Showing 24001 words to 27000 words out of 67181 words
Chapter 9 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx
saida ta busa kusan rabin kwali sannan ta sha wiwi sosai kanta ya fara ɗaukan chaji duk da haka damuwar bata tafiba kawai sai tasa aka kawo mata giya mai sanyi ta ɗaga kwalbar ta kallah sannan ta jijjigata cikin yanayi na gaggawa ta zuba a glass cup ta ɗaga ta ɗiɗɗiketa du jitai Kofi dayan bai mataba dan haryanzu tuno abinda ya faru take dan danan ta ɗaga kwalbar sukutin ta kafa a baki tana ɗiɗɗika sai ta gaji ta sauke idan ta huta ta cigaba,
Agidan su malak kuwa Ammee ce tafito da niyar zuwa takuma rarrashin malak sai taga wayam bata nan , cikin matsakaicin tashin hankali taje tasamu papy tasanar masa, sosai shima ya shiga ɗimuwa bai yardaba saida suka duba lungu da sako na gidan sannan suka tambayi masu gadi suka sheda musu ta fita , papy yanata kai kawo yana kiran number ta bata ɗagawa ya kalli mom yace ,
" kingani ko kinga abinda wanchan ɗan iskan yaron yake kokarin jamana ko soyake ya kashe mana ƴar ya huta, tagumi mom tayi tace , " menene lefin fayez danyace yanada wadda yakeso da har zata zata ɗagawa kanta hankali namiji ai ba mijin mace ɗaya bane , wani irin banzan kallo papy ya watsa mata yace, " banasan maganar banza hafsa ke ba a zama da mace ɗaya nazauna dake sama da shekara talatin idan da kariyn auren dolene na karamana, gum mom tayi da bakinta papy yashiga kiciniyar danna waya sai tsuma yake ya dannah kira ya kara a kunne , tanata ringing sam ba a ɗagawa dogon tsaki yaja yana nunawa hajiya Hafsah wayar kira yake kingani ko kinga ɗan iskan yaranan yaki dagamin waya ko bari ubansa zan kira shine daidai dani
Ana ɗagawa yace , " ayman ka tabbatar ka faɗawa danƙa duk abinda ya faru da malak bazan taɓa kyalekuba, waro ido mom tayi tana mamaki taji ya kuma cewa, " babu ruwana nafaɗa maka duk abinda yasamu ƴata ɗankane sanadi kuma bazan kyalekuba harsai yaje ya nemomin ita idan ba hakaba kai kasan sauran idan shi bai saniba, bai jira jin me za a ceba ya kashe wayar
*
Fayez yana cikin tuƙi yaga kiran dady da sauri ya ɗaga haɗi da sallama cikin ɗaga murya yaji dady yana cewa, " mai kayiwa malak ne fayez mai yake faruwa, birki fayez yaja dandan zufa tafara karyo masa dukda lafiyayyan Ac na motar , cikin rarrashi yake bawa dady hakuri amma yaƙi saurararsa kawai cewa yake yanemo malak duk inda take karya sake yazo gidan ba tare da itaba
✍🏼 zeenariya
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf zeenariya
WhatsApp number
+218912472599
__________________________________
GARGAƊI
Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (15)
Shiru yayi na yan mintina chan ya kirata kozata ɗauka abin mamaki sai gashi ta ɗaga da sauri ya kara wayar akunne yana cewa, " hello malak kina ina yanzu haka, jin Muryar ta yayi wani iri cikin yanayi na maye sosai ya maida hankali wajen tambayar ta inda take amma taki bashi amsa, da kansa ya katse kiran cikin sauri ya kirawo wani abokin sa yatura masa number malak yace ya bibiyar masa duk inda mai lambar yake a yanzu ya turo masa location, haka kuwa akai cikin mintina ƙalilan saiga sakon inda takenan ya shigo da sauri yaduba ya jamota yanufi wajen
Saida fayez yakai kusan minti ishirin yana tafiya kafin ya isa wajen yana karasawa yayi fakin yashiga da sauri yanata karo da makakkun mutane maza da mata chan ya hango ta ta taso sai layi take yaje ya rike mata hannu cikin ɓachin rai yace, " meyasa zaki dawo da wannan mummunar dabi ar haba malak yakikeson maida rayuwar kine, ɗaga lumsassun idonta tayi da suka rune saboda kuka ta zuba akansa chan tayi murmushi ta faɗa kirjinsa hannun ta riƙe da kwalbar giyar ta ɗaga zata kuma sha da sauri ya kwace ya ajiye ya rungumota a jikinsa suka fito
Sata yayi a mota yashiga ya tada saida ya hau kwalta yafara tuki a hankali saboda yanayin da take ciki kartayi masa amai, malak kuwa sai kallon sa take cike da ƙauna ta buɗe baki daker tace , " kar ka maidani gida , shiru yayi mata chan tasa hannu takama gefan rigarsa tana kiciniyar rungumeshi a hakan da sauri ya tsaida motar daidai lokacin data faɗo kansa ta makal kaleshi kanta a kan kirjinsa hannuwanta zagaye dashi, karamin tsaki yaja yanajin kamar ya tureta yace , " malak wai menene hakan ki matsa nakaiki gida mana, taɓe baki tayi kamar wata yar jinjinniya tace , " yaya ni a wajenka zankwana bazan sake kwana a gidanmuba , kai kawai fayez ya gyada mata dan yasan idan yace zai bida ita ta faɗa abin bazai musu kyauba , daker ya samu ya lallaɓa ta ta zauna a kujera yasamu damar dannawa mota wuta ,
Saida yaje ƙofar gidansu malak yayi fakin chan ya juya ya kalleta a ransa yaji matukar kunyar kaiwa iyayenta ita a buge kuma sunsan shine sanadin dayasata ta aikata hakan, waya ya curo ya kira Ammee yake shaida mata ga malak din ya kawo amma ga halin da take ciki, Ammee najin haka cikin ruwan bala i tace, " hakan zakai sallama dole kakai musu ita ai kaine sanadin komai dan haka karkaji wani kunya kawaidai kasa a ranka idan har malak ta salwanta ta halaka kanta saboda kai bazan taɓa yafe makaba , cikin mamaki yabude baki zaiyi magana tuni Ammee ta katse wayar , dafe kai yayi chan dai yayi ta maza yazo ya rungumota jikinsa yabuga get aka bude masa ya shigo da ita ,
Yana shiga babban falo yagasu papy a zazzaune da sauri suka tashi suka nufoshi papy yana salati yace, " innalillahi kaddai wani abune ya faru da ita naga ka rungumota?, kai kawai fayez ya girgiza masa mom kuma ta kama hannun malak da nufin ta kaita tazauna da sauri malak ta fusge hannun ta ta rungume fayez ƙaƙam tana cewa,
" banasan zama da kowa sai shi Allah nidai dashi zan zauna bazan dawo gidannan ba, a yanda tayi magana ne ya tabbatar wa da kowa a buge take, papy ya sosa kai ya kwantar da murya yana kallon fuskar ta yace, " malak nanfa gidanku ne kizo muje kiyi wanka kici abinci ki huta, kuma noƙe kafaɗa tayi alamum bazataba, iska fayez ya furzar a bakinshi cikin haɗe fuska ya ɓanɓa reta daga jikinshi ya dafa kafa ɗunta yace, " malak ki zauna a gida nima inanan yau anan zan kwana kije kici abinki kiyi bacci ki huta, malak najin haka ta marai raice fuska tasa hannu ta shafi fuskar sa tace, " fayez kayimin alkawarin bazaka taɓa rabuwa dani ba, kai kawai ya gyaɗa mata ta kuma rungumeshi kamar gaske ta juya zata tafi taku ɗaya biyu ta faɗi da sauri mom da malik suka tarota suka kamata izuwa bedroom ɗin mom
Papy ne ya juyo ya kalli fayez yace, " kaji daɗi ko?, kallonsa kawai fayez yayi zaiyi magana kenan papy ya dakatar dashi da cewa, " bazan saurari komai ba magana ɗaya zan faɗa maka wallahi tallahi idanma mafarkin rabuwa da malak kake to kayi gaggawar farkawa bazan taɓa rangwanta makaba akan ƴata tunda kace kanason ta tofa idan kaga baka aureta ba sai dai ko mutuwa kayi ko kuma itace tace tafasa, sunkuyar dakai kawai fayez yayi saida papy yagama zazzaga masifar sa tsab da bala i sannan yabawa fayez damar yafiya ,
Fayez yana shiga gidansu yaci karo da Ammee afalo tana jiransa, sallama kawai yayi mata zai wuce kenan ta dakatar dashi itama dai maganar malak ɗin tayi masa sosai ta nuna ɓacin ranka akan hakan sannan tayi rantse rantse akan bazata yarda ya auri wata ƴa mace a duniya ba sai malak , sam fayez bai tanka mataba saida tagaji dan kanta ya tashi ya wuce bedroom dinsa ,
*
Washegari da safe binta ta shirya tsab kamar yadda tasaba kullum sai dai ga mamakinta jamel baizo ɗaukar taba ganin zata makarane yasata tafiya tasamu abin hawa ya kaita,
Da sallama ta shiga falon papy da mom suna zazzaune mom ce kawai ta iya amsawa papy kuma hankalin sa yana kan wayar hannun sa, durkusa wa binta tayi ta gaishesu abinda ya bata mamaki papy ya ganta amma bai ce uffan ba itama mom ba kamar kullum yadda tasaba sakar mata fuska tayiba, jiki a sanyaye binta ta tashi ta haura sama ɗakin laila taje ta ajiye jakar ta tafito tana shiga ɗakin malak taga wasu maza suna ta aikin fita da kwalabai da kayan tarkaje duk sunyi rugu rugu , neman guri kawai binta tayi ta tsaya tanata mamakin yadda akai haka , saida suka gama fita daduk abubuwan da suka lalace itakuma tahau gyaran dakin ,
Lailah ce tashigo tana ganin binta tayi turus cikin mamaki ta ƙaraso tace, " chab amma gaskiya binta bakida hankali ki iya aikata wannan danyan aikin kuma kizo aiki yau bakya tsoran suyi miki wani abun, cikin mamaki binta tace, " lailah mai nayi mai ya faru ko sata sukace anyi musu, girgiza kai lailah tayi tace, " kina nufin bakisan malak ta gano fayez yana soyayya dake ba?, dafe kirji binta tayi idanunta take sukai rau rau alamar taoro tace, " nashiga uku lailah waya faɗa mata, murmushi lailah tayi tace" shiya faɗa mata da bakinsa idan kinga bala in da malak tashiga jiya saikin tausaya mata duk da ba abar tausayi bace ita tayi fashe fashennan data gama taje tashawo giyarta tadinga hauka a gidannan, girgiza kai binta tayi cikin tausayin malak tace , " innalillahi wlh sam wannan abu baimin dadiba haba shiyasa naga iyayenta sun chanzamin ashe suna kallo na da lefin jefa ƴarsu a damu gaskiya to lokacin barin aikina yayi,
Fita lailah tayi binta tafara aikin ta chan aka fara shigowa da wasu sababbin kayan ta tayasu suka gyara komai tsab, kuma gyare gyare tayi tasawa ko ina turare, kiraye kirayen sallah aka fara take binta tayi alwala taje ɗakin lailah tayi sallah bayan ta idar tadawo ɗakin malak dan ta rage Ac ta saki manya manyan sofa din , ganin malak tayi a tsaye kamar ta koma haka taji sai ta yanke shawarar ƙarasawa malak tana binta da wani irin kallo na zunzurutun tsana,
Wani yawu ta haɗiya cikin fidda rai da aikinta ta buɗi baki tace, " malak ina mai baki hakuri amma dan Allah ki saurari baya nina, jinjina kai kawai malak tayi taje tasamu waje ta zauna chan ta buɗi baki tace, " bani wayarki?, binta hannu na rawa tazaro wayar a aljihu ta miƙa mata, malak cikin tsanaki tabi wayar da kallo ta taɓe baki ta shiga WhatsApp kamar yadda tayi tsammani hirar soyayyah ce sukasha tsakanin ta da fayez, fita tayi ta shiga shafin kira hima gashi kiraye kirayen sune barkadai, sashin message nanma ta duba, chan awani irin harkitse ta ɗago tana kallon binta cikin tsananin ɓachin rai ta miƙe ta ƙarasa kusa da binta ta tsaya
✍🏼 zeenariya
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf zeenariya
WhatsApp number
+218912472599
__________________________________
GARGAƊI
Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (16)
Hannu ta ɗaga zata kwasheta da mari sai kuma ta dakata chak gadai hannun ta kawoshi dai dai fuskar binta amma ta kasa marin ta bige da shafa kai tana huci ta juya taku ɗaya biyu ta kuma juyowa ta kalli binta
Binta dake tsaye tsoro duk ya mamaye kowane gurbi na jikinta azuciyarta addu'a take Allah yasa tabar gidannan lfy idan ta fita bazata sake dawowa ba, jitai malak ta kira sunan ta da sauri ta ɗaga kai tana kallon malak, cikin yanayi na nutsuwa da sassauci a sautinta tace, " mekike tunanin zanyi dan kamarki tamin kwacen saurayi?,
Sunkuyar dakai binta tayi chan ta ɗago tace, " wlh bansan yanada budurwa ba tunkan nafara aiki anan na sanshi, hannu malak tayi saurin ɗaga mata cikin daure fuska babu annuri ko kaɗan tace, " duk da ɗewarki dashi kinkaini ne shekaru nawa muka kwashe , shiru binta tayi a wannan karan
Malak kuwa sai huci take tana cije baki aranta take jaddada badan shirin da sukai itada Ammee ba yau da tayiwa binta wulaƙancin da harta koma ga Allah bazata sake marmarin haɗa fuska da fayez ba, wani dogon numfashi taja ta sauke a hankali cikin sai saita kai tace, " indai fayez ne binta kije nabar miki shi Allah ya sanya alkhairi kuma kicigaba da zuwa aikinki nibanida wata matsala dake komai ya wuce,
Waro ido binta tayi afili mamakinta ya bayyana cikin rawar jiki taɗan matso kusa da malak tace, " da gaske kin hakura kuma zaki barni na cigaba da zuwa aikina ? , kai kawai malak ta gyada tace, " eh da gaske nake mace kamar ni ai baidace nazauna ina neman soyayyar wanda nasan babu ni a zuciyar sa, sunkuyar dakai binta tayi duk da tanacikin farinciki wani sashin na zuciyarta bakin cikin wannan sadaukar war yake dan harga Allah yanzu tausayin malak take,
Ficewar ta malak tayi a harabar gidan jamel ya dauketa bayan sun hau kwalta ya tambaye ta ina zasu nufa tace masa hospital ɗin fayez, mintina kadan suka isa tafito tana zuwa ta tadda office dinsa a kulle cikin yanayi nadamuwa ta danna masa kira a waya tana ringing amma yaki dagawa, sallama taji anyi a bayanta ta juyo batare data amsaba tana kallon mai sallamar
Dogon saurayine ha ɗaɗɗe mai yalwar suma datasha gyara a shekaru zai yi dai dai da fayez, shima ita yake kallo ko kifta ido babu yanata sakar mata murmushi , dan danan malak ta haɗe rai zatai magana kenan saiga fayez yazo gurin ga mamakinta sai taga ya miƙawa saurayin hannu sun gaisa cike da fara'a yana cewa, " haba yazakai min haka kaifa kacemin gakanan kakusa zuwa, fayez yana kokarin buɗe office din yace, " sorry waheed wata waya mai muhimmanci natsaya amsawa , shiga office din sukai itama tabi bayanzu fayez yana ganin ta shigo yace, " yadai?, kallon sa tayi cikin mamaki tace, " gurin ka nazo, okay kawai yace waheed kamar ya gane malak hakan yasashi cewa, " abokina ko wannan ce mutuniyar, kai fayez ya gyada masa take waheed yace, " wow ammafa abokina kayi sa a haka malak ɗin taka take haba dole ka damemu da maganar ta, wani irin murmushi malak tasaki tana lumshe ido shi kuma fayez yayi yake a fakaice yana hararar waheed,
Jin dadin ko ɗatan da waheed yayine yasata cewa, " barka waheed, waheed dakamar jira yake tayi magana yayi saurin amsawa da, " barkadai haɗaɗɗiyar tauraruwa mai haskaka mana wannan abokin namu, fayez ne ya karɓe maganar da cewa, " malak wannan shine abokinnan nawa dana taɓa baki labarin sa Dr waheed likita kwararre a bangaran dai daita rayuwar wanda ya kamu da ciwan damuwa ko kuma wanda yake kan mataki na daf da kamuwa da ciwan hauka wato irin mutanan da zakika tsabagen damuwa yasasu suna kebance kansu dayin wasu ɗabi'u da za a dinga ganinsu kamar mahaukata kuma ba mahaukatan bane , " Dr waheed kwararrene ta fanni kala kala ina matukar jidashi a abokaina saboda na dabanne, murmushi tayi ta miƙawa waheed hannu suka gaisa tace, " naji daɗin haduwa dakai abokin mu, abinsha mai sanyi fayez yasa aka kawo musu bayan sun taɓa hira duka su ukun malak ta tashi zata tafi tace , " fayez idan katashi daga aiki kabiyo gida zamu tattauna magana mai muhimmanci , to yabata amsa sukai sallama da waheed tafita ,
Binta na zaune lailah tace, " tunda bazaki faɗan yadda kukai ba ai shikkenan daman so nake naji ta bakinki amma naji komai data faɗa miki koba cewa tayi ta barmiki shiba, rike baki binta tayi cikin mamaki tace, " lallai na yarda lailah munafurcinki yakai a gidannan wato idan ana magana ma laɓe kike, harara lailah ta watsa mata tace , " bansan raini Binta ki shiga tai tayinki, tsaki kawai binta tayi tace Allah ya kyauta ta tashi tashiga shirin tafiya gida
Tana fitowa harabar gidan taga Malik yana ƙoƙarin fita amota da sauri yayi mata alama da hannu ta karaso, bamu su binta taje bayan ta gaisheshi yace tazo ya rage mata hanya, tana shiga motar daidai lokacin da motar malak ta shigo wani irin kallo malak tayi musu wanda su bama susan itace acikin motar ba,
Suna fara tafiya Malik yace, " kanwata menene haɗinki da fayez, shiru binta tayi batai mamakin tambayar ba kai tsaye tafaɗa masa yadda akai suka haɗu, shiru yayi chan yakuma cewa, " mai malak tace miki yau akansa, ɗan sakin fuska binta tayi tafaɗa masa duk yadda sukai da malak, gyada kai kawai yayi cikin mamaki aranshi ya tabbatar malak bata hakuraba ta wata hanyar zata bullo mata, afili kuwa dan karya tsorata binta yace, " natayaki murna Allah yabarku tare ya sanya alkhairi, cikin jin dadi binta ta amsa da amin
Daga bakin hanyar layunsu binta tace ya sauketa ta taho a ƙafa tana zuwa dai dai dandazon taran samarin unguwar su tayi musu sallama dukansu kamar haɗin baki suka amsa, tana shiga taga dattijai guda biyu Abba na uku sun fito daga falon baƙi suna yiwa junansu godiya da sauri ta tsugunna ta gaishesu ɗaya daga cikinsu yace, " wannan itace yar tamu?, Abba yabashi amsa da eh mutumin yasa mata albarka sannan suka fita itakuma tashiga ciki,
Ummah da mama ne a tsaitsaye suna ganinta sukai mata sannu da dawowa ta amsa haɗi da ɗaukan buta da gudu taje tayi fitsari