Showing 36001 words to 39000 words out of 88726 words

Chapter 13 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt

shagwaɓa da kuma last but not d list wacce muke ganin kamar tafi kowacce itace iya kwanciyar aure, ```ƴammata ku gafarce, amma maganar gaskiya ce, duk macen da ta iya waɗannan kissosin sai dai wani ba mijinta ba```


da kuma sauran su duk waɗannan abubuwan idan muka riƙe su gam sannan muka haɗa da roƙon Allah day in day out in shaa Allah sai dai muji anayi rigimar aure a maƙota ba dai gidajen mu _Allah ka bamu dacewa da ƙarshe me kyau_



Ilimi sosai take koya min kuma nake naɗewa ina ɗauka ina haddace wa burina kawai Allah ya kaimu lkcn da zan kashe wannan auren nawa na bautaswa inyi auren soyayya 😍




👩🏽‍🍳 *menu of d day*👩🏽‍🍳


*tuwon semovita miyar egusi and kunun tsamiya*


*tuwon semo*

```ingredients```

-semo
-flour
-butter

*ki zuba ruwa a tukunya sai ki rufe, idan ya tafasa sai ki zuba wani ruwan daban a bowl sai a dinga zuba semo ɗin ana juyawa har yayi kauri


2) daga nan sai a ɗauki talge a talga tafasash shen ruwan, idan an talga sai a saya murfin sannan a rage masa wuta talgen ya dahu a hankali


3) idan talgen ya dahu sai ki haɗa flour da semo, kamar flour ya fi semon yawa sai a tuƙa bayan yayi ta sai a saka butter a ƙara tuƙawa sannan a rufe a rage wuta ya turara idan ya turaru sai a kwashe a leda


*miyar egusi*

```ingredients```

-kayan miya
-man ja
-egusi
-egg
-alayyahu
-maggi
-nama
-crayfish
-kifi


Method

1) ki saka naman ki a tukunya ki zuba maggi, albasa da tafarnuwa sannan ki rufe, idan tafasa sai ki zuba kayan miyar ki ki barshi ya dahu


2) a wata tukunyar daban kuma sai ki zuba man jan da zakiyi miyar da shi idan yayi zafi, sai ki wanke kifinki ki zuba a mai ki soya sannan idan ya soyu sa a tsane

3) daga gefe kuma sai ki kwaɓa egusi ɗin ki da ruwa sai ki zuba a man jan sannan sai ki rage masa wuta yai ta dahuwa a hankali, idan ruwan ya ɗan tsotse sai ki fasa kwan ki ki kaɗa shi sannan sai ki zuba shi akan egusin ki bar shi ya ɗan dahu sannan ki juya idan kina son egusin ki ya dundunƙule kar ki juya shi sosai


4) sai ki juye egusin a miyar sannan ki zuba crayfish, ki ƙara maggi da albasa sannan ki rufe, in ruwan yai kaɗan sai ki ƙara ruwan


5) idan miyar ta yi dai dai sai ki zuba alayyahun ki wanda kika yanka kika wanke sai ki zuba kifin ki ki rage wutar sannan ki rufe


Minti ɗaya sai ki sauke


*kunun tsamiya*


*ingredients*

- ƙulun kunu
-tsamiya
-lemun tsami
-sugar


```method```

1) ki zuba ruwa sannan ki saka tsamiyar ki, idan ruwan ya tafasa sai ki tace sannan ki ƙara mayar da ruwan don ya ƙara tafasa


2) ki zuba ƙullin kunun sannan idan yayi kauri sai ki ɗan ƙara masa ruwa daga nan sai ki zuba a cikin ruwan zafi ki rage, idan yayi kauri sai a sauke


3) sai ki kuma ɗiban ƙullin ki sakar masa ruwa sannan ki ɗauraye kunun sannan ki ɗan matsa lemun tsami sannan ki juye a flask



👩🏽‍🍳 *BON APPETIT*👩🏽‍🍳




*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:51] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)



P⃗a⃗g⃗e⃗ 15🌹




Yin karatu a wajen malama ta anty fannah ya sani ƙara wayewa da yanayin zamantakewa ta ɗan adam, kasancewar garden ɗin gidan a bayan part ɗin su ga sanyi ga iska ya sa kusan kullum a can muke karatu



Idan nagama aiki sai in je part ɗin su sai mu koma garden ɗin mu zauna muyi ta karatun mu ko tai ta min fatawowi da dai sauran su


Har akai sallah lfy muna karatun mu kuma na ɗau alwashin ko bayan sallah zan ci gaba da biɗar ilimina don ilimi shine hasken rayuwa, in babu shi mutum zai kasance kamar a duhu yake Allah dai yasa mu wanye ƙalau kuma ya bamu ilimi me amfani da mu da ƴaƴan mu amin summa amin



Rannan muna garden ɗin sai ga isma'il ya zo

"ina ta neman ki a ciki ashe kina nan" ya ƙaraso yana faɗawa anty fannah, gaishe shi nayi sannan nayi niyyar tashi don in bar su su shana



Hana ni yayi tace shima aiki ne ya kawo shi in zauna muyi karatun mu, komawa nayi na zauna muka ci gaba, kasancewar doguwar riga ce ƙirar dubai a jikina me belt wacce ta saka belt ɗin na ɗaure jikina da shi sai ɗan kwalinta da nayi rolling kaina da shi


Ya sa sam ban sake ba ni da na saba yawo a cikin hijab kamar bukka 🤣, karatun mu muka ci gaba amma sam a nutse nake



Sallamar gogan na badia na ji a bayana inda duk muna amsa ni kuma na haɗe raina don bana son wannan shishshige min daya ke yi



Ƙarasowa yayi ya zauna dai dai kusa da ni har jikin mu yana ɗan gogar juna wanda hakan ne ya sa ni kuma na ɗan kuma matsawa ko ya sake amma bada ni ba, basarwa yayi kamar be san me yi ba sannan yace


"ku ashe anan kuka yini kuna shan iska me daɗi shine sam ba a san a gayyaci mutum ba ko" ya ƙarashe zancen sa da sigar tambaya yana kallo na



Iskar data kwaso shi ma ban shaƙa ba balle in tanka masa littafi na na ɗauko na rufe fuska ta da shi kamar ina karatu


Anty fannah ce ta tanka masa

"yo ai ba a damu da ba, balle a san a ina muke yini" na san martani ta mai da masa murmushi yayi sannan yace


"ai matsalar taku ce ba kwa fara'a ga shegiyar shariya ko an muku magana kun san da ku ake amma sai ku share mutum kuyi kamar baku jiba"


"wannan shine cikar mace me aji" inji anty fannah


Su ka ci gaba da maidawa juna martani wannan ya faɗa wannan ya mayar dana ga abin nasu ba na ƙare bane sai kawai na miƙe na sannan nace


"anty fannah naga alamar kin samu abokin hira bari ni in wuce maci gaba da karatun nan gaba" ina gama faɗar haka nai gaba abina




Nayi nisa naji yana ƙwala min kira ban tanka masa ba haka zalika ban tsaya ba, sai kuwa gashi ya sha gaba na

"baki ji ina kiran ki bane wai asmau me yasa kike da taurin kai ne"


"ai ban ɗauka da ni kake ba, na ɗauka badia kake son kira ka manta kace asmau" murmushi yayi wanda yai masa kyau kamar kar ya dena


"ashe kice abin naki kishi ne, to in banda abinki ai badia alba sa ar ki bace, yarinya kyakkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa fara me kyan ɗaukar hankali"



Haushi ne da takaici suka cika ni tsayawa kulashin da nayi gashi nan ya ɗige da yaɓa min magana



Raɓa wa nayi ta gefen sa na wuce

"sai kace gurin ta ni kuma ka ƙyale ni Allah zai kawi min wanda zai soni ba don abinda nake da shi ba"



Wannan kalmar tai mutuƙar ɓata masa wanda har ya sa shi shan gaba na tare da damkar hannun da ƙarfi wanda hakan ya sani wani radaɗi a hannun daga dukkan alamu matse mun hannun yayi


"saboda baki da hankali da auren nawa a kanki kike maganar samun wani, to wallahi karki ga ina ɗaga miki ƙafa ina nan a sabit ɗin da kika sanni in kika sake na kuma jin wannan kalmar daga bakin ki sai ki yaba wa aya zaƙin ta"



Wulli yayi da ni inda na faɗi ƙasa har da gurje gwiwar ƙafa ta, kuka na saki dama me hali yana fasa halin sa ne na faɗa, kuma wallahi abinda kake nema a wajen nawa baza ka samu ba sai dai wata



Kuma neman rabuwa da kai ban ma fara ba sai lkcn da na tara iya kuɗin da nake so zaka san cewar shayi ruwan na faɗa a raina tare da miƙewa ina karkaɗe kayan jikina mugu kawai


********************


Tun daga lkcn na shiga wasn ɓuya da shi don duk abinda na san zai haɗa ni da sabit bana ma tunkarar sa shima a nashi ɓangaren naga alamun haka


Don yawan kiran da ya ke min da yanzu ya daina sam kamar ma be fara ba,



rannan da rana na gama lunch na kaiwa mummy na tarar da ita tana ta mita, zama nayi sannan nace

"mummy lfy kuwa"


"ina fa lfy ni da wannan har iskar kishiyar taki wai tayi tafiya amma sai da ta sauka sannan mijinta ya sani, shi ma da yake be san ciwon kansa ba ko a jikin sa" dariya ce ta so kubce min amma sai na dake


Kaɗan ya gani be gama ganin komai ba ba dai zalinci ya riƙe ba ai ba abinda ya soma gani ma,

"mummy garin ƙaƙa akai haka" na tambaye ta da alamar damuwa a fuska ta


"ai da yake kin san ta riga ta shanye shi tas baya ganin laifin ta, kome tayi sai yace ai duk abinda take yi tana sane, be san mace ba a sakar mata, kai wannan yaron wai sai yaushe ze farka ne ya fahinci abinda nake nuna masa" ta faɗa tana dafe kanta alamar abun yana damun ta


" ke ma hadda ke sam baki san amfanin mace ga mijinta ba, kin saki mijinki wata sai juya miki shi take sam kin kasa jawo hankalin sa zuwa gare ki, gashi dai kinje kin sha gyara amma sam bashi da amfani tunda duk da gyaran naki kin kasa jawo hankalin mijinki gare ki, kullum sai dai a ganki a ɓangaren wannan yaro (isma'il) kina bibiyar fannah amma ke mijinki ko a jikin ki



Haka kika ga fannah ta nayi wa nata mijin, wallahi har da laifin" faɗa ta shiga min tare da ƙarawa wai duk laifi na ne na kasa shishshigewa sabit balle har in samu fada a wajen sa ya jani jikin sa har ya banbance tsakanina da badia


Kallon baiwar Allah nan kawai na tsaya yi lallai so sone amma son kai ya fi, wato ma lefi nane, ni bata san ko a ƙafa a ɗaura min wannan koɗaɗɗan ɗan natan ba sai na yanke na gudu balle har a kai ga faranta masa ko shishshige masa Allah ya kyauta min Allah ya tsare ni



Sai da ta gama faɗan ta sannan ta sallemi tare da ja min kunne akan in fara jawo hankalin sabit zuwa gare ni,


Binta kawai nayi da to amma kuma nace hmmm wayaga wallahi badai ni asmaun ba sai dai wata ai ni da sabit hayhata hayhata



Na koma ɗakina ina tunanin abinda mummy take son nayi wa sabit wato da yake abin son kai ne, ni da nake mace nice za a ce inja hankalin sa me makon amatsayin sa na namiji ace ya fara ɗaukar action ni kuma a matsayina na mace a bani damar duba wa ko zan iya manage da shi amma sam abin ba haka yake ba nice ma zan cusa kaina lallai mummyn nan har yanzu baki san wace asmau ba



Da yamma ina cikin yin dinner na kusa kammalawa ma sai naji call na intercom ɗin kitchen ɗin yana ringing kasancewar ba kowa ya sani zuwa ɗauka,


"hello" naji ance ko bacci nake yi nasan muryar ɗan renin hankalin nan amma sai na nuna ban sani ba


"hello waye" na amsa

"mijinki ne" na ji ya bada da amsa, murmushin mugunta nayi sannan na mai da masa martani bayan na maƙe muryata na shake ta sannan na gyara ta


"kana nan ƙalau ya gidan da komai da komai wallahi ina kewar ka sosai" ina jin ɗan murmushin daya saki sannan yace min

"da gaske"

"zan maka ƙarya ne kasan ni kasan zuciyata kasan banda wani sai ka, lkc kawai muke jira ya kasance mu kasance waje ɗaya har abada"


Daɗine ya lulluɓe shi kamar me, ni kuwa da yake nasan abinda nake shukawa ya sani ƙara sakin baki sai faɗa masa kalaman soyayya nake yi shi kuma yana biye min sai can dana ga ya shiga sosai sai nace masa


"ya maidugurin kuwa, Allah dai ya san ƴam matan can basa kalle min kai dan sunga bana kusa da kai" shiru yayi na ɗan wani lkc yai jim


"ABDUL baka jina ne" na kuma maimaitawa


"uban waye abdul" na ji ya faɗa, sai da na ɗauke phone ɗin daga kunne na na ƙyalƙyala dariya ta sannan na mai da ta na kuma cewa

"ba abdul ɗina bane na maiduguri ba, don Allah waye ya kira ni sannan yace min matar sa" wani ƙasurgumin zagi da luluƙo ya antayo min ni da abdul ɗin ya sani cire phone ɗin daga kunne na na kuma ƙyaƙyacewa da dariya



"Abinda kike yi Kenan dama da auren ki to yau Allah ya tona miki asiri kuma wallahi zaki san baki da wayo" sai da ya gama bala'in sa sannan ya kashe wayar



Dariya na ci gaba da yi gobe ma ka kuma kirana, ni abin ma dariga ya bani wai mijin ki ne, ko ta ina ya zama mijin nawan mijin suna dai girki na na cigaba da yi ina yi ina maimaita conversation ɗin mu ina dariya ni kaɗai lallai yau na kunna sabit



********************


Takaicine ya ishi sabit har ya rasa yadda zai yi, tun yana kwance ya tashi ya zauna ya kuma kwanciya amma duk da haka ya rasa mafita, ya ze yi da wannan ƴar iskar yarinyar


Wai da auren shi akanta amma take kula wani ƙato, har da cewa lkc kawai take jira su kasance tare, kenan da take nufin kashe auren da gaske take



Gaskiya da sake ya za ayi ma in bar ta ta tafi, lallai ma dole ne in samu mafita, mummy ce kawai ta faɗo masa a rai, lallai mummy ce kawai zata iya kawo ƙarshen wannan lamarin



Miƙewa yayi ya nufi ɓangaren mummy sam be nuna mata komai ba kawai sai yace mata


"mummy kinga badia bata nan part ɗin nawa ba mace don haka me zai hana ki saka waccen yarinyar ta koma tunda akwai spare ɗaki a ƙasa sai ta zauna anan"


Daɗi ne sosai ya kama mummy har tana jin daɗi ita a tunanin ta asmau ce ta ɗau shawarar ta ta fara aikin da ta saka ta


"to shike nan auta ai dama tun farko kai kaso hakan kana da mata har biyu amma ki ɗige a guda gudar ma mara quality" ɓata ransa yayi shi sam har yanzu be ga aibin badia ba da mummy kullum take cikin kushe ta



Ko ma dai menene yanzu ba lkcn maganar badia a bane yanzu ta ƴar iskar yarinyar can ake yi



Mummy shawara ta ci gaba da bashi akan yadda zai kula da asmau da kuma yadda asmaun zatai masa rana da kuma yadda zata kula shi fiye da badiar


Jinta kawai yake yi amma yanzu ba lkcn wannan bane yanzu burin sa kawai yaga asmau a part ɗinsa ya koya mata hankali



******************


Sai da na gama dinner tsab sannan na zuba aka raba aka kai wa kowa nashi sannan na ɗauki na mummy domin kai mata


Ina shiga part ɗin ta tana zaune tana kallo nai sallama na jiye mata na tashi zan fita kenan sai ta kira ni


"asmau idan kin gama abinda kike yi ki tattara kayanki a yau ki koma part ɗin mijin ki da zama zaman naki a BQ ya ƙare, su ma ragowar ƴan uwan nakin na gaya musu daga yau koya ya dinga girkin sa kin dena mijin ki yace ki koma"



Tsayawa nayi na saki baki kamar wata wawiya ina kallon ta me wannan yake nufi kenan in koma ɓangaren sabit wulaƙanci ke nan sunfari sunfari zan dinga kwasa gaskiya da sake bazan iya ba


"mummy amma me yasa zan koma kin............" bata bari na ƙarasa ba ta hau yi min faɗa kamar zata ari baki, wai dama ni shegen taurin kai gare ni,


Wata macen ce mijinta ya gayyace ta ta koma ɓangaren ta a matsayin matar sa kamar yadda kowacce mace take da matsayi amma ta ƙi kina nufin kin ta zama kenan a matsayin cook ai dama wataran dolr ne ya nemi ki koma ki karɓi girki



Faɗa ta dinga min daga nan kuma ta hau faɗa min wai yadda mallaki zuciyar sabit cikin ruwan sanyi, sannan da yadda zan dinga masa biyayya tare da yin duk abinda ya sani



Duk wani faɗan ta ya ƙare ne akan yadda zan farantawa ɗan ta sabit sam bata damu da halin da zan shiga ba ƙiri ƙiri na nuna mata bana ƙaunar komawa amma hakana sam be gamsar da ita ba itadai in koma in farantawa ɗanta





Miƙewa nayi jikina a sanyaye na kama hanyar fita, sai naji mummy tana kiran me aikin ta wai ta raka ni ta taya ni haɗa kayana sannan ta raka ni ɗakina

"ai ba a bar amarya ta tare ita kaɗai ba ba ɗan rakiya"


Wannan kalmar ta amarya tafi komai ƙona min rai lallai ma waya ga amarya


Tas matar nan tasa na haɗe kayana na kwashe su ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login