaya min menene dalilin ta na sace min ɗa"


Tanka ta be yi ba saboda yanzu haushin ta yake ji duk ita ce ta jawo sam bata san ciwon yaron ba wai har kana gidan amma a sace yaro sam bata sani ba



Kaya kawai ya canza yana ji tana waya tana faɗa wa mmn ta asmau ta sace annur, takaici ne ya ishe shi yadda yake ta jinta tana ta zage zagen sai kace bamagujiya


Yana canza kaya ya fito zai fita

"sabit ina zaka na ga ka shirya wallahi ko asmau ta dawo min da ɗana sai munyi sharia da ita akan sace min ɗa da tayi sai kotu ta raba su wallahi sai na saka an mana katangar ƙarfe tsakanin mu da ita, duk babu muna fiki sai kai ko kunya baka ji ƴar cikin ka kake kwanciya da ita saboda ka zama sallamamme wallahi kaji kunya"


Har ya fice sai ya dawo, wani kyakkyawan mari ya kwaɗa mata sannan ya juya yai ficewar sa, yana jinta tana zagin sa ta uwa ta uba amma sam ba ta ita yake shi dai kawai burin sa ya ga ɗan sa



Ɓangaren mummy ya shiga ya saka mata kuka, lallashin sa ta farayi sannan ta sanar da shi ai ta aika a gano musu ko asmau taje garin su


Kuka ya dinga mata wiwi

" mummy wallahi asmau ta cuceni ta raba ni da farin ciki na annur shine komai nawa shine farin cikina ya zanyi idan banganshi ba don Allah mummy ki taimaka min, don Allah mumy ki cece ni ki dawo min da ɗana"


Tausayi ɗan nata ya bata, gaskiya asmau bata kyauta ba duk da dai duk abinda sabit yayi mata ai bai kamata tayi masa haka ba



Sallamar hjy munnira suka ji, da sauri mummy ta tashi ta tare ta sabit wanda yake zaune yai shaɓe shaɓe da hawaye ya rarrafa yaje wajen su


"don Allah ina ɗana yake" ya tambaya


Mummy ce ta daka masa harara gabaɗaya sabit ya susuce

"wallahi hjy har garin su aka je bata je, babu wanda kuka san ta sani a garin nan, wallahi tunda kika kirani jiya wallahi hankalina yake a tashe na rasa kwanciyar hankali yarinyar nan a dalilina aka san ta kuma ace ta ɗauki ɗan masu gida ta gudu da shi wallahi tun jiya jiki na yake ɓari"


"wallahi hjy na san bata wajen ki, asmau ce tayi wauta sosai" inji mummy


kuka sosai sabit ya saki kamar wani ƙaramin yari, kunya ce ta rufe mummy kamar ta nutse ƙasa sam be ji kunyar hjy munnira ba, kun san tsakanin ɗa da uwa tun tana masa faɗa akan kukan


Har ya karyar mata da zuciya, ita ma sai ga hawaye, hjy munnira sai ta saki baki tana bawa uwa da ɗa haƙuri



Suna cikin wannan halin ne sai ga ƴen uwan badia nan sun shigo
[10/05 09:52] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




*HIKIMA WRITERS ASSO.*




P⃗a⃗g⃗e⃗ 26🌹








Duk yadda daddy ya so na samun dr. amma hakan be samu ba, haka har lkcn komawa yayi



Muka koma ko da aka tambayi ni in dr. ɗin sai nace bamu san inda take ba


Nan da nan alƙali ya ce ai banninda magana

Lawyern badia ne yace

"ya mai sharia duk da dai mu muke da gaskiya amma muna son bata dama ta ƙarshe a yi musu gwajin jini"


Alƙalin ya yadda cewar ai mana gwajin jini, tun daga lkcn sabit ya fara rashin mutuncin sa


"wallahi aka gama case ɗin nan aka bawa badia ɗan ta dama ki kama hanyar garinku don kuwa nai wa badia alƙawarin rabuwa da ke ana gama case ɗin nan"


Wallahi ni yanzu ɓurɓushin sabit
bana son gani, balle wai son zama da shi


Asibiti muka je aka ɗebi jinin mu ni da badia da annur,


Sannan muka koma gida, kasancewar kwana uku aka bamu court ya sa muna cika kwana ukun muka koma


Sai da alƙali ya kuma kuran mu yace duk mu sake faɗin yadda a ka samu annur


Kowannen mu ya faɗa sannan ya sa aka ɗauko masa test ɗin da aka yi yana buɗe wa sai ya ce


"sakamakon bincike ya nuna asmau ita ce uwar annur ba badia ba, don haka court ta barwa asmau ɗan ta"



Wani irin ihu da badia ta saki sai da ya firgitar da court ɗin,

"wallahi da ƙwai na aka dasa aka samu cikin annur wallahi jini nane ba na asmau ba, sabit don Allah kai musu bayani sosai" inji badia nan da nan court ɗin ta ɗau surutai ƙanana


Alƙali ne ya doka ƴar gudumar sa sannan yace, sai da kowa ya nutsa sannan ya fara yanke hukunci


"asmau, an mayar mata da ɗanta, sannan sabit da badia court ta ci tarar su akan ƙaryar da suka yi sannan kuma aka yanke musu kuɗin da zasu biya asmau sakamakon dashen da sukai mata bayan sun san be halatta ba, daga nan sai alƙali ya doka gudumar sa an kashe case



Asmau ce tai magana

"ya mai sharia ina son sabit mijina ya sake ni don kuwa na gaji da zaman da muke yi da shi"


A tsorace sabit ya juyo ya kalli asmaun wacce fuskar nan tata take a cunkushe


magatar ka ne yace mata wai tazo daga baya ta shigar da case ɗin in yaso sai a sake zama, daga nan aka sallame su



Tunda suka fito jikin sabit sai rawa yake yi lallai ma yarinyar nan, ita kuwa badia suna fitowa ta chukumi sabit sai zagi


Da ƙyar aka ɓanɓare ta daga jikin sa tana ta ɗura masa zagi wai shi munafiki ne


Abune suk taru sukai wa sabit yawa shi sam be ji komai ba da aka ce asmau ta riƙe annur ko ba komai ya san annur zai ci gaba da zama a gidan su


Amma yadda asmau ta shigar da ƙara wai ya sake ta shi ta ina zai fara ba wai yana son asmau ne a a shi har yanzu be ji yana son ta ba amma asmau ta zama kamar wani ɓangare na jikin sa wanda sam be damu da ɓangaren ba amma idan ba ɓangaren rayuwar sa zata tawaya



Har suka je gida ya na saƙawa yana warware wa yasan tabbas asmau tace zata faɗawa daddy tana son rabuwa da shi daddy zai goya mata baya don haka dole ne ya taka wa abin burki


Yana shiga ɓangaren mummy ya zayyona wa mummy abinda asmaun tayi

"hakan shine dai dai kai sabit, rabuwa da asmau shine kwanciyar hankalin mu gabaɗaya, tunda kusan shekara nawa kuna aure amma har yanzu ba samu kwanciyar hankali ba sai yaushe sannan za a samu ai gwanda ku rabun ya fi"


Hankalin shi ne ya kuma tashi, ya za a yi ma ya rabu da asmau yarinyar da duk abinda yai mata tsab take shanyewa


Ita badia sam baza ta ɗauki cin kashin da zai yi asmaun ba, ban da ɗibar albarkar da tai masa a court yanzu wane zama zasu kuma yi da wata badia


Ga asmau wacce yanzu ta zama ita kaɗai ce hope ɗin sa ita ma ta fara wayewa kai wallahi da sake



Ɗakin ta ya tashi ya shiga, annur kaɗai ya gani yana zaune akan gado yana wasa da wayar ta, ɗaukar yaron yayi yana ƙara jin son sa a rai


Lallai wannan abin da mamaki to ya akayi asmau ta haifi ɗa fari kuma ya akayi annur ya kasance ɗan asmau bana badia ba



Duk wannan tambayoyin yana yin su a cikin zuciyar sa ne a lkcn da yake kallon yaron wanda ba abinda ya dame shi, buɗe ƙofar toilet ne ya dawo da shi daga tunanin sa



Asmau ce ta fito ɗaure da alawa ta na ganin shi ta haɗe rai

"me ya kawo ka"

"in zan zo ganin matata da ɗa na sai na nemi permission ɗin" ya faa da fara'ar sa


Haɗe ranta tayi sannan tace

"pls sabit bana son wani abu na shiga tsakanin mu don Allah in annur ka zo gani ka gan shi ka fice don bana son wani false alaƙa ya shiga tsakanin mu bayan kasan wannan auren namu ba fashi sai na kashe shi, don haka kar ma kayi tunanin creating wani false relationshio tsakanin mu don kuwa bazaka samu hakan ba, asmaun da ka sani ada ba ita bace wannan ba


Wannan wacce ta san ƴancin kanta ce, kuma zanyi komai don ganin na ƙwatar wa kaina ƴanci daga azzalumin kamar don haka ka fice min daga ɗaki"


Sam sabit be ɗauka asmau zata mai haka ba shi a tunanin shi zata kasance yana juya ta yana mata abinda yake mata har abada ashe akwai lkcn da asmau zata ce zata rabu da shi


"asmau in banda abinki yanzu kika ce zaki rabu da ni ai kwashe ƴaƴana zanyi harda wanda ke cikin ki daga ranar da kika haife shi a ranar zan raba ki da shi" ya faɗi haka don ya razana ta


"ai kasan ban san hanyar court ba ko kuma kana tunanin court ɗin mahaukaciya ce da zata ɗauki ƴaƴan da baka san darajar su ba su baka, wallahi ko bammu da abinda za muci gwanda na zaun da ƴaƴa na akan in basu"






Fita yayi daga ɗakin daya ga alamar banni da niyyar sallama masa,


Part ɗin daddy ya nufa, yana zuwa ya tarar da daddyn yana karatun newspaper


Wuri ya samu ya zauna ya fara gaisar da daddyn, ƙin kula shi yayi sai daya shaƙa saboda sabit ya gama ɓata masa ransa


"naji asmau tace tana neman saki kooo, nayi wa lawyer na magana shi zai tsaya mata sai ya ga an ƙwatar mata ƴancin ta"


Sam ba haka sabit ya so ba, ji yayi kamar ya rusa ihu

"kuma ita ƴar lelen taka kaje ka dawo da ita, ita kuma wannan wacce baka so ka bata takardar ta inya so ni zan ci gaba da kula da ita har Allah ya haɗa ta da wanda zai so ta tsakani da Allah"


Faɗa sosai daddy yayi masa sannan ya karta masa warning akan ya je ya dawo da badia, sam daddy be goyi bayan sabit ba duk kuwa abinda sabit ɗin ya faɗawa daddy sai daddyn yace ai shine babba a cikin su kuma babban banza


Dayaga sabit ya dame shi da magiyar yana son ya bar masa asmaun sai ya fatattake shi


Ɓangaren mummy ya koma ya fashe mata da kukan din Allah kar a raba da asmau


Ina ɗakina ina jin sa wai wallahi zai dinga kyautata min, to kasan tsakanin ɗa da mahaifi barin ma ace uwa duk sai hankalin ta tashi


Kira na tayi na fito daga ɗakin da tirtsetsen cikina

"asmau ga mijin ki nan ya zo yana neman afuwa a wajen ki me zaki ce"


"gaskiya mummy yanzu zuciyata ta riga ta gama cire sabit daga cikin ta, wallahi sabit tun da nake da kai ban taɓa son ka ba saboda baka taɓa kyautata min ba ko a ɓoye balle a fili, kullum burin ka ka cutar da ni, yanzu kuwa lkc ya yai da zan ƙwatar wa kai na ƴanci" na faɗa hankalina a kwance


"to in abin asmau baki ganin kuma kina zaune a gidan su amma kina cewa ya sake ki" ban kai ga amsa ta ba sai naji muryar daddy


"ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login