Showing 39001 words to 42000 words out of 88726 words

Chapter 14 - AUREN BAUTA(1 to End) complete By Maman Walid And Walida Mrs Aliyu.txt

taimaka min kwasar su sai part ɗin sabit abin haushi ma yana zaune a falon yana kallo



Wani takaici ne ya ziyarce ni danaga mun shigo ya wani taso har da karɓar jakar hannuna na tare da yi mana welcome, ita kuma babar har wani washe baki take tana cewa


"ga amarya nan na kawo maka ita Allah ya bada zaman lfy ya kawo ƙazantar ɗaki" nuna mana ɗakin yayi


"ga ɗakin ta can sai ta shiga da kayan natan" tare muka shi da babar ni ko ƙala bance masa sai da taga na shiga na ajiye kayan nawa sannan tai min sai da safe ta fice


Kayana na fara gyarawa inda duk na jera su a kwabar da nagani a ɗakin sannan sai kayan kwalliyata waɗanda na jera su a kan dreesing mirrow



Sai dana ga na gama gyaran sannan na shiga toilet nai wanka na ɗauro alwala, sallah na gabatar ta ishsha sannan na kwanta



Ina cikin addua naji an buɗe ƙofar ɗakin, gabana ne ya yanke ya faɗi, ko da dai fitilar ɗakin a kashe take amma ai nasan sabit ne


Da sauri na miƙe na nemi wani zani da ke kusa da don in ɗaura, ban kai ga ɗauka ba naga hasken pitilar ɗakin ta kauraye ɗakin ya ɗau haske



Ga wata ƴar mitsitsiyar rigar bacci da ke jiki na, saurin lalubar zanin nayi sannan ɓata rai tare da ce masa

"me ya kawo ka"


"zuwa nayi in karɓi haƙƙin ta ko ta ƙarfi ko ta tsiya na ga alamar innai sanya sai a kai wa wani abanza a wofi" gaba na ne ya yanke ya faɗi amma sai na dake don kar yaga ma tsorata ya rena min wayo



Matsowa ya fara yi kusa dani gabana yana ƙara faɗuwa

"abinda kike burin kaiwa abdul ne nake son ruguza wa, tunda yanzu halak ɗina ne me zai hana in mori kayana tun kafin a kai wa wani banza, gwanda in karɓi kayana da hujja" fara matsawa nayi baya kashe fitilar yayi sai ɗakin ya ɗau duhu wanda hakan yasa na kasa gane a ina yake,



Haƙuri na fara bashi na don Allah ya ƙyale ni wallahi wasa nake masa, jinshi nayi kusa da ni wannan ya ƙara firgita ni


Ganin bashi da niyyar ƙyale ni yasa ni ma na fara kokawa da shi wallahi bazan bari yayi abinda yaga dama dani ba ai nia ina da ƙarfi



********************

Wayyo Allah sabit ya cuce ya raba ni da budurcina ba lallami ba daɗin baki ba komai sai azaba da nuna ƙarfi in short zan iya cewa raping ɗina ma yayi


Kuma abun takaici yana gamawa yayi wulli da ni sannan ya fice bayan rashin mutuncin da ɗiban albarka daya min, ina kwance nai rigingine ina ta kuka ba abinda nake ji sai tsabar raɗaɗi


Wayyo ni asmau wannan wace irin rayuwa ce mijina ya same ni budurwa sannan yai min wannan aika aikar amma sam a lamarin sa ba tausayawa wayyo sai yaushe wai zan samu me sona ne na gaskiya gashi abinda nake ta tattalin sa ina alfahari da shi yanzu babu kuma a wulaƙance ya ba wani daraja ko nuna mutunci ko wani abu gaskiya sabit ya gama cutata har abada








👩🏽‍🍳 *menu of d day* 👩🏽‍🍳


*fatan doya, meat balls and mixed fruit juice*

*fatan doya*

```ingredients```


-doya
-wake
-attaruhu
-albasa
-kifi
-salt
-sugar
-mai



*method*

1) ki zuba mai a tukunya da albasa idan yayi zafi sai ki zuba jajjagen ki na attaruhu da albasa

2) idan ya sayu sai ki zuba ruwa da maggi da salt daga nan sai ki bar shi ya tafasa idan ya tafasa sai ki wanke waken ki ki zuba sannan ki rufe ki barshi ya dahu


3) ki fere doyar ki sannan, sai kin tabbatar da waken ya dahu sannan sai ki zuba doyar ki zuba sugar ki ƙara albasa sannan ki dagargaza soyayyan kifi a ciki ki rufe har dahu idan ya ɗauko dahuwa a rage masa wuta


*Meat balls*

```ingredients```


-nama
-kwai
-garin bushashen burodi
-maggi
-albasa
-attaruhu
-mai


*method*

1) ki dafa naman ki da albasa maggi, tafarnuwa idan ya dahu sai ki sauke sannan sai ki daka


2) bayan ya daku sai ki fasa masa kwai ɗaya sannan sai ki zuba daddakekken attaruhu da albasa da maggi in yana buƙata ki zuba garin burodi ki ɗaure shi sannan sai ki fara dunƙule wa kamar ƙwallo


3) ki fasa ƙwai a bowl daban sannan ki kaɗa shi, ki ɗora mai a wuta idan yayi zafi sai a ɗauko ƙwallon naman nan a saka shi a cikin garin burodi a jujjuya sannan a tsoma shi a kwai daga nan sai kasko a soya idan yayi brown sai a sauke



*fruit salad*


```ingredients```

Seasonal fruits


*method*

1) a samu duk fruit ɗin da kike son amfani da shi amma wanda yake bozo ki wanke ki fere sannan a yanka shi sannan a markaɗa sai a tace a zuba sugar a saka a ƙanƙara a sha



👩🏽‍🍳 *BON APPETIT*👩🏽‍🍳


*ASMA'UN SABIT*
[10/05 09:51] YAYA HAYAT: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*

🍷🍽🥛


👩🏽‍🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽‍🍳




🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠



ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)




*A sakamakon ramadan dake matsowa sannan gashi ina fatan kammala littafin kafin lkcn in shaa Allah, nake so in cire menu ɗin da nake kawo wa sannan in ƙaɗa yawan read more, in shaa Allah kafin ramadan na kammala, sannan in shaa Allah zaku dinga samu 2pages each day saboda ao sauri a gama*



```masu comment ina gani ina jin daɗi da masu miƙo min addua Allah ya amsa mana baki ɗaya ya kuma biya mana buƙatun mu gabaɗaya```





*ALLAHUMMA BALLIGNA RAMADAN BIL IMAN*




P⃗a⃗g⃗e⃗ 16🌹









Ina kwance kamar wata matattaciya can dai dana ga ba sarki sai Allah sai na miƙe na shiga toilet na samu na ɗan gyara jikina na fito na kwanta


Bacci ne yake son kwashe ni amma kuma sam bana jin ɗadin yanayin da nake ciki kyanta ace ina da pain killer dana shaa



To cikin ikon Allah a hankali bacci ya soma kwasata kamar a mafarki naji ana yaye min mayafin dana rufa da shi bude idona nayi a hankali


Kasancewar da duhu a ɗakin yasa na kasa gane wane amma kuma kamar ƙamshin turaren sabit yake


Gabana ne ya ƙara faɗuwa kar dai sabit ne ya kuma dawo wa


"sabit don Allah kaji tsoron Allah ka ƙyale ni wallahi bana jin daɗi"


"da kina tsoron Allahn zaki dinga mu'amala da wani gardi da aure na akan ki, ai na faɗa maki sai kin gane kurenki"


"wallahi wasa nake maka"


"ni sa an wasan ki ne, kinsan a matsayin baiwa na ɗauke ki amma kike wasa da ubangidan ki, to ki sani baki da wani matsayi har yanzu a wajena daya wuce na baiwata wacce na siya don haka duk yadda naso yi da ke haka zanyi baki da wani zaɓi, ko an gaya miki ana wasa da ni ne, hankalina kike son jawowa gare ki ko, to albishinki kin samu amma sai kin rena kanki"


Fuzge zanin jikin nawa yayi yai wulli da shi sannan ya hankaɗa ni, azabar da nake ji da ce ta kuma ƙaruwa inda na saki wani kuka me ciwo amma sai yace


"ki buɗe bakin ki kiyi da hujja ba me ceton ki"


Banni da ƙarfin yin kokawa da shi don haka sai kawai na zuba wa sarautar Allah ido na miƙa wuya in ma kashe ni zaiyi a daren yau shike nan na ma huta



Be ce min ƙala ba sannan be bi ta kaina ba yana gamawa ya fice hannuna ma kasa ɗagawa nayi balle in motsa ban da kuka ba abinda nake yi ga raɗaɗi da azaba kamar ana yankani da reza



Kafin meye wannan zazzaɓi ya rufe ni ruf zanin gadon na ɗan jawo na rufe jikina da shi ina ta karkarwa a haka har wani wahallalen bacci yai gaba da ni




Ina cikin bacci naji an sheƙa min ruwan sanyi akai na, da sauri na farka na buɗe ido na ɗan halak ɗin ne yana tsaye fuskar sa a murtuke yana ta kallona


"bana son ƙazanta, ina da rules don haka dole u have to abide by it, har ƙarfe 06:30am amma baki tashi ba balle kiyi wanka in ina da buƙata da safen nan are u expecting me in doshe ki a haka kina wannan yanayi oyaa maza go and wash up kizo ina jiranki a ɗakina"



Gabana ne ya kuma faɗuwa wayyo Allah yau da wane bunsuru Allah ya haɗa ni, me nayi haka da sabit yake min wannan wulaƙancin na tashi zan miƙe naji jiri na ɗauka na ga jikina nawa da zazzaɓi sosai ga kuma azaba wallahi duk abinda za a yi ayau bazan kuma barin wannan mara imanin ƙara kusantata ba



A hankali na miƙe ina tafiya a sanɗa sanɗa har naje na buɗe ƙofar parlon na mu na kama hanyar part ɗin isma'il gurin anty fannah gwanda in gudu daya kashe yanzu a halin da nake ciki in ya kuma kusantata ai sai dai wata ba ni ba


********************



Yana ta window ɗin ɗakin sa ya hango ta tana nufar part ɗin isma'il tsab ya san wajen fannah zata, wani haushin ta ya ƙara ƙule shi lallai ma yarinyar nan nufin ta bata daddara ba ke nan



Lallai wannan tabbas ne sai ya ƙara hukuntata tunda ta zama wacce bata da sirri sai ya sa gane shayi ruwa ne, ko da yake gwanda ma taje wajen fannar don ita fannar ta gano cewar asmaun yanzu ba budurwa bace ko ta faɗawa ɗan iskan yaron nan da ya liƙe mata



Lallai ma kowane wannan abdul ɗin lallai ma ya rena shi matar sa wai ace wani ɗan iska yana shirin raba su ko be kula ta ba be sata a cikin lissafin sa ba ai matar sa ce mallakar sa don haka dole ta yi haƙuri da shi


Amma ƴar iskar yarinyar nan wai har da wani cewa lkc suke jira su kasance tare, lallai ma asmaun nan, shi bama wannan ba wani irin abu ne a tattare da yarinyar wanda sam ko kaɗan badia batta da shi



Shi a rayuwar su da badia sai su shafe sati ba abinda ya shiga tsakanin su amma ita kuma sau biyu a dare ɗaya kuma duk da haka jin shi yake yi kamar a wuni anayi



Lallai wannan yarinyar daban take, ita iya girki gyara da komai da komai matsalar ta ɗaya baƙa ce, duk da dai ta sha gyara amma shi har yanzu bashi da ra'ayin baƙar mace


Daga dukkan alamu sha'awace take jan shi zuwa yarinyar nan daya kau da ita zan yi disposing yarinyar fatan shi ma kafin badia ta dawo ya kau da duk wata sha'awar sa akan ta kije ki huta maa haɗu da daddare ya faɗa yana rufe window tare da faɗawa toilet don yin wanka



*******************


A ƙofar part ɗin fannah ta fara knocking ta ɗan jima kafin anty fannah ta zo ta buɗe ƙofar cike da mamakin wa ye yake mata wannan knocking ɗin da sassafe



Ganin asmau a cikin halinda take ya saka ta yi salati sannan ta ruƙo hannun asmaun wanda yai zafi rau da shi


"me ya same ki" ta faɗa ta ƙoƙarin zaunar da ita akan kujera, cikin kuka asmaun ta amsa

"sabit ne ya........." anty fannah bata bari ta ƙarasa ba ta toshe mata baki


"mara tarbiyya ce ke fallasa abinda ya wakana tsakanin ta da mijinta, amma me ya sa har ya kai ga haka, ince dai gardama kikai masa don nasan ki da taurin kai barin in haɗa miki ruwan wanka ki gasa jikin ki" ta faɗa tana shige ɗakin ta don haɗa ruwa



Ajiyar zuciya asmaun tayi tare da ɗan kwanciya a kan sofa ɗin tana ɗan maida numfashi kaɗan kaɗan

Fannah bata daɗe ba sai gata ta dawo,

"tashi muje na haɗa miki ruwan ki samu kiyi wanka ko kya ji daɗin jikin ki" miƙewa nayi ina tafiya da ƙyar tana bina abaya tana kallon yadda nake tafiya sai tace


"wai garin ƙaƙa akai haka asmau kokawa kukayi yai miki haka, waya faɗa miki anawa namiji musu ne a gado ai kawai daya doso ki ko kibi yarima ku sha kiɗa ko ki sakar masa linzami yayi yadda yake so


Gaskiya baki kyauta ba shima sabit ɗin har da shi wannan abu sai kace be san yadda abin yake ba, kar ki kuma yi masa gardama ki zubawa sarautar Allah ido wallahi ko ba daɗe ko ba jima sai sabit ya durƙusa miki ai ba ƙaramin haɗi kika sha a garin mu ba


Laƙani ne wanda duk ya kuskura ya fara ɗanɗana wa to shikenan shi kuma da haƙura da mace sai dai wani ba shi ba"




Allah ma ya sauwaƙe min wai ni da sabit har abada mutumin da ko a ƙafa aka daura min sai na tsinke na gudu balle wai ace na zauna amatsayin matar sa



Muka ƙarasa toilet ɗin ta cika bath da ruwan zafi sai wani ƙamshi yake tashi na misk


"Maza shiga ki gasa jikin ki kuma ki tabbatar kin daɗe sosai a ruwan don ya ratsa ki sosai amma kafin ki shiga ki fara yin wanka don kar dauɗar ƙafar ki ta ɓata ruwa" tana gama faɗa ta fita


Wanka na soma yi, sai yanzu ma naji yadda na fulani na suke ashe suma sun sha massage dai zafi suke min


A hankali na wanke jikin nawa sannan na shiga bath ɗin, zama na keda wuya wani raɗaɗi da azaba daya shige ni ban san lkcn da ƙwalla ƙara ba sannan na miƙe da sauri



Muryar anty fannah naji


"kar ki sake ki fito yana miki zafin haka zaki shiga a hakan ne zaki warke in baki gasa kanki ba baza ki taɓa warke wa ba kuma sabit ba zai daina kawo miki ziyara ba kema kin sani haka kawai ki lalace a banza maza ki shiga ki gyara kanki in ba haka ba in shigo in miki da kaina"




Ƙara shiga nayi ina kuka kamar ana tsaga min wurin haka nake ji, dama haka mata suke ji ko kuma ni kaɗaice don na haɗu da mara tausayi
\

Wallahi sabit zai gane bashida wayo ni da part ɗin sa hayhata hayhata, sai da ruwan ya ɗan fara sararawa sannan na fara jin daɗin jikina



Na daɗe sosai a toilet ɗin sannan na fito inda na tarar da anty fannah ta haɗa min tea me kauri sai pepper soup



Na zauna na karya sannan na sha magani daga nan sai bacci,



*******************


Abin ya ba fannah mamaki yadda sabit yai wa asma'u aika aikar nan amma sam be bi ta kanta ba gaskiya be kyauta ba duk abinda asmaun tai masa tai ai sai ya ɗauka duk a cikin yarinta ne



Ɗaukar wayar ta tayi ta kira shi ringing ɗaya ya ɗauka, yana ɗaga wayar yace


"yayata ina patient ɗin taki take" wannan maganar ta bawa fannah haushi


"ka damu da ita ne da ka damu da ita da ba kai da kanka zakai jinyar ba"


"wallahi babu yadda banyi da ita ba akan ta bari in gasa ta amma ta ƙi wai kunya take ji ita wurinki zata zo shine nace to ta tafi nasan zata sha gyara fiye da nawa"


"au ai na ɗauka ƙyale ta kayi tayi ta kanta tunda kai ka gama biyan buƙatunka"


"haba yayata ni na isa ƙanwar taki ai ƴar baiwa ce, ni na isa in wulaƙanta ƴar baiwa kawai dai a kular min da ita zuwa dare inna dawo zan zo in ɗauke ta" ya faɗa cike da nishaɗi


"a a ba sai ma kazo ba tana farkawa anji ma zan makda ita ɗakin ta saboda ayi shirin tarar ango, amma don Allah sabit a dinga saurara mata"


"ba komai yayata yadda kika ce ɗin hakan za ayi" sukai sallama


Sabit wani daɗi ne yaka ƙara shigar zuciyar sa ganin yadda asmaun zata dawo da kanta ba tare da yaje ya bada kansa ba don shi yanzu zuwa ma wai ya dawo da asmau wani tashin hankali ne a wajen sa in shaa Allah kafin badia ta dawo duk wani daya ji a game da ita ya kau amma kuma anya zai iya 🤔 shine abinda yake tambayar kansa



Ba komai ko bazai iya ba sai kawai ya mai da ita standby duk lkcn da badiar tayi balaguro ga standby ɗin sa always available murmushin mugunta yayi daya tuno da gurasar da zai tarar yau inya koma gida


Lallai kam ya yadda da aka ce ko wacce mace da baiwar da akayi mata wata Allah ya bata kyau wata kuma Allah ya bata wani abun to amma ita asmaun matsalar sa da ita shine baƙin ta duk da dai ya ragu yanzu ta koma chocolate amma shi gaskiya har yanzu taste ɗin sa na farar mace be canza ba


*******************



Sai bayan azahar sannan ta farka ras taji ta kamar ba abinda ya faru da ita, abinci taci sannan anty fannah ta kuma bata wani papper soup ta shaa sqm bashi da daɗi ga wani uban gari a cikil amma haka ta sha


Bayan ta gama kuma anty fannah ta kuma kawo mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login