Showing 39001 words to 42000 words out of 67181 words
Chapter 14 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx
an rasa mai rarrashin wani acikin su , sir Yusuf ne yaciro ankwa ya ƙaraso kusa da Abba ya sa ɓangare ɗaya a jikin bed din jinyar Abbah sannan ya kama hannunsa yana kokarin samasa , sumama na ganin haka suka ware idanu cikin mamaki ummah tace ," ya haka mai ya aikata zaka saka masa ankwa , ɗago kai sir yusif yayi yana dakatawa dasa ankwar yace , " ya aikata lefin kisan kai ne , yana gama faɗin haka ya kama hannunsa yasa zai kulle kenan binta tayi zaurin zuwa ta riƙe hannunsa, kallon sa take da jajayen idonta dasuka gaji da zubda hawaye tace, " bazan taɓa bari kasawa babana ankwa ba haba wannan wane irin rashin imanine baka ganin halin dayake ciki ko kai ba musulmi bane ai ka tausaya masa, wani irin kallo sir Yusuf yakebin binta dashi cikin mamaki duk da babu alamar wasa akan fuskarsa , " akan aikina nake idan kikai kokarin hanani zan kulleki , ummah najin haka ta taso taja hannun binta suka matsa gefe
Binta cikin wani irin yanayi ta rungume ummah tana sakin wani azabebben kuka mai cin rai, mama da tun ɗazu matsar hawaye take sai tayi ta maza bayan sir Yusuf yasawa Abba ankwa tace, " tayaya yayi kisan?, gyara tsaiwa sir Yusuf yayi yace, " tuntuni wannan tambayar ya kamata kumin wannan bawan Allan shine wanda ya kashe mutumin nan da kukaga gawarsa sakamakon tukin ganganci shiya daki motarsa ya kasheshi har la hira, binta najin hakan ta taso a zabure ko gani bata iyayi sosai ta ƙaraso kusa da sir Yusuf ta nuna Abban ta cikin wata iriyar murya tace, " Abba na Abba na Abba bazai taɓa iya kashe mutum ba, bata ƙarasa faɗin abinda zataceba ta silale ƙasa sumammiya, ummah ce tayo kanta tana kuka sir Yusuf kuma ya fita ya kirawo likita,
Ɗaki aka chanzawa binta saida tayi kusan awa guda sannan ta farfaɗo babu kowa a ɗakin da sauri ta tsige ruwan dake hannun ta tanajin wani mugun jiri na ɗibarta ta fito abakin ɗakin taga ummah a tsugunne ta karasa kusa da ita ta zauna ummay na ganinta tace, " kinga yadda rayuwa take neman juya mana baya ko?, hawaye na fita a idon binta tace, " ummah ya zamuyi muba kowaba taya yaya zamu iya fidda Abba daga wannan mugun zargin, suna cikin tattaunawa mama tazo ta zaune a kujerar dake kusa dasu ta dafe kai itama cikin damuwa tace, " mun tattauna da yan sandan sun tabbatar min da musa mai lefine koda kuwa ace ba asan ransa ya aikata ba bashida wata mufita dan shi ya daki motar wanchan kuma yanzu matarsa tazo zasu tafi da gawar ta rantse da abinda zai kasheta sai an hukunta wanda ya kashe mijinta tace yana farfaɗowa za a kaishi kotu,
Saurin tashi binta tayi ta tambayi mama ina matar mama ta faɗa mata inda take binta ta nufi wajen tana zuwa ta tadda matar sanye da hijabinta kana ganinta kaga kamila hakan ya bawa binta kwarin gwaiwar tin kararta tana zuwa tayi mata sallama matar ta amsa ciki ciki idonta yayi jajir kafin binta tayi magana wasu maza biyu mata uku suka ƙaraso wajen matar na ganinsu ta fashe da kuka ta rungume ɗaya daga cikin matan yar dattijuwa tana cewa, " Hajiya shikkenan an kashe mana Tahir nashiga uku Hajiya yazanyi a wannan duniyar babu Tahir innalillahi wa innah ilaihirraju un, itama matar kuka take sosai mai yuwuwa mahaifiyar mamacin ce , ganin yadda suke cikin halin ɗimuwa na mutuwa yasa binta jinjikinta yayi sanyi itama kukan take kawai saita bar wajen
✍🏻 zeenariya
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf zeenariya
WhatsApp number
+218912472599
__________________________________
GARGAƊI
Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 25 )
Masu Iya magana suna cewa tashin hankali ba a samaka rana wannan rana kam batazowa ahalinsu binta da daɗiba mama ta cika da nadama wannan shi ake cewa ƙai ƙayi koma kan masheƙiya mijinta da takeso kamar ranta wanda zata iya sadaukar da komai nata akansa gashi ya shiga mummunan iftila i sanadin mugun nufinta,
Bayan dare ya fara yi mama tace binta taje gida takawo abinci dan Abba zai iya farkawa akowane lokaci, ba musu binta ta fito hannu ta reke da dayan tana tafe tana sake saken hanyar dazasu bi dan samun mufita saida ta fito titi ta tuna ashe babu ko sisi a tattare da ita dafe kai tayi cikin damuwa ta kalli hanya tana tunanin anya zata iya zuwa a kafa kuwa batai auneba taji anai mata hon da sauri ta kai ganinta ga inda ake hon din sir Yusuf ne ya faka motarsa a kusa da ita ya tsaya jim kaɗan yana kallon ta kamar bazai magana ba chan kuma ya buɗe baki yace, " ko zaki iya zuwa na rage miki hanya, binta kamar ta turje sai kuma ta tuna batada ko sisi kuma gidansu bazai zuwu a kafa ba cikin yanayi na kamar dole ta karasa ta buɗe gidan baya zata shiga ya juya yayi mata wani irin kallo tasan mai yake nufi sai ta fasa ta buɗe gidan gaba ta shiga batare dayace komai ba yaja motar suka fara tafiya a kan kwalta
Sassanyan Ac na motar ya haɗe da daddaɗan kamshin turaren sa mai kwantar da hankali mara hawa kai, sosai binta taji nutsuwa na shigarta duk da batada lokacin samun nutsuwa a wannan yanayin, sir Yusuf ne ya budi baki yace , " kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki Allah yana tare da mai gaskiya , kallonsa binta tayi duk da ba ita yake kalloba tace , " yallaɓai kaima kasan Abbana bazai iya kashe mutum da ganganba ko ?, girgiza kai sir Yusuf yayi yace, " bansan haka ba amma muna kan bincike wannan kes din ba karami bane matar Alhaji Tahir ta lashi takobin bin kadin ran mijinta acewar ta ma babu wani hatsari an tura babanki yaje ya kashe mijinta ne dan kawai ya shiga takarar shugaban karamar hukuma kin ga wannan babbar magana ce dole mu zurfafa bincike a kanta,
Binta najin haka ta fashe da kuka tana girgiza kai tace, " innalillahi wa innah ilaihirraju un tayaya zaku gane wannan hatsarin tsautsayine kawai wlh abbana bazai taɓa karɓar kwangilar kashe raiba,
Shiru sir Yusuf yayi yanajinta tana ta gursheken kuka har ya shiga layinsu saida yayi parking a kofar gidan su sannan yace mata, " to yar Abbanta anzo gidan, dago kai tayi tana share hawaye har zata fita daga motar sai kuma ta juyo tana kallon sir Yusuf tace, " ya akai kasan gidan mu, murmushi yayi yana sa bakin glass dinsa yace, " duk yana ɗaya daga cikin bincike na, fita kawai binta tayi yaja motarsa yatafi tana nufo get ɗin gidansu taga fayez a tsaye ya harɗe hannuwa ta baya fuskar nan kamar dare yana kare mata kallo yace, " daga ina kike wane ɗan iska ne wannan ya ajiyeki, kallonsa kawai binta tayi tanaji kamar ta zube bayan tashin hankalin da take ciki wani irin mugun ciwan kai da baƙar yunwace ke damunta kafafunta na yunkurin kasa ɗaukarta , fayez shirin datai masane yasashi kara fusata ya matso kusa da ita da kakkausar murya yace , " amanata kike shirin ciko tambayarkifa nake uban wanene wanchan , yakare maganar yana dafa kafaɗar ta yana jijjigata da karfi ,fashewa binta tayi da kuka tana mai fincike rukon da yayi mata tace , " bansani ba fayez ka kyaleni naji da masifar da take damuna mana haba yakakeso nayi babana yana gadan asibiti ga kuma tuhumar kisa da ake masa kai kuma baka san komai ba kazo kana azalzalata saboda bakin kishi, tana gama faɗin haka ta shige gida tabarshi tsaye cikin mamaki
Dakinta ta shiga ta zauna tafashe da wani sabon kukan tanaji aranta kamar bazata iya jure wannan tashin hankalin ba, wayarta taji tana kara ta duba taga fayez ne ta ɗaga tajishi da sassanyar murya yana cewa, " kiyi hakuri ki fito dan Allah kifadan mai yake faruwa mai yasamu Abba, katse wayar kawai tayi ta tashi ta saɓa hijabinta ta fita, a tsaye ta taddashi itama gyara tsaiwa tayi ta laburta masa duk abinda yake faruwa
Sosai fayez ya jinjina wannan abu sai sallallami yake chan ya sauke ajiyar zuciya yace, " indai wannan ne karki damu binta kinada Ni zanyi kokari naga nafidda Abba daga cikin wannan halin idan ma takama diyya za a biya zan iya tattara duk abinda nake dashi nabada
Sosai Binta taji ranta ya danyi sanyi fayez kuwa cewa yayi tazo suje restaurant su siyo abincin,
*
Bayan ya koma gida da daddare ya samu dady akan maganar hospital dady ya haɗe rai kamar ba shiba ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yace, " fayez ni magana ɗaya nake baka isa dan kana ɗana ba ka haɗani gaba da ɗan uwana koda kuwa ace hospital ɗinnan shikadai ne a wannan duniyar tunda na mallakawa ɗan uwana dole ka hakura dashi, fayez yanajin haka ya tashi kawai ya tafi yasan halin dady magana ɗaya yake,
Yana shiga bedroom dinsa ya shiga wanka bayan ya fito ya zauna akan bed yana tunanin mafita chan sai ya yanke shawarar kiranta a waya, lokacin karfe sha ɗaya na dare ya kira tana ganin shine ta ɗauka bayan sun gaisa yace yanason magana da ita tace yazo gida ya sameta yanzu
Ba shiri ya tashi ya shafa mai yasa boxar da singileti ya dora farar jallabiya akai ya dau wayarsa ya fito, bayan ya isa gidan nasu ya tadda ba kowa afalo yaso ya kuma kiranta sai kuma kawai ya nufi ɗakin nata , yana zuwa bakin kofa ya kwankwasa chan yajiyo Muryar ta tace a shigo ya buɗe ya shiga ya maida ƙofar ya rufe, a tsaye ya ganta tana shan coffee sanye da kayan bacci ajikinta ta baza gashin kanta sai baza kamshi take mai jan hankali
Zama yayi akan doguwar kujera ita kuma ta ƙaraso ta miƙo masa kofin coffee ya karɓa ya ajiye ta zauna a kusa dashi tana cewa, " fayez ina jinka wace magana zamuyi ?,
Fuskantar ta yayi yace, " malak dan Allah kibar maganar saida hospital dinnan kinfa san muradinane bawai dan kuɗi ko wani abunba kawai nafi jin daɗin ganina a cikin sa sama da kowane hospital, murmushi malak tayi ta gyara zama tace, " ashe babu daɗi raba mutum da muradinsa duk irin soyayyar danake nuna maka kasa ƙafa kayi fatali da ita akan wata banza kuchaka yar matsiyata, shiru fayez yayi mata ita kuma taɗan kara matsowa kusa dashi tasa hannu a hankali ta shafa fuskarsa tana kallon kwayar idon sa tace, " fayez ka tausayamin kabarni na rayu dakai idan kaimin haka kagama min komai ina sonka ina sonka fayez ka daure ka fahimci yadda nake jinka a raina, takarashe maganar tana shagwaɓe murya ta kwantar da kanta a kirjinsa , fayez wani irin nauyi yaji jikinsa yayi masa da sauri yayi firgigit yasa hannu ya ɗago ta daga rungumar datai masa yace , " malak banaso na yaudareki ne shiyasa na sanar miki da gaskiya bazan iya aurenki......, saurin toshe masa baki tayi da nata tana sakar masa wani irin shu umin kiss na bazata, hannu yasa ya turata ya mike tsaye yana cewa, " malak bakida hankali ne kinsan abinda kike shirin aikatawa kuwa?, marai raice fuska tayi kamar tai kuka ta miƙe ta riƙe gefe da gefan dama tsanshi tace, " pls fayez wannan fa ba wani abu bane muddin zaka dawo da muradinka na aurena to zan magance maka duk wata damuwarka tun daga kan kuɗi da komai da komai kayi yadda kake so dani, ta karashe maganar tana kuma sake kai masa wata irin fitinanniyar runguma mai saurin gayyato sheɗan tsakanin mutanan da ba maharraman juna ba, shiru fayez yayi yanajin wani irin yanayi mara misali a jikinsa a hankali fitar numfashinsa yafara sauyawa yasa hannu ya ɗago kanta suka haɗa ido yaji kamar ta soka masa mashi, yatsunsa yasa yafara zagaye saman kyawawan leɓanta dasu yanajin kamar ya cinyesu a hankali ya soma kai bakinsa saman nata kafin su haɗe sukaji an banko ƙofar da sauri suka juya suka kalli ƙofar a tsorace ,
A yanayin data gansu ne yasata rafka salati tana cewa , " fayez kai ne har gida kariga ka furta baka santa kuma kake biyo dare kake aikata abinda kaga dama da ita , fayez yanajin haka ya girgiza kai cikin matsanancin nadama yace , " wlh mom ba abinda kike zata bane, katse shi tayi dacewa, " mezaka cemin fayez daman ni na daɗe da zarginka akan yarinyar nan shiyasa kace bazaka iya aurenta ba ashe kagama da ita , papy ne ya shigo jin muryar Hajiya hafsa tanata ruwan bala i yace ,
" meyake faruwa ne, ta nuna masa fayez tace, " gashi nan na kamashi ya rungume ta tamkar wata matarsa sunaiwa juna kiss a wannan daran kalli kayan dake jikinta , shiru papy yayi chan ya dago ya kalli fayez yace , " zoka wuce , ba musu fayez ya fice abinsa malak kuma ta koma kan bed ta kwanta hadi da juyawa iyayen nata baya tace , " idan kun gama surutun kuficemin a daki zanyi bacci , kallon juna sukai tsakanin mom da papy
✍🏻 zeenariya
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf zeenariya
WhatsApp number
+218912472599
__________________________________
GARGAƊI
Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 26 )
Cikin hassala mom tanufi gunta tana cawe, " mu kamaki da ƙato a ɗaki kuma munai miki magana ki ɗaukemu mahaukata , da sauri malak ta tashi tana yaye blanket ɗin data rufa dashi tace , " kan uba to dukana zaki da kika wani tasomin , mom najin haka ta waro ido aikuwa ta ɗaga hannu zata shararawa malak mari taji papy ya daka mata tsawa da cewa , " karki kuskura ki taɓata kinji na faɗa miki , cikin mamaki mom ta sauke hannunta ƙasa ta kalleshi kawai saita fashe da kuka tana cewa , " wlh khabeer ka cuceni duk kaine sanadin lalacewar ta tun tana ƙarama kake hanawa koda tsawa nayi mata yau gashi ta girma da rashin tarbiyar da ban taɓa ganin ɗan musulmi da itaba itace shan giya itace wannan itace wanchan a matsayina na uwa bazan taɓa jure ganin hakanba kullum zuciyata ƙuna take mai nayiwa Allah daya jarrabeni da mummunan kaddara kan wannan yarin...., bata ida rufe bakiba taji papy ya kwasheta da mari da sauri ta dafe kunci tana sakin wani marayan kuka papy ya nunata da yatsa yace, " karki kuskura kiyiwa ƴata baki narasa mai yasa kika tsani yarinyar nan sai kace ba jikinki ta tsaka ta fitoba wannan mugwayen alkaba in dakike mata su suke jawo mata matsala a rayuwar ta ke kullum bazaki faɗi alkhairi akanta ba kullum sharri kike faɗa to bari kiji ni ban yarda malak da fayez suna aikata wani abu na alfasha ba dan da ace sunayi da yanzu ta ajiye miki ƴaƴan shegu na shaidar hakan dan batun yau suke tare ba,
Malik ne ya shigo ya gansu alamunsu ba lafiya cikin kiɗima ya ƙarasa kusa da Hajiya Hafsah dake dafe da kunci tana kuka yace, " mom lfy meyake faruwa mom me akai miki kike kuka?, tsaki malak taja tace, " waifa kawai dan tazo ta tarda fayez ya rungume ni take cewa takamamu , papy najin haka yayi saurin cewa, " uhum kaji gaskiya ta fito ko ashema rungumarta yayi tazo take nema ta ɓatawa ƴarta ta cikinta suna, itadai mom batace komaiba kawai saita fice Malik yabi bayanta,
Fayez yana komawa gida ya zauna yayi shiru yana tunanin lallai yau Allah ya taimakeshi da tuni ya faɗa tarkon malak abinda ta daɗe tana masa yau saura kiris ya afka mata, dafe kai yayi afili ya furta, " alhamdulillah Allah nagode maka daka kawo mom da shikkenan malak ta rusani ta sani a tarkonta ,
*
Washegari da safe bayan Abba ya farfaɗo sir Yusuf yayi masa tambayoyi Abba yabada bayanin yadda abin ya faru sir Yusuf yayi rubuce rubucen sa ya cirewa abba ankwar hannunsa bawai dan magana ta kareba sai dan tausaya masa da yayi yanaso yadan kuma murmurewa kafin a kaishi kotu, sosai binta taji daɗin hakan tazo ta zauna kusa da abbanta ta riƙe masa hannu tace, " Abba lfy lfy aka bani motarnan sabuwa dal nina tukota gida tayaya akai kai da kahau burki yaƙi aiki dole akwai abinda ya faru da motarnan a gida, jin jina kai Abba yayi alamar eh da sauri mama tace, " banasan rainin hankali to mekike nufi wannan fa kawai tsautsayine tunda kema kince motar lfy take amma saboda muna furci kin tsaya kina kwararo zance adole akwai abinda yafaru , kallon mama kawai binta tayi tai shiru
Kwanan Abba uku a hospital akai zaman kotu, a wannan ranar binta da iyayen ta suka shiga tashin hankali babbah duk da fayez ya ɗaukar musu lauya hakan bai hana a aika da Abba gidan yari na sati biyu adawo acigaba da shari'ar , abin ba sauki mrs Tahir marigayi ta lashi takobin ɗaukar fansa akan Abba kuma taɗau kwararran lauya wanda yasan zahirin bita da kulle akan harkar Shari'a ,
Bayan sun dawo gida kowa yakasa koda kurbar ruwa kamar wanda akaiwa mutuwa haka sukai itadai mama haɗa kayanta tayi a akwati ta fice daga gidan bayan ta kulle ɗakinta kuma ta kulle na Abba, sosai kuncin ya ƙara ƙaruwar wa ummah tarasa inda zatasa kanta hanya ɗaya gareta shine addu'a ,
Bayan sallar isha binta na