Showing 42001 words to 45000 words out of 67181 words

Chapter 15 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx

zaune akan dadduma fayez ya kirata tana dagawa tafashe da kuka saida yayi shiru yana sauraren ta chan tace, " fayez ina cikin wani hali ummana batada kowa sai Abbana bazata iya jure rashinsa ba nikuma farin cikin iyayena shine nawa bazan jure ganinsu haka ba,

Fayez dake zaune cikin mota yana rike da wayar yayi tagumi cikin damuwa yana sauraren bayaninta haɗi da kukanta chan data gama yace , " kiyi hakuri bafa ayanke hukunci gaba ɗaya ba ,

" fayez babu wata alama da tanuna zamuyi nasara a wannan Shari'ar , " haba Binta kinsanfa Shari'a saɓanin hankali ce , binta na shirin yin magana taga ummah ta shigo kawai saita cewa fayez tana zuwa zata kirashi ta kashe wayar,

Zama ummah tayi ɗauke da charbi a hannunta tace, " fayez yayi iya bakin ƙoƙarin sa binta bashi da yadda zaiyi ne dayanada shi daya fidda abbanki, jinjina kai binta tayi tana hawaye,

Bayan sati ɗaya,

Malak bata kumaiwa fayez maganar saida asibiti ba shima kuma bai kuma shiga harkarta ba amma duk da haka da maganar yake kwana yake tashi ga kuma matsalar binta yanzu ko waya basayi sosai bare zanchan wata soyayyah kullum yana kiranta a waya daga gaisuwa kawai saitace tanada abinyi ta kashe, duk da haka yana mata uzuri saboda halin da take ciki amma abin yana damunshi dan har ya rame kallo ɗaya zakaimai ka gane da damuwa idan har ka sanshi a baya,

*

Binta na gama shara taje kitchen zata ɗora girki sai ta tarar shinkafar ta kare buhun ba komai daman mama ke siya kuma batakai ga siyan ba wannan iftila in ya faɗo gashi yan kuɗin da suka ragewa binta duk sun ƙare a jigilar lamarin Abba, dafe kai binta tayi ta duba kwalin taliya shima sai ɗaya makaroni da fulawa duk babu, sai da binta tayi kwalla sai a wannan lokacin ta tuna da aikin ta da sauri taje ɗakin ummah ta zauna ummah na kwance binta tace ," ummah komai ya ƙare mana gobe insha Allah zan koma wajen aikina tunda banida ko sisi yanzu idan yaso sai nace tabani rabi insai mana abincin , sosai ummah tayi naam da wannan zance,

Da daddare Binta na kwance sai fargaba take da zullumi Allah dai yasa malak bata sake yar aikiba, lailah ce tabaɗo mata arai ta wajenta kawai zata iya samun amsa aikwa sai ta danna mata kira bata iya jira sai gari ya wayeba, bayan lailah ta daga sun gaisa tace," au wai daman kece ina kika shiga inata neman lambarki ban samuba , " haba lailah baki damu dani bane shiyasa baki ajiyeba , yatsuna fuska lailah tayi tace , " hmmm Binta akwai gagarumar jaridar danakeson nasiyar miki shiyasa naketa nemanki ido rufe,

Gyara zama binta tayi tace, " to suda uwar labarai shaƙamin abinda kika ƙunsa, " uhmm binta ina tsoran faɗa mikine karkice a bakina kikaji, marai raice fuska binta tayi cikin damuwa tace, " kinga lailah abar wannan maganar indai bata shafeniba,

✍🏻 zeenariya

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

WhatsApp number

+218912472599

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (27)

Binta wannan magana ai ke tashafa da bata shafekiba ba zan tayin zumuɗin faɗa mikiba,

" ni kuma lailah ? to inajinki mai yake faruwa ko dai sokike kice malak ta chanza mai aiki?,

" inda batun chanza mai aikine ai da sauki shin kinsan kuwa banda satinnan wanchan satin daya wuce aka kama fayez da malak a gida suna zina turmi da taɓarya?, binta najin haka wata uwar kwarankwatsa ce ta sauka a farfajiyar zuciyar ta wanda hakan yasata kamewa cikin wutar mamaki, shirin da lailah tajine yasata faɗin, " hello hello binta kina jina kodai network ne, binta dake zaune sharaf ko wayar bata iya hange saboda hawayen dake sitata a idon ta ba kakkautawa tace, " lailah menayi miki zaki gayamin wannan muguwar maganar dakinsan illar da maganar nan zatamin da bazaki faɗan ba innalillahi wa innah ilaihirraju un,

Yar ajiyar zuciya lailah ta sauke taƙara da cewa, " kiyi hakuri binta nidake duk ɗaya ne tausayinki ne yasani sanar miki gaskiya wanda zaki aura mugun fasiƙine ita kanta malak ɗin sau biyu yana mata ciki tun batakai hakaba shiyasa kaf family ɗinsu suka damu sai an musu aure shikuma yaƙi dan yariga yagana da ita,

" pls lailah ya isa haka Nagode sai anjima, binta ta faɗa cikin mawuyacin hali, lailah saurin cewa tayi, " zan kashe amma dan Allah karkice a bakina kikaji wannan sirrin family dinsu ne bazasu kyaleniba idan sukasan na fallasa, to kawai binta tace ta kashe wayar ta saki kuka mara sauti cike da tausayin kanta sai yanzu ta gano abinda yasa malak ta bar mata fayez ashe tasan abinda ke tsakaninsu kenan ko auren akai karshe dai dole sucigaba da sheƙe ayarsu ita kuma abarta hoti ho, ta lula duniyar tunani sosai gefe ɗaya kuma na zuciyar ta haushin fayez da tsanarsace keneman wajen zama ,

*

Yana zaune a office yana wasa da biron hannunsa fayez ya shigo ya amsa masa sallamar haɗi da nuna masa waje ya zauna mamakin waheed sam ya kasa ɓoyuwa duk da haushin fayez yakeji hakan bai hanashi gyara zama yace, " fayez lafiya kuwa kake naga karame haka kodai kayi cutane banida labari, jinjina kai fayez yayi ya shafi fuskarsa yace, " ina cikin matsala waheed narasa yadda zanyi ko abinci bana iyaci sosai malak ta matsamin wai zata saida hospital dinnan saboda naki aurenta, dalla dalla fayez yayiwa Dr waheed bayani saida ya gama yace masa, " to menene abin ɗaga hankali anan ka aureta mana ai malak ba irin macen da namiji zai guda bace kai kasani basai na faɗa makaba duk abinda namiji zaiyi kulafuci akan mace malak ta haɗa kyau iya gayu wayewa aji ilimi uwa uba dukiya,

Jinjina kai fayez yayi yace, " waheed ba irin wannan macen nakeso ba amma nasan duk yadda zan maka kwatance bazaka ganeba nidai dan Allah kawai ka taimakeni kasa baki a maganar nan ta jenye maganar saida hospital , " gaskiya fayez bansan da wane ido zan kalli malak ba amma zanyi tunani idan na yanke zuwa zakaji yadda mukai, kallonsa fayez yayi cikin hassala da abinda yace batare daya kuma furta komai ba kawai ya tashi ya fice,yana fita waheed yayi shiru shi kaɗai chab aransa yace gaskiya ba ayiwa fayez adalci ba idan aka rabashi da hospital ɗinnan,

Da daddare fayez rasa inda zaije yasamu sassaucin abinda yake faruwa dashi yayi kawai sai masoyiyarsa ta faɗo masa ya nufi gidan yana zuwa yayi parking a ƙofar gidan ya shiga kiran wayarta sau uku ana katsewa saida ya cigaba da kira ta ɗaga cikin mamaki yace, " yadai ina kira kina katsan waya lafiya, shiru yaji tayi masa kawai sai yace, " kinga ki fito ina kofar gida, katse wayarta tayi ya kalli fuskar wayar ya rasa mai yake masa daɗi sai da binta ta shafe kusan minti goma sai gata ta fito,

Tana zuwa ta buɗe motar ta shigo ya kalleta ba gaisuwa sai shi ya gaisheta da kyar ta amsa yace, " binta na kasa gane mikifa abin naki kullum ci gaba yake kodai kin daina sonane, ya faɗa yana kafeta da ido kozai karanci wani abun, shiru tayi chan kuma ta buɗe baki tace, " fayez ka faɗamin dalilin dayasa kakeson aurena , kallon ta yayi cikin mamakin wannan tambayar yace ," binta wannan wace iriyar tambaya ce wani daliline yake sawa a auri mace?, " akwai dalilai da yawa fayez wani sam bason Allah bane wani kuma yana amfani da kimar aurene ya rufe haramtacciyar dabi arsa,

" binta , fayez ya furta shiru kakeji na kusan minti biyar babu wanda yayiwa wani magana chan dai fayez cike da damuwa da wasu wasi yace, " kodai bakyasan aurenane?, saurin kallonshi tayi chan kuma ta sunkuyar dakai a hankali tana ƙoƙarin danne kukan dayazo mata , kallon ta kawai fayez yake yacigaba da cewa, " kinsan shi ɗan adam ajizine bansan menamiki ba binta idan da laifin danai miki kifaɗa min idan kuma kinsamu wanda ya finine to karkiji nauyin faɗamin kifito kibayyana abinda ke ranki karki cutar dani ta hanyar nan pls, hawayen dake fuskarta ta share a hankali tafara magana, " wata zuciyar takance min na hakura dakai sai dai azahirin gaskiya fayez rashinka babban tashin hankaline dabazan taɓa dawowa dai daiba kuma haka aurenkama hatsarine dan bazan iya jure ganin kowace kazantaba , " kazanta?, ya maimaita yana kallon ta cike da neman ƙarin haske kawai sai ta tashi tafice, shiru yayi na dan wani lokaci tunani yake tabbas akwai abinda taji ko tagani to amma mai take nufi da kazanta shi dai ba maciyin haramba ba manemin mataba bamai shaye shaye da sauran muggan lefuka ba,

Washegari da safe ta shirya ta wuce wajen aiki a harabar gidan taga Jamel yana goge mota harta wuce taji yace, " wata sabon gani, murmushi tayi ta tsaya tana gaisheshi bayan sun gaisa yadan jata da hira bata saki jikiba amma taji daɗin yadda ya keta tambayar lafiyar yan gida, bayan ta shigo gidan ta tadda mom a falo taje ta tsugunne har ƙasa ta gaisheta mom bayan ta amsa tace, " ina kika shigane kwana dayawa haka shiru, ɗan murmushi tayi ta zauna ta laburtawa mom matsalar data samu mahaifin ta, mom sosai ta jinjina abin haɗi da addu'ar Allah ya kawo mafita,

Daga wajen mom kai tsaye ɗakin malak ta shiga tana zuwa tasameta tana waya, malak kuwa na ganin binta tasaki murmushin ganin yadda ta rame tai duhu a wayar datake ne take cewa, " karka damu Dr har yanzu baiji wuya bane idan matsar tayi matsa zai dawo yabi hanyar data dace ,

Rakabewa binta tayi tana tsaye malak ta gama wayar sannan ta gaisheta yadda malak ta amsa gaisuwar ne cikin fara a da nishadi yasa binta jin haushi aranta take tunanin wato malak ma kallon mahaukaciya take mata wadda batasan metakeba shiyasa taketa sakarmata fuska,

A gurguje tayi aikinta tazo wajen lailah duk yadda lailah taso taji maike faruwa da binta yanayinta da kamanninta suka sauya taki faɗa mata,

Bayan kwana uku binta ta anshi rabin kudin aikinta tasai musu duk abinda ya kamata sannan taje tasamu lauya sun zauna sun tattauna sosai abinda ya hanata sukuni shine maganar da lauyan yace an tabbatar da motar da Abba ya hau an cire mata burki kafin hawansa dan haka wannan hatsarin shirya shi akai ba tsautsayi bane,

Koda binta tadawo gida bata iya faɗawa ummah wannan maganar ba sai dai ta lula duniyar tunani tayaya birkin sabuwar motar ya cire , kai kawo taketayi a ɗakin chan ta ciji yatsa lokacin data tuna maganar da lauyan yake mata na ta tuna ko akwai wanda suke gaba ko yake nuna baya jin dadi ganinta , girgiza kai kawai tayi lokacin data tuna da mama aranta ta raya tabbas alamun rashin gaskiya ya bayyana a tattare da mama afili binta ta furta, to idan ba mamace ba wanene zaizo har gida ya kwance burkin mota dole akwai wata kullaliya

✍🏻 zeenariya

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

WhatsApp number

+218912472599

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 28 )

Yau saura kwana uku a koma kotu lauya ya kira binta a waya yake sanar da ita babu wata matsaya babu makama zasu iya yankewa Abba hukunci kan kisan dayayi bisa tukin ganganci, binta sosai ta shiga tashin hankali tace, " dan Allah yallaɓai ka taimaki Abbana ka tausaya mana wlh bada niya yayi kisannan ba, " kiyi hakuri banida wani sauran hanya dazanbi da inada ita da kodan fayez mutumin kirki zanyi muku wannan ƙoƙarin to amma bamuda wata hujjah ita kotu da hujjoji suke amfani idan babu hujjah duk abinda akacewa mutum yayi dole ya karɓa sai dai inada wata dabara ƙwaya ɗaya dazata iya sauya wannan shari ar,

Cikin sauri binta tace, " inajinka yallaɓai wace shawarace ?,

" mai zai hana kusamu mrs Tahir ɗin kuroƙeta kozata tauyasa muku idan ya kama wasu kuɗaɗe za a biyata sai kuyi kokari kubata idan kuma kunada wani babban mutum da kuke mu a mala dashi ko ɗan uwanku irin masu kuɗi kuma masu faɗa aji ku roƙesu su shiga wannan zanchan za a iya samun nasara, binta najin haka gidansu malak ya faɗo mata da sauri tayiwa lauyan godiya ta kashe wayar taje sukai shawara da umma akan hakan, ummah na zaune tace, " tabbas wannan shawara ce babba ina tunanin kisamu Hajiya Hafsan tunda kuna shiri ta taimaka mana akan maganar, girgiza kai binta tayi tace, " ummah Hajiya Hafsah bazata iya sa baki akan maganar nan ba dan ba ita take juya gidanba kuma ma malik bazai iya komai akan maganarnan ba dan ba shikeda cikekken iko a gidanba sannan papy wato Alhaji khabeer oga kwata kwatan bazai taimakamin ba saboda ƴarsa , ajiyar zuciya ta sauke taƙara da faɗin, " mutum dayace zata iya shiga zanchan nan muyi nasara , ummah cikin mamaki tace, " wace? , " malak Ummu malak ce keda ikon da konawane zata ɗiba tabayar kuma idan harkar Shari'a ce tasan yadda zatai tasamawa babana adalci, ummah saida tayi shiru nawasu sakanni tace, " kuma kina ganin zata iya taimaka miki duk da kin mata kwachen abu mafi muhimmanci a rayuwar ta?,

Hawaye ne suka gangaro a kuncin binta ta taso ta zauna kusa da Ummah ta kwantar da kai a kafaɗarta tace, " ummah malak bata kaunata amma itace mataki na karshe zan roƙeta bisa kaskanci zan tsugunna akan gwaiwoyina harsai ta yarda ta amince zata taimakamin, ummah cikin tausayawa binta ta ɗago kanta ta share mata hawaye tace, " binta karki risina nayi imanin Allah zai taimaka miki kije ki roƙeta insha'Allah zata taimaka mana Allah yayi miki albarka yabaki ya'ya masu tausayinki da tsananin kaunar ki kamar yadda kike tausaya mana,

*

Yana zaune a ɗaki yakasa fita koda palo shikadai yaketa shawara akan hukuncin daya yankewa kansa sai dai abu ɗaya ne yasashi shayi binta yana tsoran ya tafi yabarta cikin halin da take ciki hakika yanzu take bukatar kulawa, ya daɗe yana kissime kissime shi kaɗai chan ya yanke shawarar yadda zaiyi cikin murnar samun matsaya ya kirata a waya bayan ta ɗaga sun gaisa yake ce mata, " wai har yanzu fishin kike dani?,

Girgiza kai tayi kamar tana gabansa tace, " aa,

Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke yace, " bakisan meke faruwa daniba ko, zama yayi ya zayyane mata kaf halin da suke ciki shida malak,

Binta tanaso ta gasgata maganar amma ta kasa gani take tamkar tsabar rainin hankali ne sugama sheƙe ayarsu sannan yazo ya nuna mata Malak na neman tozartashi, hmmm kawai tace ta nisa taƙara da faɗin, " to fayez ka aureta mana ai kana santa kuma inda sabo ai kunsaba tunda bayau kuke tare ba,

Wani iri yaji da amsar data bashi sai kawai ya basar yace, " ni na hakura da asibitin kawai shawarar dana yanke muyi aurenmu nanda 2 weeks mu koma America da zama zan nemi aiki achan muyi rayuwar mu,

Shiru binta tayi tana nazari tace, " gaskiya fayez bazan iya tafiya nabar Abbana a daure ba akan lefin danasan bai aikata ba sannan kuma idan natafi ummana ita kaɗai ce batada matai maki sai Allah yan uwanta duk suna kauye suma suna fama da rayuwa,

" karki damu da batun umma zan kula da ita zan bata gidan zama zan mata duk wani abu daya chan chanta nidai pls karki tarwatsa wannan shirin nawa saboda shizaisa musamu kwanciyar hankali dagani har ke zamu huta,

" okay tom kabani kwana biyu zanyi tunanin kuma zanyi shawara, tana gama faɗin haka ta kashe wayar,

Tashi tayi ta shirya ta fita, tun a adaidaita taketa zullumi haɗi da addu'ar Allah yasa kar malak taki taimakon ta, tana isa gidan ta shiga a babban falo taga malak da papy suna tattaunawa, sim sim ta shigo ta tsugunna ta gaida papy ya amsa ciki ciki sannan ta gaida malak, aranta taketa saƙa tafaɗa yanzu ko sai anjima kawai sai taga papy ya tashi yana gyara babbar riga yana cewa, " to sweetheart nizan wuce, " ok thanks papy saika dawo, yana ficewa malak ta ɗaga wayarta ta kara a kunne haɗi da mikewa tsaya tana kai kawo chan da alama an daga wayar da take kira tayi saurin cewa, " naga message dinka dazu sorry kabani time mu haɗu mu tattauna akan wannan, chan tace , " ok bye , tana sauke wayar ta kalli binta dake tsaye tace , " lafiya koda wani abun ?, kai binta ta gyada mata alamar eh tace " ok ina jinki ?,

Cikin sassanyar murya binta tafara bayani, " da

Tai makonki nake nema haƙiƙa kinkai ne tunda nazo wajenki banida wata dama ko hanya dazata ceci mahaifina pls ki taimaka ki shiga zanchan nan, nan binta ta zauna ta kwashe komai daya faru ta sanarwa da malak

Jinjina kai malak tayi tana cije leɓanta na ƙasa ta zauna akan kujera ta ɗora ɗaya kan ɗaya ta ɗaga wayarta ta kalli lokaci sannan tayi shiru tana tunani chan ta ɗaga kai ta kalli binta tace, " shi masoyin naki bazai iya taimakonki akan wannan ba sai ni,

Hawaye ne suka gangaro a kuncin binta ta tsugunna akan gwaiwoyin ta ta haɗe hannaye alamar roƙo tana kuka tace, " fayez ya daukar mana lauya sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login