Showing 33001 words to 36000 words out of 67181 words

Chapter 12 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx

zauna bayan sun gaisa yace ," dady ya fitane, cikin mamaki ta kalleshi ta taɓe baki tace, " eh ya fita ai daman nasan dan karan kanka da wuya haka siddan kazo dakina dan ka dubani saidai idan mun haɗu a falo ka gaisheni fisha kamar wata miƙiyarka , sosa kai kawai fayez yayi yace , " ni na isa Ammee ai uwa uwace duk duniya banida kamar ke , waro ido tayi chan tasaki dariya tace , " sabon salo yau kuma fayez din dayakemin kallon kullum ba akan daidai nakeba shine yake cemin uwa uwace to faɗamin mekakeso ? Nasan dai ba abanza ba ,

Kallon ta kawai yayi chan ya marairaice fuska yace, " Aure nakeso, tsaki taja tace toni menene nawa a ciki da dagaske kanason auren ai da tuni kayi ka wuta, tashi yayi daga inda yake zaune ya dawo kusa da ita ya kama hannun ta yana wasa da ya tsunta yace, Ammee ki sauke nauyin ki na matsayin mahifiya ki barni na rayu da wadda nakeso na amsa sunan namiji kamar kowa, kallon sa tayi kamar ta rufeshi da faɗa sai kuma ta saisaita zuciyar ta tace, " fayez duk duniya babu wanda zai soka kamar ni duk abinda kaga nayi mai daɗi ko mara daɗi dan na gyara maka rayuwar ka ne, " na sani Ammee nasan kinasona amma dan Allah ki tabbatar min da wannan soyayyar taki ta hanyar barina na auri binta, ya karashe maganar yana mai ƙanƙame hannun ta a kirjinsa ta buɗe baki zatai magana kenan yace , " pls Ammee karkice aa ki taimaki rayuwata yafaɗi maganar daidai lokacin da hawaye suka sakko akan fuskarsa , jikin Ammee ne yayi sanyi a karo na farko kenan dataji tanaso ta sassauta masa ko yadaɗa kaunatar ta matsayin uwa , share masa hawaye tayi tace , " na Barka ɗana ka auri wadda kakeso fatana Allah yasa tazama mafi alkhairi a wajenka, fayez rungumeta yayi dan farinciki sam baiyi tsammanin zata risina lokaci gudaba dan yasan halinta da taurin kai idan ta kafe kan abu ɗaya ,

A daran fayez bai iya jira saida safe ba ya samu dady lokacin yana cin abinci yaje masa da maganar auren binta sam dady yaki yarda saida Ammee tasa baki dady yace to zaije gidansu malak su tattauna da ɗan uwansa idan har hakan zatayu malak ta hakura shikkenan,

*

Washegari da safe kuwa dady yaje bayan sun zaune yafara bayani, " nazo mu tattauna akan yarannan ne naji menene matsaya ko sun hakura da juna ne ?" Wani irin kallo papy yayiwa dan uwan nasa yace, " ɗan ka dai ya hakura,

Sunkuyar dakai dady yayi yace, " ni na haifi fayez bashi ya haifeniba duk da inada sanyi bazan sakar masa ragama yayi abinda yakeso ba nazo inji ta bakin malak ne akan maganar auren idan har tace tana son fayez to a yau za a daura musu aure kafin rana ta faɗi akawo karshen duk wani cece kuce mu huta idan kuma tace bata sonshi ta hakura to kuzama shaida ni zan fita cikin maganar nan salin alin mu barta tamkar ba a taɓa batun haɗasu aureba ,

Papy yaji daɗin bayanin Abba dan yasan yau muradin malak zai ciki zata samu abinda takeso ta huta shima ya huta da tashe tashen hankula , " na yarda da wannan sharaɗin naka kuma nima na amince idan taga tana sanshi duk da wulakancin dayayi mata to a daura musu aure a yau amma kafin a kirata abata wannan zabin a kirashi ayi komai a gabansa , Abba yayi naam da hakan take yaɗau waya yakira fayez kuma yace yazo da Hajiya zainabu tazama shaida,

Cikin mintuna ƙalilan aka hallara a falon Hajiya Hafsah da Hajiya zainabu fayez da yaya Malik , saida akai musu bayanin abinda ya tarasu a wajen tukunnan sannan papy yaƙara da cewa , " duk duniya ganinake babu ɗan da darajarsa takai ya wahalarmin da ƴata ɗaya kwalli akan soyayyah, fayez yanajin haka ya ɗago ya kalli papy chan ya sunkuyar dakai cike da takaici da fargabar zaɓin da malak zatayi ,

Binta da shigowar ta kenan gidan tasa ƙafa zata shiga palon kenan tagansu dukansu sunyi rukuni tsayawa tayi chak ta rakube bata shigoba dan tsoro take ta shiga akwai fuskokin da bazasuji daɗin ganinta ba, kamar daga sama taji Muryar fayez yana cewa, " dan Allah dady ku kyautata muradina nifa namijine ina ganin bai kamata ace za a shiga rayuwa ta haka ba, malik ne yayi saurin karɓe zanchan da cewa, " ni bantaɓa ganin inda akai hakaba tunda yace baya so taya za a zauna ayi wannan rukunin ace tace tana sonshi a daura musu aure a yau nifa ko a Film bantaɓa ganin inda akaiwa namiji wannan karfa karfar ba,

Binta dake tsaye sai yanzu ta gane inda maganar ta dosa kuma mannewa tayi da jikin bango tana dafe da gefan zuciyar ta jitake kamar ana soka mata allura,

Dady ne ya rufe fayez da Malik da faɗa saida yayi musu tattas sannan yace, " kinga malak babu wani batun jin kunya ranar wanka ba a boyan cibi ki fito ki faɗamana gaskiya kina son fayez ko a a, Malak datai shiru ta sauke sassanyar ajiyar zuciya tana bin mutanen gurin da kallo inda kowa ita yake tsumayi yaji mai zata ce

Bugun zuciyar binta karuwa yayi takuma lekawa taga da gaske ta bakin malak kawai ake jira, cikin wani irin yanayi taji kafafunta sun kasa ɗaukarta bugun zuciyar ta na karuwa duk da haka bata cire raiba jira kawai take taji mai malak zatace eh ko a'a

✍🏻 zeenariya

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

WhatsApp number

+218912472599

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (21)

Kallon fuskar fayez tayi inda shima ya kureta da ido cike da zullumi a hankali ya bude baki yayi magana batare da sautinsa ya fitaba saida ta gane abinda yake cewa ta yanayin motsawar bakinsa yake kiran, " Please Please , rintse Ido Malak tayi ta buɗe tana wasa da yatsun hannunta tace , " a tunanin idan naso mutum to kawai ya wadatar ban damu daya soniba koya ƙine sai dai yanzu na fahimci ban bancin son da mutum yake shikadai dason maso wani duk da nasan fayez yana sona kawai soyayyar watace tayi masa kutse cikin rayuwarsa magana ɗaya dazan iya faɗa muku shine a halin yanzu ni na hakura da fayez inaso kuma ku hakura ku kyaleshi ya auri wadda yakeso daga baya idan yaji zai iya aurena sai yazo muyi aure , yadda tayi maganar ne yasa zuciyoyin kowa yin sanyi fayez baisan sanda ya ɗaga hannu gaban kowa ba yana kiran , " alhamdulillah, papy cikin matukar mamaki yace , " anya kuwa malak baza a baki lokaci ki nutsu ki yanke hukunci ba?,

Kai kawai Malak ta girgiza alamar aa sannan tace, " wannan hukuncin shinaji yafi kwantamin papy , kallon ta mom tayi tace, " dadai yafi miki sauki kam haba wannan soyayya saikace masifa gara da kika hakura kika huta, mom na gama faɗin haka ta tashi ta tafi dady ne yayi gyaran muryar yace, " to alhamdulillah gaskiya naji daɗin yadda kikai dogon nazari ba komai Allah yasa hakan shiyafi alkhairi Allah yayi miki albarka, miƙewa malak kawai tayi tabar wajen Malik ma tashi yayi

Binta najin abinda ya wakana taji kamar an yayyafa mata ruwan sanyi cikin farinciki ta dinga yiwa Allah godiya a ranta, ganin suna kokarin fitowa ne yasata saurin barin wajen ta wuce bayan gidan abinta

Sallama papy da dady sukai, tare dady da fayez suka fito tundaga harabar gidan dady yace, " ka gayawa iyayen yarinyar da kakeso cewa da yamma zamu zo tambayi Aure dasa rana ayi lokaci ɗaya, haba murna wajen fayez ba iyaka jiyake kamar duk wata natsalarsa ta kare binta tazama tasa shikkenan an huta ,

Ammee tashi tayi tsam ta wuce sashin malak, a zaune ta taddata kan bed da hanzari Ammee ta karasa kusa da ita tana dariya tace, " wato abinda mukai yayi matukar yin kyau kinga munsamu nasarar kaɗa hankalin sa saura filanin na gaba, murmushi malak tayi tace, " Ammee ban taɓa ganin mace irinki ba tunda nake kanki yana matukar kawo wuta mafita bata karewa a wajenki,

Cikin jin daɗin yabon da malak tayiwa Ammee ta gyara zama tace, " ai nayi nazari kaf na gani a wannan lokacin idan nace dole saimun tilastashi anyi auren bazaiga darajar ki ba zai cigaba da sonta ne kuma zaima iya aurenta shiyasa nace mufara bari su sakankance suji kamar matsalarsu ta ƙare daga baya sai daf da bikin mu kirkiri abinda zaisa suji sun tsani junansu suma fasa auren da kansu,

Binta na shigowa tayi karo da Ammee jiki na rawa ta tsugunna ta gaisheta saida Ammee ta ƙare mata kallo ta amsa ba yabo ba fallasa,

A ranar akasa ranar binta da fayez, Abba yasamu kwanciyar hankali yanzu dan yaga fayez da gaske yake sannan kamar yadda yayi tsammanin iyayensa bazasu yarda ba sun yardan kuma sun zo cikin mutum tawa sun nemi auren binta, a unguwar kuwa ko ina zance ya baza anata kace nace masu fatan alheri nayi masu na sharrin ma nayi, yadda unguwar taɗau bakin sababbin galla gallan motoci ne yasa mutan unguwa susucewa

*

Bayan kwana biyu Abba yasamu lokaci ya kira baban jamel suka zauna yayi masa bayani gamsashshe sannan ya haɗa da basu hakuri ya mayar musu kudinsu, baban jamel sam baiji haushiba dan shima ubane bayabin goyon bayan Auren dole dan haka ya amshi kuɗinsa ya kara gaba,

A kwanakinnan binta ta samu cikakkiyar salama dan ko ganin jamel batayi idan ma tafito waje yana wajen da sauri yake barin gun ta wajen malak ma ba ruwanta ba yabo ba fallasa duk da labari yazo mata ansa ranar fayez da binta,

Bayan sati biyu ta samu kira daga Companyn su esha tana murna taje isha take sanar mata za ai taron baje kolin kaya kuma Company da kayanta zasu halarci taro wato da fashion and designer dinta zasu gwabza, sosai binta tayi farinciki

Washe gari dataje gidansu malak takanas ta kano ta kaiwa malik albishir yayi murna sosai sai dai binta ta fahimci malak ma tana shirye shiryen taron nan dan tanada tabbacin zata lashe kamar ko yaushe,

*

Koda fayez yazo zance da dare yake mata magana akan ta ajiye aikin malak saidai binta taki ƙemaimai tace haka kurin ba laifin zaune bana tsaye muna zaman lafiya da baiwar Allah saina aje aiki, kallon ta kawai fayez yayi yana mamakin karfin halinta cikin wasa yace, " lallai ƙawance yayi daɗi keda mutuniyar har bakyasan rabuwa da ita amma dai nasan dole idan aurenmu ya matso ki hakura kibar mata aikinta ta nemi wani,

,

Washegari da sassafe wajen takwas esha ta kira binta tace ," yaunefa , binta na murmushi tace , " ranki ya daɗe ai ɗoki bazai taɓa barina na manceba , dariya isha tayi ta sanarwa da binta bayan isha za a fara taron dan haka su hadu a dakin taron , binta ta amsa da to tatashi ta shirya abinta ta wuce wajen aiki

Malak kai yaɗau chaji sai waya take tana tsarawa yan aikinta kalar mutanan da takeso su sa kayan da Companyn ta suka fitar su kece raini a wajen taron, binta na shigowa malak na shirin fita bayan ta gaisheta ta amsa har ta nufi hanyar fita ta tsaya chak ta juyo ta kalli binta tace , " anjima da daddare munada taro zamuje dake a matsayin memin hidima kamar dai wanchan time din , malak na gama faɗin haka ta fice shiru binta tayi tana nazari aranta tace lallai malak batasan kimar ɗan adam ba kwata kwata,

Gyaɗa kai kawai tayi tahau aikinta

Bayan magriba fayez yazo cikin kyakkyawan shirinsa na halartar taro daman sunyi da binta zashi yaga irin kayan data zana da kuma kalar darajarsu kasancewar wannan ne na farko a rayuwar ta, binta na murna kamar sabuwar amarya daman tazo da kayanta dazata sauya ta watsa ruwa ta tsantsara kwalliya a ɗakin lailah tasa kayanta ta fito a bakin get suka haɗu da fayez ta shiga mota suka tafi

Kai tsaye wajen taron suka nufa a ka idar wajen irin wannan taron duk motar da tazo ta babban mutum zatai parking a tsakiyar filin harabar wajen taron mutane da ƴan jarida na zagaye da wajen za aita tafi ana ɗauke ɗauken hotuna, motar fayez ce tayi parking fayez yafara fitowa yan jarida sunyi redi zasu fara ɗaukan hoto dan sunsan ka ida da malak yake zuwa aduk irin wannan lokacin dan soyayyarsu sananniyace a duniya , juyawa yayi cikin takunsa na ƙasaita yaje ya buɗewa binta murfin mota tana ƙoƙarin fitowa ya miƙa mata hannu kamar karta kama sai kuma ta kama ta fito, abinda yabawa kowa mamaki ganin ba malak bace dan danan yan jarida suka shiga dandazan daukarsu hoto danko ba komai an samu sabon update daza a wallafawa duniya

✍🏻 zeenariya

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

WhatsApp number

+218912472599

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 22 )

Malak da shigowar motar ta gurin kenan taga abinda ya girgiza ta kuma ya ɗaga mata hankali, fayez da wata tsaleliyar budurwa ce cikin shiga mai matukar kyau sun maƙale hannayen juna anatai musu hoto, kuma ɗaga kai tayi tanajin zufa na karyo mata Allah Allah take taga dawa yake tare , cikin sa a kuwa wadda suke tare ta juyo wani irin ƙamewa malak tayi a cikin motar bugun zuciyar ta na jaruwa mai zata gani haka binta da fayez saboda su zubar mata da mutumci a idon duniya shine zasu bayyana kansu a gaban ƴan jarida,

jamel dake tuƙa motar malak ne yaga uwar ɗakin nasa ta shiga wani yanayi tanata haki da sauri ya duba ruwa a kusa dashi ya miƙa mata robar yanata sallallami ƙarba tayi ta ɗiɗɗike tana gumi idonta yana zubda hawaye,

Shima kansa jamel dauriya yayi daya shiga kwatankwacin halin da malak ta shiga dan ya ganewa idonsa abinda ta gani, fasa parking yayi a inda yan jaridar suke kawai kai tsaye wajen aje motoci yaje yayi parking ya juya ya kalli malak da zuwa yanzu tafara dawowa hayyacinta saboda ruwan data ɗiɗɗika yace , " madam kozan kaiki hospital ne a duba lafiyanki tukunna ?, hannu Malak ta girgiza masa alamar a'a sannan ta kwantar da kanta a kujerar motar tafara sauke ajiyar zuciya a hankali a hankali tanaso ta lalubowa kanta nutsuwa,

A ɗakin taro kuwa kowa ya hallara binta sai washe baki take daɗi kamar ya kasheta wai yau itace a wannan matsayin ga tsalelen handsome fayez ga kyakkyawan business dazai iya sawa ta mallaki Company nata na kanta, esha ce ta hango binta da sauri ta ƙaraso kusa da ita suka gaisa sannan ta buƙaci tazo suje ɗakin gwaji taga kayan nata, jiki na rawa binta ta mike tabi bayan esha kai tsaye ɗakin baje kolin kaya sukaje binta taga wata tsaleliyar budurwa ita ba yar Afirka ba ita ba yar America ba ruwa biyu itace tasa riga ta farko nan take binta ta susuce dan kayan sunyu masifar kyau bazata iya ɓoye farin cikinta ba ,

Bayan sun fito take bawa fayez labari shikam sai kuma fasa mata kai yake yana cewa yasan ma zata iya cinye gasarnan sama da kowa, suna cikin hira sukaga malak ta shigo ko kallansu bataiba tazo ta zaune kusa da Malik,

taro yayi taro kowa ya hallara mai gabatar wa ya karɓi lasifika yafara yiwa manyan baƙi barka da zuwa cikin su harda malak amma ba a sa Malik da fayez ba,

An fara gabatar da kaya ta wani labule dake kan tudu mace zata fito sanye da kayan a jikinta ta tako tazo tayi juyi takai ta kawo kamar sau biyu haka sai ta koma sai ta wani Companyn ma ta fito, kowa ya ƙwalala ido anata Shige da fice na kowa yazo anga kaya ya koma anata tafi sai aka shiga zagaye na biyu, idan macen dake sanye da kayan ta hau dan damali sai a kira asalin wanda yayi zanan ko ma mallakin zanan yazo kan dandamalin aita taya kayan har sai yaji tayin dayayi masa sai ya siya,

Masu kaya sunata zuwa ana tayawa suna siyarwa har akazo kan oganniya malak aka kirata tafito ta tsaya ta kama hannun wadda tasa kayan data zana ta ɗaga sama guri ya kece da tafi aka fara tayi chan dai data gama jan lokaci tace ta siyar ba lefi duk wanda suka siyar nata yafi tsada hakan yasata sauka daga dandamalin cikin isa da izza

Sai da aka kuma kiran kamar mutum uku aka gama sannan aka kira sunan Fatima musa, kowa ya ware ido dan sunan musanne babu wanda sunan ubansa yayi kwatankwaci da haka a wajen binta cikin farin ciki ta taso ta hawo dandamalin sai guri yayi tsit ba a tafa ba, fayez yafara tafi sai malik sai esha dan danan kamar haɗin baki guri ya tsinke da tafi,

Malak cikin matuƙar mamaki take kallon binta tama rasa wane tunani yakamata tayi sai tuhumar kanta take a ina binta tasamu damar shigar da zananta wannan gasar, malak bata dawo daga duniyar tunaninta ba saida taji tashin farko anyiwa binta tayin dayayi daidai da nata chan kuma aka taya wanda yafi nata tuni binta ta siyar guri ya kuma kecewa da tafi,

Bayan angama siyar da kayan akazo bada lambar yabo, anan kam malak ta samu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login