Showing 36001 words to 39000 words out of 67181 words

Chapter 13 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx

sa ida dan tasan ka ida ne ita za a ware a matsayin zaƙaƙurar datafi kowacce, cikin natsuwa mai gabatar wa yafara jinjinawa ƙanana ƙananan masu fashion and designer sannan ya gyara murya yace, " to kowa ya saurara zamu ware zaƙa ƙurar mu,

Malak najin haka ta gyara zama daidai lokacin dazai faɗi sunan ta miƙe tsaye dan tagama tabbatar wa kanta itace, sai dai sunan dataji ya faɗane yasata jin wani irin baƙon jiri na shirin fuzgar ta da sauri ta juya tana kallon binta binta kuwa tanajin an kira sunanta ta tashi tana murna tana tafawa kanta ,

Mai gabatarwa ya kara da cewa, " muna buƙatar mai girma sister malak khabeer muhd tazo ta miƙa kyautar wannan ka wataccen shaidar girmamawa ga zaƙwaƙurar mu ta babbar gasa ta wannan shekarar wato Fatima musa, hakinne ya kuma dawowa malak saida malik ya riƙe ta cikin rikita yace, " malak bakida lafiya ne?, idon ta yana ƙoƙarin kawo ruwa tana dafe gefan zuciyar ta ta ƙan ƙame hannun ɗan uwan nata cikin dauriya tace, " ina lafiya,

Binta tashi tayi taje ta tsaya a dan damalin saida mai gabatarwa ya kuma maimaita cewa yana neman malak sannan ta tashi cikin karfin hali taje tanajin jikinta tamkar ana turata, hannu na rawa taɗau abin karramawar mai kama da kofin zinare samansa da wani mulmule mai matukar daukar hankali tanaji tana gani ta miƙawa binta, binta na murna ta karɓa haɗi da miƙawa malak hannun suka gaisa

*

Dundaga inda motar ta tayi parking ta shigo gida a birkice tana haki tana zufa ta shiga sashinta ta jingina da bango tana dafa kanta kukan takeson yi amma suyar da zuciyar ta take mata ta hanata samun sararin fasa ihun, malik ne ya banko ƙofar ɗakin da sauri ya ƙaraso inda take a tsugunne ya rungumota jikinsa yana shafa kanta, sai yanzu tasamu damar fashewa da wani irin marayan kuka tana rirriƙe rigarsa kam, shiru yayi cikin tausayinta dan yasan abinda ta ganine yake barazanar fasa zuciyarta ,

Cikin sassanyar murya ta sigar rarrashi yace, " haba malak ya kike nema ki kashe kanki kawai dan tasamu ɗaukaka haba ki saurarawa zuciyarki kisama mata sa ada kinfi binta komai fa banga dalilin dazaisa ki damuwaba dan tasamu wani dan matashi a rayuwar ta , waro ido malak tayi tana kallon Malik kamar mai tunanin wani abun take binsa da kallo da jajayan idanunta chan ta zabura ta tashi daga jikinsa tana tsuma ta nunashi da yatsa tana cewa, " duk laifinka ne kai ka jamin malik idanda baka kaita tasamu aikinba da batayi fito na fito da daukakata ba ,

Shiru yayi yana kallon ta cikin mamaki yace , " yaya akai kikasan nina kai Binta wajen aiki ?,

✍🏻 zeenariya

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

WhatsApp number

+218912472599

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 23 )

Wani irin kallo tayi masa da jajayan idanunta cikin tsawa da ɗaga murya tace, " kafitar min a ɗaki munafiki azzalumi bazan kyalekuba saina tozarta ku sainaci mutumcin ku saina hanaku kwanciyar hankali, kasaƙe kawai malik yayi yana kallon ta yanzu sam ta daina hassalashi tausayi take bashi,

Ihunta dasu papy suka jiyone yasasu shigowa ɗakin mom jikinta na tsuma ta ƙaraso tana cewa, " yaya akayine mekuma yasake faruwa?, kuma rushewa malak tayi da kuka ta zauna akan bed tana ɗora hannu aka tamkar wata karamar yarinya, papy zama yayi kusa da ita yana rungumota jikinsa yana rarrashi cikin muryar kuka take cewa, " papy baƙin cikinsu zai kasheni papy meyasa ɗan uwana baya sona duk wani abu dazai kawo tangarɗa a rayuwa ta shiyake yi, papy najin haka ya kalli malik dake tsaye yace, " mekayi mata eh, ya karashe maganar cikin hargagi, saida malik yaja dogon numfashi yace, " papy hassadace kawai take damunta dan batasamu kyautar karramawar datai tsammani bane yasata duk wannan abin,

Mom najin haka ta ce masa to ya fice daga ɗakin ba musu ya fice suka zauna ita da papy sukaita aikin rarrashi papy kuwa sai cewa yake, " akan shedar karramawa zaki zubar da ajinki ki tashi hankalin ki haka haba malak kefa mai darajace maɗaukakiya wadda ba aiwa koda kallon raini darajarki ta wuce yadda kike tunani kinada kyau kuma kinada kuɗi ga ilmi ga izza kin isa a gida kuma kin isa a waje kowa kika taka ya taku kuma komai kika zartar ya zartu, duk da halin damuwar da malak take ciki saida taji wani irin girman kai da ɗagawa ya sake hawar mata ka jitake ai kamar babu macen da takaita ,

_

Angama taro lafiya binta tadawo gida murna ba iyaka sai dai duk da haka tanada damuwa ƙwaya ɗaya yanzu matar babanta sam ta fita shirginsu tunda akasa ranar binta da fayez ta chanza fuska a gidannan acewar ta basajin shawara su adole sai sun aura mata dan masu kuɗi shiyasa suka mayarwa da talaka kuɗinsa,

Da daddare daman Abba yau a dakin ummah yake hakan yasa binta zuwa ɗakin mama tayi sallama ta ansa mata ta shiga ta zauna jim gurin yayi chan binta tayi ta maza tace, " dan Allah mama kiyi hakuri idan nayi miki lefi idan kuma akan maganar fasa auren Jamel ne dan Allah kiyi hakuri tunda har aka fasa to Allah yayi niba matarsa bace ,

Murmushin takaici mama tayi ta harda kafa tana cewa, " nibakimin komai ba amma inajin haushinku gaba ɗaya keda uwar taki da uban naki duk yanzu a kule nake daku da fari nace karkiyi aiki kuka tubure kukace sai anyi na biyu nace kar ayi aurennan da mai kuɗi kuka tubure kukace sai anyi wannan iyakar tawa da kuka nunamin har sau biyu shine yasani chanzawa dan anga ban haifa bane, hakuri binta tafara bata amma kemai mai mama taki hakura karshema sai korar binta tayi daga ɗakin,

*

Kwalliya sosai ta tsantsara riga da wando na fitar hankali yau ko mayafinma bata yafaba haka tasaki dogon gashinta dayaji gyara kunnen ta ɗauke da siririn ɗankunnan diamond sai sheƙi yake ba lefi ko makiyi ya ganta saiya yaba, harabar gidansu ta fito tana waya hannun ta ɗaya ɗauke da wasu File tashiga mota, kai tsaye hospital ta nufa tana zuwa ta haɗu da wasu mutane biyu inyamurai kana ganinsu kaga kuɗi sun zauna, saida ta miƙa musu hannu suka gaisa daya zaiyi shekara 65 ɗaya kuma zaiyi 40 , tare suka nufi cikin asibitin a reception suka tsaya ta tambayi matar wajen fayez yana office matar ta amsa da eh , saida malak tayi murmushi sannan tace takira mata fayez ,

Nan danan ta ɗaga waya takira salular dake office dinsa bayan ya ɗaga tasanar masa yayi baki batare data faɗa masa sunan wadda tazoba, izinin zuwa yabasu suka nufi office dinsa, suna shiga yaganta da maza cikin mamaki yace, " yadai lafiya, murmushin da take masane yasashi tsarguwa kawai saiya nuna mata kujera alamar ta zauna, saida ta ƙarewa kujerar kallo sannan ta taɓe baki tace, " bazama yakawoni ba nazo nagabatar maka da waɗannan mutanan amatsayinka na shugaba ka nuna musu lungu da sako na hospital dinnan sune wanda zasu siya, waro ido fayez yayi cikin mamaki yace, " ban gane masu siyaba nace miki ina neman masu siyan hospital ɗin nan ne ,

Yatsuna fuska tayi tana mai tura masa File din dake hannun ta kan table tana cewa, " mai yuwa agidanku ba a sanar maka cewa nasiyi wannan hospital dinba, miƙewa fayez yayi yana bubbuɗe File ɗin tabbas ba karya mallakinta ne yanzu gumine yafara karyowa fayez dan danan yaji zuciyar sa na ƙuna aduniya babu abinda yafi kauna sama da wannan hospital din idan aka cire iyayensa da binta ,kyasta masa hannunta tayi ganin ya faɗa duniyar tunani tace , " malam fayez karka ɗauki wannan wani abu hakan ba komai bane daman chan naki faɗa makane dan nasan dik rintsi kaida kaya mallakar wuyane yanzu kuwa da abubuwa suka juya shine naga zaifi kyautuwa na saida abina wanda ya siya ruwansane ya barku kucigaba da aiki ruwansa ne ya koreku ruwansane yama rushe hospital ɗin yagina gidan karuwai , wani irin wawan kallo fayez ya jefeta dashi yana tunanin tabbas yarinyar nan so take ta tozarta shi, haɗe rai yayi sosai tamkar baisan wani abu wai shi fara a ko sassauci ba ya tura mata File ɗin gabanta yana gyara kwalar rigarsa yace, " hospital nawane nina ginashi ya kawo matsayin dayake kai yanzu karki soma tunanin zaki amfani da wannan damar ki wulakanta ni bazan taɓa lamunta ba ,

Yana kaiwa nan a maganar sa yafice daga office ɗin, murmushi kawai malak tayi ta juya ta kalli inyamuran da lafiyayyan turancinta tace suje zata nemesu,

Kai tsaye fayez gidansu ya wuce a wajema yayi parking ɗin motar ya shiga gida a fusace ya faɗa ɗakin Ammee, tana ganinsa ta ware hannu cikin mamaki tana tambayar yaya, yana huci yace, " yaushe aka siyar musu da hospital ɗin,

Cikin mamaki tace, " daman nasan za azo wannan gaɓar toni menene nawa aciki zakazo kanamin huci kamar wani kumurci ai daman abinda naketa hango maka kenan tunda mutanan nan sun fimu abin duniya ka lallaɓa ka aureta ka mallake duk wata dukiya data mallaka ka bijire kai ɗan daɗi soyayyah gashi tun ba aje ko inaba inda kake taƙama dashi yazama nata kuma zatai yadda taso, fayez yana tsaye jin maganar Ammee yake kamar ruwan wuta a zuciyar sa dogon tsaki yaja ya fice,

Yana fita ta ɗaga waya ta kira malak babu batun gaisuwa malak na ɗaga kiran tace, " yakikaga kafcen nawa, dariya Ammee tayi tace, " gaskiya kema gwanace amma nifa ina ganin wannan hanyar bazata taɓa sawa yasoki ba,

murmushi malak tayi tana kunnawa sigarin hannunta wuta tace, " wannan somin taɓine Ammee nayine dan na ɗan ɗana masa kalar ɗacin danakeji kuma a hakanma namasa da soyayya ta tsinanniyar yarinyar chan bazataiwa kowa kyau ba,

*

Binta yau bataje aikiba kuɗin da aka bata taje suka zauna da esha Company yaɗau kaso biyu ita kuma taɗau kaso ɗaya tanata murna taje tasiyo dalleliyar mota abinta batare da kowa ya saniba ta kimanin 5 milion ta kawo gida, tana zuwa ta sanarwa da iyayenta tasai mota a kuɗin kayan data samu, kuzo kuyi kallon murna a wajen iyayen ta saidai duk wannan farincikin da ake babu mama aciki da aka faɗa mata sai tayi tsaki kawai ta koma ɗaki,

Bayan dare ya tsala tali taini mama ta fito harabar gidan inda motar binta take ta tsaya tanaiwa motar kallan tsana chan taje bakin get ta buɗe wani matashin saurayi mai kama da ɗan daba ya shigi cikin sanɗa hannun sa riƙe da kayan aikin mota kamar baka nike yana zuwa mama tace, " yauwa maza maza ka cire birkin sonake gobe idan ta fita tayi hatsari ta mutu kowama ya huta,

Cikin hanzari matashin yafara gudanar da aikinsa saida ya gama tabashi kuɗi a leda ya fice cikin sanɗa itama ta shiga gida

✍🏻 zeenariya

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

WhatsApp number

+218912472599

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 24 )

Washe gari binta ta tashi da ciwan kai hakan yasa sam batayi wani yunƙurin zuwa aikiba Abbane ya shigo ɗakin bayan yamata ya jiki yake cewa, " abamu aran motar mu ɗana musa mata albarka , binta cikin jin daɗi tana dariya tace, " aikuwa baba koda baka faɗaba inaso ka hau kazaga gari kaji yadda take, mukullin binta ta ɗakko ta bashi ya fita abinsa,

Kai tsaye yaje ya tada motar ya fice, mama na ɗaki tanajin alamar fita da motar tasaki wani sassanyar ajiyar zuciya a fili tace, " garama ta mutu kowa ya huta wannan shizai rufa asirina har abada bazai tonuba dan ganinta yanzu tsoratani ma yake,

Abba na kan kwalta ya dage sai zuba gudu yake yana murmushi shi kaɗai jinsa yake cikin jin daɗi kwatsam sai ga wata babbar mota ta shawo kwana tayi kansa da sauri ya juya kan motar gefe dan danan motar ta kwace ta nufi wani mutum daya taho a mota shima, Abba kokarin jan birki yayi yaji burki yaƙi jawuwa cikin makurar tashin hankali yaketa matsa burkin da karfi yaki tsayuwa har motarsa ta daki motar mutuminnan suka gangara suka kuma gan garawa, mutanan dake wajen cikin ƙalilan ɗin lokaci suka cika maƙil anata salallallami tsakanin Abba da ɗaya mutumin duk bamai numfashi,

Motar ambulance dake hospital ɗin kusa dasu aka kira ta kwashisu,

Binta nagama cin abincin ta fito tsakar gida tana kwashe shanyar ummanta kawai sai mama ta fito tana ganinta tayi wani mugun firgita harda dafe kirji tace, " baki fitaba dama?, cikin mamakin yanayin mama binta tace, " eh kaina kemin ciwo shiyasa, kuma zaro ido mama tayi tanaso ta ɓoye damuwarta tace, " to waye ya fita da mota naji karar fita da ita ɗazu, murmushi binta tayi tace , " Abbane , wani irin razana mama tayi saida ta dafe kirji haɗi da dafe bango cikin mamaki da tsoro binta ta riketa tana cewa, " innalillahi mama lafiya, zazzaro ido mama ta shigayi tana magana kasa kasa binta batajin metake cewa da sauri ta fuzge hannunta daga na binta tana tafe kanta

Binta ta rausaya kai tace, " mama ko bakida lafiya ne?, girgiza kai mama tayi tana kuma dafe kirji tace , " kawai jiri naji yana ɗibata, mama na gama faɗin haka ta wuce dakinta binta ta daɗe a tsaye tana tunani chan kuma ta wuce abinta

*

Yan sandane suka rubuta rahoto duba da yadda mutanan wajen suka bada labarin yadda hatsarin ya kasance dattijon ne ya daki mutumin da mota shine sukai hatsarin baki ɗaya, wayoyinsu ɗan sandan ya karɓa sai dai mai babbar wayar ta farfashe layin kawai ya cira karamar kuma mai madannai babu abinda tayi , karamar wayar yafara amfani da ita cikin tsanaki ya duba jerin lambobin yaga ansa maman binta sai kuma wadda akasa umman binta yanata dubawa yanaso ya samu ta shakikin mai wayar kai tsaye ya nufi sashin kiraye kirayen da akai kiran maman binta dana umman binta akafi yi a wayar chan kuma yaga number da suna binta sai yaji yanason kira kawai sayya danna kiran

Saidai ta katse ya kuma mai maitawa aka daga, wata zazzaƙar murya yaji mai jan hankalin nafadin, " Assalamu alaika Abba yakaji kan motar tayi ko, shiru yayi chan yace , " wslm,

waro ido binta tayi jin ba muryar Abba bace kafin tayi magana taji ance, " sunana sir Yusuf ko zan iya sanin dawa nake magana ina nufin matsayinki a wajen wannan mai wayar, binta kirjin ta na dukan uku uku daker ta iya cewa, " sunana binta ni yar mai wannan wayar ce, " good, sir Yusuf ya furta ya ƙara da cewa, " tom daman yasamu hatsarine a babban titin cikin gari yanzu haka yana Alkhairat hospital, binta bata gama saurara ba ta fasa uban ihu tana jifa da wayar gefe, da sauri ummah ta shigo tana cewa, " ya ya ya ya binta waye ya mutu , binta na kuka tace , " ummah yanzu aka kirani ake cemin abbana yayi hatsari , salati ummah ta rafka tana nema guri ta zauna a kasa daɓas dan jirine yafara dibanta

Mama na daki tana jiyo kukan binta ta fito har tin tiɓe take ta shiga ɗakin tana cewa, " ya mutu ko, girgiza kai binta tayi cikin kuka ta jawo wayarta dake ringing ta kara a kunne tana cewa, " yallabai gamunan zuwa yanzu zamu zo dan Allah Abbana yana raye ko?, " shiru sir Yusuf yayi chan yace, " kudai zo muna jiranku,

Ba shiri su binta suka rankaya duk su ukun hospital ɗin suna zuwa suka haɗu da sir Yusuf suka tambaye shi lafiyar Abba yace jiran fitowar likita yake, bakin emergency room suka je suka tsai tsaya saidai likitan ya fito yace sir Yusuf ya bishi office da sauri suma sukabi bayansa bayan sunje office ɗin sir Yusuf yake cewa Dr iyalan ɗaya daga cikin majinyatan ne, saida Dr ya zare glss ɗin fuskarsa sannan yafara magana da cewa, " mummanan hatsarini ɗaya cikin ikon Allah ya rayu ɗaya kuma ya rasu dan bama a shigo dashi hospital dinnan da raiba , kuka binta ta fashe dashi tana tsugunnawa akasa cikin tausayawa Dr yace ki daina kuka kuyi hakuri muje kugansu sai ku tattance naku ,

Suna shiga dakin gawar suka ganshi a rufe cikin wani irin bari da jikin binta yake ta tsaya ta zuba masa ido kirr tana rayawa a ranta wai yanzu abbanta ne wannan ya mutu ya barta, ummah da mama sai kuka suke sun kasa buɗe fuskar gawar sir Yusuf ne ya matsa kusa da gawar ya bude suna ganinshi suka saki ajiyar zuciya a fili suna hamdala ga Ubangiji da yasa ba Abba bane,

Sai da suka fito suka cewa sir Yusuf ba shi bane , sir Yusuf ya jinjina kai dai dai lokacin da yan sanda suka zo wajen suka miƙa masa wasu ta kaddu ya karɓa ya karanta chan ya zaro biro a aljihunsa yasa hannun sannan ya basu takaddin ya maida ganinsa gasu binta yace suje

Inda aka kwantar da Abba ya kaisu suka shiga gaba dayansu bin ta na ganin Abban taje da sauri ta riƙe hannun sa tana zubar da hawaye sosai yaji rauni dan kansama yasha naɗi da bandeji ga kananan ciwuka anyi dinki, sosai suka shiga tashin hankali sai koke koke suke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login