Showing 60001 words to 63000 words out of 67181 words

Chapter 21 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx

ɗauke da cikinka , kallonta papy yayi yace, " ta tabbata malak batada gaskiya ni tunda naga malik ya kira yan sanda har gidannan sun tafi da ita nasan to koma mai ta aikata ya girmama ni tsoro na ɗaya kar Jamel ya kashe musu yarinya azo a hukuntata mukuma a dinga zaginmu ana cewa mun sakar mata har kisan kai take saboda ba kwaɓa ba harara, dafe kai mom tayi cikin damuwa dan itama a tsorace take ,

*

Tana murɗa ƙofar tajita a rufe ta fasa wata uwar ƙara taita dukan ƙofar da hannunta harta gaji ta durkushe ƙasa tana kuka, durkusawa yayi a kusa da ita yace, " dan Allah ki saurareni kiji mai zan faɗa miki, hannun sa dayake kokarin kaiwa fuskar ta zai share mata hawaye ta doke cikin muryar kuka tace, " bazan yafe maka ba Jamel ka cuceni cuta mafi muni kabarni na koma ga iyayena dan Allah ka kyaleni na tafi,

Komawa gefe yayi yai tagumi yanata sauraran kukanta chan ya kasa jurewa yazo ya tsugunna a inda take yace, " na amince zan maidaki gida, kallon sa tayi saurin yi sannan ya cigaba da cewa, " zan kaiki amma sai idan har kin yarda munje wani gurin inda ba a sanmuba an ɗaura mana auren zahiri idan kuma ba hakaba binta maganar gaskiya sai dai mu mutu a gidannan nida ke bazan taɓa barinki kije ki auri fayez ba idan kuma kika matsamin da maganar tafiya zan iya fusata na kasheki sannan nima na kashe kaina inyaso duk mu mutu kowama ya huta,

*

Kai tsaye gidansu binta ya nufa yana tafe yana dukan sitiyari dan gani yake kamar baya sauri ya matsu yaje yaji ya akai aka nemi binta aka rasa sa,

Yana ƙarasawa layin yaga taron maza da mata yan jarida a kofar gidansu binta malik na tsakiyar su sai hayaniya yake, da sauri fayez ya ƙarasa ya kutsa ya samu malik yace masa, " mai yake faruwa ne wai da gaske ne ansace ta?,

" eh jamel ne ya ɗauketa labarin yanada tsayi ka tayani mu kori yan jaridar nan dan maifinta baya bukatar ganinsu yanzu ma haka hawan jininsa ya tashi inaso na kaishi asibiti amma banaso na fito dashi a gabansu zasu iya ɗaukan bidiyansa su ƙarawa labarin gishiri a jaridar gobe, jin jina kai fayez yayi dajin bayanin malik sannan ya soma magana cikin ɗaga murya da cewa idan basu bar wajenba zai kira musu yan sanda

✍🏻 mai alƙalamin zeenare

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 37 )

Hukuma sun gama tuhumar su tsab akan malak sai dai taki yarda ta jingina laifin da ita ƙemai mai taƙi sauya magana akan wadda ta kafe da farko hakan yasa suka kyaleta haɗi da kulleta dan suma basuda tabbas akan tanada masaniyar sace binta kokuwa batada ita,

Da daddare malik na kwance a ɗaki mom ta shigo ta sameshi ya gaisheta ta amsa ta zauna tace, " magana nakeso muyi dakai mai mahimmanci, mai da ganinsa yayi gareta yace, " ina jinki mom, " kaje ka karɓo yar uwarka karka bari ta kwana a station, kallon ta yayi yace, " mom bai kamata a kyale malak ba yazama dole ta karbi hukunci , dafashi tayi tace , " nasan kasan halin malak sarai yarinya ce da takeda kafiya akan abinda tasa gaba idan har mukace ta hanyar nan zamu matseta to tabbas saidai a kasheta dan bazata faɗaba duk da nasan tanada tsoron hukuma karmu bari wannan tsoran ya gushe a ranta har taji komai ma zata iya aikatawa mubi komai a hankali mu karbota musa mata ido mu lura da duk wani motsin ta tahakan zamu gane inda bakin zaren yake , " hakane mom toba damuwa bari naje na karbota, yana fiya ya kira fayez a waya yake shaida masa shima fayez yayi naam da sharawar mom dan danan shima yace ya chanchanta ayi hakan

Haka kuwa akai malik da kansa yaje yayi belinta saida suka ƙaraso gida yayi parking yana shirin fita ta kalleshi tace, " karkayi tunanin kaci banza wannan wulakantanin dakai wlh saina rama dan bana yafiya, malik najin haka ya ɗaga hannu zai kwaɗa mata mari ta riƙe hannun cike da zarra da rashin tsoro a idanunta, malik cikin tsananin mamaki yake kallon ta yama kasa cewa komai ta ture hannun sa ta fice daga motar,

Ta parlour ta wuce mom da papy suna kallon ta batace musu uffanba ta shigesu da sauri, kallo mom papy yayi yace, " kingafa yadda ta wucemu kamar batasan da mutane ba, " kaji zamin shariyar data maka kenan?, mom ta tambaya yabata amsa da, " dole naji zafi mana, " hmmmm, kawai mom tace ta wuce dakinta abinta,

Malak da hanzari ta kunna wayarta Allah yaso tana gida kai tsaye tafara kiran layin jamel data sai masa da kanta sabo ta danƙa masa haɗi da kafa masa sharadin lallai karya buɗe wadancan layikan nasa, yana daga wayar ta sanar dashi duk halin da ake ciki yanzu haka cikin tsoro yace, " ki kula wlh sakinnan da sukai miki tarkone, ai kwa batai auneba taji an fizge wayar ta ɗago kan idonta yakai kan mai kwatar wayar taji an wanketa da mari saida ta hantsila kan sofa cikin dacin rai ya katse kiran sannan ya kalli fayez dake kusa dashi ya bashi wayar yana cewa, " aje a lalubo mana inda yake a darannan, malak najin haka ta yunkuro cikin zafin nama zata cukumi malik kawai saitai kaciɓus da fayez a tsaye take wata mummunar faduwar gaba ta saukar mata ta dafe kirji tana jada baya cike da tsoran ganinsa , takowa fayez yayi saida ya ƙaraso daf da ita fuskarsa babu rahama yace , " a yanzu acikin raina inaji duk duniya babu wadda na tsana sama dake malak wlh badan darajar iyayenki data dan uwanki ba saina sa hukuma tayi aikinta akanki saidai zan iya hakuri ne idan har wani abin bai samu binta ba kisani idan yarinyar nan ta cutu tofa ko da hannun uwata a cutar da ita saina dau fansan aure kuma tsakanina dake na faɗa zan maimaita baza a taɓa yinshiba har abada , yana gama fadin haka ya juya ya fice, malak mutuwar tsaye tayi takasa ko kokkaran motsi maganganun fayez ne suke ragar gazarta malik kuwa harɗe hannayensa yayi yace, " ina so wannan kiyayyar tazo karshe tsakaninki da binta karki soma yarda wata matsalar ta sake faruwa idan ba hakaba mu zamu sallamaki, yana gama faɗin haka ya fice shima ya barta,

*

Jamel yana zaune sai zullumi yake yakasa nutsuwa yasan ba lallai fayez ya kyaleshi ba akan binta hakan ne ya dasa masa wani sabon tunanin da hanzari ya tashi ya shiga kitchen ya dakko wuka , binta na daure da igiya kafa da hannunta bakinta kuma da salatif dan tunda ta dameshi da bige bige da ihu ya kukkulleta , ƙarasowa yayi inda take zaune idonta jajir sai hawaye take ya zauna yana kallon wukar dake hannunsa yace , " binta nasan da wuya na tsallake daran yau ban shiga hannuba shiyasa naga yadace kawai mu kashe kanmu mubar musu wannan duniyar hakan shizai hana fayez samunki , kukane ya kwace masa daƙer ya tsagaita kamar wani ƙaramin yaro ya rungumota kirjinsa yana cewa , " kiyafemin binta saboda ke zan rasa duniya kuma in rasa lahira amma nasan Allah zai tausayamin tunda shi kaɗai yasan yadda nakeji a raina , abinda ya liƙa mata a baki ya ɗaye ta fashe da kuka tana girgiza kai tace ," jamel zaka aikata kuskuren da bashida yafiya jamel namaka alkhawarin zan wankeka awajen hukuma bazan taɓa bari a hukuntaka ba amma dan Allah karka cutar dani kuma karka cutar da kanka ka tuna kaifa musulmi ne ɗan musulmai jamel idan har soyayyar da kakemin ta gaskiya ce to na rokeka dan ita kada ka cutar dani kada ka cutar da kank...., ɗora mata hannusa yayi akan bakinta alamar tayi shiru yace, " basai kin ƙarasa ba namiki alkhawarin ke zaki tsira amman ni dana bari inaji ina gani ki auri fayez gara na kashe kaina , yana gama faɗin haka ya ɗaga wukar da karfi ya saukawa kansa, wata iriyar mahaukaciyar kara binta tasaki kan kace kobo ya faɗi jini nata malala, bayan 5 minit Jiniyar yan sanda ta karaɗe unguwar suna zuwa gidan suka ɓalle ƙofar fayez da malik ne a gaba gaba wajen kutsawa gidan fayez duk ya kidime sai kwala mata kira yake chan daga gefe yaga mutum a kwance da sauri suka ƙarasa yaga Jamel kwance cikin jini male male cikinsa soke da wuka ita kuma binta na zaune a gefansa hannunta a daure kafarta a daure ta ƙame kikam ita ba sumammiyaba kuma ita bamai motsiba , da sauri ya ƙarasa inda take yasoma kwanceta yana jijjigata amma taki koda tari idonta akan gawar jamel dake kwance , rungumeta fayez yayi yana sakin kuka tamkar wani karamin yaro ,

Dan danan malik da fayez suka wuce da binta hospital, shikuma jamel yan sanda suna kokarin saka gawarsa a mota dan aje ayi bincike sukaga hannunsa yana motsi ba shiri suka wuce dashi asibiti,

Babban asibiti mafi kusa suka wuce fayez daman yasan wasu manyan likitoci da suke aiki anan dan danan yasa aka kira masa Dr amal,

Tana zuwa taga fayez ne daman ta masa farin sani babu tsayawa dogon jawabi aka shiga da binta emergency room Dr amal nashirin shiga fayez yace, " Dr zan shigo ayi aikin nan da ni tana cikin yanayi na firgici da tashin hankali sai, dakatar dashi tayi da tace, " Dr fayez kai kanka a yanzu baka cikin nutsuwar dazaka iya duba mara lafiya kayi hakuri ka nutsu nasan kasan kwarewata akan aikina shiyasa ka nemeni inada tabbacin insha Allah zanyi aiki tamkar kaine kayi, malik ne ya dafashi alamar ya amince da hakan babu yadda fayez ya iya dole tasashi ya amince ,

Bayan kamar minti talatin Dr amal ta fito tace su bita office , suna zuwa suka zazzauna ta kalli fayez data sani tace , " Dr an samu sa a tana lafiya dan yanzu ma haka na mata allurar bacci dan ƙwaƙwalwarta ta huta zuwa wani lokaci sannan abu na gaba She was brutally raped kuma sannan an mata ɗinki har uku, " innalillahi wa innah ilaihirraju un du kansu fayez da malik suka furta , cikin kunar zuciya fayez yace , " Dr amal ina fatan you have checked thoroughly and there is no problem with urinary leakage , " yes Dr naduba hakan saida nayi mamaki dan duk fyaden dazakaga anyishi har ansamu dinki to zai iya haifar da yoyon fitsari amma kam ita alhamdulillah Allah ya taimaketa dazarar ta warke zata dawo kamar ba aiba dan an riga an dinketa ,

*

Baba na zaune suna tattaunawa da Ummah malik ya kira su yake sanar dasu an samo inda take, farincikin da su Abba suka tsinci kansu bashida misali dan danan sukace a faɗa musu sunan asbitin suje aikwa a daran malik yazo ya daukesu ya kaisu sannan ya wuce gida,

Suma iyayen malak sun samu labarin samun binta sai dai abu mai ratsa zuciya shine jamel ya raunata kansa hakan ne yadasawa mutane da dama tausayinsa tayu zafin sone yasashi aikata hakan

Sai wajen asuba binta ta farfaɗo lokacin an chanza mata ɗaki tana buɗe idonta ta dorashi akan mahaifiyar ta aikwa da sauri ta ware hannu tana kuka alamar tazo gareta da sauri ummah ta rungume ta suna kuka fayez da Abba ne suka shigo suna ganin ta farfaɗo suka ƙarasa cike da farinciki suna mata sannu binta chan tayi firgigit kamar wadda ta tuna wani abu ta zabura ta dire kafafu zata fita da sauri fayez ya rukota yana girgizata dan kokarin kwacewa take cikin kiɗima take cewa, " ina jamel dan Allah kada kucemin ya mutu saboda ni dan Allah fayez kacemin bai mutuba banaso sanadin soyayya ta yakashe kansa, kuka take mai tsuma zuciya fayez ya rungume ta cike da soyayya da tausayi yace, " jamel yana nan bai mutuba addu'a kawai yake bukata kuma insha Allah bazai mutu saboda keba,

✍🏻 mai alƙalamin zeenare

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

WhatsApp number

+218912472599

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 38 )

Komawa tayi gefe ta zauna tana cewa, " ba a san ransa ya cutar dani hakaba kuma yayi dana sani gudun abinda zai farune idan aka kamashi yasashi yunƙurin kashe kansa na roƙeƙa fayez kada kabari a hukuntashi wlh sonda yakemin da kuma tsoran kada ya rasani yasashi aikata haka, ummah najin abinda binta ke faɗi tayi saurin katseta da cewa, " kinsan mai kike faɗe kuwa binta ai dole a hukunta jamel abinda ya aikata bana yafiya bane idan ke bakisan mutumcin kanki da irin illar dayayi mikiba mu iyayenki mun sani kuma kobadan keba dan hakkinmu da hanamu kwanciyar hankalin dayayi sai an hukuntashi, yadda ummah ke magana cikin fishine yasa Binta sassauta kukanta tana bata hakuri Abba ne ya dafa ummah yace, " usaina baki fuskanci zuciyar Ƴarkiba tausayi ne yasata faɗin hakan bawai dan batasan ciwan kanta ba kumafa azahiri idan za a bayyana asalin wanda ya hassasa abin nan mamanta ce da kawunta su sukasa jamel ya ɗauketa batare da an daura aureba , fayez yana tsaye agefe sai yanzu yasa baki da cewa , " kayi hakuri Abba kana magana na katse ka wato masu laifin ai sun bayyana ƙarara jamel ne da Malak kuma ko kowa ya yafe ni bazan kyaleba ,

" yaro banƙi ta takaba amma idan ɓera nada sata daddawa ma da warinta da ace maganar a yaɗa an ɗaura aure bata fito daga gidana ba to da tabbas malak da Jamel basuda hujjar zuwa su ɗau binta sai dai idan saceta zasuyi , Abba ya faɗa cikin nutsuwa yana kallon fayez binta ce ta ƙara da cewa, " naji lokacin da jamel yake waya da malak tabbas ita tabashi gidan daya kulleni a ciki kuma ita ta turo masa likita lokacin dana fita a hayyacina ina tunanin malak tayi hakan ne saboda tsoran yarjejeniyar da mukai zata iya rushewa,

" wace yarjejeniya kukai?, fayez ya tambaya

" a lokacin dana rasa yadda zanyi Abbana ya samu kuɓuta sai naje na sami malak na roketa ta taimaka tasabaki tabawa mrs Tahir hakuri kozata hakura ta jenye sharrin da suke kokarin lakabawa babana Malak ta yarda zata taimakeni amma sai na amince na fasa aurenka kuma sannan saina yarda zan auri jamel kafin ayi zaman kotu na karshe nikuma ganin banida zaɓi na amince amma wlh koshi jamel baisan cewa yarjejeniya mukai akan na aureshi ba, yarfe hannaye fayez yayi cike da takaici yanaji aransa lallai rashin imanin malak ya wuce inda ake tunani

*

Zaune take a kyasa kunnanta manne da karamin Bluetooth headphone fuskarta cike da hawaye take cewa, " nakasa hakuri nakasa juriya Ammee da bakin sa yake cemin duk duniya babu wadda ya tsana sama dani Ammee akan tarabu dashi har 100 milion nabada diyar kisan da ubanta yayi amma yanzu kowa ni yake tsinewa gashi an buga jaridu an ɓatamin suna wai nasa anyi garkuwa da ita saboda saurayina, kukane ya kwace mata mai karfi chan ta kuma cewa, " wlh Ammee nida binta dole ɗaya ya hakura kuma ni ata ɓangarena bazan taɓa zama da kishiya ba ko mutuwa zatai saidai ta mutum amma indai taga na bari ta aureshi sai dai idan bana numfashi

*

Bayan kwana biyu

Jamel yana asibiti yana jinya amma a karkashin tsaran hukuma suna tsare dashi har sai ya samu lafiya za a turashi kotu ta yanke masa hukuncin akan laifin sa

Itama binta tana cikin jinya amma da sauƙi yanzu jikinta ya dawo dai dai illa kawai ɗinkin da bai warkeba,

A ɓan garan mama kuwa har asibitin tazo ta durkushe tana kuka tana neman yafiyar binta da mahaifiyar ta sannan ta roƙi Abba alfarmar ya maidata ɗakinta haɗi dayi masa alƙawarin bazata kumaba,

futu futu Abba yayi mata ya nuna mata ta aikata laifin dabashi da yafiya haka mama tabar asibitin nan cike da bakin ciki da takaici , su binta da mahaifiyarta sun babbawa Abba baki amma sai cewa yayi bashida lokacin magana akan mama karsu sake masa ita,

Yau aka sallami binta a asibiti suka koma gida abinsu sai dai suna zuwa suka tadda bakon abu mamace da ƙawarta sukai bake bake a gidan har sun fara fito da wasu kayan na umman binta sunyu watsi dasu a tsakar gida rana tana duka, cike da mamaki Abba ya leƙa ɗakin yace, " menene hakan fatima mai zan gani?,

Mama na taunar cingom ta karkata dankwali gefe ta kalli Abba a wani shekeke tace masa, " abinda idonka ya gane maka ko ka manta nan ɗin gidanane shekara da shekaru kana cikin sa ba biyan haya ba komai abincin ma ni nake sai muku amma saboda butulci irin na ɗan adam rana tsaka ka sakeni saboda ɗan kuskure ƙanƙani ka rushe duk kyautatawar danai maka sama da shekara 40 , shiru Abba yayi ransa abace ya fita yaje waje ya samu guri ya zauna yana tunanin yanzu idan Fatima ta koresu asirinsa yagama tonuwa dan bashida komai da ita ya dogara tun yana saurayi itace rufin asirinsa ,

Binta naganin Abba ya fita tasa kuka tace, " haba mama koda zaki wulakanta mu bai kamata ki haɗa da Abba ba dan Allah ki tausaya masa yaushe ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login