Showing 6001 words to 9000 words out of 67181 words
Chapter 3 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx
/>
Aɗaki kuwa fayez jan dady ƙarami yayi yabashi tarin chocolate shida anam ya kalli hafiza da haryanzu kuka take yace, " kiyi hakuri wannan abin na Ammee ba baƙo bane awajen ki duk da babu daɗi tadinga miki haka amma bai dace kidamu ba duk abinda kikeso karkiji komai kiyimin magana ko abbanmu zaki samu ke idan da halima kidaina zuwa akai akai kibari sai wata wata idan suna jimawa basu gankiba zasu nemeki da kansu,
hawayenta ta share ta ɗago idanun nan jajir tace ," yaya ina son Ammeena daku dasu Abbah baki ɗaya ina matukar jin daɗin ganinku banida kowa sai ku amma narasa mai yasa Ammee take nunamin halin ko inkula nida ƴaƴana tunda na auri nura narasa soyayyah irinta ƴa da uwa tsakanina da Ammee bata ko so taga wani ya temakeni kwanaki na nemi aiki a kamfanin su uncle khabeer wlh har an karɓi takadduna dataji labari taje har gida ta zuga Abban malak aka dawomin da takarduna wai saina rabu da mijina nura zasu bani duk abinda nakeso, kuka mai karfine ya kwacewa hafiza
Innalillahi wa innah ilaihirraju un kawai fayez yake furtawa yasan halin kowa babu musu abinda yafi hakama zasu aikata, cike da damuwa yace, " kinajina kanwata tunda kinada ƙananan yara ga ƙaramin ciki kinadashi yanzu aiki bai kamaceki ba kizauna agida kihuta kicewa nura gobe yazo office ya sameni yazo da takar dunsa zan duba asama masa aikin dayafi wanda yake yadda zai samu ya kula daku kuma maganar motarki nasiya miki sabuwa tun ranar Alhamis mantawa nayi ban aika miki itaba bari nabaki mukullin tunda tana gidannan ki ɗauka kitafi da ita, wani farin cikine yamamaye gurbin damuwar hafiza lokaci guda tasaki murmushi duk da fuskarta jage jage take da hawaye tace," Nagode ɗan uwa Allah yasaka maka da gidan aljannah Ubangiji yabaka abinda kake nema duniya da lahira yabaka mace tagari duk duniya babu wanda yake sharen hawaye ayanzu daga kai sai abbana ,
Sosai fayez yaji dadin addu'ar datayi masa yana washe baki yace ai albishirin ki nakusa aure nan bada jimawaba, " Allah yaya kace bikin yazo kaida malak, shiru fayez yayi sai a wannan lokacin ya tuna ashefa malak ce matar dakowa yasan zai aure ɗan cije baki yayi ya gyara zama yace, " hafiza kinsan bana boye miki komai kuma banida abokiyar shawarar data kaiki, kai ta gyaɗa masa tace, " sosai kuwa yaya,
" to wlh nagano wata yarinya da tunda nake bantaɓa jin nataɓayiwa wata ƴa mace son danake mataba, riƙe baki hafiza tayi cikin mamaki tace, " chab yaya wacece wannan a ina kuka haɗu, " wata baiwar Allah ce mai kamala ga nutsuwa kuma ƴargidan tarbiya da mutumci iyayen ta masu ƙaramin karfine sunan ta fatima ana kiranta da binta,
" chab yaya to malak ɗin yazakai da ita kasanfa akwai alkhawarin aure a tsakaninku tun shekara goma sha biyar baya, cikin damuwa fayez yasa hannu yashafi fuskarsa yace, " ina tsoran abubuwan dazasu faru idan nabijirewa wannan alkhawarin kuma gaskiya bazan iya rabuwa da bintaba dan itace kalar matar danakeso sannan banida ra,ayin yin mata biyu gashi ina matukar tsoron matakin da malak zata ɗauka akan binta idan tagano ina sonta,
" matsala babbah yayah zaka jefa kanka idan kabijoro da maganar yarinyar nan ina jiye maka tsoron kar Ammee ta tsaneka kamar yadda ta tsaneni silar auren nura,
" gaskiya kika faɗa hafiza amma ba komai zantayin addu'a ina neman zaɓin alkhairi wajen ubangiji idan Allah yayi ni zan auri binta sai ya dai dai ta abin yadda bazasuyi komai akaiba, cikin jimami yaya da kanwar sukayiwa junansu fatan alkhauri yaduba account numberta yatura mata 4 millions take sannan suka fita harabar gidan yanuna mata motar daya semata tanata godiya daman a adai daita tazo take taja motarta dayaranta tatafi,
*
Cikin sati biyu binta da fayez sukai muguwar shaƙuwa kusan kullum da yamma sai yazo zance har ƴan unguwar su binta sun ganeshi saboda ɓarin kuɗin dayake musu gidan su bintama duk sun sanshi
Yau da safe suna zazzaune a dining table na ɗakin mama suna breakfast dukansu ummah tace, " fatima wai saurayin naki baya baki kuɗine naga daga waya babu abinda yase miki kuma sai naji anata magana a unguwar nan dubbanni yake rabawa, sunkuyar dakai binta tayi tace, " ummah yana bani kawai dai bantaɓa karɓa bane shiyasa yasuyomin wannan wayar kuma itama kanta kuɗin ta yakai miliyan,
dogon tsaki ummah taja tace, " amma ke anyi shashashar yarinya idan baki karɓaɓa ubanki za a kaimasa ɗakin kinsan dai masu kuɗi irin wannan ba a kaimusu gallafirin kayan gadoba gakuma na kicin,
Haɗe rai Abba yayi ya ajiye chokalin cin abincin nasa yace, " usaina meyasa kike hakane kinfi kowa sanin ni banbawa ƴata tarbiyan son kuɗba hakaba ,
yar dariya Hajiya mama tayi tace, " haba kaikuwa malam ai banga lefin usainaba gaskiya tafaɗa idan yabata kuɗi ta amsa atara kaga saimu haɗa da abinda Allah yabamu muyimata kaya nagani na faɗa yadda baza a rainata ba , ummah ce tayi saurin amshewa da , " faɗamasa dai Hajiya fati shi namijine baisan kan garinba , kwafa Abbah yayi yace , " nidai ban yarda da wannan tsarinba idan kuɗin akeso ina aikin da kikace kunyi magana da Hajiya halima akai kukaita tayi aikin tunda bana kwana bane kinga idan taɗau ko albashin wata biyune sai asai mata kayan dasu ,
" nayi magana da haliman abinda tacene ni baimin ɗaɗiba harna fidda rai da aikin, mamace ta kalli Ummu cikin mamaki tace, " usaina mai tace miki ne haka ?'
" cewa tayi agidan aikin akwai wata yarinyar su da suke matuƙar jida ita duk ƴan aikin da akakai sai tace basuyi mataba a nemo wasu shiyasa nake tunanin bintanma ba lallai ta ɗauketa ba ,
" gaskiya kam Gara dai a hakura, cewar mamah kenan Binta cikin ladabi ta ɗago tana kallon iyayen nata tace , " Abba mai zai hana na gwada zuwa ko Allah yasa adace, nisawa Abba yayi yace, " ƙwarai kuwa mebi kiga Allah yasa aikin rabon kine , nan suka yanke shawarar zuwan Binta tagwada sa,arta
A sashin malak kuwa tsawan kwanakin nan kaf ya cenja mata baya yawan zuwa inda take kamar da kuma baya yawan kiranta awaya idan ta kirashi lokacin da tasan baya aiki sai taji yana waya haka intaje office ɗinsa sai yashareta yayita chatting ɗinsa tana gani,
Kamar yadda tasaba zuwa office dinsa lokaci zuwa lokaci yauma takai masa ziyara suna zaune suna hira text message yashigo wayarsa dayake wayar tana kan table sai tayi saurin kallon kan screen din wayar bata iya gane mai aka rubuta ba saboda tazararsu da wayar amma taga imoji na love da kuma kiss, wani irin radaɗi taji zuciyar ta tayi mata tabbas yanzu ta kuma tabbatar wa da kanta fayez soyayyah yake aranta ta ƙudire gona wace mai tsautsayin ce tayi kutse cikin rayuwarsu
✍🏼 zeenariya
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf zeenariya
__________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (5)
Kalar murmushin datai masane yasashi tsarguwa cikin sanyin murya tace, " ina tunanin acikin wannan shekarar zamuyi aure , Yar dariya yayi duk da yaji mamakin jin wannan maganar daga bakinta , sosai ya maida dubansa gareta yace , " yanzu kinji kina ra ayi kenan? , dan yatsuna fuska tayi tace, " banyi zatan zaka faɗan hakaba fayez abinda kakesone fa, jinjina kai yayi yace, " alokacin danaso muyi Auren ƙi kikai malak nayi mamakin yadda naji keda kanki kince kinason muyi Aure yanzu ,
Cije lebe malak tayi cike da takaici tabbas abinda take zargi ya tabbata fayez akwai wadda yake soyayyah da ita tunda gashi yanzu suna jayayyah akan maganar aure, " malak, yakira sunanta ta kalleshi ƙarƙashin zuciyar ta cike da ƙuna bata iya cewa komai ba kawai ta tashi taɗau jakarta tafice daga office ɗin, yana ganin tafita yadafe kai cikin mamaki aransa yake tunanin kodai tagane yafara soyayyah kiran binta daya shigo wayarsa ne yasashi faɗaɗa fara arsa kamar yana gabanta ya ɗaga yana murmushin jin dadi,
Tana komawa gida bata yiwa kowa magana ba tawuce ɗakinta cikin tsananin bachin rai tashiga kai kawo chan wani tunanin yazo mata cikin hanzari taɗau waya ta dannawa Ammee kira ba ɓata lokaci ta ɗaga bayar sun gaisa Ammee tace,
" malak inata kiranki baki samudamar ɗaukaba, shafa gashin kanta tayi tace, " Ammee na ɗanyi bizine yanzuma kiranki nayi nasanar dake akwai matsala fayez ya chanzamin gaba ɗaya ina zargin mafa yafara soyayyah ,
Ammee tana zaune saida ta mike cikin ɗaukar zafi tace, " shi ya isa ai bazai taɓa yiyuwa ba malak wlh da fayez ya auri watanki gara yamutu ba Aure, wani daɗi malak taji dik da haka bataji zuciyar ta ta gamsuba saida tace, " inaso kisa masa ido yanayinsa da komai nasa naji suhaima ma tacemin yanzu kullum da yamma yake sake kwalliya ya fita baya dawowa sai dare kuma ni ba gurina yake zuwaba idanma nakirashi saiya cemin zai maido kuma baya maidomin kiran,
" ka haifi ɗa baka haihi halinsaba karki damu malak zan miki ƙoƙarin gano mai yake faruwa sannan mu tsara yadda zamu magance matsalar , malak taji daɗi sosai sukai sallamah ta kashe wayar, lailah ce tashigo hannunta ɗauke da kulolin abin ci takawo ta jera mata a table ko mai a nitse take saboda tasan halin uwar ɗakin nata, bayan tagama komai cikin ladabi da girmamawa murya a tausashe tace , " anty malak anbani sako nafaɗa miki , wani irin mugun kallo malak tayi mata tace , " lailah banace miki karki kara cemin antyba bana bukata , bakin lailah har rawa yake wajen bada hakuri chan tace , " wana sako aka baki?,
" Halima ce takira tace afaɗa miki tasamo wata yar aikin gobe zata kawota kiganta, dogon tsaki malak taja tace, " nifa bana bukatar wasu yan aiki saboda mom ne nasa akawo ki kira haleeman kifaɗa mata banaso, har lailah ta amsa da to malak tace, " bashshi ma tazo goban zan mata kashedi da kaina,
*
Tunda garin Allah yawaye da sassafe binta tatashi tayi duk aikinta ta haɗa musu breakfast bayan sun karya misalin goma na safe halima ta kira awaya tace gatanan zuwa binta ta shirya ba wata wata binta tanata ɗoki tayi wanka tasa riga da siket na leshi kayan sosai suka amsheta dayake farace leshin kuma chocolate ne mai haske haske jikinsa duk adan duwatsu fari tas farin mayafi tayafa batayi wani kwalliya ba tasa hoda da kwalli sai man laɓe sosai zahirin kyanta ya bayyana turare ta fesa tasa farin takalmi mara tudu irin nasu namasu ƙaramin ƙarfi, harzata fita da wayarta mai tsada saita fasa taɗau ƙaramar hawel dinta tasa layukan ta aciki taɗau jaka madai daiciya tafito Ummah dake tsaye da Hajiya haleema suka saki baki suna kallon ikon Allah mama ce cikin jin wani iri tace, " irin wannan kwalliya binta karfa ki kwace musu mai gida, dariya suka kwashe da ita binta cikin jin kunya tana sunkuyar dakai tace, " mama banaso naje suyimin kallon rainine shiyasa na kimtsa, Hajiya halima najin haka tace, " gaskiya ne dankuwa basason ƙazaman yan aiki sunfison irinku,
Nan suka fito Hajiya halima a motarta takai , unguwar wajen wasu dan datsa dan datsan gidace masu haukata tunanin mai karamar ƙwaƙwalwa cikin mamaki binta takasa hakuri tace, " Hajiya daman akwai irin wannan gidajen a garinnan, dariya halima tayi tace, " gaskiya nimadai tunda nake alaƙa da manya manyan masu kuɗi ma aikatan gwamnati masu milki da ƴan kasuwa bantaɓa sanin gida masu kyan wannan ba kinga wannan na ɓangaren kudunnan gidan Dr ayman ne wannan kuma wanda yafi kyan gidan Alhaji khabeer ne anan zakiyi aiki idan sun karbeki, jinjina kai binta tayi tana kuma bin gidajan da kallo kamar baza a mutu a barsuba
Suna shiga gidan kai tsaye a babban parlour aka saukesu Hajiya Hafsah ce tafara fitowa ta zauna a kujera binta na zaune a ƙasa ta gaisheta cike da fara'a Hajiya Hafsah ta amsa dan kallo ɗaya tayiwa binta taji tashiga ranta tace, " kyakkyawa kuwa masha Allah ya sunan ki, " Fatima ana kirana da binta, " masha Allah binta gaskiya kinyi inason kisamu aiki a gidannan, lailah ce ta ƙaraso palon tace , " halimah wai kishigo malak tanason ganinki, ba wata wata halima tace binta ta taso su shiga , suna shiga ɗakin binta taga al jannar duniya wangameman dakine ansa komai aciki ga ƙatan bed a gefe wanda shima kansa abin kallone wajen sif din zuba kayama kamar ɗaki akai masa ga kaya mirror websites komai yagaji da haɗuwa binta baki asake takai ganinta ga wani tafkeken hotan malak a bangon ɗakin wani irin dum taji kirjinta yayi daidai lokacin da malak tajuyo karaf suka hada ido da malak , wani irin wula kantaccen kallo na tozarci malak tajefi Binta dashi wanda Binta tasa jin jikinta yayi sanyi yar dariya malak tayi tace , " haleema ina kuma kika samo wannan , halima na washe baki tace , " Yar wasu makotanmu ne , jinjina kai tayi , " okay na ɗauketa aiki , hamdala halima tayi tana godiya itama binta duk da tsorata da ganin wadda zataiwa aiki saida tagodewa Allah
Muryar malak sugaji tace, " haleema zaki iya tafiya, sallamah halima tayiwa binta ta fita tana fita binta tace, " ranki shi daɗe barka da safiya, malak bata ko kalletaba tana shafa hoda a fuskar ta tace, " ranki shi daɗe bata hana mutuwa sake min wani sunan banaso ki kirani da malak gatsal saboda ban bancin dake tsakanina dake, wani irin yawu Binta ta hadiya tace, " anty malak, girgiza kai malak tayi tace, " bana bukatar anty saboda naga kamar da raini a anty, nisawa binta tayi chan tace, " sister malak?, rausaya kai tayi tace, " wannan ma baimin ba kikirani da malak kai tsaye kafin na sama miki sunan dazaki dinga kirana dashi ,
Takowa tayi kusa da lailah dake rike da kaya a hannun ta tace, " lailah wannan yarinyar ce zata dinga gyara min ɗaki goge goge wankin toilet dadai sauran aiyukan dasuka dan ganceni , cikin girmamawa lailah ta amsa da to , ganin zatasa kaya yasasu fita daga ɗakin bayan tagama sa kayan ta fito , binta kallo kawai takebin malak dashi haƙiƙa itace wadda tace zata iya kasheta ta kashe banza lallai kudi sune mutu idan kanada kudi zaka iya aikata komai dan ganin da binta tayiwa malak sosai tafahimci yar kwalisace ga gayu da iya ɗaukar wanka kamar baturiya musamman da take shigar turawan ga dukkan alamu batasa kayan su atamfa da leshi , lailah ce taƙaraso tacewa Binta, " kishiga kifara aikinki
Tare suka shiga lailah na nunnunawa binta yadda zata sa komai a mazauninsa abinda yabawa binta mamaki itama kanta lailah cikin wulaƙanci da raini take mata magana sosai ran binta ya ɓaci sai tayi shiru ta danne bayan tagama aikin tass ko ina tsaf tsaf lailah tace tabiyo ta tanuna mata ɗakin dazata dinga zama kafi yammah ta ƙarasa yi
Ma daidaicin ɗakine dayaji kayan alatu daga gani ɗakin lailah ne binta na shiga ta zauna a ƙasa tagaji likis dan har aikin mugunta lailah ta sata dai dai da jikin mukunnin kwai sai da ta goge, kishin giɗa tayi tana maida numfashi lokaci ɗaya wani tunani yazo mata idan har masu kuɗi haka suke rayuwa da talaka yaya kenan matsayin ta zai kasance a wajen yan uwan fayez duk da batasan komai game da suba alamunsa ya nuna ɗan hamshakai ne yazatai idan akasamu masu irin ra ayin malak, saurin katse tunaninta tayi ta ɗau wayarta ta kirashi kamar jiranta yake ya ɗauka suka fara shan hirarsu ta soyayyah murya ƙasa ƙasa malak take magana kar ajita,
Sai Yammah likis malak ta dawo tasa aka kira mata binta tana shigowa tace, " wannan wane irin banzan aiki ne ko an faɗa miki yadda kuke ƙazanta a gidajen ku haka ake anan, binta dake tsaye sosai taji zuciyar ta tana raɗaɗi ta ɗago takarewa ɗakin kallo ita bataga abinda ba daidai ba cikin jin ba daɗi tace, " kiyi hakuri lailah ce tanuna min duk yadda zanyi kuma nayi aikina da kyau,
Tsaki malak taja tana watsa mata lalataccen kallo ta zauna kan doguwar kujerar dake bedroom din tace, " ina shigowa naji ɗakin yana tsami da wari ban sani ba ko jikinki ne yake warin lailah nuna mata turarukan da ake samin aɗaki tasa ta tafi, wannan karon idon binta cika sukai da hawaye taf ƙoƙarin ɓoyewa tadingayi Allah ya tai maketa basu zuboba, turaren lailah takawo mata ta kunnan binta tabi ko ina dashi bayan tagama tayi musu sallahma zata fita kenan malak tace, " ke wa kike da suna?, binta tajuyo tace, " binta, " okay gobe idan zakizo ki tabbata kin yi wanka banasan jin wannan bashi bashin jikin naki, kai kawai binta tasamu damar gyaɗawa tafice haba tana fita hawayen da suketa ƙoƙarin zubowa suka fara zuba aran binta take ayyana tunda iyayenta suka haifeta bata taɓa riskar wulakanci irin wannan ba tunda take babu wanda ya taba kusheta da kazanta sai yau tun tana ƙarama kowa yaba kyawunta da tsabtar ta yake,
✍🏼 zeenariya
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf zeenariya
__________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (6)
Tunda ta fito daga gidan take kuka takaicin irin yadda taga an matane fal zuciyar ta, a ƙafa tafito bakin babban titi Allah ya taimaka tana zuwa batasha wuyar samun abin hawaba
Jiki a sanyaye tashigo gida su Ummah sunso ganewa gudun karsuyi ta tambayar