Showing 1 words to 3000 words out of 67181 words

Chapter 1 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

__________________________________

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah daya bani ikon kawo muku wannan littafi mai cike da darasi , tsira da aminci sukara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad s,a,w,

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (1)

Taku ɗaya bayan ɗaya take da takalmin ta mai matukar tsini har ta kammala sakkowa daga step ɗin benen ta zauna a wani makeken dining table yadda take cin abinci anitse Cikin aji da yangane zai tabbatar maka da maiji dakanta ce wata farar matace tashigo palon kallo daya zakai mata kasan kudi sun zauna , kai tsaye inda matashiyar take cin abinci ta nufa ta tsaya kamar mai shakkar yin magana chan ta buɗi baki tace

" malak tun jiya da daddare nace inason magana dake amma kinki saurarata mu tattauna maganar mai muhimmanci ce, shiru malak tayi ta cigaba da cin abincin nata , karamin tsaki matar taja wanda bai fito filiba ta ƙara marai raice fuska tana cewa, " malak dakefa nake?, dogon tsaki malak tayi ta ɗago kai ta zubawa matar ido duk da fuskar malak bata nuna ɓacin raiba amma matar taji a jikinta tsakin datayi na nuna bataji daɗi bane,

mikewa malak tayi tana taku jikake wani kwas kwas tafiyar isa dajin kai take ta ƙaraso kusa da matar ta tsaya ta naɗe hannayen ta tadan motsa baki kamar wadda akaiwa dole sai tayi magana tace, " mom banace kidaina shiga harkata ba ?, yar ajiyar zuciya mom din Tata tasauke tace , " haba malak nafa baki hakuri bana iya jure wannan fushin da kike dani pls malak kiyi hakuri, malak bata ko kalli mom ɗin tataba tanufi hanyar fita a harabar gidan ta hango farar mota a fake wani irin birki taci dan danan fuskarta ta koma ta zallar ɓacin rai cike da ruwan Bala,i malak ta fara dokawa mom kira , mom dake ciki da gugu gudu sauri sauri ta fito ta ƙaraso kusa da malak tace , lfy kikemin wannan kiran , takarashe tambayar tana dafa kafaɗar yar tata, malak cikin zafin rai ta ture hannun mom ɗin tata tajada baya tana nuna motar tace , " yau 3 days kenan dasiyan irin wannan motar inason nazama mace ta farko dazata fara hawan irinta a garin nan shine kika siyo dan kinuna ban isaba ?, malak cikin ɗaga murya take maganar tata tana nuna mom, mom kuwa saroro tayi ta harɗe hannaye cike da mamaki duk da tasaba da halayan malak na nuna isa akan komai da kowa amma idan tayi wani abin mamaki take bata, wani saurayi ne ya ƙaraso wajen kyakkyawa mai kama da mom jikinsa sanye da kayan wasa masu ruwan sararin samaniya riga da gajeran wando a jikin rigar an rubuta i love cricket , yana karasowa yace " haba malak mom ɗin kikewa Clutter kina daga mata murya, saurin ɗaga masa hannu malak tayi taƙara so kusa dashi ta karɓi sandar cricket din dake hannunsa ta ƙarasa kusa da motar tafara da gilashin gaban tadinga loda masa iyakarfin ta saida ta farfasa kowane gilas najikin motar sannan ta yada sandan tana haki , tsakanin mom da yayan nata kawai kallo suke binta dashi , mom takai kololuwa a bacin rai dan danan tashiga kwalawa mai gidan kira dayake hangosu tasaman bene tunda akafara rikicin ,

" kabeer kana ganin abinda taminko ? jiya da daddare aka kawo motar nan gashi ta fasata yau, dattijon dake hango su tasaman bene hanunsa rike da jari yayi dari yace, " malak yanzu kika nunamin kin haifu kin cika jinin kabeer Muhammad naji dadi sosai, yaƙarashe maganar yana dariya haɗi da gyara tsaiwar farin gilashin fuskarsa, mom takaici yaƙara cikata kamar tayi kuka tace, " hakama zakace?, " eh to mekikeso nace?, malak ce takatse maganar mahaifin nata da cewa, " papy banga amfanin kasancewar ka attajiriba indai zaka bari adinga jadani ana gasa dani dole na ban banta da kowa ban yarda aja daniba ko a nuna an kamoni bare kuma afini, papy yanajin haka yasaki murmushi yace, " angama gimbiya malak za,a kiyaye, malak najin haka tawani kaɗa ido tana sauke harararta akan malik yayanta dake tsaye yana mata wani irin kallo mai cike da bayyana tsanar ɗabi,un ta

" ke hafsa , papy yafaɗa yana tamke fuska saida ta ɗaga kai suka haɗa ido yace, " namiki iyaka da harkokin wannan yarinyar ki barta tayi abinda ranta yake so kafin ki haifeta babu irin jindaɗi da fantamawar da bakiba dan haka kibarta taci zamaninta ke naki ya wuce tsofai tsofai dake kina ƙoƙarin dai daita kanki da ƙanƙanuwar yarinya yar 22 years

Jinjina kai kawai Hajiya hafsa tayi tawuce cikin gida, Malik dake tsaye ya kalli malak yace, " Allah zai nunamiki iyakarki malak kibi duniya a sannu, dogon tsaki malak taja taɗaga waya ta dannawa direba kira batare da ɓata lokaci ba ya ƙarasa da dalleliyar jibgegiyar mota ya bude mata tashiga ciki har motarsu ta fita daga gidan papy yana ɗaga mata hannu,

***

malam musa ne zaune kan ɗaya daga cikin gujerin palon ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yana shan kan kana, wata yar matashiyar yarinya ce fara tass sanye da doguwar rigar atamfa sai mayafi madai daici ta lullube jikinta tana zaune a kan kafet ta sunkuyar dakai tana wasa da yatsun hannunta, Hajiya fatima dake zauje kusa da malam musa ce tace, " binta, matashiyar ta dago kai ta kalleta tace, " naam mama, " binta tunda har kinkai labil one amatakin karatun nan kiyi hakuri ki nemi biji kiyi aurenki kina ganin sa,annin ki wasu suna ɗaki wasu kuma ankawo kuɗinsu amma ke kina zaune,

ajiye chokalin dayake shan kan kanar malam musa yayi ya ture ƙaramin table ɗin da aka ɗora masa farantin kankanar gefe yafara magana da cewa, " towai ma Hajiya narasa me takwarar nan taki take nema kuɗin fa karatunnan tunda kika fara daga nazire bani nake biyaba har kikakai yanzu ke bama ɗawai niyarki ba har ɗawai niyar mahaifiyarka Hajiya ce take cinki da shanku da sittirar ku babu wanda yake taimaka mata ai yakama ace zuwa yanzu kin rage mata wata ɗawainiyar ta huta haka , murmushi Hajiya fatima tayi tace, " duk bama akai ga hakaba malam Allah yagani inada halin dazan cigaba da ɗaukar ɗawainiyarta har ƙarshen rayuwarta na ɗauki binta Kamar ƴata Allah bai bani haihuwa ba jin binta nake har cikin raina gani nake ko usainan data haifeta bazata nunan santaba,

" eh gaskiya ne fatima Allah dai yayi miki albarka, malam musa yafaɗa sannan ya kalli binta yace, " kinaji binta kihakura wannan umarninmu ne idan Allah yabaki miji kiyi aurenki idan yaga zai iya sai kici gaba da karatunki,

Binta cikin ladabi da nutsuwa tace, " insha'Allah abba na yarda da hukuncin ku na hakura da karatun, dariyar farinciki Hajiya fatima tayi tace, " yauwa yar albarka tashi kije abinki Allah yakawo miji nagari namiki alkhawarin gwangwajeki da kayan gata sai kowa yayi mamakin irin kudin dazan kashe a aurenki, binta tana murmushi ta tashi ta fice yar tafiya kaɗan tayi ta ƙarasa inda ɗakunan ummanta suke a jere guda biyu tafaɗa bedroom din umman nata , a zaune tasamu umman nata tana shirya charbi binta tayi sallahma ta ƙarasa kusa da ita tazauna tana tayata haɗa charbin , kallon yar tata tayi ganin tashigo babu walwala tace, " binta ya kukayi da maman naki ? ,

Ɗan murmushi binta tayi tace, " cewa tayi na hakura da karatun haka idan nasamu muji nayi aure, " uhumm daman kece kikaƙi dakin biye ta tawa daga secondary zaki dagata kiyi auren ki, hawaye ne suka fara zuba a idon binta cikin hikima ta share a tunanin ta mahaifiyar tata bata ganiba tace, " ummah ina burin nayi karatu mai zurfi nasamu aiki adinga biyana duk wata nasai miki tankameman gida mai AC nasaki a ciki kihuta kiji dadi sannan natai makawa su kawu balarabe da kawu mansur baba ladiyo ma na taimakawa marayun ƴaƴanta ,

Dariyar farinciki ummah tayi tace, " Allah sarki binta tun kina ƙarama kike mana takidin wannan alkhairin nida yan uwana wlh binta koda baki samu damar yimana ba inajin daɗin yadda kike kulawa damu dayi mana addu'a karki wani damu kanki komai rabone bawai dole sai kinyi karatu zaki samu damar yin wannan ba idan Allah yaga dama zai iya buɗa miki ta kowace hanya,

" to ummah kimin addu'a Allah yasa hakan shiyafi alkhairi, " karki damu binda hakan shine mafi alkhairi insha'Allah Allah yayi miki albarka yabaki miji nagari wanda ko bayan babu raina bazakiyi kukan maraici ba sai dai na shaƙuwa da soyayya, rungume Umman tata tayi ta amsa da ameen,

**

Kai tsaye hospital suka nufa anayin parking tafito sanye da riga da wando masu dan karan kyau da tsada ba matsatstsu bane amma kyakkyawar surarta ta fito wani siririn mayafi tayafa ta baya tazubo da dogon gashinta dayasha rini coffee kalo hannun ta reƙe da jaka madai daiciya wadda tai kala da kayan , ɗaya hannun kuma wayar tace matsakai ciyar kwalliya ce a sukarta kamar ma babu hoda dan zallan kyawunta ne ya bayyana duk da akwai kwameman glass a fuska ta kalar kayan nata ga wanda baisanta ba saiya rantse baturiya ce dan hasken sak na turawa fatar ta har wani kyalli take idan ta shiga rana,

Cikin takunta na manyan yara ta ƙarasa cikin hospital din wajen masu badata kati ta tsaya wata yar lukuta mata dake ciki tana danne danne computer tana ganin malak ta mike cikin girmamawa ta gaishe ta

batako amsa gaisuwar ba tace, " Dr fayez yana nan, cikin girmamawa tace mata yana nan , kai tsaye office dinsa tanufa bawani noking tatura ƙofa ta shige

Haɗaɗɗan saurayin dake zaune yana duba File ne yaɗago kai yana kallon ta harta karaso taja kujera ta zauna murmushin da suka sakar wa junansu ne zai nuna masoyane sunyi matukar dacewa yadda take haɗaɗɗiya haka shima yagaji da haduwa,

" malak yanzu nake tunanin ki,

" meyasa baka kirani ko,a wayaba?,

" jiya ban koma gida da wuriba kuma nagaji shiyasa, ɗan yatsuna fuska malak tayi suka cigaba da hirarsu ta soyayyah

Kusan mintina 20 suna hira ankawo kayan lemuka masu san chan malak tace, " nizan wuce tunda yamma tayi muje kasaukeni agida, batajira yabata amsaba takara waya akunne tacewa direban ta ya tafi, tana gama wayar fayez yatashi yadau key yace tazo sutafi haka suka fito harabar hospital ɗin ya dakko motarsa mai matukar kyau tashiga gidan gaba suka fice suna hawa kwalta yafara sheka guda suna tafe suna hira ,

Binta ce tsaye a bakin baban titi tanata ƙoƙarin tsallakawa takasa gashi hannunta kayane niki niki wayarta ce tafara ringing aje kayan ɗaya hannun tayi ta curo wayar a karamar jakarta dake rataye a kafaɗar ta tana ganin mai kira tayi dariya takara a kunne tace, " hello Khadijah ykk, chan tayi dari tace, " kiyi hakuri wlh kinga mamace ta aikeni na anso mata kaya kuma kinsan Yammah tayi sai naga kamar ba kowa ina hawa sai naga mota a miliyan kamar zatahau kaina, " ganinan kijirani dan Allah, binta ta faɗa tana ƙoƙarin tsallakawa wata bakar mota tayo kanta gaba ɗaya binta ta diririce jikinta sai ɓari yake batasan sanda tasaki kayan dake hannuntaba ta ɗora hannu aka ta tsugunna tana kwallah ƙara, " birki fayez yaja daf da ita Allah yataimaka yadana zafin nama datuni ya takata , shirun da binta tajine yasata buɗe ido taga a duniya take ko,a lahira ganin babu abinda ya sameta ne yasata sauke nannauyar ajiyar zuciya tana hamdalah ga Ubangiji , dogon hon taji an mata hakan yasata mikewa jikina rawa atamfofin dake ledar tafara kwasa ɗago kan dazatai karaf idanunta suka hadu dana malak , binta jitai kirjinta yabata daram dasauri ta kauda kanta tana ƙoƙarin basu hanya ta koma baya kadan ta tsugunna tana kulle bakin ledar daya tsinke ,

" wow wannan yarinyar badai kyauba , fayez yafaɗa yana kara binta da kallo, jiyayi malak tace , " nima nayi mamaki wai dama ana samun kyawawa acikin yayan talakawa kamar wannan, murmushi fayez yayi yace, " yes, kallansa malak tayi tace tana zuwa tabuɗe motar tafita ta tsaya kusa da binta dataketa kiciniyar kullah ledar atamfofin data tsin ke

✍🏼 zeenariya

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

__________________________________

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah daya bani ikon kawo muku wannan littafi mai cike da darasi , tsira da aminci sukara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad s,a,w,

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (2)

" karki yadda tsautsayi yakuma haɗani dake da,ace ni nake tukinnan da babu abinda zai hanani bitakan ki nakasheki na kashe banza koke yar gidan uban wanene a garin nan, tsoro da mamakine suka haɗarwa binta gu guda tana kallon ta harta wuce tashiga mota suka tafi bata iya cewa uffanba a zuciyar ta take tunanin wannan wace irin zuciya ce da ita haka tabbas dan taga tanada arziki ne yasa take abinda taga dama, wani shashin na zuciyar binta yace Allah ya kyauta, tashi tayi ta rungumi kayanta niƙi niƙita tsallaka

Abakin get fayez yayi fakin harzata fice yace, " wai mekika cewa yarinyar nan ne, juyowa tayi ta kalleshi tace, " cemata nayin da ni ce nake driving ta tsaya a gabana babu abinda zai hanani bita kanta ta mutu, fayez baiyi mamakin jin wannan maganar ba dan yasan halin malak zata iyayin duk abinda taga dama babu mai ja da ita, jinjina kai kawai yayi haɗi dayi mata sallahma yaja motarshi ya wuce,

Tana shiga gidan nasu taga wasu ma,aikata sabbabbi an kawo mata biyu maza biya kallo ɗaya zakai musu kasan masu tsabtane, rusunawa sukai gaba ɗaya suna kwasar gaisuwa amma malak batace uffan ba tawuce, falon papy ta sameshi zaune yana kalo ta zauna kusa dashi yana washe baki yayi mata oyoyo taja karamin tsaki dan har yanzu ranta a ɓace yake papy ya lura da hakan cikin tausasa murya yace, " waya taɓanin farinciki nane?, iska ta busar daga bakinta tace, " yau anmin abinda ba,a taɓa minba, cikin mamaki ya gyara zama cike da fargaba yaji tace abinda ba,a taɓa mataba, " papy yau naga wadda tafini kyau kuma har fayez ya yaba kyanta agabana yace ta hadu, cikin matuƙar mamaki papy yace, " kin lura dakyau kuwa malak nifa har yanzu Ban yarda akwai wadda tafiki kyau da gayu a yan matan garinnan ba,

" papy akwai kuma bama yar gidan uban kowa bace kana ganinta kaga talaka fitik , dogon tsaki papy yaja yace ," ashema yar mutsiyata ce kuma shine zaki damu kanki kyan ɗan talaka aina banzane yazo a wahala ya koma a walaha wlh nabayar yar wasu hamshakan ce , dariya malak tayi dan aduniya babu abinda yafi faranta mata rai sama dataji ana kushe talaka, nan ƴa da uban suka cigaba da hirarsu har mom ta shigo ganin sai raha suke suna sheƙa dariya yasata zama ayi da ita

Malak tana ganin ta ta murtuke fuska a hassale tace, " mom waya baki izinin kicika mana gida da ƴan aiki?, mom ɗan sosa kai tayi cikin tausasa murya tace, " wlh malak aikin ne ba,a yinsa yadda ya dace saboda karancin ƴan aiki kinga jamila ita take kula da girke girke lailah kuma ita take gyara miki ɗakinki dasauran ayyukan gidan nan shine naga yadace na daɗo wasu su dinga kula da tsabtar lungu da sako na gidannan sannan mazan su dinga gyare gyare a waje da kula da Garden , " mom banason kwashe kwashen kowane kuchakai ki sallamesu sai muduba masu tsafta ,

Mom taji daɗin yadda malak tayi mata bayani batare da ɗaga murya ba tasan tana cikin farinciki hakanne yasata washe baki tace ," yacce kikeso haka za,ayi shalelan papy, tashi malak tayi ta wuce ɗakinta

Tana shiga ta ajiye jakar dawayar ta akan bed ta cire takalmin ta taware mayafin tasa hannu ta hargitsa dogon gashin kanta dayasha gyara zama dayi a haɗaɗɗiyar duguwar kujerar ta kicin ɗaga murya tafara kiran, " lailah lailah, da hanzari lailah ta ƙaraso ta tsaya nesa da ita tarisina tace, " ranki shi dade gani, " jeki hadan ruwan wanka a bathtub karki cikamin shampoo da yawa, kuma rusunawa lailah tayi ta wuce tafkeken bathroom din dake cikin ɗakin

Tashi malak tayi tashiga cire kayanta ta sa rigar wanka lailah nagama haɗa mata ruwa taje ta shiga kafin ta fito lailah ta gyara kayan tsab dukda a gyare yake kayan da malak ta cire ta tattare ta kuma ƴan ƙaƙale ƙaƙalen ta tasawa ɗakin sassanyan turaren feshi wanda aka tanada na musamman dan ɗaki,

Bayan ta fito ta shafa mai tasa ƙananan kaya riga da wando masu taushi ruwan kasa masu talewa kuma basa kama jiki gyara gashinta tayi ta fito palo wajen dining aka haɗa mata abinci tafaraci Malik ya shigo harya wuceta sai yadawo ya tsaya a kusa da ita yana murtuke fuska yace, " daga gidansu doctor fayez nake Ammee tace kiɗaga wayarta magana zakuyi , abinda ya kular da Malik yagama bayanin ko arzikin kallo baisamu a wajentaba haka yatashi yana kunkune duk da shine sama da ita bai isa yamata faɗa ba yanzu saiya jawowa kansa wajen papy har mom ɗinma ba kyaleshi zataiba

*

9:40 na dare a Zazzau ne suke gaba ɗayansu a palon suna kallo usainace ta nisa tace, " yauwa maman binta da Abban binta dama kuwa inason mu tattauna wata magana daku, Abbane yace, " to muna sauraranki, nisawa tayi tafara magana, " jiya Hajiya halima tazomin da wata magana game da binta tace min akwai wani aiki da tasamo mai tsoka duk wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login