Showing 21001 words to 24000 words out of 67181 words

Chapter 8 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx

tasa kike ganin kamar kanmu ɗaya, kai kawai binta ta sunkuyar bata ce uffanba ita kuma malak tacigaba da cewa, " zan dinga biyanki dubu ɗari uku idan kuma kinji bazaki iya aikin a hakaba kitafi na koreki, takowa binta tayi a hankali kamar wadda kwai yafashewa a ciki ta saisaita murya tace, " kiyi hakuri malak wlh bansan hakan ba taarin gidanku bane cin abinci da talakawa kuma insha'Allah namiki Alkawari bazan sake aikata makamincin wannan ba sannan kuma albashin da kika rage nagode duk da haka inason aikina Allah yaƙara huce zuciyarki , wani banzan kallo ta watsawa binta ta tabe baki bata furta komaiba ,

Binta na tsaye malak ta gama gwallinta ta fesa turare tasa takalmi ta kalli Binta dake gefe tayi mata nuni da hannu taɗau jaka tabiyo bayanta, haka kuwa binta tayi malak nagaba tana takun isa wanda zuwa yanzu ba sabon abu bane ganin hakan a wajen binta, suna fita harabar gidan wata dalleliyar mota baka tazo tayi parking a gabansu fayez ne yafito yana ganin binta yayi wani irin sororo bayyi tunanin zai gantaba hakan yasa ya kasa hakuri yacewa malak, " wannan fa?, wani irin watsa gashi malak tayi cikin salo najan hankali tace ," mai rikemin jakace kasan taron zai iya ɗaukar awa uku shiya zani da ita idan ina bukatar ruwa ko wani abun saita kawomin, kai kawai ya gyada yashiga mazaunin direba ita kuma malak ta zauna kusa dashi binta kuma tana tsaye ganin fayez ya tada mota yasata saurin zuwa jikin motar zata bude gidan baya ta shiga , wata uwar tsawa malak ta daka mata take jikin binta ya hau ɓari cikin ruwan bala i malak tace, " kinyi haukane motar mijin nawa zaki hau wacece ke a matsayin ki nawa,? jikin binta na ɓari tayi baya da sauri malak tana kuma banka mata harara ta karɓi jakar ta tace, " kitsaya anan jamel zaizo shizai kawoki,

Binta na tsaye kamar jira take motarsu tawuce hawaye suka fara sassarfa a fuskar ta chan ta hango jamel yazo da mota da sauri ta share hawayenta ta shiga yaja suka tafi,

Wani katafaran wajen tarone daya amsa sunansa wanda dagasu sai su ke iya kama wajen saboda haduwar sa binta tana fitowa taga kalar shigar matan wajen ba karya kowa kuɗi ya ratsashi ƴaƴan wane da wanene fal wajen sunata zuwa a manya manyan motocin su, shiga tayi lokacin ɗakin taron yacika maƙil har anfara kaddamar wa abinda yakuma bawa binta mamaki yadda taga manya manyan jiga jigan gurin sunata haba haba da malak sosai binta ta karanci girma da matsayin malak a wannan kasar ta Nigeria

Ratsowa binta tayi ta gefe inda wasu kamar masu raba abinci suke tsaye ta rakube a wajen dan ita bataga mazaunin irintaba, taro yayi taro ana kaddamar da kayan mutane maza da mata chan aka kira sunan malak wani irin tafine ya hargitsa wajen malak ta taso tana ɗagawa mutanan wajen hannu alamar gaisuwa ta hau kan dandalin da ake bukatar ganinta ta karbi lasifika cikin lafiyayyan turanci mai cike da kwarewa tafara bayani, tana gama bayanin ta nuna wata hanya take wata kyakkyawar baturiya ta fito jikinta sanye da wata arniyar riga mai masifar kyau waje yakuma ruɗewa da tafi sai a yanzu binta ta fahimci kayan jikin baturiyar shine wanda malak ta zana, masu manya manyan Company ne suka fara taya kayan tayi na manyan kuɗaɗe idan wannan ya faɗa sai wani ya tashi ya faɗi kuɗin daya zarce haka malak batace ta siyarba tanata jira taji farashin kuɗin daya ninka na sauran saboda matsayinta ya kuma ƙaruwa a idon mutanen wajen , chan fayez ya mike yace ," 100 million dollars , wani irin mahaukacin tafi wajen ya ɗauka take yan jarida suka juya Camera zuwa kan fayez ,

Malak daɗi kamar ya kasheta wata irin izza takumaji a tattare da ita a ranta ta aiyana babu macen da zata kaita cikin wani irin salo na shauki takara lasifika a bakinta tace, "one is like a thousand ina alfahari dashi kuma ina mai farincikin sanar daku nanda watanni biyu masu zuwa we will get married ,

Binta dake gefe wani irin danƙa taji zuciyar ta tayi ga kanta yana sarawa saboda tsantsar takaici tanaji tana gani akan idonta fayez ya nunawa duniya san dayakewa malak, speaker ne ya bukaci fayez ya hawo dandali ana nemanshi fayez ya mikey cikin takunnan nasa mai jan hankali ya ƙarasa inda malak ta ke, malak ta kashe masa ido ɗaya ta ruko hannun sa bai auneba sai jiyayi tayi masa kiss a kumatu, tafi gurin yakuma kachamewa dashi kowa yana faɗin sun dace haɗuwa ta haɗu da haɗuwa an haɗe kyau ya haɗu da kyau haka speaker yake kira,

Malak a hankali takebin yan taron da kallo chan idonta yakai kan binta tayi yaƙe ta miƙa hannu tayiwa binta alama tazo, binta dake sandare kamar mutum mutum saboda tafasar da zuciyar ta take mata tana ganin malak ta kirata hankalin ta ya kuma tashi dan wajen baiyi kala dana zuwan irintaba sai da malak ta kuma yi mata alama da hannu Binta tajawo ciki a hankali ta keto wajen yan jarido sunata daukar hoto wutar Camera ce kawai take tashi haka binta ta ƙarasa tana sunkuyar da kai,

Alama malak tayi mata data hawo saman wajen binta naganin ido yayi mata yawa jikinta yasoma ɓari ta hau ta matsa kusa dasu malak tayi mata raɗa a kunne, " ki tsugunna kiduban zobena ya faɗi kasa ,

Durkusawa binta tayi kasan wajen tanata lalubawa tana bubawa bataga gomaiba fayez ransa yayi matukar ɓaci dan yaga abin na malak tsantsar wula ƙancine ita kuma malak ko a jikinta sai sakin murmushi take tana gyara salon hoto, chan taɗan daki binta da Ƙafa binta ta ɗago kai malak tace, " barshi kawai jeki tsaya a mazauninki, tashi binta tayi ta fice daga wajen taron gaba ɗaya

Chan bakin get ta tsaya tana kuka mai cin rai tunda take ba a taɓa wulakanta ta irin na yauba, guri tasamu ta tsugunna ta haɗe kai da gwaiwa tana raira kuka mara sauti kozata samu sassaucin raɗaɗin da zuciyar ta take mata

Acikin wajen taron kuwa fayez yana ganin binta ta fita shima yafito malak tana kallon sa,

a bakin get ya hango binta a tsugunne cike da tausayinta yaje ya tsaya akan ta ransa idan yayi dubu ya ɓaci saboda abin da malak ta aikata mata cikin zullumi yayi ta maza yace ," kiyi hakuri binta, ɗaga kai binta tayi ta kalli mai maganar tabbas shine cike da ƙunar rai ta mike tsaye tana masa kallon tsana ta ce, " kabani mamaki fayez a gabana kanunawa duniya kana sonta bakada bakin bani hakuri tunda kariga kanunamin zahirinka , zaiyi magana kenan Binta ta juya zata tafi charab taji an rike hannunta tana juyowa taga shine tabuɗe baki zatai magana kenan taga malak a tsaye tana kallon su, Binta naganin haka tayi saurin fusge hannun ta tafita daga wajen taron,

Shiru kawai fayez yayi ya kai kusan minti biyar yana tunani, malak kuwa tunda taga lokacin da fayez ya riƙe hannun binta ta ƙufulu sosai tashiga tunanin manufar hakan,

Binta kai tsaye motar haya tahau tana tafe tana kuka a adaidaita idon nan nata sun kumbura sunyi jajir , har ƙofar gidansu mai mashin ya kaita ta bashi kudinsa tashiga gida,

Sai wajen biyu na rana aka gama taro abinda ya kuma ɗaurewa malak kai shine yadda fayez ya tsaya a mota yaki dawowa ɗakin taran ana tashi kuwa ta je tasameshi bayan yaja motar sun fara tafi ta kalleshi tace, " menene haɗinka da yar aikina har kake riƙe mata hannu , banza yayi mata baice uffan ba , cije baki tayi takuma cewa , " tambayarka fa nake fayez menene haɗinka da Binta ?, a fusace yaja birki saida ta tsorata ya waigo cikin ruwan bala i yace mata , " santa nake budurwa tace kuma aurenta zanyi,

✍🏼 zeenariya

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (14)

Wani irin ɗauke wuta malak tayi haɗi da kafe idanun ta a kansa , fayez yana dukan sitiyari yaƙara dacewa ," ina santa kuma wallahi bazan taɓa aurenki ba harsai na sameta, wasu irin zafafan hawaye suka shiga sarara akan kuncin malak cikin wani irin raunin zuciya tace, " fayez ni zakai wa haka ?, ta karashe maganar tana nuna kanta, kai ya gyada mata alamar eh sannan ya ƙara da cewa, " kina daukar kanki wata tsiya keba komai bace mata irinsu binta sune matan da kowane namiji zayyi sha awar hada zuri'a dasu basa shaye shaye basa mu a mala da maza uwa uba addini sunsan kansu matsayin musulmai sun rike addinin su suna sallah sannan kuma sunada ilimin addini, malak bata iya ƙara furta ko wace kalma ba dan maganganun daya faɗa mata su suketa ƙoƙarin tarwatsa mata zuciya, dogon tsaki fayez yaja baikuma cewa komaiba ya dannawa motar wuta da mugun gudu kamar akan motar yake hucewa,

Binta tana zuwa gida umma ta titsiye ta da tambayoyi mai yake faruwa tayi kuka haka idonta suka kumbura, duk da binta bata yanayi na nutsuwa hakan baisa ta faɗawa ummanta gaskiya ba sai tace kantane yake ciwo shiyasa datasha magani tace zata dawo gida,

Suna isa fayez yayi parking a bakin get yace ta fitar masa daga mota ba shiri ta fita tundaga harabar gidan tayi cilli da jaka kafin ta shiga babban falo tayi watsi da takalman kafar ta dagudu ta haura saman bene tana zuwa bedroom dinta taje ta tsaya abakin dressing mirror tana kallon kanta maganganun da fayez ya faɗa matane suketa yawo akanta wani uban ihu ta kurma iya karfinta ta durkushe ƙasa tana buga hannunta a ƙasa tana raki kozata samu sassaucin raɗaɗin da takeji,

Mom tana ɗakinta tajiyo ihun malak ihu mai karfi bana wasaba dagudu ta fito har gware suke da juna itada papy wajen shiga ɗakin, suna ganin halin da ƴarsu take ciki suka ƙarasa suka rirriketa suna haɗa baki wajen tambayar mai yake faruwa, dafe gefan zuciyar ta tayi tana gunji haɗi da nannauyan haki tana kiran, " saina illatata bazan barmata shiba wlh saina illatata ƙaryane fayez nawane ni kaɗai danni aka yishi , maganar tata ce ta cije saboda hakin da take, da sauri papy ya zubo ruwa ya kawo mata tayi wani mugun cilli da kofin ya fashe, tashin hankali ba a samaka rana babu yadda mom da papy basuyiba da malak taki rarrasuwa bare susan gundarin abinda yake faruwa hakan yasa mom takira Ammeen fayez ta faɗa mata dan tasan ita kaɗai zata iya rarrashin malak indai akan fayez ne ,

Jiki na rawa Ammee tazo tana zuwa taga halin da malak keciki duk ta faffasa kayan kwalaben da ke ɗakin tana ta cilli da kaya tana zage zage, cikin yanani na tashin hankali Ammee ta ƙarasa malak na ganinta takuma sakin marayan kuka ta rungume ta , cikin tsananin tausayin malak ta zaunar da ita a kujera itama ta zauna tana riƙe da hannayen ta tace, " malak mai yake faruwa mai fayez yayi miki dan ko kaffara babu nasan akansa kawai ranki zai ɓaci haka, sai a lokacin hankulan papy da mom suka dawo daidai suka baza kunnuwa suna sauraran abinda malak zatace, malak na buɗar baki tace , " wlh Ammee zan iya kisa akan fayez bazan taɓa kyale binta ba ashe itace wadda take huremasa kunne akan aurena kuma dabakinsa yace ita yakeso bazai taɓa aurenaba sai ya aureta , Ammee ce tajuyo ta kalli mom tace, " wacece Binta?, mom najin haka ta taso ta zauna kusa da malak tace, " wace bintan?,

Malak tace, " binta mana wannan dai yar aikin nawa, kama baki mom tayi cikin mamaki papy kuwa jinjina kai yayi yace, " malak banda shirme ke yanzu akan wannan zaki tsaya kina ɗagawa kanki hankali, tsaki kawai yayi ya fice mom ma ta keɓe baki ta fice ɗakin yarage daga malak sai Ammee , malak ta kalli Ammee tace, " ashe yar aikina ce musabbabin da tasa fayez ya juyamin baya abinda yakuma ɗagan hankali shine akan wachchan yar mutsiyatan zai nuna niba komai bace ya fifitata akaina ,

Ammee cikin hassala tace , " shiyama isa ai wlh komai zai faru saidai ya faru idan har bai aurekiba tosaidai ya mutu ba aure , rungumeta malak tayi tace, " Ammee menene mafita bazan iya jure rashinshi ba,

*

Bayan sallar magriba ta zauna tayi addu'a sosai akan halin da take ciki taroki Allah ya cire mata son fayez daga zuciyarta ta sannan kuma ya dasa mata son jamel , ummah ce tashigo da abinci a hannunta saida ta jira binta tagama addu'ar tace mata , " ga abincin ki kisamu kici saiki kuma shan maganin , karba binta tayi ta ajiye sannan tace , " ummah inason na ajiye aikina , waro ido Ummah tayi tace, " Binta akan me zaki ajiye aiki ?, sunkuyar da kai tayi tace, " ummah ki gayawa Hajiya haleema ta samamin wani aikin banason wannan , ajiyar zuciya ummah ta sauke tace , " binta babu wani aiki dazaki samu kuɗi irin wannan kuma yawanci aikinsu duk na kwanane kuma kinga wannan bana kwana bane a kaiki adawo dake kyauta batare da kudinki yayi ciwoba saidai koda wata matsalar ne bakyaso kifadan , girgiza kai kawai binta tayi tace , " ummah bawata matsala, haka ummah ta tashi tabar ɗakin bawai dan ta yarda da abinda binta taceba ,

Misalin bakwai da yan kai fayez ya kirata a waya tana gani taƙi ɗagawa ya kuma kiranta taƙi ɗagawa chan sai ga message ya shigo tana gani ta duba, ( kifito ina ƙofar gidanku yanzu magana ƙalilan zamu tattauna pls ) tsaki kawai binta taja tana shawara da zuciyar ta taje ko karta je chan sai ta yanke shawarar zuwa dantaji mai kuma zai ce mata,

Tana fita ta ganshi a jingine a jikin motar sa bata ƙarasa ba yana ganinta ya ƙaraso ya tsaya daga bakin get ita kuma tana daga ciki, ƙaramar ajiyar zuciya ya sauke yace, " binta kifahimce ni karki cutar da zuciyar ki wajen tilasta rabuwa dani bayan kuma tana sona, kallonsa tayi taja numfashi ta sauke a hankali hawaye na bin fuskar ta tace, " fayez haƙiƙa da gaske zuciya ta tana sanka amma bazan taba yarda na aurekaba saboda malak kuma ga dukkan alamuma tamu bazatazo ɗaya da mahaifiyarka ba kaga kuwa babu amfanin kasancewar mu tare fitintinu ne kawai zasuyita faruwa,

saurin katseta yayi da cewa, " kisa a ranki babu abinda zai faru sai alkhairi babban tashin hankali agunmu shine rabuwa da juna,

" fayez banason nazama sanadin tarwatsewar rayuwar..., saurin toshe mata baki yayi yana girgiza kai alamar aa yacigaba da cewa, " ki yarda kiyi imani da Allah mudawo da soyayyar mu namiki Alƙawarin babu abinda zan bari ya sameki ni kikeso kuma dani zaki zauna bada malak ko Ammee ba, shiru binta tayi tana Nazarin maganar sa chan ta nisa tace, " na Amince mukoma soyayyar mu, fayez yanajin haka yasaki dariyar farin ciki ya chafko hannayen ta ya sumbacesu cike da farin ciki jiyake kamar ya ɗagata sama yayita juyi da ita, " gaskiya naji daɗi dakika fahimceni Allah yayi miki albarka, cikin wani kayataccen murmushi ta amsa da Ameen ,

Jamel ne yashigo layin a ƙafa dayake dare yafarayi lokacin aikinsa ya ƙare shiyasa baizo da mota ba hannunsa riƙe da bakar leda yana tafe idonsa nakan wayar hannunsa yanata dannawa binta kira amma bata ɗauka , tunda jamel ya fara hango ƙofar gidansu binta yaga alamar mutum a tsaye a bakin get ga jibgegiyar mota afake aran jamel bai kawo komai ba atunaninsa Abbane yayi baƙi hakan yasa yana karasawa kofar gidan yayi sallama , fayez da bayansa yake juyene yaji sallama yajuye haɗi da amsawa , wani irin ƙamewa jamel yayi saboda abin mamaki da bazatar da idonsa ya nuna masa cikin girmamawa ya buɗe baki yace , " yallabai barka da dare , " barka dai fayez ya amsa , binta dake maƙale a bayan ƙofa ta dafe kirji cikin zullumi tayi ta maza ta leko, kallo ɗaya jamel yayi mata ya sunkuyar dakai cikin kunar rai da tunanuka kala kala

, cikin sanyi jiki tace, " jamel barka da zuwa,

" barka dai binta ya jikin?, sai a wannan lokacin binta ta tuna ta faɗa masa batada lafiya, " jiki da sauki,

" to Allah ya ƙara sauki, yafaɗa haɗi da miƙo mata bakar ledar hannunsa, hannu tasa ta karɓa tayi masa godiya ya juya yatafi, Binta cikin tsananin tausayin jamel ta bude ledar taga kayan marmari ya siyo mata a fili ta furta, " Allah sarki bawan Allah, fayez dake gefe sosai ya karanci soyayyar bintace a zuciyar jamel ita kuma binta tausayin jamel ne fal zuciyar ta, nan suka cigaba da hirarsu ta yaushe gamo abin da yabawa binta mamaki sam fayez bai tambayi menene tsakanin ta da jamel ba itama kuma bata cemasa ga abinda ke tsakaninsu ba,

*

Ammee batabar gidansu malak ba saida ta gama kitsa mata duk matakin da zasu ɗauka da kuma hanyar dazasu ɓullo wa lamarin, bayan tafiyar Ammee malak taji gaba ɗaya duniyar takumai mata zafi raɗaɗin da takeji da baƙin kishin fayez yadawo mata sabo hakan yasata ta ɗau makullin mota ta zare jiki batare da kowa yasan ta fitaba ta fice abinta,

Kai tsaye wata ke ɓantacciyar mashaya taje wanda bakowa ne yasan da itaba sai manyan ƙwari, tana zuwa taja kujera ta zauna da taba tafara daman ta kwan biyu bata shaba saboda gargaɗin da fayez yayi mata kwanakin baya,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login