Showing 48001 words to 51000 words out of 88726 words
Chapter 17 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt
shan ƙwayar kullum to gaskiya zan so hakan"
Duk da dai mummy taga rashin dacewar hakan amma kuma bata iya yiwa ƴaƴan ta musu, sam bata so ba amma kuma sabit be san a a ba
"to shi kenan amma baka tunanin ya kamata ka bari ko ɗaya ne ta gwada kafin a hanata"
"mummy akwai probability na asmau zata haifi baƙin ɗa kuma abinda bana soo kenan inda ace dukkan chances ɗin na fararen ƴaƴa me da zan fi kowa murna amma baƙin ƴaƴa inyi yaya da su"
Duk yadda mummy ta so hana abin amma sam sabit ya ƙi yadda ba yadda ta iya haka ta karɓa tare da yiasa alƙawari kullum asmau zata dinga shaaa
Sulale wa nayi na zauna a ƙasa gabaɗaya duk wani service nawa ya ɗauke, shin wai baƙi lefi ne da mijina baya son kalar nan
Na ɗauka Allah ne ya hallicce mu kuma yake son ganin mu a haka, kallon skin ɗina yayi wanda yake a chocolate colour, wanda a kowane lkc yake glowing
Kusan sai dai in ban fita amma sai an ta yaba kyau na amma wannan kyaun nawa sam baya burgr mijina, shi kawai baƙin nawa yake gani
Sam be damu da abinda yake cikin zuciyata ba, jin takun sa ya sani miƙewa a tare muka buɗe ƙofar falon
Sam ban nuna masa wani abu ba inda na miƙa masa agogon nasan sannan na shige don gaida mummy
Tana zaune da sachet ɗin maganin a hannun ta tana kallo, tana ganina sai ta ɗan firgita amma kuma sai ta ɗake
Zama nayi sam sai na nuna mata ma ni ban san me ake ciki ba, gaisawa mukayi sannan na miƙe zan fita
"asmauk naji ta kira ni, komawa nayi na zauna sannan nace
"na'am mummy kina son wani abun ne"
"sam ko ɗaya maganine dai na samo miki, naga ƴar uwar ki har yanzu bata haihu ba shiyasa nace bari na samo miki magani ke sai ki dinga sha ko a dace"
Murmushi ne sosai a fuskar ta da badan naji komai ba da abinda zai sa ince ƙarya ne, tashi nayi na shiga kitchen na ɗebo ruwa na kawo
Guda ɗaya ta bani na haɗiya da in haihu da sabit ɗan ya hanani barin sa gwanda ban haihu da shi in yaso in lkcn tafiya ta yayi babu abinda zai hanani tafiya
Hawaye ne taf ido na wanda a hankali suka dinga gangarowa duk wannan abunda nake wa sabit be sa shi ya fara so na ba to sai yaushe, shin wai baƙi laifi ne
Ya Allah ka dube ni ka saka min cutar wa nan da nake fuskanta ba tare da wani hakkin na ba, ganin ina kuka ya sa mummy tambayar menene
"ba komai mummy kawai da ina farin ciki ne yadda kike nuna min soo" sanyi jikin ta yayi ta jawo ni ta rungume ni sannan tace
"wani lkcn ni kaina nakan yi judging abinda nake yi amma i cant help it, wataran idan kika haihu zaki fahimci halin da nake shiga in terms of deciding wat mah kids want"
Sam ban fahimci abinda take nufi ba amma na san cewar ita uwa wacce bata saba kwaɓar ƴaƴanta ba balle ta nuna musu sun yi ba dai dai ba, wannan shine weekness ɗin ta
Her weekness is her boys kuma ban taɓa jin haushin ta ba saboda kowa a duniyar nan yana weekness ɗina sa
Amma wannan karon gaskiya ta kaini bango sam na daina ganin mutumci ta at least in ɗan ta ya tashi yin abu wanda tasan be dace ba ai sai ta kwaɓe su ko amma sam ba haka take ba
Tashi nayi na kama hanyar part ɗin mu ina shiga ɗakina kawai nayi, na kwanta kuka ne ya ƙwace min lallai maraici be yi ba
Inda ace iyayena suna nan a raye da ko hakan zata same ni zai kasance ya zo min da sauki, amma yanzu bani da wanda zan tunkara
Don ko idan na faɗa wa anty fannah hana ni shan maganin zata yi tace sai na yadda na yi cikin ni kuma kamar yadda baya son haihuwa da ni, nima haka na tsani haɗa jini na da shi, wani wahalallen bacci ne yayi gaba da ni
Sai la'asar na tashi gabaɗaya bana jin daɗim jikina da kyar ma nayi dinner, ko da na gama ma sam banci ba shayi na haɗa na sha sannan na kwanta sai bacci
Ina cikin bacci naji mutum yana tashina tare da balbale ni faɗan nayi bacci ban jira shi ba
Kaina ciwo kawai ya ɗauka sakamakom tashin nan da yayi min, toilet na shiga nayi wanka kamar yadda na saba in yazo nayi bacci nayi brush sannan na fito
Yana matsowa kusa da ni da ƙamshin turaren nan nasa ya doki hanci na sai naji amai yana taso min, danne zuciyata mayi amma a gaskiya na ina cutuwa
Yana shirin ɗaga ni wani yunƙuri da nayi sai amai ya fito gabaɗaya na wanke masa fuska da shi, sai da na amaye duk abinda ke cikina sannan na iya maida numfashi
A gaskiya turaren nan ya cutar da ni dani dayawa, ido na a rufe banyi aune sai jin saukar mari nayi, na kuma jin wani a ɗayan gefe
Dafe fuskar tawa nayi na buɗe idon nawa, nan naci karo da fuskar sa wanke tas da amai na, duk da zafin marin nan da nake ji amma hakan be hanani murmusa wa Allah ya kara ya faɗa a raina
Ɗaga ni yayi ya shige toilet inda ya watsa ruwa yana fitowa ran shi a ɓace yace
"ki kwashe bedshit ɗin nan ki wanke min su tas idan na dawo da asuba na tarar da su ba a wanke ba a bushe ba zaki gane kuren ki"
Ficewa yayi daga ɗakin ni kuma na miƙe tare da kwashe kayan shinfiɗar na nufi toilet don wanke su, to me ya saka ni aman nan, ni ko kaɗan banci wani abun a zo a gani ba balle ince ko shi ya ɓata min ciki
Ina wankin ina tunani na, ko da na gama sai na fita waje na shanya su sannan na samu na tsarkake jikina ni ko ya gama ma oho masa, ban damu ba zani na na shinfiɗa sannan na kwanta
Asuba ta gari 😴😴😴😴😴😴🤤🤤🤤🤤🤤🤤
[10/05 09:52] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*
🍷🍽🥛
👩🏽🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽🍳
🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠
ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
🤲🏻 *ALLAHUMMA BALIGNA RAMADAN BIL IMAN*🤲🏻
P⃗a⃗g⃗e⃗ 19🌹
Da asubar fari ya zo lallai mutumin ya iya doka sammako tashi na yayi sannan ya karta min warning kar ya sake ya dawo daga masallaci ban gyara ɗakin ba
Wanka na fara yi sannan na ɗauko shayata na gyara ɗakin, sannan nayi sallah asuba, na idar ina lazimi ne ya shigo ɗakin nawa lkcn garin ya fara wayewa
Ƙamshin turaren sa ya fara dukan hanci ma wanda hakan ya sa zuciyata ƙara tashi, da gudu na ruga toilet na fara amai, har banɗakin ya biyo ni
"wane irin iskanci ne yake saki wannan aman"
"wallahi ban sani ba ni bama abinda na ci" na faɗa a marairaice
Matsowa yayi kusa da ni ya damƙi gashi kaina sannan ya ɗago min fuskata wani azaba naji ya ziyarci kaina fuskar nan tasa a tamke sam ba fara'a
"yaushe rabon ki da menstruation" ya tambaye
Shiru nayi don wallahi ni na manta ba calculating nake yi ba, indai yazo min shikenan in bai zo ba matsalarsa, ƙara jamin gashin nawan yayi wanda hakan ya sani sakin wani ƙara
"wallahi ban sani ba bana lissafi"
Sakin kan nawa yayi sannan yace
"ki yi brush ki fito ina jiran ki" brush nayi sannan na fito daga toilet yana kwance akan gadon, alamar inzo in kwanta kusa da shi yayi min sannan yace min
"kika sake kika ƙara min amai wallahi sai na zane ki"
"wallahi warin turaren ka ne bana jin daɗin sa shi yake sani aman"
"Wannan matsalar kice don baki isa in dena saka turare ba saboda ke"
Ƙarasawa nai kusa da shi na kwanta ina mai ɗauke numfashi na, Allah dai cikin ikon sa dai banyi aman ba amma kuma na wahala
Bayan ya fita ne naje toilet na kwarara shi kamar ba gobe kai wannan amai sai kace me, kodai ciki gare ni 😱 ni mau naga ta kaina. Ciki a wannan marrar gaskiya dole ne in faɗawa anty fannah don ta san abinyi
********************
Sabit yana fita daga ɗakin asmau ɓangaren mummy ya nufa, fuskar nan tasa kamar an aiko masa da labari mafi muni
Tana zaune tana lazimi ya shiga ɗakin, sai da ta idar sannan ta juyo ganin yanayin fuskar sa tasan ba lfy
"auta lfy me ya faru"
"mummy ina jin fa yarinyar nan ciki gareta kuma wallahi bana so"
"wake nan kake nufi kardai asmau"
"to in banda abin mummy cikin wa zan ƙi inba nata ba gaskiya i cant stand being a father to her black kids" ya faɗa bayan ya firzar da wata iska daga bakin sa
"sabit baka ganin ya kamata kayi murna da farin ciki ganin cewar an daɗe ana neman haihuwar amma sam badia bata haihun ba ɓarin ma da take yi kwana biyu shiru"
"mummy badia zata haihu tunda ta taɓa amma ni gaskiya banason baƙaƙen yara, itama a matsayinta na matata ina manage ne da ita sannan kuma ace nazo na haɗu da ƴaƴa baƙaƙe gaskiya bazan iya ba bana sooo"
Tsayawa mummy tayi sam tama rasa abinda yake mata daɗi, wai sai yaushe sabit zai hankali ne ya fahimci halin matansa sam ita bata ga alamar badia tana son haihuwa ba, asmaun kuma da zata iya haifa masa ko nawa ne batare da ta gaji ba shi wai baya son kalar ta, hmmmm wannan abun yanzu gaskiya ya fara isar ta
"To yanzu me kake son ayi"
"mummy ai ba akan ta aka fara cikin da ba a so ba kawai sai a zubar da shi sannan sai in ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki akan ta"
"kana nufin zaka zubar wa da asmau cikin da ke jikin ta, haba sabit me yarinyar nan tai maka haka dat u soo much hate her"
"mummy sam baki fahince ni ba bana son baƙin ƴaƴa, farare nake so kamar ni, ki duba cikin gidan nam kowanne ɗan sa fari ne haka kurum akai na sai a fara haifar baƙaƙe kawai ƴaƴa na su zama bare a cikin dangi gaskiya banyi wa ƴaƴana wannan planning ɗin ba ina son su saje a cikin dangi"
"to gaskiya ba da ni ba, duk yadda kaga zaka iya kayi tayi amma ni na riga na dawo daga rakiyar ka kullum am trying my possible best inga na nuna maka amfanin da darajar yarinyar nan amma kullum sai ƙara botsarewa kake yi to wallahi kaje kayi duk abinda zakayi amma banda ni aciki"
Tana gama faɗar hakan ta miƙe tayi ficewar ta tare da barin sa a falon, sam be tsammaci hakan daga wajen mummyn nasa ba ita me goya masa baya akan komai da yayi amma wai yau itace ta zaɓi wata akan sa,
Lallai dole ko menene sai ya zubar da wannan cikin na asmau don bazai yadda ya haifi baƙaƙen ƴaƴa ba, wayar shi ya ɗauko sannan ya kira wani abokin sa likita ne, sun jima basu haɗu ba
Abokin nasan ya kasance me shegen neman matan tsiya wannan ɗabiar tasan ce ya sa suka ɓata da sabit ɗin har suka raba hanya, yasan tabbas indai yana neman mata to bazai hana sanin yadda ake zubar da ciki ba
Ringing ɗaya abokin ya ɗauka tare da cewa
"manya ashe za a neme mu"basar wa sabit ɗin sannan ya fara gaishe shi
Bayan doguwar gaisuwa da tambayar juna iyali sai sabit yace masa
"aboki na har yanzu ana halin ne ko an daina"
"wallahi sabit tunda matata ta haifi ƴa mace na sallama, sai dai ɗan abinda ba' a rasa ba amma bana ɗaukar yara sai waɗanda suka jiƙu a abin kaga ban farka ba balle a farke min tawa" ya ƙarashe zancen nasa cikin shaƙiyanci
"ashe dai ba a dena ba" inji sabit
"yo me za a fasa mutuwa ko hisabi muna dai fatan denawa kafin mu tsufa, don kar a tsufa kuma ana bin ƴaƴan ciki"
"Allah ya shirya ka wato kai abin ma wasa ka maida shi ko to Allah ya baka sa a kar ka shiryu ɗin" inji sabi
"kai fa ɗan iska ne ya ina neman shiryuwa amma kana min wani fatan, wai ma meye na nemana nasan dai ba halin da nake ciki kake son jiba"
Shiru sabit ɗin yayi don shi sam be ma san ta inda zai fara ba, can dai da ta matse shi sai yace
"wallahi abortion nake son ayi wa wata ban sani ba ko kana yi"
"ɗan iska kace kaima kayi joining grp ɗin namu ya akai haka ta faru bakwa using protection ne"
"wane grp ɗin naku Allah ya kikaye ni, kai in kasan inda za ai min kawai ka faɗa min bana son long story" ya faɗa a fusace don yanzu haƙurin sa ya fara ƙarewa
"sorry bro abin bai kai nan ba kawai ka shigo asibitin mu ana yi ni ma da kaina zan mata kar
ka samu damuwa"
"kai ka isa wallahi baza ka taɓa min matata ba, in kuna da macen da zatai aikin ka haɗa ni da ita in kuwa babu in nemi wani"
"haba bros kawai ka taho, amma me yasa kake son zubar wa da matar ka ciki"
"ai ba exams nake ɗauka ba balle ka tambaye ni kowane question sannan in amsa wannan personal matter ɗina ne, ko kana so in dinga bayyana sirrin gidana gare ka" inji sabit
"sorry bros kawai kuzo in shaa Allah kafin nan na tanadar da komai ready har dr. ɗin"
"ok see u, zan shigo da daddare"
Sallama sukai sannan sabit ya koma part ɗin sa, yai wanka ya fice ko abinci ma be tsaya ci don yarinyar haushin ta yake ji sosai wai tayi ciki to garin ƙaƙa hakan ta faru lallai yayi sanya dayawa
Jiya jiyan nan yakai wa mummy pills akan ta dinga bata amma wai a yau wai a tashi da ciki, kai wallahi da sake bazan iya ganin baƙaƙe a matsayin ƴaƴana ba
********************
Sai gab da la'asar sannan ya dawo, ina kitchen ya same ni ina wanke wanke
"idan anyi sallah la'asar zamu je a sibiti a duba ki wannan aman naki ban gane shi ba"
To kawai nace na cigaba da aiki na, sai da na gama sannan, nai wanka na ɗauro alwala na gabatar da sallah la'asr
Sannan na je falo na shi yana zaune
"na gama" na faɗa
"muje waje ki jirani gani nan zuwa"
Wajen na fita be wani daɗe ba sai gashi, motar muka shiga muka kama hanyar asibitin hankali na a kwance nasan dai me za a ce ciki gare ni shine dai be san ina da shi ba
Muna ƙarasawa asibitin ya kira wani abokin sa a waya sai kuwa gashi kamar daman mu yake yi, gefe sabit ɗin ya ja shi suka fara ƙus ƙus ban san me suke cewaba daga ƙarshe dai naji abokin yana cewa
"haba bros ai nai mata bayani baka da matsala"
Sai da suka gama gulmar su sannan suka ƙaraso, shi yayi mana jagora har wani ɗaki in da muka tarar da wata likita tana zaune akan wata kujera
File aka buɗe mana sannan ta fara mana ƴan tambayoyi ina bada amsa iya sani na,
Sai da ta gama rubuce rubucen ta sannan tace min in kwanta a kan ɗan gadon da ke ɗakin, kwanciya nayi sannan ta ɗaga min rigar da ke jiki na
Wani abu ta matsa min akan cikin nawa wanda yake a shafe kamar ba komai a cikin sa sannan ta kunna ƴaɗ computer da ke kusa da gadon ta ɗauko wani abu tana goga shi a kan cikin nawa tana kallon cikin computer
Sai da ta gama sannan ta bani tissue wai in goge, in sauko, hakan kuwa nai, ƴan rubuce rubucen ta ta kuma yi a file ɗin nata sannan tace
"positive ya nuna cikine amma kama son ayi proceding da allurar"
"abinda ya kawo mu kenan"
"ok bari in rubuta mata sai kuje ku siya sai nurse tai mata ai bazai bada wani matsala ba 6weeks kawai yake"
"ok mun gode" sam ban fahimci me take nufi ba na ɗauka tana nufin cikin bazai bani matsala ba don haka sai muka karɓi
Allura ce guda ɗaya muka siya sannan muka je nurses room akai min, allurar shegiyar zafi gare ta ga sagar da ƙafa, ko da muka fito sai muka kuma haɗuwa da wannan abokin nasa inda ya ce mana ba wani matsala in muna son zama mu zauna in kuma zamu tafi in matsala ta faru sai mu dawo
Sabit shine ya matsa mu tafi kawai don akwai abinda zai yi a