Showing 9001 words to 12000 words out of 67181 words
Chapter 4 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx
ta yasata sakin fuska duk da cikin zuciyar ta cunkushe take da damuwa,
*
Misalin karfe tara nadare Ammee tafito daga ɗakin dady taji motsi alamun shigowa parlour tsayawa tayi dan taga mai shigowa kamar yadda tayi tsammani shitagani yashigo kamar sabon ango yasa danda tsetsiyar shaddah kamshin shi duk ya cike falon kafin yakai ga shiga hanyar da zata sadashi ga ɗakinsa tayi saurin ƙwala masa kira ya tsaya yana mai amsawa, ƙarasawa tayi tana cewa, " daga ina kake a wannan lokacin nasan dai ba gurin malak kajeba, kai yadafe alamun jin babu dadi da tambayar ta yace, " Ammee bakisaba min irin wannan tambayar ba nifa namijine kuma yanzu ai badare bane 9:02 , harara ta watsa masa harzata fara bambanin masifa sai kuma ta tuna da halin ɗan nata idan tace masifa zatamai bazata samu yadda takeso ba, cikin sassanyar murya tace, " haba fayez ɗin ammeen sa muje ɗaki inaso mu tattauna wata magana dakai, gaba kawai fayez yayi batare dayace komai ba shidai yasan ba a banza take faɗa masa magana mai ɗaɗiba,
Bayan sun shiga suka zauna tana fuskantar ɗan nata tace, " fayez inason ka faɗamin tsakanin ka da Allah kanason malak, waro ido yayi ya kalleta cike da mamakin tambayar datamai yace , " Ammee wannan wace iriyar tambayace , saurin ɗaga masa hannu tayi tace, " amsa kawai nakeso kabani,
" eh ina sonta mana , jinjina kai tayi haɗi da sakin wani murmushin jin daɗi tace, " da kyau to daman maganar da nakeso muyi dakai akan aurene fayez kaga kai yanzu ba yaro bane shekarar ka 30 ya kamata ka yunkuro asa ranar aurenku, fayez yanajin haka walwalal fuskarsa ta sauka cikin jin babu daɗi ya kauda kai dan danan ya gano Ammee sunyi magana da malak shiyasa aka ɓullo masa ta haka,
Kallon sa Ammee tayi tace, " aa naga ka kauda kai ka chanja fuska fayez wannan ya nunamin akwai damuwa nifa mahaifiyar kace mai zaka boyemin, kallon fuskar ta yayi yaga ta marairaice fuska sai ya mike tsaye yafara kai komo yanaso ya faɗa mata gaskiya amma yana tsoro kuma bayaso yayiwa Ammee karya kawai saiya yanke aransa zai faɗa mata gaskiya duk abinda zai faru ya faru, zama kusa da ita yayi ya nisa yace,
" Ammee dan Allah ki fahimci abinda zan faɗa miki kinga tunda farko kece kika umarceni nace inason malak kuma nabi umarninki ganin babu wadda naji inaso a lokacin Ammee bazan boye miki ba yanzu nasamu yarinyar danaji inaso kuma so na Aur... tass kan fayez yarufe baki yaji ta daukeshi da mari,
dafe kuncinsa yayi cike da tsantsar mamaki yace, " Ammee mai namiki kika marene, tsawa ta daka masa wadda tasashi yin shiru yana huci idonsa sunyi jajir tace, " baka isaba fayez malak itace matar da aka halittah danka aure wallahi tallahi idan har ina numfashi adoran duniya babu wata ƴa mace data isa ta aureka ba wadda nazaba makaba ,
Tana huci ta kara da cewa, " banda kai shashasha ne fayez mai malak tarasa yarinyar dakowa zaiso haɗa jini dasu shine kai kake gudunta dan kaga tana sonka ai wlh nayi imanin ko wacce ƴa kagano bazata kama kafar malak ba kaga ga kyau ga iya kwalliya kwarkwasa ilimi uwa uba dukiya ubanta ba abinda bai mallakaba kuma duk duniya ita yafiso babu abinda bai bataba kai inta ƙai ce maka abinda nasan kasani malak ita take juya kowa agidan su,
" ya isa haka Ammee, fayez ya katseta cikin tsawa yaƙara da cewa, " kamar yadda nafaɗa miki wlh bazan chanzaba ni bance bazan auri malak ba amma kozan aureta sainafara aurar yarinyar da nakeso, yana gama faɗin haka ya juya yabar Ammee tsaye baki a wangale cikin tsantsar mamaki zuciyar ta sai tafasa take gefe guda kuma tsoran rasa babbar damar data samu take , suhaima ce tashigo ɗakin cikin mamaki tace, " Ammee lfy naji kunata hayaniya da yaya, kasa magana Ammee tayi ranta a matukar bace yake chan taja ajiyar zuciya tace, " suhaima yayanku yanaso yasamin hawan jini, suhaima aje wayar hannunta tayi ta zaunar da Ammee fridge ta nufa ta ɗauko ruwa mai sanyi tazuba a cup glass ta mikawa Ammee ba musu Ammee ta kwankwaɗa ko zata dainajin zafin zuciya,
" Ammee nasan duk yadda akai bazai wuce akan anty hafiza yaya fayez ya ɓata miki rai ba?, " wane hafiza ai na hafiza mai saukine suhaima fayez yafara soyayyah kuma yacemin bazai auri malak ba koma zai aureta saidai tazo a ta biyu, dafe kirji suhaima tayi tace, " shi yama isa Ammee kefa kika haifeshi ai wlh wuƙa wuƙa zaki masa sai muga yadda zaiyi auren idanma kika kwantar da hankalinki babu yadda za ai anty malak ta barshi ya auri wata ba itaba, wannan maganar ba ƙaramin sanyaya ran Ammee tayi ba sai yanzu ta tina wacece malak wata dariyar mugunta tayi tace, " Allah yayi miki albarka suhaima kinma tinamin tabbas ba acin malak da yaƙi ita kadai gayyace mai zaman kanta ,
-gari na wayewa Ammee takira malak ta faɗa mata abinda fayez yace duk da bata faɗa mata yace baya sontaba kuma batace yace saidai ya aureta a ta biyuba tadai ce mata yace yasamu wadda yakeso ,
Asashin malak tunda tagama waya da Ammee tayi shiru tana ƙarewa kanta kallo a makeken madubin ɗakin jambakine a hannun ta takasa sawa saboda ɓachin rai wayarta ce taɗau ruri cikin sauri ta ɗau wayar ganin mai kira ta kara a kunne batace komai ba taji yace,
" hello malak naga kiranki har 2 miss coll lokacin ina wanka ne, jim kaɗan malak tayi daker ta iya saita muryar ta yadda bazai fahimci ranta a bace yakeba tace, " eh daman inason ganinka ne kabiyo kafin kafita office,
Ajiyar zuciya ya sauke yace, " ahhh malak kiyi hakuri sauri nake, " pls fayez, tafurta a tausashe, okay yace mata gashinan zuwa,
Binta ce tashigo da sallahma ga mamakinta malak bata amsaba ta juyo tana kallon agogon dake tsintsiyar hannun ta tace, " karfe nawa yanzu?,
binta saurin duba wayar ta tayi tace, " karfe 9:52 , miƙewa malak tayi daga kujerar datake kai tana tafiyar yanga wadda ta zame mata jiki ta ƙaraso kusa da Binta tace, " karfe tara nakeson ganinki anan idan kinason aikin ki, kai binta ta ɗaga mata da sauri alamar to, kallonta malak tayi tundaga ƙasan takalmin ta har saman kanta rigace iya gwaiwa da wando fashion kayan basu ɗametaba yar dariya malak tasaki harda tafa hannaye sai kuma tajuya tana kwarkwasa tace, " banda abin talaka komai kace saika kwaikwayi masu hali, tin tsirewa da dariya takuma yi binta batace komai ba ta kwashi kayan aikinta tawuce tafara ,
✍🏼 zeenariya
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf zeenariya
__________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (7)
Cikin kyakkyawan shirin shi nafita aiki ya sakko yana zuwa palo yaga dad ɗinshi da Ammee a zaune tana ganin shi ta tamke fuska haɗi da cewa, " gashi nan sai kayi masa magana , tana gama faɗin haka tatashi tabasu waje zama fayez yayi suka gaisa da mahaifin nasa, cikin nutsuwa dady yafara magana da cewa, " fayez mai yake faruwa ne tsakaninka da Ammee naga tazomin dawata magana wadda ban fashimta ba, ƙaramar ajiyar zuciya fayez yasauke yace,
" dad maganace akan malak Ammee take cewa nafito ayi maganar aurenmu shine, shiru fayez yayi da maganar sa yakasa faɗin abinda yakeso ya faɗa saboda tsoron kar dady yaɗau zabi
" shine me fayez ina jinka, " dady maganar gaskiya nasamu wadda naji inaso kuma ita nakeson Aure dazaku taimaka min sai abawa Abban malak hakuri a nema mata wani mijin, kallon sa dady yayi yajinjina kai yace, " fayez ban sanka da magana biyuba meyasa kakeson maidamu kananan mutane?, kame kame fayez yafara da sauri dady yadaga masa hannu yace, " ban yarda da wannan zanchan naka ba akan me zakace naje na cewa ɗan uwana kafasa Auren ƴarsa kanaso karaba zumuncin dake tsakanin mune?,
Fayez jiyaye jikinsa yayi sanyi zuciyar sa takarye wani bangaren na gefen zuciyar sa cike yake da kaunar binta gani yake kamar bazai iya rayuwar Aure yadda ya daceba idan har ba ita ya aureba, dady daya lura da yanayin fayez ne yace, " ina mai baka shawara ɗana kafitar da tunanin rabuwa da malak daga ranka idan kuwa kaga kafisan waccen to kafara auren malak daga baya saika auri wadda kakeso kaga hakan yafi masalaha , jinjina kai fayez yayi yace, " dady naji kuma zanyi amfani da shawarar ka Nagode,
wucewa yayi kai tsaye gidansu malak ya shiga a palo ya tsaya papy yana zaune ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallon labare shigowar fayez yasashi washe baki cikin jin daɗin ganinsa yace, " handsome barka da zuwa kwana biyu ina kashigane?, ƙaƙalo murmushi fayez yayi ya karaso yabawa papy hannu suka tafa suna sakin murmushin jin daɗin ganin juna papy ne yayiwa fayez nuna da hannu ya zauna kusa dashi
Zama fayez yayi papy yasa aka kawo masa bakin shayi mai zafi, Malik ne ya sakko daga beni cikin shirinsa na fita yana zuwa yabawa fayez hannu suka gaisa ya wuce, " ya harkokin my child ?, papy yafaɗa yana dafa kafaɗar fayez, " normal wlh papy yauwa daman kuwa ina so na tam bayeka yasunan wannan kwararran likitan zuciya na U,S,A ?, " wai Dr thomas kake nufi?, " eh papy shi inason zamu tattauna ne meyuwa idan mun daidai ta na ɗaukeshi aiki a hospital ɗinmu,
" okay ba matsala ka tambayi malak tabaka number James kaninsa ne kuma boyfriend din malak ne, shiru fayez yayi aransa yake tuna irin ta asar da malak tadinga yi da boyfriend dinnata ashe har yanzu suna tare kuma mahaifinta yake faɗa kansa tsaye , sakkowar malak ceta katse musu hirar su tana zuwa tazaune a gefan fayez tace , " good morning papy , morning yacata amsa yatashi zai tafi malak tayi saurin dakatar dashi da cewa, " yi zamanka papy wancan palon zamu koma nan yafiya shige da fice, okay yace yazauna , tamike batare da tace komai ba tanufi hanyar karamin parlour shima fayez yabita bayan sun zazzauna ya kalleta a hassale yace, " ashe daman har yau baki daina kula James ba?, ko dar malak batajiba ta harde ƙafa ɗaya kan ɗaya tace, " fayez ba wannan maganar ce tasani kiranka ba, kwafa kawai yayi ƙasan zuciyar sa cike da haushinta
" nakiraka ne naji dalilin dayasa ka chanzan kwana biyu?, busar da iska yayi daga bakinsa yace, " aikine yamin yawa, kallo tabishi dashi cikin rashin yarda da abinda yace tace, " duk bama wannan ba sonake kayi magana dady susa ranar aurenmu,
Mikewa tsaye yayi yace, " banida lokacin tattauna wannan maganar yanzu idan nadawo zan kiraki, baijira jinta bakinta ba yafice, cikin mamaki ta mike tsaye a hassale aranta tana kuma jinjina girman yadda ya chanza mata yanzu cikin tsananin ɓachin rai tafito ta haye sama
Tana tura kofar ɗakinta taga binta tana tsugunne tana hade wasu takaddu da suka zube, cikin tsananin jin kai tatako da takalminta mai matukar tsini tabi takan yatsun binta dake ƙasa, wani irin ihu na azaba binta tasaki ta rike hannun tana kiran innalillahi wa innah ilaihirraju un, saida malak takai bakin mirror dinta tasaki wani murmushi takalli binta da itama kallon ta take tace, " sorry,
Binta tsana karara kawai take hangowa a kwayar idon malak cike da jin zafin wulakancin datake mata wanda har yau batasan dalilin hakanba, lailah ce tashigo daɗan saurinta jin ihun datai yasata zuwa tana ganin binta nahawaye yasata sakin tsaki tace " lfy kikewa mutane ihu a gida, kallon ta binta tayi batace komai ba dan raɗaɗin da zuciyar ta take mata idan tace zatai magana bazata taɓa furta magana my dadi ba, yar dariya malak tayi tana fesawa kanta turare tace, " hannunta ta bazamin akan hanya nikuma nabi takai yo wai ni lailah faƙirai irin waɗannan ai kamata yayi su dinga kwanciya mu masu hannu da shuni munabi ta kansu , dariya suka kuma tuntsurewa da ita sosai binta taji zafin hakan a yanzu ko zafin hannunma bataji kunar da zuciyar ta take mata yamaye wannan gurbin , tashi tayi tamaida takaddun ma adaninsu tafice batare datace komai ba
Dakin lailah taje ta kintsa lokacin tafiyar ta baiyiba saboda ɓachin rai yasata tafiya yanzu , tana fitowa harabar gidan taga momin malak cikin hadaddiyar shiga mai matuƙar kyau da ƙawa da alama fita zatai tana ganin binta ta saki murmushi tayi mata alama da hannu tazo, binta bataso hakanba dan ranta babu daɗi azahirima haushin iyayen malak tafiji saboda da dukkan alamu sune basu koya mata tarbiyyar mutunta mutaneba, karasawa tayi jikinta a sanyaye ta tsaya bayan sun gaisa tace, " bintana har kin gama aikin nakine zaki tafi yau da wuri haka, ɗaga mata kai binta tayi alamar eh, mom ta dafata tace , " to shigo mota musaukeki alayinku , binta na kokarin shiga taji Muryar namiji acikin motar ance , " awace unguwa kanwar tawa take ?, ɗago Kai tayi ta kalleshi suka haɗa ido tasaki karamin murmushi ta faɗa masa sunan unguwar ta shiga motar ta rufe momy na gidan gaba tace, " malik idan ka sauketa mufara biyawa gidan oum farhan,
A daidai kan layinsu aka sauke binta tayi musu godiya ta fito ta wuce tana isa gida ta tarda ummah bata nan sai mama, bayan tayi wanka tasa kaya tafito kitchen ta zuba abinci taci sannan tawuce sashin mama, akwance ta tardata tanata latse latsen waya Binta ta karasa da Sallama ta zauna tace, " mama sunnu da hutawa, " yauwa sannu binta har an dawo yau da wuri haka, binta tabata amsa da eh sannan ta tambayeta koda wani aiki ko aiken dazatai mata mama tace ba komai ta gode,
Ɗaki binta takuma komawa ta kwanta bacci mai daɗi ya dauketa sai yamma likis ringin din wayarta ya tasheta ta tashi ta daga bayan sun gaisa yake sanar mata gashinan yana hanya zaizo, da sauri ta mutsuke ido tana faɗaɗa fara arta ta tashi tayi alwala tayi sallah ta fiddo riga da sike na atamfa mai matikar kyau tasa tafeshe jikinta da turare wadataccen mayafi tayafa tasa takalmi tafito falon waje na baƙi tafesa masa turaren kamshi tasake shirya falon tsab ta koma tasanarwa mama zatai bako,
Cikin kan kanin lokaci sai gashi yakuma bugo mata waya yace yana ƙofar gida da sauri ta fito zuciyar ta fal jin daɗi tazo tabuɗe kofia ta ganshi tsaye cikin farar shadda ba karamin kyau yayiba kamshin sassanyan turaransa ne yafara rasha hancinta wani irin kallon so da tsantsar kauna yake mata wanda yasata sakin murmushi fararan kyawawan hakoranta suka bayyana shima murmushin ya sakar mata yana cewa, " amincin Allah ya tabbata ga sarauniyar kyau da ado kirki tarbiyya haɗi da nutsuwa kamala kai dakomai ma ke sarauniyar sace, dariya tayi tace, " tare dakai sarkin birnin zuciyar wannan muskiniyar yarinyar da rayuwar ta tazautu da zazzafar soyayyarka, hanya tabashi tace yashigo ,
Bayan sun zazzauna afalon sun gaisa sun ɗan taɓa hira yalura da hannun ta yatsun kamar sun kumbura sunyi ja dandanan ya sauya fuska yace,
Zeenariya ✍🏼
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf zeenariya
__________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (8)
" subhanallah meya sameki a hannu, batai auneba taji ya rike hannun nata , waro ido tayi cikin mamaki tayi saurin zame hannunta tana kallonsa tace, " bigewa nayi, cikin nuna damuwa a fuskar sa yace, " wannan baiyi kala da bigewa ba binta ki faɗan gaskiya kinsan nifa likita ne,
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon yatsun dan danan abinda ya faru yashiga dawo mata hawayen dabatai tsammanin su ba suka shiga zubowa akan fuskarta ta sharesu tana kallon sa, gaba ɗaya ya rikice ganin tana zubda hawaye yasashi tabbatar da akawai abinda yake faruwa cikin matuƙar buƙatar san sani yace, " munyiwa junanmu alkawarin gina rayuwar mu kan gaskiya babu boye boye dan Allah ki faɗan meyake damunki kuma garinyaya kikaji wannan ciwan ?,
Share hawayen ta takumayi ta kalleshi lokaci ɗaya tunaninta ya chanza data tuna shima mai kuɗine kuma ɗan masu kuɗi, cikin nuna fusata akan fuskarta tasaki dogon tsaki tace, " wannan ciwan nasameshi ne saboda niyar talakawa ce wadda kuma tajimin shi yar masu hannu da shuni ce karka damu mu talakawa ai bayinkune komai zakuyi mana bamuda ƴancin damuwa, fuskar fayez ce ta chanza dan danan jin abinda binta tace yakasa gane mai take nufi,
" Binta banfa ganeba mekike nufi?, murmushi tayi tace, " karka damu fayez sanin mai yake damuna bazai amfaneka da komai ba kawai dai ina fatan Allah karya jarabce ni akanka, a wannan karan dayaji tace haka bai kuma cewa komai ba tunani kala kala yake tambayar kansa yake mai take nufi kuma mai yake faruwa chan ya tsunkaye ta tana kuma cewa, " bazan barka a duhu ba zan faɗa maka gaskiya, ɗago kai yayi ya kalleta ya gyara zama sosai ya fuskance ta yace , " ina jinki,
" saboda maganar aurenmu nanemi aiki danna rufawa kaina asiri na tallafawa iyayena wajen siyan kayan ɗaki saboda kace idan akazo maganar aure befi asa wata ɗaya ba komai da komai shiyasa nafara shiri dan mu masu ƙaramin karfine, " a gidan danake aiki ne yar masu gidan budurwa bata sona kyarar yau daban ta gobe daban gacin mutumci kala kala yau ma itace ta takan hannu har ya kumbura haka batare danasan mai nayi mataba, binta nakaiwa nan