Showing 30001 words to 33000 words out of 67181 words

Chapter 11 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx

tsana jamel ya ƙaraso ya tsaya daf dashi yace , " ina girmamaka amma akan yarinyar nan zan iya yin komai ciki kuwa harda karta maka tsagwaran rashin mutumci inaji ina gani bazan bari kalalata wadda zan auraba, Malak dake bayan fayez cikin mamaki ta jinjina kai tana kallon fayez chan taga yayi murmushi yace, " yaro yarone ashe kaima kashigo layin masusan rabani da ita , yar dariya fayez yakuma saki ya dafa kafaɗar jamel kawai ya shige abinsa , wani irin kallo malak takebin Jamel dashi da alama idonsa ya rufe bai lura da tana wajenba lokacin dayake gayawa fayez magana, taɓe baki tayi tana jinjina kai cikin mamaki tace, " a ina kasan wannan yarinyar naji kana cewa matar dazaka aurace,

Yar ajiyar zuciya ya sauke ya gyara tsaiwa cikin girmamawa yace, " a gidan nan nafara ganinta har muka kullah soyayyah yanzuma zanchan danake miki nakai kuɗin aurena gidansu jiya, wani irin murmushi ne ya suɓuce a fuskar malak jitai kamar tayi shewa tsabar farin ciki kawai saita basar ta haɗe rai ba alamar wasa a fuskar ta tace, " ko yayi wuce kaje zan nemeka, juyawa tayi ta shige gida

A falo ta taddashi tsaye, karasawa tayi kusa dashi dayake ba kowa a falon sai shi da ita ta nemu gu ta zauna, ganin ta zauna shima yasashi zama fuskarnan ba yabo ba fallasa yace, " kiran me kikemin haka?, malak najin abinda yace tasan basu haɗu da waheed ba dan dasun haɗu da bazai tambaye ta kiran da take masa ba, kallon ta fayez yayi yace, " kinga nifa inada abin yi kifaɗan maganar da kikeso mu tattauna, ɗan cije baki tayi a gaggauce tace , " daman akan maganar aurenmu ne, wani irin kallo yayi mata yace , " akan maganar aurenmu kuma bakincewa binta kin hakuraba, kallonsa malak tayi chan kuma saita marai raice fuska tace , " dan Allah fayez karka tilasta zuciyata daukar mummunan mataki akanmu baki ɗaya kaima kasan babu abinda zai iya goge soyayyar da nake maka,

Miƙewa tsaye yayi yana cewa , " kin daɗe baki ɗau mummunan matakin ba ke har wacece dazaki tilastani zama dake ninace banaso haba ai ba a dole, tashi itama tayi a fusace tana nunashi da yatsa tace, " fayez wlh sai anyi aurennan komai zai faru saidai ya faru kuma ina mai shawartar ka kafita a harkar yarinyar nan karka jawo mata baƙar kaddara mafi muni, zaro idon yayi cikin mamaki yace, " to kuwa kirubuta ki ajiye duk abinda yasamu yarinyar nan kece kuma idan duk duniya ne zasu tsaya mike saina ɗau mataki akai, yana ida maganar sa yafice daga gidan, Malak rasa inda zatasa kanta tayi wani irin zugi da radaɗi zuciyar ta take mata jitake kamar tasa hannu aka ta kurma ihu ,

Binta tana aiki damuwoyi da tunani kala kala ne sukai mata taran dangi tarasa ta ina zata fara ɓullo wa lamarin, bayan ta gamane ta je kitchen zata dau abinci taci kamar yadda aka saba kullum ana zuba mata,

a kitchen ɗin ta tadda Malik cikin fara a tace, " aa yaya da kanka me kake dafa mana, yar dariya yayi yace, ba girki nakeba nazo daukar lemone , hira suka fara yi shiya tayata dakko abincin da filet da ruwa suka bito dining table, abinda yabata mamaki gani tayi ya zauna kusa da ita shima yace zaici , babu yadda ta iya dan tana matukar ganin girmansa haka suka faraci da cokali daya idan takai bakinta ta ajiye shima saiya kai, suna cikin cin abincin ya tambayeta game da fashion and designer din da tayi , shiru ce ta ratsa tsakaninsu dan harta mantama ganin bazata samu mai siyaba , cikin yanayi na damuwa ta yatsina fuska tace , " yaya ni nahakura da wannan zanan , dariya yayi ya tambaye ta saboda me , ƙin faɗa masa dalilin tayi dan karyaji haushin yar uwarsa kawai sai tace ba mai siya , murmushi yayi yace , " zan haɗaki da esha na tabbatar zata siya musamman ma idan taji nina turoki kuma suma sunada babban Company idan Allah ya taimakeki kika zama babbar mai yimusu zane to ganinki sai yayi wuya a nigeriya , dariya binta tayi tanaji a ranta indai dasu madam malak to ba lallai takai wannan matsayin ba

✍🏻 zeenariya

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

WhatsApp number

+218912472599

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (19)

Lailah dake rakuɓe ta saman bene tana hangensu ne taji kamshin turaren malak a kusa da ita, cikin yanayi na rashin gaskiya ta matsa tana sosakai malak ta leƙa ƙasan banen dantaga mai lailah take leƙawa, abinda tagani yayi matukar ɗaga mata hankali ɗan uwanta mai daraja shine ya tsaya na cin abinci da binta har suna musayar yawu cikin shauƙi mai kama dana soyayya, lailah kamar tasan abinda malak ke tunani cikin ƙasa da murya tace, " maganar gaskiya binta tazo ta farraƙa muku gidane kawai waifa jinai tana cemasa ya haɗata da masu siyan fashion and designer kuma naji yace zai haɗata da wata mai babban Companyn kaya sunanta esha, saurin kallon lailah malak tayi ta jinjina kai batare datace komai ba ta nufi matattakalar tafara takunta na takama har ta karasa, binta na ganin ta taji a jikin ta da matsala da sauri ta mike tsaye tana cewa, " barka da futowa, wani irin kallo tayiwa binta wanda duk wanda aka jefa da wannan kallon yasan na tsana ne, cikin yanayin mamaki ta gyara tsaiwa tace, " ni abinda ban gane mikiba shine maza uku zaki aura ko yaya?, saurin kallon ta binta tayi tanajin kirjinta na dukan uku uku

Yar dariya malak tayi ta maida ganinta ga Malik tace, " kai kuma kaji kunya wlh karasa da wadda zaka tsaya kaci abinci saida wannan kazamar dubetafa me ake da talaka irin masifa irin bala i, tashi malik yayi yana dariyar takaici yace, " dai dan wani karkataccen wani, bai jira ta kuma cewa komai ba yabar wajen, maida ganinta tayi ga binta ta nunata da yatsa tace, " zaifi miki kyau ki tsaya iya matsayin ki karkiyi kuskuren tunanin zakiyi amfani da ɗan uwana kisamu wata ɗaukaka , tana gama fadin haka tafice, binta gaba daya hawaye ya wanke mata ido a zahiri tafi ganin lefin kanta da take bawa malik fuska harsuyi wasa da dariya kamar duk dayane bayan kuma sunada banbanci ,

*

Tun safe yakeso ya samu sarari ya kira fayez a waya sai dai ayyuka sun masa yawa hakan yasa shi tura masa message yace su a hadu a diamond restaurant ,

Fayez yana zaune yaga message dinsa yayi murmushi ya turama masa message " It seems that work is too much for you ,

Koda waheed yaga sakon bai maida masa amsaba dan harga Allah yanzu haushin fayez yakeji wani sashin na zuciyarsa kuma tausayin malak yakeji

*

Koda binta ta fito harabar gida zata fita bataga jamel ba hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba dan bataso ya ganta yace saiya maidata gida, kan layin ta fito zata karasa titi ta samu abin hawa sai da tayi kusan rabi sai ga wata farar mota ta shawo kwana binta tana ganinta taɗan ƙara matsawa daga kusa da hanyar ,motar a hankali ta shigo layin amma sai ta ƙara gudu tayo kan binta gadan gadan, binta na ganin haka tayi wani muguwar razana taga motuwa chak ta tsaya ta ɗora hannu aka takasa koda motsi gashi saura kiris motar tabi ta kanta cikin zafin nama taki an fuzgota ta gefe ta faɗi ƙasa motar kuma ta wuce bata samu nasarar bita kanta ba, binta na haki ta tabi bayan motar da kallo a daidai ƙofar gidansu fayez taga anyi parking wata matashiya ce tafito daga mazaunin direba gefe guda kuma Ammee ce ta fito karaf suka haɗa ido da binta Ammee tawani cije baki ta nuna binta da yatsa alamar kashedi suka shige ,binta ta fada duniyar mamaki kamar daga sama taji a gefanta ance , " ke kwa baiwar Allah me kikaiwa waɗannan mutanan suke neman rayuwarki , juyowa binta tayi ta kalleshi saurayine da bazai wuce 18 year ba sai a wannan lokacin ta tuna shine ya fuzgota da tuni ta mutu, cikin sanyin jiki ta haɗiye wani bushashshan miyau daya tsaya mata tace , " inaga sitiyarinne ya kwacewa mai tukin Allah dai ya kiyaye sannan kaima da taimakonka nagode da cetan rayuwata, murmushi matashin yayi yace, " wannan dai daga gani kwararriyar mai tukice, shiru binta tayi dan har yanzu a tsorace take tanata tunanin ashe duk abinnan da take ɗauka da wasa ba wasa bane mutanan nan zasu iya kasheta lallai kuwa su Abba sunada gaskiya ,

Godiya ta daɗewa matashin ta tafi tahau adai daita wayarta ta duba lokacin karfe huɗu ta duba address ɗin Company da malik ya turata kai tsaye tace mai adai daitar ya kaita chan , tana sauka ta shiga kanta tsaye ta gafi sunan wacce aka turota wajenta abin mamaki kamar sunsan da zuwanta haka aka dinga wani girmamata harda kawo mata ruwa da lemo ba jimawa akace ta shigo, ran tsatstsan office ne dayaji kayan ƙawa binta tana zuwa ta kame a kujera ganin yadda matar taketa mata faran faran yasata sakin jikinta bayan sun gaisa matar ta nemi ganin kalar zanan da binta tayi ba shiri binta ta buɗe wayarta daman tanada hotunansu ta mikawa esha , guda hudune zanan sosai esha ta yaba da kyansu sai yanzu ta fahimci binta yar baiwace dan a matsayin ta na sabuwar mai zane tayi zanan da kwararrun ma ba lallai suyi kalarshi ba, take esha tayi na am ta lamunce zatayi aiki da binta kuma wannan zananma zatasa a buga samfarin kayan a wallafa a wajen baje koli na manya manyan yan kasuwa na bangaran tufafi a siyar , sosai binta taji dadi ta dinga godiya harta fito bakinta ɗauke da fara a, tun a adaidaita ta kira yaya malik ta faɗa masa an karɓa sannan takumai masa godiya , fayez ma saida ta kirashi tayi masa wannan albishir din,

Koda ta karasa gida tanata murna jinta take fes dan burikanta na tara kuɗi ta taimaki iyayenta yana daf da cika, bayan Abba yadawo daga masallaci taje ta sameshi ta bashi hakuri akan abinda tayi masa cikin jin dadi Abba ya tambaye ta shinta amince da auren Jamel binta najin haka tayi tsit dan ko za a ɗau ranta jitake bazata taɓa iya juyawa fayez baya ba cikin yanayin rashin jin daɗi aranta tace,

" Abba hakika kai ubane da baka chanchanci nayi jayayya dakai ba akan zabinka, murmushi yayi yace, " binta badai zabina ba zabinki dai, jinjina kai tayi tana hawaye tace, " Abba na kawo maka shine don na goge mana raɗaɗin fayez a lokacin da muke tunanin aurena dashi ba abune mai yuwuwa ba amma gaskiya Abba bazan iya rayuwa da Jamel ba inaiwa fayez sonda zan iya kare rayuwata batare danaji wani ɗa namiji ya koda burgeniba wallahi abba idan na auri jamel bazai taba samun farinciki ba duk da bawai ina nufin zan munana masaba saidai bazai samu sahihiyar kauna daga gareniba zan rayu tamkar mutum mutumi a karkashin sa , kukane mai karfi ya kwace mata , shiru Abba yayi a matsayinsa na mai hankali yana nazartar maganar ta chan yace ta tashi ta tafi kawai ,

Zazzaune suke a harabar diamond restaurant kamar yadda suka shirya wa kansu haɗuwa fayez ya fahimci sauyi a fuskar waheed cikin yanayi na matsuwa yaji abinda yasashi neman suyi irin wannan zaman yace ,

" yadai bro ina jinka kiran me kakemin , gyara zama waheed yayi yana maida hankalinsa kan fayez yace ,

" inaso ka gayamin kwakkwaran dalilin daya sauya ra ayin aurenka akan Malak, shiru fayez yayi yana jinjina kai chan ya gyara ya fuskunci waheed sosai yace,

" kafi kowa sanin kowane namiji yanada kalar ra ayinsa akan mace to nima hakanne ra ayina ya sauya daga kan malak daman chan kawai dan banga wadda naji tayi daidai da rayuwata bane, cije baki waheed yayi yace " fayez ka zalunci yarinyar nan kaci amanar soyayyar data daɗe tana nuna maka bazan ɓoye maka gaskiya ba kai ne kake ƙoƙarin aikata kuskure idan ka rabu da ita shiyasama iyayenka sukaƙi baka damar ka nemi auren wata, fayez sosai ya musata da maganar waheed kawai saiya dakatar dashi da cewa , " waheed bazaka ganeba tsakanin malak da binta akwai wani muhimmin abu dayasani daukar ɗaya kuma ya tilastani barin ɗaya kamar rufaffan abinci ne da buɗaɗɗe kana ganin mai tsabta ya zaka kai kanka kazamar rayuwa wadda gaba bazata haifar maka da komaiba sai nadama, waheed yanajin haka ya fusata ya miƙe yana cewa, " eh dole kafaɗi haka tunda ka gama da ita watakila kasamu duk abinda kake kwaɗayi a tattare da itane shiyasa kake harin sabuwa, shima fayez yanajin haka ya miƙe a fusace yana nuna waheed alamar gargadi yace, " ka kiyaye niba mutumin banza bane tunda nake bantaɓa neman malak ba ka tambaye ta duk da a rashin kamun kanta tasha sakarmin kanta amma ban taɓa yin kuskure wani abu ya shiga tsakanina da itaba, murmushi kawai waheed yayi cikin dacin rai yace, " Allah ne kawai zai iya tabbatar da zahiri nidai ina mai baka shawara karka yadda kwadayi dasan zuciya yasaka barin rayuwar malak ta salwanta saboda kai ka sani a wannan takin tana daf da halaka kuma idan ta hakala ubangijima bazai taba yafe makaba bare kuma iyayenta da naka , waheed yana gama faɗin haka yabar wajen zama fayez yayi yai shiru yana nazarin maganar waheed,

✍🏻 zeenariya

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

WhatsApp number

+218912472599

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (20)

Waheed yana tuki yana tunanin maganar da fayez ya faɗa masa a wani sashin na ransa yanaso ya gasgata shi dan yasan halinsa baya neman mata amma kuma idan ya tuna yadda shaƙuwarsu take da malak tsawan shekaru sai yaga inaaaa ai dole akwai abinda ya shiga tsakaninsu shiyasa ya daina sha awar aurenta yanzu,

Kasa hakuri waheed yayi bayan yayi parking a ƙofar gidansa yana daga cikin motar ya kira malak a waya bayan sun gaisa yake ce mata, " nasameshi yanzu ma muka rabu har nazo gida,

ajiyar zuciya malak ta sauke tana gyara zaman Bluetooth din kunnan ta tace, " ina jinka ya kukai?, yar ajiyar zuciya shima ya sauke yace , " maganar gaskiya bansan inda fayez ya dosaba ni inada zafi bana iya jure ganin ga gaskiya kuma mutum sai yaƙi bi ƙiri ƙiri dan harsaida mukai hayaniya dashi kafin mu rabu , shiru malak tayi chan da sassanyar murya tace , " nima nasameshi da safe danai masa magana akan auren saiya nuna ai shi kawai yama rabu dani , " kawai kiɗan bani kwana biyu zansan abinda zanyi akai amma pls karki ƙara shan komai kinga ke ƴar kasuwace da kike juya Company bai da kyau sam kidinga tittilawa kanki fetur kuma kina wasa da ashana idan kikace zaki biyewa fayez zaisaki kima rasa kwakwalwarki nan gaba kinga daganan sai yasamu hujjar dazai

Fake da ita yaƙi aurenki

Malak yi tai kamar ta ɗauki shawarar Dr waheed dan ta kuma cusa tausayinta cikin zuciyar sa, suna gama waya ta kira Ammee bayan sun gaisa take cewa, " Ammee nagajifa zan dau mataki akan yarinyar nan Ammee bazan iya jure ganin ta da fayez ba, shiru Ammee tayi tace, " kibi komai a sannu jada baya ba tsoro bane salan yaƙine shima, nan suka gama yan kulle kullensu da kitse kitsensu sukai sallama

*

Washegari da safe binta tagama shirinta tsaf taje tasamu Abba a daki yana lazimi ta gaisheshi ya amsa tayi masa sallama ta tafi, tana fitowa kofar gida taga Jamel a cikin mota da alama ita yake jira aranta tace jarabar duniya kenan, karasawa tayi ta shiga daga gaisuwa batace masa uffanba yanata kokarin janta da hira ita kuma taki sakin jiki daga umm sai uhm uhm har suka karasa tafita ta shiga gidan abinta,

Dakin malak kai tsaye ta nufa tana shiga taga bata ciki da alama ta fita da sauri binta tafara aikinta

Da yamma binta ta koma gida farincikin data gani a idon ummah ne yasata tsan tsar mamaki kamar anwa ummah albishir da gidan aljanna binta tayi tayi Ummu tafada mata abinda yake faruwa ummah taki faɗa wai saita huta tukunnan binta da naci haka ta titsiye ummah tana shagwaɓe mata saitaji abinda yasata farinciki, chandai da ummah tagaji ta kama hannayen binta tana sake sakin fara a tace, " Abbanki yacemin ya a mince kicewa fayez ya turo iyayenshi, Binta najin haka batasan sanda tasaki ihun murna ba ta rungume ummah cikin tsantsar farin ciki tana godiya,

Kasa hakuri binta tayi tana fita daga ɗakin ummah tashiga nata ta kulle ta baje akan bed tanata hamdala ga Allah ta ɗau waya ta kira fayez, ko jiran su gaisa bataiba tayi masa albishir ga mamakinta sai taga kamar baya farinciki duk da ya nuna mata yayi murna amma yanayinsa ya tabbatar mata akwai damuwa aranta ta raya kodan yana ganin duk rintsi bazai rasata bane,

Bayan sun gama wayar fayez yayi shiru yana tunanin ta inda zai bullowa lamarin tunda ga damar neman auren binta tazo a sauki,

Da daddare bayan ya koma gida ya kasa zaune ya kasa tsaye yanaso ya shawo kan Ammee kuma yanajin tsoron abinda zai faru , a haka dai yayi ta maza yaje ya sameta a ɗaki ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login