Showing 84001 words to 87000 words out of 88726 words

Chapter 29 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt

kansa hmmm wata sabuwa inji ƴan caca



Dole tasa akai emergency operation na kansa inda akai masa fixing matsalar

Awan su shida a cikin theater inda daga baya aka gangaro shi aka fito da shi kamar matacce,


Babu wanda bai yi kuka ba lkcn da muka ganshi kamar ba rai a tattare da shi,


Awa 48 aka bamu akace in bai tashi ba dole a kuma wani, addua ce kawai tamu yanzu da kuma fatan ya miƙe, kusan bana daɗewa sai na kalli agogo ina yi ina lissafin awowin kamar basa gudu



Anty fannah ma ranar da akai masa theater ta dawo lkcn kwanasu goma sha ɗaya, itama tana ganin sa kuka kawai ta saki sabida gaba ɗaya sabit ya canza kamaninsa na da sun canza ya wani kunbura kamar ana hura shi



Har dare ta kai sannan ta tafi akan itama zata koma ɗakin mummy ta ci gaba da jegon ta saboda ta dinga saka ido akan yaran namu


Sosai mukai mata godiya ni da mummy don kuwa ragowar ba wanda ya kawo wannan abun a ransa


********************


Yau kusan kwanan mu goma a asibitin amma sam ba badia balle wani wani nata tun abin baya damuna har ya fara damuna nai wa mummy maganar


Kuka kawai ta fashe min da shi

"asmau kin san kuwa badia itace silar wannan abun da ya samu sabit, wallahi har duniya ga naɗe bazan taɓa yafe wa ƴar iskar yarinyar nan ba wallahi ta cutar min da ɗa ba kaɗan ba"


Jikina ne yayi sanyi yadda naga mummy na kuka lallai na koka da lamarin badia amma sam ban ɗauka za a ce mijin ta na wannan halin ba amma ta kasa zuwa ko wani nata ya zo ya duba shi



Hira mukai da ita sosai inda ta dinga bani irin rayuwar da sukai da badia a turkey yadda suka dinga faɗa, akan ita lallai sai sun sake yin dashen don taga ƙwan ta a duniya



Ooooh ni asmau na ɗauka badia ta bar wannan maganar ashe ba a barta ba, ashe har yanzu badia batai hankali ba


Yanzu gashi nan abinda ta jawo wa mijin ta kuma sam ko a jikin ta abin be dame ta ba, shin dama akwai mutane masu irin wannan halin a duniya



Wallahi ko da kuwa za a ce sabit yankan naman jikina yake yi saboda tsabar ƙiyayya na ganshi cikin wannan halin wallahi sai ba zqn bar shi ba sai na kula da shi in yaso idan ya farfaɗo sai mu ɗora daga inda muka tsaya




Hira muka dinga yi da ita har kusan 12 :30am na dare inda nishin sabit ya tayar da mu daga wajen hirar tamu


Nishi kawai yake yi na alamar zafi ko azaba, dr. na kira inda ya zo ya duba shi sai yayi murmushi yace aiki yayi kyau



Wata allura ya kuma yi masa a cikin ruwan da aka saka masa sannan ya fice, wallahi a ranar haka ya kwana yana wannan gunji wanda kuma ni da mummy muka kwana muna masa addua tare da kuka shaɓe shaɓe


Sai gab da asuba sannan yai shiru alamar bacci, sai a lkcn nima na ɗan rintsa inda mummy ta ɗauro alwala ta tayaɗ da sallah


Tun daga lkcn kullum da daddare sai sabit ya mana wannan gunjin indak aka ce sha biyu tayi na dare ya fara kenan sai a suba


Kuma duk wannan abin da yake yk sam be farka ba balle ya zauna


Rannan da yamma wajen ƙarfe huɗu na yamma, lkcn watan mu guda da sati biyu muna zaune sai ga badia da bbn ta


Nai mamakin ganin ta, sosai muka gaisa da mahaifin natan inda ya bada haƙurin wai wallahi baya gari ne sai daya dawo sannan ya samu lbr


Sam badia bata ji kunya ba ta ƙaraso kusa da gadon da sabit yake kai, kallo. Shi tayi sannan ta taɓe baki

"Allah ya sauwaƙe" bbn ta ne ya hauta da zagi da faɗa, wallahi wani haushi da ya ziyarci zuciyata kama in maƙe ta


"hjy fatima gatan su haɗu ita da ƴar uwar tata suyi jinyar mijin su ke kuma ki koma gida ki huta, ai ba haƙkin bane jin yar saba"


Ƙiri ƙiri mummy tace bata yadda ba in badiara zatai jinyar ta zauna mu haɗu mu uku amma ita sam baza ta bar ɗan ta ba


Ganin hakan ne yasa itama badiar tace

"daddy kawai ka barsu su dinga kwana ni na dinga wuni, don Wallahi ni ban ma san ta yadda zan fara kwanan asibiti ba"


Harara ya bita da shi sannan sukai sallama akan zata dinga zuwa da safe tana wuni mu kuma mu dinga kwana sai mu dinga shiftinga kamar gaske



Sam badia bata nuna tausaya ga sabit ba sai ma dai kamar wani da take yi kamar da gayya







Badia aka fara zuwa jinya amma sam ba abinda take yi wuni take tana chatting ko kuma idan ta zo sai ta ajiye jakar ta ta fice


Ba zamu kuma gani ta ba sai dare, dats in ta zo ma kenan, wannan abun ya fara bawa mummy haushi rannan da ta zo mummyn tai mata tas ta ce kuma idan ta kuma takowa sai ta saka an mata duka, tun daga lkcn ta daina zuwa


*******************


Sai da sabit yai wata biyu sannan aka cire masa naɗin gaskiya yanzu ya samu sauƙi sosai, yanzu fara koyan tafiya kawai ya rage mana



amma kuma wani abun mamaki ga sabit shine sam baya magana


Baya wani abu ko na farin ciki ko baƙin ciki, baya umm baya umm umm, haka yake kamar wani mutum mutumi


Kuma wani abu da yake yi shine, kawai yana zaune sai ya saki pupu ko fitsari, ran da muka fara ganin wannan abun ni da mummy mun yi wani abu wai shi kuka


Ko da daddy ya zo aka faɗa masa shima abin ya bashi mamaki, dama tun kafin lkcn ya na complain ɗin rashin maganar sabit ɗin


Dole ta sa aka sake yi masa check up, mu dai ba a faɗa mana ko menene ba daddy de yace mana dole sai an fita da sabit waje an duba masa kan sa,


Sam ban kawo komai ba, muka ci gaba da jinyar sa inda yanzu ƴan uwan sa maza suke koya masa tafiya


Rannan sai ga badia da mmn ta sun zo, tunda sabit ya kwanta a asibiti in banda bbn badia da yake zuwa a kai akai ba wanda muke gani nata


A tsats tsaye muka gaisa don mummy ko kallon inda suke ma bata yi ba



"sannu sabit ashe kuma haukace wa akayi, Allah ma ya taimake ka kana da wata matar ta kula da kai amma wallahi ƴata ba kalar wahala bace don haka wallahi baza ta wahalta maka ba"


Mummy ce ta miƙe ranta a ɓace ta matso har kusa da mmn badiar kamar zata dake ta

"duk rashin mutuncin da kuke yi ban taɓa tanka muku ba amma ki rasa abinda zaki ce wa wanda ya rufa wa ƴar ki asiri sai haukace wa, ai in ya haukace ya shafi ƴar ki tun za ace mijin ta ya haukace"


Wani banzan kallo ta bi mummy da shi sannan tace

"au ance fa ku ba a faɗa muku maganar haukan sa ba, ai ya samu matsala ne a ƙwaƙwalwar sa" ta faɗa da fara'ar ta


"wannan abun da yake yi ai duk samun taɓin haukan ne, baki gani, in ba mahaukaci ba wanene be san komai ba sai dai komai ayi masa, haba ki duba mana"


"maama ni fa wallahi bazan iya zama da mahaukaci ba haka kurum a dinga ce min matar mahaukaci" inji badia


"barsu a wallahi dole ne ma a sakar min ƴa da ƙuruciyar ta baza ta ƙare a jinyar mahaukaci ba, wallahi ko a samu me sakar ta a cikin ku, ko in kai court a ƙwatar mata ƴancin ta yana lafiyayye ne ya ke mijin aure amma yanzu ya zama sai dai yai depending akan wani to wallahi ba dai badia ta ba" inji mmn badia


Gaba ki ɗaya service ɗin kaina ne ya ɗauke na rasa abinda ke damu na haba biri yayi kama da mutum ashe matsala ya samu a ƙwaƙwalwar sa


Tausayi ya kuma bani kallon inda yake nayi yana kwance idon shi a buɗe yana kallon sama, baya umm baya umm umm,


Wasu hawaye naji suna zubar min na tausaya masa Allah sarki sabit Allah ya tashi kafaɗar ka


"wallahi ba ɗa bare jika bazan zauna a matar mahaukaci ba, Allah na gode maka ma annur ɗin ba ɗana bane Allah na gode maka banni da ɗa da shi balle ace min ko don ɗana in zauna"


Kallon inda nake tayi

"kema wallahi ki kama gaban ki tun da jajayen sahun ki kar ki zauna ki yi jinyar sa a banza ya haukace bashi da wani amfani yanzu" mari kawai taji na sauka mata shi a fuskar ta wanda ni kaina ban san lkcn da na yi hakan ba


Ɗaga hannun ta tayi zata mare ni wanda kafin ta sauke shi a kan fuskata, na kuma ƙara mata wani sannan na rufe ta da duka


Mmn ta ce ta hau duka na wanda sam bana ji buri na sai nayi wa badia illar da ita sai an kwantar da ita don ta san cewa tsautsayi yana kan kowa


Sai da mummy taga abin namu da gaske ne sannan ta kira nurses suka raba mu


Zage zage suka dinga tare da kiran sabit mahaukaci miskini mara amfani wannan kalmar itace take ƙara ƙona min rai na


Sai da suka fita sannan na fashe da kuka naje na faɗa kan sabit ɗin wanda duk abinda ake yi yana nan kwance sam be ma san anayi ba


Kuka nayi wanda itama mummy iɓa jin nata, haka muka zauna muna ta abinmu babu me lallashin wani, har mukai muka haƙura kowacce ta lallashi kanta sam wannan abun ba abin kuka bane


"asmau kema kar ki zauna anan ki ɓata lkcn tunda kinga yadda Allah yayi da shi"


"mummy wallahi ko sabit ya fi haka bazan iya rabuwa da shi ba, balle sam ban yadda da maganar badia ba, kusan yawancin maganar ta ƙarya ce ƙalilan yake gaskiya"


Mummy ba babu yadda batai da ni ba amma sam naƙi yadda dana ga ta matsa min sai na fashe mata da kuka

"mummy ya za ayi in iya fuskantar ƴaƴana ince na bar mahaifin su ne kawai saboda kawai wata jarabawa ta same shi, wallahi mummy yanzu ne ma nake son zama da sabit fiye da daa, wallahi bazan taɓa barin shi ba wai don wani ya same shi ba"


Kuka sosai mummy tana gode min tana ƙarawa, muna cikin wannan halin ne daddy ya shigo ya ganmu


"to menene kuma ku da bakwa rabo da kuka"


Nan mummy ta kwashe tas abinda mmn badia ta faɗa mana ta faɗa, jikin shi yayi sanyi sai ya samu wuri ya zauna sannan ya kalle yace


"sam asmau mijin ki be haukace ba, jijiyace ta toshe jijiyar da ke comtrolling tunanin ɗan adam, duk da dai wannan rare case ne ba a cika samun sa ba cikin mutane saboda jijiyar tana can cikin kan mutum amma ba wani abu bane, da an masa aiki an masa flushin ɗinta zai dawo dai dai in shaa Allah"


Wani ajiyar zuciya muka saki ni da mummy inda daddy yai mana bayanin cewar suna ta processing yadda za afita shi inda za ai masa aikin a china



Sosai daddy ya kwantar mana da hankalin mu inda yace zai dinga sa ɗaya daga cikin maza su dinga kwana ana shifting saboda yanzu ya riga ya warke


Gwanda ace da namiji abin sai ya fi sauƙi, tun daga lkcn ƴan uwansa maza suka fara



Zuwa suna taya mu jinya, kwana ɗai ɗai suke yi in wannan yazo ya kwana gobe wani ne zai zo,



Mun sai da muka ƙara wata ɗaya a haka kafin a gano lkcn da sabit yake yin pupu ko fitsari, tunda aka dai daici lkc sai ya kasance da lkcn yayi za akai shi toilet kuma cikin hukunci Allah yayi ɗin


Sam bana ƙyanƙyamin aiki kashin sa ko wani abun, haka ma mummy, ni dai kawai amai ne yake yawan taso min


Rannan da safe bayan ya gama cin abinci sai ya ɓata bedsheet ɗin da fitsari sam mantawa nayi ban saka shi ba


Tare da mummy muka kwashe kayan inda amai kwai yake ta taso min, bamu gama ba nayi toilet a guje na dinga sheka amai kamar zan amayar da kayan cikina



Sai da nagama sannan na fito, sannu kawai mummy tayi min sannan tace in je gida in huta zata ƙarasa


Karɓar kayan naje nayi inda naga ta kauda kayan daga kusa da ni

"asmau kin ma yi ƙoƙari wallahi bazan taɓa judging ɗin ki ba, amma wallahi bazan taɓa zama inga kina takura ba saboda jinyar sabit, jinya sam bata da daɗi kna da zaɓin da kike so ko ki zauna da shi ko ki tafi, amma ya za ayi ina kallon yadda kike kuma ince ki cigaba wallahi asmau na yafe ki koma gida ki kula da yaran ni kuma zan kula da shi har Allah ya bashi lfy"


"wallahi mummy ba a takure nake ba, kawai dai haka kurun sai inji zuciya ta na ta tashi, ko me naci sai ya dawo"


Kallo na tayi

"yaushe rabon da kiyi period ɗin ki"


Tsayawa nayi ina tunani, kai 😱😱 kar dai ace ciki gare ni, murmushi na gani a fuskar


"dama yace yaje maiduguri ranar daya dawo ashe rabo ne ya kai shi, kai amma naji daɗi" ta faɗa tana rungume ni


Cikin nawa na kuma shafawa wanda sai yanzu na fahimci ɗan motsin da nakan ji akai akai a cikin nawa


Wajen sabit ɗin ta jani, yana zaune akan kujerar sa, hannun shi ta ɗauka ta kai kan cikina


"sabit kaga ajiyar ka kayi sauri ka warke kafin ya zo duniya"


Kamar ba shi ake ba sam be kalle mu balle ya tanka, wannan abun ya kuma bani tausayi da lamarin sabit kai Allah ka bawa wannan bawan naka lfy


Ko da daddy ya zo sai da mummy ta faɗa masa sosai ya nuna murna da wannan labari, shine ma yace wa mummy muje muji yadda babyn yake



Lami lfy haka aka gano babyn mu ƴar wata huɗu da ƴan sakita, wannan ya fi komai farin ciki, inda daddy ya kafa dokar dole in daina kula da sabit nima in zauna in kula da kaina


Sam ƙin yadda nayi, inda daga ƙarshe aka bar maganar akan zan dinga zaman asibitin amma kuma bazan kuma wani aiki ba saboda nima mara lafiya ce



Sosai nake kula da cikin jikina har lkcn da sabit ya iya tafiya, yana iya tafiya yanzu sosai ba tare da taimakon komai ba, amma matsalar itace yana ɗingishi


Badia sun zo ita da bbn ta inda ya kawo ta ta bada haƙuri daddy ya so ace an bawa badia takardar ta amma sam sai bbn ta ya ƙi, yace a bari a ga in kai masa aiki da za ai masa a waje yadda hali zai yi


Wannan ne yasa har yanzu badia take a matsayin matar sabit amma sam bata zuwa ko bbn ta ya matsa mata zata zo amma maganar da zat dinga yaɓa wa sai kace dama bata zo ba


Lkcn da muka tashi tafiya china yayi a lkcn cikina yana da wata bakwai ya ɗan fito amma ba sosai ba, ba kamar na twins ba



Da ni da mummy, isma'il sai anty fannah mukai tafiyar domin neman lfyr sabit,


Ranar da muke je a ranar akai admitting ɗin mu a asibitin na ƙwaƙwalwa a wani ɗan ƙaramin gari da ke garin yangshuo a birnin Guangxi na garin china




Sam garin bashida wani girma sosai sannan a zagaye yake da duwatse sai tafkeken kogi dake gefen gari


Hanya ɗaya ce wacce zaka shiga garin kuma ka fita ta shi inda a mota zaka sai dai ko in a jirgin ruwa ne shine zaka shigo ta kogi



Shi kanshi asibitin ba wani babba bana amma kuma duk faɗin china yana ɗaya daga asibitocin ƙwaƙwalwa da ake ji da shi


Kwanan mu uku aka shiga da sabit theater inda sai da suka sake masa sabon general check up anan suka gano ɗorin da akai masa a ƙafar sa sam be yiwu ba don haka sai an sake ɓalla ƙafar sannan asake masa sabon ɗauri



Gyaran ƙafar ne yasa aka ɗaga aikin a alkcn da aka saka don dole sai an ɗauko orthopedic dr. sannan ayi masa aikin rana ɗaya



Sati biyu babban likitan na ƙashi ya bamu kafin yazo, wanda ranar da ya zo a ranar aka shiga da shi theater


Tun ƙarfe 10 :30na dare suka shiga operation ɗin inda za afara masa na ƙafar dana nan ayi masa na ƙwaƙwalwar


Wannan jar danjar da ke kunne a ɗakin theater room itace nake ta kallo wacce in tana a kunne hakan yana nuna operation ɗin ake yi


Fatana da burina sabit ya samu sauƙi, awan likitan ƙashin uku cur sannan ya fito, in da yai mana bayanin an gama komai amma sai da akayi masa ciko da ƙarfe a ƙafar tasan


Inda zai dinga zuwa ana duba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login