Showing 48001 words to 51000 words out of 67181 words
Chapter 17 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx
bata iyaba sai ɗan banzan raini da rashin kunya , saurin ɗaga mata hannu papy yayi yace, " malik fa ɗanane duk abinda na yanke akansa babu jayayya, yafaɗa yana ɗaga murya hakanne yasa malik bai tankaba kawai sai yayi shiru yana jin duk duniya bashida maƙiyya sama da malak,
Saida papy yayiwa mom kacha kacha sannan ya juyo ya kalli malik yace, " gobe ka tabbatar gaje gidansu zance kun tattauna kun fahimci juna kuma kar ka yarda naji kayi ba daidaiba na faɗa maka, to kawai malik yace ya tashi ya fita
a matuƙar fusace ya nufi ɗakin malak yana zuwa ya banka ƙofa da ƙarfi,
Shirin fita take dan a tsaye a bakin ƙofar ya ganta tanasa ɗan kunne batare da yayi maganaba kawai ya shaƙi wuyanta da hannu ɗaya ya fara turata da baya da baya idon nan nasa jajir yake cewa, " kafin ki kasheni nizan kasheki kowa ya huta sheɗaniya, cikin tsananin azaba take dukan hannun sa tana kakari takasa kwacewa saida ya jinginata da bango ya ƙara matse shaƙar dayayi mata sosai yake cewa, " malak nizan kasheki kafin baƙin cikinki ya kasheni
lailah ce ta karaso gurin su da gudu wadda tana banɗaki tana wankewa ta jiyo kakarin malak , da wani irin hanzari ta riƙe hannun malik tana kuka tana bashi hakuri cewa take , " zaka kasheta fa malik idan fa ka kasheta iyayanka bazasu yafe makaba , tuna hakanne yasa malik sakinta da sauri ta riƙe wuyan tana wani irin numfashin azaba lailah ta kawo mata ruwa tasha tayi jifa da kwalbar cikin bala i da jajayan idonta tace , " koba aureba wallayi babu fashi saika aureta garani wuyana kashaƙe kai rayuwarka na shaƙe kuma sainasa kayi nadanar abinda kamin zan nuna maka iyakarka saina tarwatsa maka rayuwa malik,
kuma zaburowa yayi zai shaketa lailah ta shiga tsakani sai hadashi da Allah take kar papy ya jiyo shima malik tuna hakanne yasashi barin ɗakin a fusace saboda bayason ɓacin ran iyayensa kuma yasan akanta tsaf zasu iya tsine masa,
Malak naganin fitarsa taje bakin mirror tana kallon shatun hannunsa daya fito raɗa rada a wuyanta da tayi tunanin ta faɗawa papy sai kuma ta tuna hakan zai iya jawo gagarumin hargitsi wanda ka iya sawa maganar aurensa da suhaima tasamu matsala, tuna hakanne yasata yin ƙwafa dai dai lokacin da wayarta tayi ruri ta ɗaga tayi magana sannan ta katse tasawa wuyanta hoda danya ɓoye shatun hannunsa ta kuma gyara fuskarta ta fita,
Restaurant na manyan yara ta wuce bayan tayi parking ta shiga tana takunta mai jan hankali doguwar rigace a jikinta mai siririn hannun tsayin rigar iya gwaiwa sosai ta kama jikinta ta kwanta lif lif chocolate colour ce mai duhu shiyasa ta kuma haskata kanta babu mayafi gashin kawai ta saki sai yar jakarta mai ɗaukar ido, tana tsayawa a wajen tafara hange cikin mutanen dake zazzaune kowane a gaban dining table chan ta hangoshi shi kaɗai a cikin VIP murmushi tasaki ta ƙarasa
Yana Ganinta yakasa ɓoye farin cikinsa yaja mata kujera ta zauna bayan sun gaisa sundan taɓa hira kaɗan take cemasa, " babu lokaci waheed kamin ƙarin bayani akan message din daka turamin, murmushi yayi ya shafa gyararran gashin kansa yace, " gaskiya dai kamar yadda na faɗa miki malak ina sonki wlh idan kika bani dama zan goge miki soyayyar fayez daga zuciyar ki, saurin katseshi malak tayi da cewa, " tayaya zaka iya sawa na manta da fayez,
" karkiyi mamaki malak nidai damarki kawai nake buƙata tunda kikaga na iya bayyana soyayya ta agareki duk da nasan irin mamayar da soyayyar abokina tayi miki ai naga zan iyane,
" shine nace tayaya zaka iya?,
" ta hanyar Aure nasan kinsan cewa soyayyah ta zahiri wadda babu yaudara acikinta tana cikin aure ki yarda muyi aure cikin ɗan ƙanƙanin lokaci wannan zai zama makamin rama cin amana da cin fuskar da fayez yayi miki,
Lumshe ido malak tayi tana tunanin ta wace hanya zata ɓullowa waheed sam bataso yagane tana wani shiri akan fayez kuma bataso yasan tana son auren fayez har yanzu saboda idan yasan haka zai nisanceta kuma bata buƙatar alaƙarta da waheed ta yanke dan zai mata amfani , " kinyi shiru tunanin me kike ?, ya faɗa yana kallon ta, glass cup ɗin dake ɗauke da lemo a kusa da ita ta ɗauka tasha sannan ta maida ganinta ga waheed tace,
" waheed ina tsoran faɗawa wata sabuwar soyayyar dan gudun mai maicin abinda ya faru dani waheed ni yanzu ko maganar aurenma banaso pls ka tausaya min ka ɗage wannan maganar zuwa wani lokacin idan zuciyata ta huce dajin zafin abinda fayez yayimin zan maka magana nida kaina,
Kai waheed ya dafe cikin takaici yace, " banaso muja wani lokaci ne nifa bazan iya ɓoye mikiba wlh tun ganina dake na farko naji na kamu da kaunarki dan tsarin ki yanayin ki dakomai ma irin na matar da nakeson aurene,
" waheed idan ka aurene da ragowar soyayyar fayez a zuciyata bazaka taɓa jin daɗin zama daniba,
Haka tattaunawar tasu tacigaba da tafiya hardai ya samu suka tsaida matsaya akan ya bata lokaci ta huce daga yaudarar dayayi mata,
*
Daran yau sam bai iya rintsawa ba idanma ya kwanta sai dai yaji hawaye nabin fuskarsa tsabar radaɗi da zugin da zuciyarsa ke masa baya iya gane komai ita kawai yake tunawa sam yakasa ganin laifin ta shidai kawai so ɗaya yake mata yanajin kamar bazai iya rayuwa ba idan babu ita yana cikin wannan halin ne Ammee ta shigo ta ganshi sosai taji babu daɗi a ranta duk da bai gaya mata komai ba tasan cikin biyu dole akwai ɗaya kodai maganar binta ko kuma maganar hospital,
Da sassanyan jiki taje ta zaune kusa dashi yana jingine da kujera ya lumshe ido tace, " fayez yan uwanka sunce bakaci abinci ba kuma tunda ka dawo da yamma ko masallaci baka fitaba ince dai lafiya ko, kai ya girgiza ya buɗe idanu a hankali ya maida ganinsa gareta yace, " Ammee banajin zan iya cigaba da zama a kasar nan,
Kallon sa tayi tace, " a wane dalilin?,
" kawai inason na nisanceku na tsawan shekaru idan nawarke daga ciwan damuwar dake damuna zan dawo na cigaba da rayuwa daku, wannan maganar ba karamin taɓa zuciyar Ammee tayi ba dan duk cikin yayanta tafi kaunar fayez shikadai ne namiji ga shiga rai ita kanta batasan dalilin dayake sawa ta gigice akan damuwarsa ba,
Tashi tayi batare datace komai ba dan batada bakim dazata rarrasheshi sai dai idan dadyn sa yadawo tasa shi ya rarrasheshi,
*
Washegari da safe malak ta shirya cikin kyakkyawan shirin ta izuwa gidan mrs Tahir dan ayita ta kare, bataso jamel yasan tilastawar dataiwa binta hakan yasa bata ɗauke shi ya tukata ba sai tasa lailah ta shirya suje tare direban da yake tuka papy ta ɗauka da kuma kwararrun masu bada tsaro guda hudu,
Motoci uku manya manya ta ɗauka ɗaya masu bada tsaro ne guda biyu ta tsakiya kuma ita da direban papy ne motar baya ta ƙarshe kenan ragowar biyun masu bada tsaron ne sai lailah ta
✍🏻 zeenariya
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf zeenariya
WhatsApp number
+218912472599
__________________________________
GARGAƊI
Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 31 )
Wayar ta taketa bi da kallo tana ringing amma ta kasa ɗagawa duk da zuciyar ta tanason ɗagawar amma ba zai yuba dan batason wata magana ta ƙara haɗata da fayez, tashi tayi ta shirya bayan tayi karin kumallo tayi sallama da Ummah ta fito abinda taci karo dashine ya bata mamaki cikin tsananin jin zafi ta karaso inda take tace, " mama ashe zaki dawo? ,
Wani irin kallo mama tayi mata tace, " kin manta nan ɗin gidanane?, " eh kwarai da gaske gidanki ne, binta ta faɗa ta wuce abinta kawai dan batason haya niya, a bakin kofa taga Jamel taje ta shiga motar dan tasan wajibine yazo yace zai kaita wajen aiki
Da sassanyar murya ya kalleta yace , " amarya bakya laifi ina fatan kin tashi cikin aminci, " alhamdulillah, tace masa a taƙaice sannan ta sanar masa inda zai kaita wato unguwar da kanin babanta yake,
Nan danan suka dauki hanya sai fanisau,
*
Gaba ɗaya yau gidan babu daɗi duk mai son fayez yana cike da alhini na halin da yake ciki, dady ne daya dawo ya kira fayez ɗakinsa ya zauna ya karemai kallo yayi shiru yana nazarin hanyar dazai shawo kan matsalar tasa dan yanzu ya fara damuwa akan damuwarsa, da tattausan lafazi dady yace, " fayez menene duk wannan kanafa cutar da kanka kuma muma kana cutar damu dan bamajin daɗin ganinka a wannan yanayin kaki chin abinci tun jiya daga gida sai masallaci ka kashe wayoyinka idan ma ka kunna na ƴan mintina ƙalilan ne ka gayamin me kakeso ni mahaifinka ne zanyi duk wani kokari wajen ganin na rabaka da damuwa, sun kuyar dakai fayez yayi chan kuma ya ɗago ya kalli dady yace, " dady yarinyar dazan aura tace tafasa aurena dady ni namijine mai juriya akan kowane irin mummunan abu daya sameni amma na kasa jurewa akan hakan inaji kamar bazan iya rayuwa ba,
Murmushi dady yayi yace, " akan soyayyah kake neman kassara rayuwarka ya kamata ka tuna kaifa yanzu ba yaro bane kakai munzalin da ko mutuwa tayi zaka iyayin rayuwar ka, nisawa dady yayi ya dafa kafaɗarshi yace," kaga fayez Allah bawai ya haliccemu bane dan mu shagalta da farin ciki ko bakin ciki ya haliccemu ne dan mu bauta masa mugina lahirarmu inaso kadau shawarata ka manta da ita kasa aranka rabon mutum baya taɓa wuceshi duk rintsi duk wuya idan Allah ya rubuta matarkace zaka sameta idan kuma Allah ya kaddara ba matarka bace tofa duk rintsi bazaka taɓa samuntaba rayuwarka tanada matukar muhimmanci karka ɓata lokacinka a banza my son ,
Sosai fayez yaji zuciyar sa taɗau wani layi bisa ga kalaman mahaifinsa hakika rayuwar sa mai amfanice saboda haka zai manta da binta ya fuskanci sabuwar rayuwa bawai dan yadaina santaba shi yasan da santa zai ƙare rayuwar sa, kallon sa dady yayi ya ƙara da cewa, " yanzu ina kakeson cigaba da aiki kozaka koma hospital dinka ne ?,
" no dady tace saidawa zatai idan har ban amince na aureta saboda shiba, jin jina kai dady yayi yana murmushi yace, " ok ashe saboda haka ta siya badan tanaso ta amfana dashiba tom ba matsala zansan yadda zanyi akai kaje ka cigaba da aikinka daga yanzuma ka shirya ka koma hospital kayi aikinka, sosai fayez yaji daɗi aransa yasan dady zaiyi wani abun tunda har yayi wannan maganar, godiya fayez yayi ya tashi ya fita,
Yana zuwa ɗakinsa ya kunna wayoyinsa guda uku daman ɗaya yana yawan kunnata saboda kiran binta biyunne na business ya kashesu saboda yana bukatar kadaici, wanka yayi yai sallar nafilah ya sanarwa Allah damuwarshi haɗi da neman zaɓi sannan ya shirya cikin hadaddan shirinsa ya fesa turare ya dau mukullin mota ya fito falo zai fita Ammee na ganinsa ta washe baki cike dajin daɗi ta nufoshi tana cewa, " Masha Allahu hakika Allah yayi madarar zallar kyau wa wannan ɗan tilon ɗan nawa ina kake shirin zuwa haka ?,
Batare da wata fara a afuskar sa ba yace, " zan tafi hospital ne, " tom zomuje kafara cin abinci, bai mata musuba suka wuce dining room da kanta ta haɗa masa komai ta sashi agaba tanai masa hira yanaci,
Dady yana ɗaki yana shirin fita kira ya shigo masa ya ɗaga bayan sun gaisa mai kiran yace masa yanason magana dashi, tattara nutsuwarsa yayi yana sauraran mai ɗan uwan nasa zai ce masa , bayan yayi masa bayanin kudirin sa na neman irine yasashi farin ciki mara misali sai dai wani hanzari ba guduna dady yace,
" nayi farin ciki da wannan maganar amma suhaima har yanzu yarinya ce mai zai hana musa bikin nanda 2 years kannan ta kammala jami a ,
" tayi agidan sa banaso aurennan yaja lokaci muyishi da wuri kafin matsala ta kunnu kai,
" tom shikkenan ba matsala na amince zanyi maganar da yarinyar yanzu, sukaiwa junansu godiya sukai sallama, parlour dady ya fito ya zaunna suhaima da siyama suna zaune ya kalleta yace, " kinji maganar da akai akanke da ɗan uwanki Malik ?,
Cikin murna tace, " eh naji dady,
" to menene ra ayinki akai?,
" na amince dady ina sonsa nima,
Fayez ne ya karaso wajen ya zauna cikin mamakin abinda yakeji yace, " ashe auren zumunci za ai, siyama ce tayi saurin amshewa da cewa, " eh yaya ai anty malak har nan tazo tace......, saurin katseta Ammee tayi da cewa, " to uwar surutu fadi ba a tambaye kiba wannan ba maganarki bace, shiru tayi fayez cikin mamaki ya fara tunanin mai malak tace,
Dady ne ya katse tunanin fayez da cewa, " naji daɗin wannan abu sosai kasan Malik yaron kirkine babu ruwansa bashida wata matsala, jinjina kai fayez yayi yace, " tabbas wannan hakane Allah ya sanya alkhairi, suka amsa da amin ya fice
*
A bakin ƙofar gidan sukai parking haɗi da danna hon getman ya fito yaga jerin maka makan motocin da sukazo ya koma da sauri ya isa yasanar wa da matar gida dayake an gama zaman makoki kuma ita batai magana da kowa zaizo ba sai tafara tunanin to suwanene haka dai tace ya buɗe musu su shigi,
Zuwa yayi kamar yadda tace ya wangale get suka danno hancin motocin su, zabga zangan masu bata tsarone suka fara fitowa daya daga cikin su ya buɗe murfin motar da malak ke ciki ta fito lailah na biye da ita suka nufo inda zai sadasu da babban parlourn gidan
Ta window mrs Tahir ta gansu ga mamakinta batasan matashiyar ba
Komawa mrs Tahir tayi kan kujera ta zauna dai dai lokacin da malak ta shigo cikin falon lailah kawai tayi sallama mrs Tahir ta amsa malak ta ƙaraso tana karewa gidan kallo ba laifi sunada hali daga ganin yanayin gidan amma baza a iya sasu a layin shahararru ba, " barkanku da zuwa ga guri kuzauna, mrs Tahir ta nuna musu kujera ,
Zama sukai malak ta kalli matar babbace akalla zatai 40 da murmushi akan fuskarta ganin yadda matar take mata murmushi yasata tace, " barka da wannan lokaci yakike ya yara ya karin hakuri,
" barkanki dai lafiya kalau yara suke hakuri da godiya sai dai ban ganeki ba wacece kuma daga ina?,
" sunana malak khabeer muhd ni yace ga khabeer muhd mamallakin babban Companyn KM fashion and designer,
" Masha Allah aikuwa inajin sunan ku kuma ɗin ina yawan jin labarin ku a jarida, gyada kai malak tayi tace" nazone akan maganar Shari'ar da kuke agame da mutuwar mijinki ina fatan zaki bani haɗin kai mu tattauna,
" insha'Allah ba matsala ina saurarenki,
Malak kallon lailah dake kusa da ita tayi tace , " kije bakin mota kijirani, lailah na fita malak ta cigaba da cewa , " mlm musa shine wanda kike zargin ya kashe miki miji ko ?,
" eh shine,
Jinjina kai malak tayi tace, " toba shi bane kuma nasan kema kinsan haka dan binceken yan sanda ma ya tabbatar da birkin motar mlm musa baya jikin motar lokacin da akai hatsarin kuma babu wanda zai hau mota babu burki idan har ya sani,
Fuskar mrs Tahir ce ta chanza lokaci ɗaya ta fusata tace, " banson tsautsayi ba kuma bansan kaddaraba yadda ya kashemin miji shima saiya mutu,
" bazai yuba nazo nanne danna baki shawara ki janye wannan Shari'ar kafin jibi a koma kotu zan baki 100 milion ki kula da rayuwarki data yayanki,
Saurin kallonta mrs Tahir tayi a ranta ta raya 100 milion ba karamin kudi baneba fa sai kuma maganar mijinta ta faɗo mata dan danan wahaye ya fara kwarara a fuskar ta cikin jin radaɗi tace, " da kinsan yadda wutar kiyayar wanda yayi sanadin mutuwar mijina take a raina dabaki tareni da wannan zanchan ba zuciya bazata taɓa samun salama ba harsai naga karshensa saina dauwamar da ahalinsa cikin damuwa kamar yadda ya sani,
" nasan akwai ciwo amma barin shizai fi alkhairi , malak ta faɗa tana sake kallon matar,
" to waike menene naki aciki ko kunada alaka da sune ?, mrs Tahir ta faɗa,
" banida wata alaƙa dasu hasalima akwai tamu dasu danni kaina ba ƙaunarsu nakeba sai dai zan ceci mlm musa ne saboda cetonsa zai samamin wani abu mai matukar muhimmanci daya bar rayuwa ta ni dai kawai abinda nakeso dake ki amince ki anshi kudinnan ki janye maganar nan idan ma kikaki amsa zan biya lauyanki kadan daga ciki kisani ko 10 milion nabashi zai juya maganar a kotu yasa kiyi biyu babu ga rashin mijinki garashin nasara kiyi tunani mai kyau,
Shiru mrs Tahir tayi tana nazarin tabbas wannan maganar haka take gara ta amshi kuɗin ta gina rayuwar yayanta, " na amince zanbar maganar amma hakan ba yana nufin na yafe dolene awajen Allah a kwatarwa mijina hakkin ransa dan har yanzu ban yarda ganganci bane,
" kinyi kyan kai bani account no nasa miki 50 milion idan aka gama Shari'ar ranar Litinin zan tura miki rabin,
Godiya mrs Tahir tayi tabada account take kuɗi suka shiga malak tayi mata sallama ta tafi,
✍🏻 zeenariya
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf zeenariya
WhatsApp number
+218912472599
__________________________________
GARGAƊI
Ban yarda a juyamin labari ta kowace