Showing 72001 words to 75000 words out of 88726 words
Chapter 25 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt
goben nan zata bar musu gidan nasun don tuni na sa an gyara mata gidan da zata zauna ta reni ƴaƴan ta sannan ta nema wa kanta rayuwa yadda take so, asmau wallahi sai na tsaya miki yadda sai kin tsaya da ƙafafunki yadda ba wani wanda nan gaba zai miki gorin gida ko wani, don kina haihuwa ma makaranta zaki koma ke ma kiyo ilimin da shi mijinki yake wulaƙan taki akan sa"
"wallahi daddy ba saboda bata da ilimi nake mata wulaƙanci ba" sabit ya faɗa da sauri
Sam daddy be bi ta kansa ya zauna yai tayi wa mummy faɗa akan itace ta ɗaure wa sabit ......... 🙊 har ya kasa riƙe iyalin sa
"kuma wallahi na faɗa maka kaje ka dawo da badia"
"daddy wallahi zan dawo da ita amma dan Allah daddy kar asmau ta bar gidan nan wallahi ban san ya zanyi da rayuwata ba in bata kusa da ni" inji sabit
"wannan kai ta shafa kana tunanin za a raba muku auren ne ku ci gaba da zama gida ɗaya wannan ba dani za ayi shi ba"
Kuka wiwi sabit ɗin ya dinga shi wallahi ko za a saka kanshi gabas a yanka wallahi bazai sake ni ba,
"wallahi daddy sai dai a rufe ni a gidan yari amma wallahi bazan saki matata ba, naji na yadda zan saki badia saki uku ma amma wallahi bazan iya rabuwa da asmau ba bazan iya sakin ta ba don Allah daddy ka barmin ita anan zan shawo hankalin ta ta fahimci cewar bazan iya rayuwa ba ita ba"
Shi kan shi daddyn jikin shi yai sanyi a yadda yaga ɗan autan nasa ya na wannan bayani tare da kuka shaɓe shaɓe kamar wani ƙaramin yaro
"daddy kai kuwa ka tausaya masa mana kasan fa shi sabit sam bai saba da shiga matsala ba tun yana yaro shi ba mai son tension bane, an dai hora shi ya horu kuma ya san cewar idan ya sake yiwa asmaun wani abu shima yasan ƙarshen sa"
Sakin baki daddy yayi yana kallon mummy tana wannan dogon sharhin nata
"lallai ma fatima wato na wani banza naki ne ɗa ko, lkcn da yake cutar ta wane hukunci kika taɓa ɗauka sai yanzu da kika ga ɗan nakin zai shiga gagari shine kike da bakin magana tooo wallahi ahir ɗinki da shiga wannan maganar, yanzu nine da yanke hukunci kuma duk abinda asmau take so shi za ayi"
Juyowa yayi gare ni
"asmau kina son zama da sabit"
Kai na aƙasa sam banji komai ba nace
"ni dai wallahi daddy nafi son in rabu da shi saboda sam banji daɗin zama da shi ba"
"shike na an gama magana, dama nace duk abinda asmau take so shi za ayi ki haɗa kayan ki dana annur gobe in shaa Allah ki koma gidan ki, sai ku zauna ke da fannah, tunda gidan flat biyu ne sai ki ɗau ɗaya ita ma ta ɗau ɗaya don kar ki zauna ke kaɗai"
Murna na dinga yi sannan na dinga yiwa daddy godiya, sabit kuwa yana zaune anan kamar an dasa shi ya rasa abinda yake masa
daka masa tsawa daddy yayi
"bazaka tashi kaje ka dawo da matar ka ba" a zabure ya miƙe yai waje jikin shi a sanyaye
********************
Badia tana zaune a ƙasan carpet ɗin ɗakin da ke falon su sai rusar kuka take tayi, ta rasa abinda ke mata daɗi
Ya akayi aka ce annur ɗan asmau ne bayan ƙwan ta aka dasa da shi, wayar ta ta ɗauko ta kira dr. da tai aikin abin takaici wayar a kashe
Asibitin ta kira akace mata ai dr. ɗin ta bar asibitin ta koma garin su wai wani matsala ta samu da wata patient ɗin ta shine ta gudu
Ko ba a faɗa ba tasan case ɗin su ne, kuka ta kuma rushe wa da shi ya akayi haka ya akayi ɗan ya zama na asmau wallahi sabit ya cuceta
Maman ta tana zaune a gefe ta zuba uban tagumi sam bata san lkcn da badiar ta cire mahaifar tata ba sai da ta gayawa mmn cewar asmaun zata zama surrogate mother ɗin su sannan ta sani
Sam da yake ita ma uwar ba me kwaɓa bace sam bata kawo komai ba kuma bata jiwa ƴar tatan takaicin cire mahaifar tatan ba sai yanzu
Kuka ta dinga rusawa tana ƙarawa, takaici ne yasa mmn nata tana jin kukan natan amma taƙi tanka mata
Sallamar sabit suka ji, da gudu badia ta miƙe ta yi kanshi ta cukume da shi ta fara kai masa duka
"munafuki dama ashe ka daɗe kana kwanciya da ita, da yake kai ɗan iska ne an mata dashe da ƙwai na, dr tace kar a kusan ce shi ne ka bi dare ka ruguza mana aiki wallahi kai zan kama sai ka biyani asarar ƙwai na da aka cire min"
Ya ji shaƙar nan sosai inda yake ƙoƙarin cire hannun ta ai kuwa ta ɗauke shi da mari ko kaɗan be ji kunyar mahaifiyar ta ya saka hannu ya kwashe ta mari biyu kyawawa, sannan ya rufe ta da kuda
Mmn ganin za ai wa ƴar ta lahani yasa ta saka ihu tare da kururuwa wai azo a taimaka mata za a kashe mata ƴar ta har gida
Har waje ta fice inda masu gadi suka je suka raba faɗan, badia bakin ta ko kaɗan be mutu ba sai zagin sa take tana ƙarawa tas ta zage shi ta uwa ta uba
Masu gadin ne suka jaa shi waje inda yaje ya shiga motar sa ya koma gida gaskiya baza ta saɓu ba shi dai wallahi sai an bashi matar sa,
Har ɗakin mummy ya shiga ya shigo ɗakin da nake ina ta haɗa kayana annur kuma yana zaune kusa da ni
Sam yaron ya kasa sakin jikin shi da kowa, wai wasa da zaka ga yaro yana yi ko yai ta guje guje ko kuma yai ta yawoce yawoce sam annur be san wannan ba
Shi dai yafi san kullum yana kusa da ni,
Banji sallamar sa ba kawai sai jinayi ya rungume ni ta baya
"asmau don Allah kar ki tafi ki barni wallahi duk abinda kike so zan miki, wallahi ko bawanki kike son in zama zan zama amma ida kika tafi ya zanyi"
Ban gama sauraren soki burutsun saba na yakice shi daga jikina don nasan innace zan saurari uzurin sa har ƙarshe ƙila ya karyar min da zuciya
"sabit ka fita ido na aure ne nace ma gama na ɗauka daddy yai mana katangar ƙarfe tsakanin mu, shin wai sai yaushe zaka san cewar ni da kai is over"
Dafe kansa yayi, yana saurare na ina kwaɓa masa duk wata magana data fito daga bakina, hmmm lallai ruwa ya daki babban zakara, sabit ne a da zai zauna ina kwaɓa masa be ɗauki mataki akai na ba
Mummy ce tazo ta janye shi jikin shi gabaɗaya ya gama mutuwa da maganganu na, ina kallon ta tana share hawaye da gefen zanin ta nace ai duk wanda yai shuka tabbas wataran dole ne yai girbi
*******************
Kashegari da sassafe muka kama hanyar sabon gidan mu da anty fannah sai isma'il
Flat biyu ne na ɗauki ɗaya suma suka ɗauki ɗaya, naji daɗin yadda tsarin gidan yake ɗaki uku ne a kowanne flat, kowane ɗaki da toilet ɗin sa
sai falo sannan kitchen da store, kuma kowanne ɗaki ya sha gyara sosai komai an saka, hatta kitchen da store ɗuk a cike suka, ɗaki ɗaya na ɗaukar mana ni da annur ragowar na rufe
Rayuwar abin sha'awa da daɗi sam babu wani hayaniya, idan isma'il yana gidan a flat ɗina nake kwana idan kuwa bayanan can wajen anty fannah nake tare wa wacce itama yanzu take laulayi
Duk da dai bata gaya min ba amma kana ganin yanayin ta kasan ta harbu,
Bamu daɗe ba mummy ta zo ta kawo min me aiki wata mata iya sannan ta kawo min duk wata siyayyar da tai min na haihuwa,
Mun sha hira da ita sosai inda take ƙara bani haƙuri akan sha'anin sabit, a bakin ta nake jin wai badia iyayen ta sin dawo da ita
Amma sam babu zaman lfy da ita da sabit kullum sai faɗa, wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare min wuya wato samun badia ne ya sa shi ko sau ɗaya be taɓa zuwa ganin mu ba ko
Sam ban ɓoye fishi na sai dana gaya wa mummy
"ai badia tafi annur shiyasa tunda muka tare be taɓa zuwa yaga ɗan sa ba" na faɗa
"ayya asmau ba haka bane, daddyn ku ne yace idan yaji labari daga gare ki cewar sabit ɗin yana takura muku da zuwa sai ya saka shi ya sake ki a take shiyasa ya ƙi zuwa, amma wallahi kullum kuna ranshi kullum sai yayi hirar ku" ta faɗa a sanyaye
"mummy to idan yazo ya ga ɗan sa sai in kai shi ƙara"
Murna naga ta nuna sosai
"kai amma naji daɗi sosai asmau lallai ke ƴar halak ce kuma in shaa Allahu zan sanar da shi ya zo ya dinga ganin ɗan sa"
Mun sha hira sosai da mummy dan bata tafi ba sai da akai isha ni nai mana girki taci tana ta santi wai tayi kewar abimci na
Har mota muka raka ta mukai sallama da ita sannan na dawo, kasancewar an kawo min me aiki yasa ranar nan kwana a part ɗina
Cikin dare na tashi da naƙuda, ni kaɗai nayi abuna kamar wasa sai gashi Allah ya sauke ni lfy
Baaba wacce mummy ta kawo sai jin kukan jaririya taji, ta fito
"ƴan nan ai sai ki ce min abin yazo amma sai kika yi ke kaɗai"
Ban tanka mata ba saboda duk da dai babyn ta faɗo amma wani irin ciwo nake ji kamar ba ayi abinba,
Janye jaririyar ta tayi wacce sai tsanya ra kuka take duba na kai ga jaririyar da ta buɗe bakin ta kamar me
Wani shegen murmushi nayi duk da dai ciwo naji na amma hakan be hanani murna da jin daɗi ba
Kalar da sabit yake sooo ne wato baƙi, baƙa ce yarinyar amma daga dukkan alamu baza ta kaini ba amma kuma sam babu alamar zatayi haske
Tsakanin ta farkon da ta biyu be fi minti biyar ba itama ta faɗo kamar su ɗaya sannan kalar su ɗaya
Wayyo ya zanga fuskar sabit idan yaji labarin na haifi baƙaƙen ƴaƴa lallai akwai drama a gaba
Tsab baba ta kimtsa mu ni da babies ɗina waɗanda abin takaici kamar su ɗaya da annur wada hakan yasa suke kama tas da bbn su
Sam na so ace ƴaƴa na da ni suke kama amma ba hakan Allah ya so sai ta ta shirya mu tsab sannan ta kama hanyar part ɗin anty fannah don ta gaya mata
[10/05 09:53] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*
🍷🍽🥛
👩🏽🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽🍳
🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠
ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
*HIKIMA WRITERS ASSO.*
P⃗a⃗g⃗e⃗ 27🌹
Ina kwance sai anty fannah,
"lallai me jego kice kina hanya amma shine ba a kira ni ina can na saki baki ina ta bacci"
Murmushi kawai nai mata, ƙarasowa kusa da babies ɗin tayi tana ƙoƙarin ɗaukar ɗaya
"lallai maa shaa Allah kalar mu kalar da sabit baya so zan ga yadda zai yi yanzu da Allah ya haɗa shi da kalar mu"
Murmushi na kuma yi
"wallahi nima anty tunanin da dinga yi kenan"
Tattaunawa muka dinga yi da ita akan irin reaction ɗin da sabit zai ɗauka idan ya ji labarin ƴaƴan baƙaƙe ne biyu ma ba guda ɗaya ba
Sai gab da asuba sannan bacci ya kwashe ni bayan na sha tea me kauri da anty fannah ta haɗa min
Ban san lkcn da anty fannah ta kira mummy ba nidai kawai naji muryar ta ne a kaina tana cewa
"maa shaa Allah fannah kin yaran nan wallahi gaba ɗayan su kama suke yi sabit"
"haka ne kuwa
mummy amma inda za ai rikici da shi idan yaga kalar su"
"hmmm fannah sabit ɗin daa kika sani na yanzu ba me tsirface tsirface ba na yanzu yayi laushi, jiya dana koma gida ake bani labari har get ta bishi tana zagin sa tare da ci masa mutunci,
Hmmm wannan ƴar iskar yarinyar da badan daddyn ku yace inya sake ta sai ya sashi ya saki asmau ba wallahi da tuni ya manta ya rabu da ita
Wallahi yanzu zancen da nake gaya miki tun daya fita tun jiyan har yanzu be dawo ba, a hanya ma ina ta trying ɗin shi in faɗa masa haihuwa amma wayar shi a kashe"
Tausayi ya bani wallahi sosai, kai gaskiya banji daɗi koman lalacewar sabit uban ƴaƴana ne kuma bazan so wani abun ya same shi ba
Tunda indai akwai wani ya same shi sai dai ƴan uwan sa su koka amma kuma ƴaƴan har abada a rayuwar su haka zasu kasance suna masu rashin uba
Tashi nayi na gaishe ta da fara'ar ta amsa min da
"sannun asmau abinda bamu taɓa samu ba kika kawo mana ƴaƴa mata, tunda aka faɗamin na faɗawa daddyn ku yake murna don ma yana da meeting ne da wasu turawa amma ana tashi zaki gan shi, suma ƴan uwan naku nasan yanzu zaki gansu"
Bata rufe bakin ta ba kuwa sai ga sallama
Dukkan mutan gidan ne suka shigo, dole ne ya sank fitowa parlour saboda yawan su
Sai hayaniya ake tayi tare da murnar samun mace a dangi, barin ma mummy ta ɗauki babbar ta goye ta baya duk wanda zai ganta sai dai ya ganta a bayan ta sai dai ƙaramar ce ake ta passing passing da ita
"mummy don Allah muga ta bayan ki" inji kishiyar anty fannah
"wannan da kuke ganin ta takwara ta ce shiya sa bana son a jagwalgwala min ita" mummy ta faɗa
Ana haka mazan ma suka ƙaraso amma banda sabit ko ba komai ai zan ji daɗi idan na ganshi ko amma sam be zo ba
Duk wanda ya zo gidan nan murnar samun ƴa mace yake a dangin nan, don kuwa har zuwa yanzu mummy bata da jika mace sai maza sai waɗan nan baƙaƙen dana haifa
Abinda ya min daɗi da ƴan uwan sabit da matan su shine babu wanda ya luɗa da cewar yaran.ba farare bane sam ba wanda ya kawo wannan
Kawai yaba kyan yaran suke yi, suna ƙara musu adduar Allah ya raya su cikin addinin islama
Ana cikin hakan ne daddy ya zo, kasancewar parlour ɗin a cike yake yasa sam bamu ji sallamar sa ba duk an saki baki ana ta hira akan jariran da Allah ya hana kowa a dangin ya ba sabit
Sai da daddy ya daka tsawa sannan aka san ya shigo
"haba tun ɗazu na shigo a miƙo min yaran in gansu amma kun saki baki sai zuba kuke yi kamar ƴaƴan kanya, dan Allah a miƙo min da baƙi nake a waje
Na kasa zaman meeting ɗin ma sai ce musu nake yi ba a taɓa haihuwar mace a gidana ba sau yau kuma Allah ya bamu guda biyu"
Sai da kowa ya dara da maganar daddy, is'mail da muktar ne suka fita da babies ɗin sai a lkcn mummy ta sauko babbar
Sunfi awa guda sannan suka dawo inda daddy yace
"lallai yaran nan daga gani da albarka suka zo, mutanen nan suna ganin su sukai mana signing contract ɗin da mukai kusan wata biyu ana ta fama akan ta, lallai in gama suna suna da rabo in shaa Allah, ko ba"
Mummy ce tace
"Allah daga zuwan su har ka fara nuna banbanci tsakani na da su"
"yoo ke ba tsohon hannu bace, kinci kuɗin kinci kuɗin har kin gaji sukuwa ai kinga sababbi ne"
Raha suka dinga yi tsakanin su inda wasu suke goyan bayan mummyn wasu kuma suna goyan bayan twins
Ni dai ina gefe murmushi kawai nake yi ina jin daɗin yadda suke nuna kulawa ga abinda na haifa
Sai da suka gama sannan ya tasa ƙeyar mazan suka fice inda aka bar gidan daga matan sai ƴaƴan su
Mummy ce ta sa anty fannah ta kaini asibiti ko akwai wani problem, muka je suka duba ni tas ba komai, sai dai magani da suka bani muka dawo gida
Gidan ƙin kyau yayi sai da kowa ya bar gidan da daddare sannan gidan ya dawo hayyacin sa
Mummy ce kawai bata tafi ba, wai ita ta dawo kenan sai bayan suna
Muna zaune a falo wajen ƙarfe 10 :30na dare muna ɗan taɓa hira kafin mu kwanta sai nace wa mummy
"har yanzu ba a san inda sabit yake ba" juyowa tayi ta kalle ni, dagani ita ma abin na damun ta
"wallahi asmau tun rana nake ta trying mumber sa amma sam a kashe take wallahi kawai ƙarfin hali nake amma hankalina ba a kwance yake ba"
Hankali na ne ya