Showing 18001 words to 21000 words out of 67181 words

Chapter 7 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx

malak tabishi dashi shikuma kota kanta bai biba ya fice, wani irin raɗaɗi da ƙuna taji ranta yanai mata cikin yanayi na ɓacin rai tabar hospital ɗin,

Bayan tagama aikinta tsab misalin ƙarfe hudu na yamma ta shirya tafito harabar gidan jamel direbane ya tareta yace , " binta har angama ne yau da wuri haka?, eh kawai Binta tabashi amsa ta cigaba da tafiya cikin sauri jamel yakuma cewa, " binta tunda nace ina sonki baki ƙara saurarata ba meyasa haka, juyowa binta tayi ta kalleshi tace, " jamel kayi hakuri banida lokacin ɓatawa akan soyayyah, bin bayanta jamel yayi kafin ta ƙarasa bakin get yasha gabanta yace, " binta kiyar da dani karki watsamin ƙasa a ido wlh da gaske nake ina sonki kuma aurenki zanyi meyasa ko wayata bakya ɗauka idan na kira kuma kindaina yadda nakaiki gida kodai kin raina matsayinane dan ina direba,

Wani tausayinsa ne ya ɗarsu a zuciyar ta lokaci guda taji tanason faɗa masa kalma mai daɗi cikin yanayi na tilastawa zuciyar ta tace, " jamel nidakai fa duka ƴan aikine a wannan ginan ina tunanin kamar bai dace mu dinga maganar soyayyah anan ba, kallon ta yayi cikin jin daɗin maganar datai masa yace, " to yau zanzo gida saimu tattauna, kamar binta tace masa aa sai kuma ta daure tace masa to, saboda jin daɗin damar data bashi yasashi ɗakko mota zai kaita gida, sun danno hancin motar su shima fayez ya danno tasa karaf idon sa yakai kan binta da jamel, cikin wutar mamaki ya tsaya chak yana kallon ta itama binta tana ganinshi ta kauda kai batason tadinga tunawa dashi shiyasa bata yadda taganshi sai idan yazama dole, jamal ne yayi baya da motarsa saida fayez ya wuce sannan shima ya shige,

Tunda tadawo daga hospital ɗin take kaikawo a ɗakinta tana cije baki cikin tsananin bukatar neman mufita kullum alakarta da fayez da ɗa ja baya take ƙiri ƙiri a aikace yasha nuna mata baya buƙatar aurenta kamar dole akai masa, lailah ce tashigo da lemo ta ajiye tace, " inason magana dake, kallonta malak tayi tace, " maganar me?, "

magana ce akan binta, zama malak tayi tana kallon lailah tace, " binta kuma mai tayi, gyara tsaiwa lailah tayi cikin samun kwarin gwaiwa tace, " binta tana soyayyah da fayez, saurin kallon ta malak tayi tana waro ido tace, " me mai maita naji, maimai tawa lailah tayi, malak najin haka ta tuntsire da dariya saida tayi mai isarta ta kalli lailah tace , " kinyi haukane waccen kuchakar kike dangantawa da fayez ?,

Jiki a matukar sanyaye lailah ta buɗe baki dakyer tace, " wlh da gaske nake naga.... , da sauri malak ta ɗaga mata hannu lokaci daye tace, " wannan wane irin iskancine kinyi haukane lailah fayez ɗin kike dangan tawa da yar aikina to bari kiji babu yadda za ai hankali yadau cewa handsome mai ji da kuɗi aji ilimi uwa uba kyau yayi soyayya da yar matsiyata irin Binta mai yawan aikatau yau da cemin kikai yana soyayyah da yar shugaban ƙasa zan iya yadda Amma faƙiriya irin wannan ba layin fayez bace

✍🏼 zeenariya

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (12)

Lailah bata karacewa komaiba tabawa malak hakuri taja jiki tafice, fitowa malak tayi falo taga mominta da Malik a zazzaune, zama tayi a gefe mom ta kalleta tace, " banga kinfara shirye shiryen aurenba lokaci fa yana kurewa, rausaya kai malak tayi tana danne dannen wayar dake hannun ta tace, " yace yanaso a ɗaga auren zuwa wata biyu, kallon ta momy tayi cike da mamaki tace, " why mai yasa fayez yake hakane meyake nufi, wani yawun takaici malak ta haɗiya idanunta sunyi rau rau sunason zubda hawaye ta dake bata ce komai ba Malik dake gefe ne ya harɗe kafa yace, " mom fayez fa baya santa taƙi gajewane dayana sonta da yanzu ya aureta,

kallon sa kawai malak tayi wannan lokacin bana faɗa bane data karta masa rashin mutunci zafi da raɗaɗin da zuciyarta take matane yasata tashi batace komai ba tashige ciki,

Mom ajiyar zuciya tayi tace, " wlh Malik ina matukar tausayin malak banaso ta auri fayez muddin da gaske ya daina sonta gara ta hakura tazabi wanda yadace,

" yes mom nima haka nake gani amma malak bata tausayin kanta duk abinda takeso shine dai dai a ganinta bata yarda da shawara shiyasa take riskan bakin ciki kala kala, kwafa mom tayi tace,

" Waima kuwa Malik kasan malak tasa babanku yasai hospital ɗin ɗan uwansa ya mallaka mata, cikin mamaki malik ya furta, " da gaske?,

kai mom ta ɗaga masa alamar eh, jinjina kai yayi yace, " nasan dalilin dayasa tayi haka,

" tayi hakane danta zabaro fayez tasan duk duniya babu aikin da yafi so kuma yake jidashi sama da hospital ɗinnan kuma shiya ginashi da dukkan taimakwansa asibitin yayi suna yazama abinda yazama kwatsam sai papy yasai mata shi wannan kamar babu adalci aciki , " to daman ina maganar adalci Malik kasan halin mahaifinka duk abin malak keso shi yake mata idan har Ayman bai siyar masa da asibitin nan ba to wlh sai babanku ya kullace shi kullata mafi muni kuma kasan yadda Ayman yakeson babanku bama zai yadda yayi abinda zai raba kan zumuncin suba

*

Bayan jamel yakai binta gida yakirata a waya sosai yaja hankalinta suka jima suna waya babu laifi Jamel akwai daɗin hiri ga hikima wajen iya zance, anayin magriba kamar yadda yafaɗa sai gashi yazo aran binta bataji daɗin zuwansa ba dan batason kullah alakar soyayyah da kowane namiji neman kudinta kawai tasa a gaba,

Bawani dogon shiri tayiba hijabi kawai tasa tafido daga ɗaki saiga Abbanta nan yashigo gida ta ƙarasa tayi masa sannu da zuwa ya amsa haɗi da cewa, " lfy naga fayez ya daina zuwa kuma ga wani yau yazo mai yake faruwane, ɗan shiru binta tayi tana tunanin a binda zata cewa babanta chan ta nisa tace, " Abba idan nadawo zan faɗa maka yadda mukai da fayez, to Abba yace yashiga ciki ita kuma ta fita ,

Ba laifi Jamel kyakkyawa ne dogo ɗan siriri sai dai shi bakine akasin fayez farine kuma fayez yanada kyakkyawar kira ta mazantaka ga kwarjini da haiba ga fuskarshi ta ƙayatu da haɗaɗɗiyar ƙasimba yanada idanu masu jan hankali wanda idan ya zuba makasu bazaka gaji da ganin kyansu ba yanada dogon hanci hakwaransa shiryayyu farare kal kallo ɗaya zakaiwa fayas kasan haihuwar hutu ne girman hutu rayuwar hutu fatar jikinsa kana gani basai an faɗa makaba zakasan akwai laushi tafin hannun sa ko audiga al barka, tuna haka game da fayez ne yasa binta jinjina kai aranta taraya har abada bazata taɓa samun irin fayez ba

Jamel yayi iya iyawar sa ya gayamata daidai abinda Allah ya hore masa kuma sannan yayi mata cikakken bayani akansa sosai ta fahimci da gaske wutar kaunarta yake kuma aurenta zaiyi,

Bayan kwana biyu binta ta ɗakko takaddun zanan datayi a ranta ta kudire yau zata kaiwa malak haɗi da addu'ar Allah yasa ta karɓa, a jaka tasa takaddun ta fito kamar yadda jamel yasaba a kwana biyunnan shiyake zuwa ya ɗauketa yauma hakance ta kasance bayan sun ƙarasa ta shiga ciki papy yana palo ta tsugunna ta gaisheshi sannan ta wuce sashin malak

Tagama shirinta tsab zata fita binta ta shigo bayan ta gaisheta tace, " Madam naji ance kina siyan fashion and designer na riguna da sarƙa da takalmi shine nima na kwatanta tawa basirar na kawo miki ko Allah zaisa suyi saiki siya , wani rin kallo malak ta jefi binta dashi chan tace " ban nagani , jiki na rawa Binta ta fiddo su daga jaka ta miƙa mata , ɗaya bayan ɗaya malak ta dubasu take mamaki ya lulluɓe ta ta kalli Binta takuma kallon zanen tace , " da gaske kece kikai wannan zanen ?, washe baki Binta tayi cike da yaƙinin zata samu shiga tace , " eh ni ce nayi da hannun na , numfashi malak taja ta watsar da zanen a ƙasa tasa takalmi ta take su ta ɗago kai tana kallon binta ta ce,

" yarinya da sauranki kitsaya a iya matsayin ki karkiyi tunanin wuce haka , tana gama faɗin haka tabi takan zanen tafice,

Cikin tsananin mamaki binta tayi saranda hawaye nabin fuskarta tana kallon malak harta ɓace mata da gani sannan ta tsugunna tana tattare zanen hawaye na diga akan takardun ita kaɗai tasan wuyar datasha saboda zanen har hana kanta bacci tayi,

Malak nafita harabar gidan tasa kafa ta daki jikin motar dake kusa da ita cikin tsananin zafin zuciya tafara kai kawo tana furta, " wai talakawa me suka ɗauki kansu ne, kwafa tayi aranta take tunanin tabbas ya kamata tasa ido akan binta tunda har tafara tunanin abinda malak tafi muradi wato fashion and designer watarana zata iya kereta tanaji tana kallo,

Aikin yau binta tana kuka ta ƙarasa shi tafito harabar gidan kamar yadda tasaba idan ranta ya ɓaci chan wajen shuke shuke take zuwa tayi zamanta, bayan ta zauna tanata tunani kala kala taji ta bayanta anyi ihu da sauri ta miƙe cikin tsoro sai taga Malik dariya yayi yana nunata yace, " amma kincika matsoraci ya, itama dariya ta kakalo tace, " yaya wlh kabani tsoro, zama yayi yana mika mata apple din dake hannun sa yace, yadai naganki anan ke kadai kingama aikinne,

" eh nagama, hira suka ɗan taɓa acikin hiran tasune yake sanar mata za ai taron kaddamar da kayan da suka zana acikin wannan wata a taronne kowane Company zai kawo kalar kayan daya buga sai a zaɓi na wanda yafi kyau manya manyan yan kasuwa zasusai kayan kuma za a karrama wanda yayi zanen , sosai binta taji ɗoki aranta inama ace da zanenta aciki ,

Bayan tagama shirinta zata tafi gida lailah tace mata , " malak tace a faɗa miki gobe kizo da wuri ki gama aikinki zakuje taron kaddamar da kayan da suka zana, a ɗan fusace binta tace, " toni menene haɗina da taron?, kallon ta lailah tayi tace, " a matsayinki na yar aiki mana riƙe mata jaga zaki ɗan mikomin wannan kawomin wanchan duk ke zaki mata, kai kawai ta gyada batare tada kuma cewa lailah komai ba tafice,

Jamel ne yaketa zuba surutu akan hanya binta takasa cewa komai ta lula duniyar tunanin yadda za ai tasamu damar shigar da fashion and designer shoes chains dakuma long dresses , abakin wani tankameman shago jamel yayi fakin ta kalli shagon shima ta kalleshi tace , " mekuma zamuyi anan ?, murmushi ya sakar mata yace , " kizo muje kizaɓi duk abinda kikeso, waro ido tayi cike da mamaki tace, " haba jamel nina cemaka ina bukatar wani abun?,

" binta nifa masoyinki ne kawai inaso naga na faranta miki kuma na kyautata miki duk da inada karamin karfi zanyi iya bakin kokarina naga nasaki kin kera sa a, tattausan murmushi tayi masa wanda ya kuma kawata kyakkyawar fuskarta batai gaddama ba tafito suka shiga,

turaruka da sabulai masu saukin kuɗi ta ɗauka dayaga bata ɗibi abubuwa masu yawaba sai yadinga magiya da ker ta kara da saitin mayukan kitso,

Bayan ya sauketa a gida tayi godiya ta shiga tana zuwa ta cire kaya ta watsa ruwa tasa riga da wando na tsakar gida ta dora hijabi mara nauyi ta fito lokacin yammah tayi likis dakin ummanta ta shiga taga tana bacci sai ta nufi sashin mama ta doshi kofar falon zata bude labule kenan taji muryar mama nacewa, " wlh zizah hankalina yakasa kwanciya tayaya zan bari wannan abu ya cigaba da faruwa, gyara tsaiwa binta tayi tana kuma kasa kunne taji muryar aminiyar mama wato Hajiya zizah tana cewa, " haba kekuwa Hajiya fati yakike abu kamar karamar yarinya idanfa har bake kika fito kika fallasa maganar nan ba babu yadda za ai asirinki ya tonu har mutuwa tunda kinga babu wanda yasan da wannan zanchan dagani sai ke sai mahaliccin mu,

" zizah bazaki ganeba nifa gaba ɗaya yanzu nadama nake suna zaune dani zuciya ɗaya nikuma nayi musu cutarwar da idan suka sani har abada bazasu yafemin ba mijina yana matukar mutuntani usaina tunda ya aurota bata taɓa sabamin asan rantaba abinda nace shi sukeyi bintama haka ta daukeni kamar mahaifiyar ta ina tsoran ranar da gaskiya zatai halinta da wane ido zasu kalleni taya zasu yafemin zunubin dana aikata musu, dafe kirji binta tayi taja da baya takoma tana tafe tana haki kamar wadda tayi gudu saboda tsananin bugun da zuciyar ta take mata

ɗakinta ta koma ta zauna a ƙasa tayi shiru tana nazarin abunda taji afili ta furta, " wane zunubi ne mama ta aikata mana haka, jinjina kai kawai binta tayi aranta tace tabbas akwai wani boyayyen al amari afili kuma daga hannu sama tayi tana rokan Allah tace, " Allah indai abinda mama take boyewa idan ya bayyana zai iya datse dukkan mutuntawar dake tsakaninmu Allah na rokeka karka bari ya bayyana anan gidan duniya ,

Sai bayan sallar isha binta taje tasamu Abba har ɗaki tayi masa bayanin abinda ke faruwa tsakanin ta da fayez sannan ta gabatar masa da jamel, ajiyar zuciya Abba yasauke yace, " binta gaskiya nayi mamakin wannan abu amma matakin da kika ɗauka yayi daidai tunda kafin kisanshi ita uwar ɗakin nakice tafara saninshi kuma shi daman sha a nin masu kuɗi sai su dawuya su auri dan talaka sai ikon Allah kiyi hakuri ki ringumi kaddarar ki gashi tunkan aje ko inama Allah ya musanya miki da mafi alkhairi daman kowace kwarya da abokin birminta, sosai binta taji dadin jawabin mahaifinta tayi masa godiya ta tashi ta tafi,

Washe gari takwas na safe daidai ta shirya cikin doguwar riga mai matukar kyau ta yafa ɗan gyale ta fesa turare kwalliya sama sama tayi ta kalli kanta a madubi ita da kanta tace , " Masha Allah,

bayan taje gidan da sallama ta karasa babban falo ta tadda su dukansu a dining table suna breakfast da fara a ta ƙarasa kusa dasu ɗaya bayan ɗaya ta gaishesu cikin girmamawa tana zuwa kan malak taga tawatsa mata wani lalataccen kallo bata amsa sallamar ba dan baƙin ciki wani sashin na zuciyar malak ne yake raya mata gaskiya ba karya yarinyar nan kyakkyawa ce amma meyasa zata chaba ado haka dan ance za aje bikin baje kolin kaya da ita? , rashin samun amsarne yasa malak yin kwafa a fili tana cije baki,

Malik ne ya kalli binta yace, " kanwata yau dawuri kuma haka nasan bama lallai idan kinyi breakfast ba zoki zauna muci, saurin ɗago kai malak tayi ta kalleshi, ita kuma binta tayi murmushi tace, " alhamdulillah yaya Malik nagode, momy ce tace ,

" haba kekuwa ai anzama ɗaya zoki zauna ƴata, godiya binta tayi ta ƙaraso taja kujera kusa da malak ta zauna, wani irin tashi malak tayi a fusace tayi fatali da abincin dake gabanta ya watse a jikin binta da sauri binta tatashi tana rike gaban rigarta cike da tsoro da mamaki kowa nagurin bin malak da kallo yake basuyi tsammanin zatai haka ba, a fusace malak tace , " kinyi haukane wacece ke kina yar aiki zaki shigi cikin family kici abinci saboda raini ,tashi malik yayi yana daka mata tsawa yace , " a she dabbancin naki yakai haka wacece ke dahar zaki wulakanta ɗan adam bakibar na gida ba bakibar na wajeba , juyowa malak tayi tana ɗaga masa hannu cikin ɗaga murya tace , " bansa dakaiba karka ɗauka, malik zaikuma magana kenan papy ya da katar dashi , wani dogon tsaki malak taja tahaye sama abinta ,

Hajiya mom da tunda aka fara tana zaune takasa cewa uffan saida malak tatafi sannan ta cewa binta, " kiyi hakuri dan Allah binta wlh bata kyautaba haka halin malak yake ki ɗauki wannan abin kamar ba komai ba, jinjina kai kawai binta tayi mom ta ƙwalawa lailah kira bayan tazo tace mata ," kai binta ɗakinki tayi wanka kibata kaya tasake , cikin girmamawa lailah ta amsa tace binta tabiyota suka tafi,

Binta ta kasa cewa komai suna shiga ɗakin lailah tawuce toilet sai a wannan lokacin taji zafin tozarcin da malak tai mata cikin tsananin bacin rai ta fashe da kuka mara suti tana nadamar zuwanta inda suke cin abincinsu

✍🏼 zeenariya

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (13)

Tana fitowa daga toilet taga lailah ta ajiye mata wata abaya ruwan madara batada tarkacen ado amma yadin yana da kyan gani gashi mai santsi, wajen mirror taje ta shafa mai tasa rigar ta fesa turare , bayan tagama shirin tsab ta tsaya a gaban mudubi tana ƙarewa kanta kallo abayar taɗan kama jikinta hakan yabada damar bayyanar kyakkyawan dirinta madaidaici wanda komace ce ta kalleta sau ɗaya saita kuma kallon ta, murmushi kawai binta tayi tana sake ƙarewa fuskarta kallo afili ta furta, " kamar ni binta ban chan chanci irin wannan wulakanci ba,

Jim kaɗan lailah tazo tace binta taje malak tana kira, bayan binta taje ta tsaya daga baya baya malak ta waigo ta kare mata kallo tace, " nakiraki ne na hukuntaki kan lefin da kikaimin, faɗuwar gaba binta taji daker tayi ta maza ta dake, malak tana saka ɗan kunne tace, " zan rage miki albashi dan na fahimci dubu ɗari biyar ɗin danake biyanki a wata ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login