Showing 78001 words to 81000 words out of 88726 words
Chapter 27 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt
min wallahi sai ta gane bata da wayo,
Haɗa kayana na fara yi maiduguri ma zan tafi,
Isma'il na kira nace yai mana booking flight ni da baaba da kuma yara zamu suna, sai dana gama komai sannan na tattara kayana naje gidan mummy na sauke mata annur sannan na kama hanyar maid.
Sai da na sauka sannan na kunna wayata, ina kunna wa naci karo da text ɗin sabit yana min faɗan wai bana jin magana bayan yace min ƙar in tafi sai ya zo
Forwarding pics ɗin ta aka turo min nai masa, bayan nayi copy and paste yadda zai gane daga phone ɗin sa aka turo min
Ƙanin anty fannah ne ya zo ɗaukar mu, ko dana sauka sam ban nuna mata ba itama sam bata kawo komai ba
Masauki guda akai mana inda aka sauke mu ɗakin da anty fannah take, kusan kwana mukai muna hira kasancewar bata san ba da san ran sabit na taho ba ya sa sam bata kawo min wani zancen yi min faɗa ba
Kuma ina ta sa ran sabit zai kira ni yai min wani bayanin yadda akai pics ɗin suna zo wayata sai naji shiru
Tun ina sa ran call ɗin sa har na haƙura, a haka na kwanta cike da takaicin rashin kirana da sabit be yi ba
********************
Da wurwuri muka tashi saboda ana ta shirye shiryen gobe suna duk wani gyara mun sha shi barin ma ni da biyu nake gyaran nawa
Kitson bare bari akain min wanda yake zuwa gaban nan sanna a tifke shi ya koma gefe bayan wanka da turare da nake ta sha
Duk wani gyara na tarar suna mun sha shi kawai jiran zuwan sunan muke yi, in ka ganni zaka ɗauka banni da wani damuwa amma can ƙasan zuciyata tana tunanin yanzu sabit yana nigeria faa
Amma sam be neme ni ba wallahi ni ma bazan neme shi ba, har la'asar muna ta hidimar mu duk da dai ni ba abinda nake yi ina kusa da anty fannah dai dai da yaran wallahi sai su wuni ban gansu ba suna can cikin gidan wajen mmn anty fannah itace take kular min da su
Ina zaune kawai naji sallama kamar muryar sabit, ina ɗagowa mukai ido huɗu da shi
Kunya ce ta kama ni na kaaa tashi daga inda nake,
"jibi ƴar ƙauyen nan dama haka karɓar baƙo" inji anty fannah
"ƙyale ta anty ni me laifi ne a wajen ta shiyasa na tako da ƙafata in bata haƙuri"
"au baki daina faɗa da mijiba, dama shine dalilin daya sa kika taho lallai ma asmau ashe bakyaji magana dama" inji anty fannah
"don Allah ki ƙyale ta wallahi am at fault kuma na karɓi laifi na kuma nazo bada haƙuri ne"
Ƙarasowa yayi kusa da ni ya tsugunna inda ni kuma kai na yake ƙasa
"baby na ayi min afuwa"
Faɗawa jikinsa nayi wallahi babu ƙarya nayi missing ɗin shi sosai
Wata kyakkyawar runguma naji ya min wanda ya sauke ajiyar zuciya tare da fara shinshina min wuya na wanda ya tsumu da ƙamshi
"anty wannan ƙanwar taki ta sha gyara sai kace wata amarya" ya faɗa muryar sa a shaƙe
"sabit ko dai in muku gadin ƙofa ne don naga daga dukkan lamu anan zaka bada tsarabar taka"
"wallahi da kuwa kin kyauta" ya faɗa
Wallahi duk a tunani na wasa suke sai naga ta ɗauko mukullin ɗakin ta miƙo masa
" ka saka key ni kuma zan zauna daga can ɗakin ina kallo ɗakin don kar a katae muku hadda"
"anty wasa fa yake yi" na faɗa
"waye yake wasan" naji sun haɗa baki sabit hadda zare ido
Shiru nayi, ban tabbatar da maganar su ba sai dana ga anty fannah ta fice shi kuma ya mai da ƙofa har da key sannan na tabbatar da rashin kunyar sabit
Tsere muka fara yi da shi a ɗakin
"wallahi ni kunya nake ji"
Yana bina yana dariya
"in banda abinki ko min yi wani abu ko bamuyi ba ai duk ɗaya ne ba gwanda munyin ba in yaso baza mu musa ba"
"wallahi ban yadda ba wayo zakai min" na faɗa ina zame wa a lkcn da ya kai hannu zai cafko ni
Taku ɗaya yayi ya cafekeni ya ɗaga ni sama inda ni kuma ina ta wuntsile wuntsile ne na ina ce bana so bana so
Sauke ni yayi dai dai fuskar sa yace min
"baby na bakya so na"
Yadda naga ya nutsu ya sani ni ma shiga taitayi na
"ina sanka mana" na faɗa ina shigar da kaina jikin sa
"to me zai hana a barni in nuna miki yadda nai missing ɗinki"
Ban tanka masa ba hakan ya bashi dama fara kwance min tsarabar da ya taho min da ita 😜😜😜😜
*******************
Lallai gaskiya sabit yai wani abu wai shi missing ɗina, don haka ya dinga min kuka, yana roƙona kar in sake in kuma cewa zan rabu da shi
Wallahi sosai ya bani tausayi, inda nima daga ƙarshe na tausaya wa kaina don kuwa tas sai dana biya bashi ba sassauci
Sai da mukai wanka sannan ya buɗe ƙofar inda yace min in kira anty fannah yunwa yake ji, tooo fa anan ake yin ta wallahi bazan iya fita
Babu yadda be yi da ni ba amma naƙi wallahi kunya nake ji, sai daya gaji da tsokanata sannan ya ɗauki wayar sa ya kira ta wanda bata daɗe ba sai gata ta shigo
"haka da wuri na ɗauka sai kun yi awa uku haka"
"wannan ƙanwar taki itace ta hana mu sake wa da yaya ma ta yadda" nintsini na mannara masa, zabura yayi kamar da gaske
"kinga har da mintsini na a gaban ki"
Harara ta doka min wacce ya sani ƙaɗa shigewa jikin sabit shi kuma jin daɗin hakan ne ya sashi ƙara rungume ni
"sai wani shishshige mishi kike yi sam baki iya saukar baƙi ba ko ruwa balle abinci amma kin iya shishshige masa"
"kai anty wallahi ba haka bane"
"ke kika sani bari inje in kawo maka abinci in kuma kafin in dawo kun kuma komawa sai a tabbatar an rufe ƙofar don kar inga abinda ya fi ƙarfin idon"
Ta fita tana dariya, ƙara jawo yayi jikin sa ya fara wasa da kitson da ke kaina yana faɗa min yadda yai kewa ta sauraren shi kawai nake yi ina ƙara tausaya masa lallai tabbas yayi kewar tawan
Har ta kawo abincin ta zauna yana ci muna ɗan taɓa hira har ya gama sai da ya gama sannan ya miƙe suka shiga ciki domin gaisawa da mutan gidan lallai ma aka ce namiji ba kunya
Ba shi ya tashi barin gidan ba sai kusan ƙarfe goma, inda anty fannah tace min in bishi sam ban so hakan ba amma sai dabta matsa min na bishi inda na bar yaran a nan gidan su wajen baaba
Hotel muka je muka kama, wanka kawai mukai sannan muka kwanta wanda duk wata maganar sabit bata wuce ta kewa ta da yayi ba,
Kashegari da sassafe ya kama hanyar abuja, inda ni kuma ya mai dani gida, da faɗa muka rabu da shi saboda badia ce ta kiɗa shi tana masa magana har ya tashi ya kama hanya ba shiri
Baza ka taɓa canza wa ba sabit na faɗa a raina
Kasancewar ina jin haushin sa yasa sam ban samu damar kiran sa ba balle inji ya ya sauka
Sai wajen ƙarfe goman dare duk hankali na yana kan sabit ko ya ya sauka wallahi tunda ya tafi, hankalina yake akan sa na so ace in sa ya ya sauka amma sam banna son kiɗan shi saboda nasan suna tare da badia kuma sam bana son kiran shi idan suna tare kamar yadda bana son ta kira shi idan muna tare da shi
Wayar anty fannah ce tayi ringing yadda naga ta kalli wayar tai murmushi yasa na san isma'il ne ɗauka tayi da sallamar ta suka gai sa
Sai naji tace gata nan, nan da na gabana ya faɗi me ya faru,
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai naji tace me ya same shi
Tuni na gama tsurewa Allah Allah nake yi ta gama waya ta faɗa min menene, Allah ya sa ba wani abun ne ya samu sabit ɗin ba
Sai da taga ma sannan ta kalle ni tace min asmau sabit ne yai accident a abuja yanzu yana asibiti be ma san wanda yake kansa ba
Wani irin kuka ne ya ƙwace min sabit ɗin nawa ya Allah kar ka kashe min sabit ɗina ya Allah ka dube ni marainiyar ka kar ka raba ni da mijina ya Allah ka dube ni ba don halina ba ina faɗa ina kuka ina haɗa kayana
"anty wallahi tafiya zanyi wallahi wajen sabit zanje inga halin da yake ciki"
[10/05 09:53] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*
🍷🍽🥛
👩🏽🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽🍳
🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠
ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
*ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN* 🤲🏻🤲🏻
*HIKIMA WRITERS ASSO.*
P⃗a⃗g⃗e⃗ 28🌹
Satin twins 2, sabit ya tattara yanasa yanasa ya koma lagos duk wannan zaman da yayi ko kaɗan baya samun daman ta, wai ko sakin fuska ko kaɗan
Idan yana parlour to ina ɗaki, sam ba abinda yake haɗa mu, amma ta ɓangaren yara kuwa kusan shi yake renon su
Don ko cikin dare sai kawai in ganshi a cikin ɗakin nawan ya zo ganin su sam na ƙi sakar masa fuska, sai dai kawai ya ta abinsa shi kaɗai ni dai ido ne nawa
Ko ran da zai tafi ya shigo ɗakin nawa inbawa hoor nono
"me jego mu office yayi kira faa, in shaa Allah yau zan koma bakin aiki na"
Kamar yadda fuskar nan tawa take haka na bar ta sannan na bishi da
" Allah ya kiyaye hanya"
"babu wani kalmar i will miss u ko love u" ƙara shan kunu nayi wanda hakam ya sashi cewa
"ayi haƙuri naga alamar har yanzu ba a sakkowa ba ni me lefi ne don haka bazan yi fishi ba zan jir har sai lkcn da Allah ya sa kka sakko dan kanki kika fahimcin irin son nake miki........
Ɗago ido na nayi na kalle shi dana ji ya furta kalmar sooo ɗin nan
"kina mamaki ne wallahi asmau i really doo love u, u r d only one i doo love"
Wai love kaji kuma zance, kamar da gaske, hmm sabit kenan u love abinda kake love de amma badai ni asmaun ba kuma wallahi abinda kake love ɗin is d last thing da zan baka
Surutan sa ya ƙaraci yi daga ƙarshe daya ga ba reply ya miƙe ya fice jikin sa ba ƙwari, a daidai bakin ƙofa ne na ce masa
"Allah ya kiyaye hanya"
Dawowa yayi fuskar shi ɗauke da murmushi, ɗan kiss ya sakar min a lips wanda ban bar shi ya daɗe ba na ɗauke fuska ta tare da ƙara shan kunu
"sorry na kasa haƙuri ne" ya faɗa, hannun shi ya kai kan fuskar hoor wacce ta daddage sai tsotsar mama take tayi
"my lil princess a sha a ƙoshi a rage wa daddy" ya faɗa da murmushi a fuskar sa, ban tanka mishi ba sai daya gama wasa da ita sannan ya juya ya fice
Ina jiyo shi shida annur a falo suna hira shi da annur a falo yana ta masa gwarancin sa shi kuma yana ta biye masa
Sai da ya shafe kusan rabin awa sannan yai sallama da su mummy wacce tunda akai haihuwa bata tafi ba
*******************
Har kusan yamma ina ta sa ran inji mummy tace sabit ya sauka ko wani abun amma na ji shiru wannan ne ya sakani fitowa parlour ɗin suna zaune ita da baaba suna hira
Baaba tana yiwa twins wankan yamma
"me jego an fito ne" inji baaba
"wallahi zaman ɗakin ba daɗi"
Na nemi waje na zauna kusa da mummyn
"mummy ya matafiya sun sauka ƙalau"
Tsayawa tayi tana tunani can sai tace
"ke yanzu tunda suka sauka baki kira kin tambaye su sun sauka ƙalau ba, haba asmau ya ina ganin hankalin ki ace mutane sun taho daga kano amma har su koma baki kira ba"
"mummy bafa su ba ai na kira waɗancen"
Na bata amsa, wallahi sam bana son ina damun kaina da lamarin sabit amma bazan ignoring ɗin shi ba
Ko da dai ace bazan masa directly ba nayi masa indirectly
"waɗannan matafiya ne kuma suka kuma tafiya bayan ƴan uwanki"
Murmushi nayi tare da sunkuyar da kaina ƙasa
Baaba ce ta ɗago ni sai naji tayi dariya tace
"lallai mmn annur wato kunya ake ji, hjy ai me gidan ta take tambaya"
Murmushi mummy tayi sannan tace
"ƙyale ta baaba tsab na fahimci abinda take nufi, yo ni ina ruwana da wani mijinki ba ke ya kamata ki kira shi kiji ya ya sauka ba"
Muryar anty fannah naji a bayana tana cewa
"lallai kam mummy ke dai ai kina gama naki tunda yanzu yayi aure ai haƙƙin kula shi ya koma kan matar sa"
"kai anty fannah don Allah yanzu har da ke ake wannan abin, don Allah kira shi muji ko ya sauka lfy"
"wallahi bazan kira ba inkin matsu ki kira shi" inji anty fannah
Kallon mummy nayi wacce kafin ma ince wani abun tace
"kar ma ki ɓata bakin ki, kije ki nemi mijinki inkuwa ba haka ba wallahi babu me kira miki shi"
Tsayawa nayi ina kallon bayin Allah nan yanzu so suke yi in zubar da ajin nawa in kira shi
"malama dalla can tashi kije ki kira shi ana so ana kasuwa Allah ya haɗa shi da matan lagos masu shegen naci"inji anty fannah
Da gudu na na miƙe nayi cikin ɗaki yanzu ace sabit zak ƙara aure ai ƙaramin hauka zanyi
Kasa kiran shi nayi don haka sai nayi masa text
```ka sauka lafiya```
Be fi minti biyu da text ɗin ya shiga ba sai ga call ɗin sa ina ɗauka yace
"baby na kina nan ƙalau"
"ba babyn ka bace asmau ce" na faɗa cike da takaici
"oh ai na ɗauka baby ta ce to ya kike mmn twins"
Wani ƙululun baƙin ciki ya zo ya tokare min a maƙogwarona da ƙyar na haɗiyi miyan da ke baki na sannan nace masa
"ka kira babyn taka kuyi hirar kawai sai anjima"
Da sauri sa ya dakatar da ni
"haba my husna ai kece babyn tawa daga ke ba wata, wallahi tun da na sauka nake son kiran ki amma bana sƙn takura miki ban ɗauka zaki damu ba don baki jini ba"
"ba damuwa nayi ba dama mummy ce tace bata sani ba ko ka sauka, shine nace bari in kira ka inji"
Murmushi yayi don tuni ya ranfo jirgin natan yana sauka yayi wa mummy waya akan ya sauka ƙalau amma shine wai take masa wannan gidogar
"kai amma wannan mummyn ta kyauta wannan ya nuna an damu da nine ko, kai amma naji da daɗin da wannan mummyn ta nuna damuwar ta gare ni"
Shiru nai masa inda shi kuma yai ta tambayar yara ina bashi amsa a taƙaice, mun ɗan jima muna waya daga bisani kuma mukai sallama
Shike nan tun daga lkcn sabit ya tsiri kirana safe rana dare kamar baya jin kuɗin wayar sa wani lkcn idan ƴan jujun suna kaina yana kira sai in haɗa shi da annur yai tayi masa gwarancin sa wani lkcn kuma in ɗauka
Sam baya gajiya da gaya min ni kaɗai ce a zuciyar sa nakan rasa gane gaskiya ne ko ƙaryar sa ce, itama badiar haka yake mata ko a a
In dai aka ce kana auren me mata sai Allah
Rannan ya kira ni a waya da yamma
"baby na kiyi min addua akwai wani course da zanje turkey inyi na wata biyar in shaa Allah nan da wata ɗaya ne tafiyar, kuma ke zaki min rakiya sai mu tafi tare da su annur ko"
Daɗi ne ya lulluɓe ni don wannan ne ya nuna ana yi da ni, ranar mun sha hira kamar baza mu gama ba har sai da wayata tai zafi sannan muka kashe
Kamar da gaske na fara sakin masa jikina, saboda tafiyar da yace za ai dani ko ba komai zan nuna wa duniya da ni miji yake yayi
Na so ace a lkcn ya kuma min maganar tafiyar amma sai naji shiru har gashi watan ya kusan cika sai na ɗauka ko ga fasa tafiiyar ne don haka nima sam sai ban ƙara yi masa zancen ba don kar yace abin ya dame ni ne, tunda dai haɗ yanzu bama ƴar hakan da shi
Kullum ya kira a waya shine yake hirar ni kuma ina sauraro ko bada amsa amma sam bana taɓa kawo mana topic
*******************
Mummy sai da mukai sati huɗu sannan ta tafi gida wai ai yanzu zamu iya kula da su, amma sai ta ƙara kawomin ƴar aiki amma wannan karan ƙarama ce
Rannan da yamma muna zaune a falo muna hira da anty fannah sai ga