Showing 57001 words to 60000 words out of 67181 words

Chapter 20 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx

almajirin ya koma ya faɗa chan sai gashi sun fito da Abba malik yana ganin Abba ne ya durkusa ya gaisheshi bayan sun gaisa Abba yake cewa, " bata faɗa maka tayi aure bane?, cikin mamaki Malik ya ɗago ya kalli Abba yace, " baba wane irin aure kuma yaushe aka ɗaura?, jin jina kai Abba yayi yace, " jiya da safe aka ɗaura da magriba mijinta yazo ya ɗauketa, cikin mamaki Malik ya sassauta murya yace, " wata aura dan Allah Abba kafaɗan?,

" Jamel ne nima bana nan aka ɗaura auren sai bayan na fito nake jin labari,

" what jamel fa kace Abba ai jamel bai aureta ba aka kama shi , zaro ido abba yayi cikin faɗa yace , " kai banason shashanci zan maka wasane , " abba ka tambayi wanda suka halicci daurin aurennan wlh ba a daurashiba , abba ɗagawa malik hannu yayi ya curo waya a aljihunsa yana dannawa malam liman kira yace , " barima nakira maka wanda ya daura kaji daga bakinsa , abba bai rufe bakiba liman ya daga suka gaisa abba yake cewa , " malam liman yagajiyar hidima nagodefa duk da bana nan anmin kara an jagoranci daurin auren yarinya kamar inanan, " bakomai malam musa aikai mutimin kirkine dan ma ansamu matsala bama afara daurin aurenba yan sanda sukazo suka tafi da angon da waliyansa to ganin shiru shiru basu dawoba yasana sallami mutane su tafi kasuwar su tunda ranar litininne , Abba najin haka ya saki wayar yayi luuuu zai faɗi da sauri malik ya taroshi abba sai furta innalillahi wa innah ilaihirraju un yake , malik ne ya shiga da abba gida mama sai sallalami take taga sai innalillahi yake cikin fargaba tace , " lafiya malam ?,

Abba duk da halin da yake ciki hakan bai hanashi jifan mama da kallon tsana da tuhuma ba cikin faɗa muryarsa har shaƙewa take yace " ashe ba a ɗaura aurenba kukace an ɗaura kukasa nabashi yata yatafi da ita , ummah dake fitowa daga daki tanajin haka tafaɗi sumammiya mama kuwa fargaba da tsananin tsorone suka kamata batasan sanda tayi suɓutar bakin cewa, " waya faɗa maka, Abba da malik suna ta ummah babu wanda ya saurareta bare ya bata amsa

*

Tinda gari ya waye yarasa yadda zaiyi binta taki farfaɗowa gashi jininta zuba yake cikin fargabar karta mutu ya kira malak ba batun gaisuwa tana ɗagawa yace, " innalillahi wlh ranki shi daɗe nakusa yin kisan kai nayi shaye shayen magunguna masu yawa na afka mata naji mata rauni gashi tunda ta suma bata farfaɗo ba ina tsoran karta mutu ki taimake ni, miƙewa tsaye malak tayi tace, " Jamel kana nufin kisa zakai min agidana masu bincike suna ganowa a gidana abin ya faru bazasu kyaleni ba nifa bance kai mata fyade ba cewa nayi ka kulle ta saita samu ciki a bayyana gaskiya, kashe wayar tayi tashiga kai kawo a dakin tana ta tsuma duk ta ruɗe dan ta tabbatar idan jamel ya shiga hannu itama tata ta kare kuma idan fayez yasan ita ta shirya wannan tuggun bazai taɓa kyale ta ba kuma batun aure a tsakanin su hat abada

Lailah ce ta shigo da kayan breakfast ta ajiye ta lura da halin kiɗima da malak ke ciki hakan yasata tana fita ta laɓe kozaji wani abin sai kuma bataji komai ba harta gaji ta wuce ,

saida malak tagama tunani sannan ta kirashi tace zata turo masa likita

Haka kuwa akai cikin ƙan kanin lokaci ta turo wani inyamuri yazo har gidan ya duba binta yayi mata duk abinda ya dace saida yayi mata dinki uku sannan yayi mata allurar bacci ya tafi tare da yiwa jamel kashedin karya sake yakuma kusantar ta idan yanaso tasamu lafiya ,

Likita na tafiya nutsuwar jamel ta dawo duk wani haushin ta dayake ji sai yaji babu wani irin mugun tausayin ta da santa na musamman ne yake ratsa duk wani lungu da saƙo na zuciyar sa amma idan ya tuna batare da aureba yayi mata karya ya kawota yayi nan yakanji kamar bazata iya yafe masaba kuma shima bazai iya yafewa kansa ba dan duk wani ƙarshen wulakanci dacin mutumci yariga ya gama gwada mata shi ,

*

Malik ya kasa barin gidan su binta har saida aka sanar da iyayen jamel sukace tun jiya da yadawo ya haɗa kayansa yace barin garin zai tunda bai samu auren ba basu kara ganinsa ba, wayar sa aketa kira shida binta duk akashe dan danan aka sanarwa yan sanda suka fara bincike cikin gaggawa,

malik ne ya tsaya akan komai duk ya shiga damuwa saboda tunanin halin da binta take ciki , ɗan sandan dake bincike akai ne yace ko akwai wanda ake zargi malik agaban iyayen binta sai yace babu amma daya fito mota sai ya kirawo shugaban yan sandan yace masa yazo da rindina guda ta ƴan sanda gidansu shima yana hanya yanzu zai zo akwai wadda yake zargin ita tasan inda jamel ya ɓoye binta,

Haka kuwa akai atare suka ƙarasa gidan malik ne yafara shiga ya sameta kwance a falo akan cinyar papy cikin haɗe fuska kamar bashiba yana huci yaje ya taya yace, " zaki faɗamin inda kikasa Jamel ya ɓoye binta Kosai nasa ƴan sanda sun shigo sun tafi dake?,

Tashi tayi tana waro ido cikin mamaki tace, " ban gane mai kake nufiba Malik ? , yana huci cikin ɗaga murya kamar bashiba saboda fusata jikinsa sai tsuma yake yace, " bazan raga mikiba wallahi komai zai iya faruwa idan bakiyi gaggawar faɗamin inda kuka ɓoye binta ba ,

papy cikin mamaki yace, " malik wace iriyar magana kakene?, malik kamar jira yake ya zayyanewa papy duk abinda ya faru papy najin haka jikinsa yayi sanyi cikin mamaki ya kalli malak yace, " nasan zaki iyayin komai akan fayez kuma nasan bakya kaunar yarinyar nan dan haka tun ta lalama ki faɗi inda take idan kuma kikaƙi zan zame hannuna akanki na barki da hukuma , malak najin haka idonta ya ciko da wahaye dan taga mahaifin nata babu alamar sassauci akan fuskarsa

Tafa hannu mom tayi tace, " nidama nasan za azo wannan ƙadamin atunanin ki bansan kulla kullar da kikeba to tun wuri

kifaɗi inda kikasa aka kai musu yarinya idan kuma ba hakaba, mom ta karashe maganar tana nuna Malak da yatsa ,shiru malak tayi ai kuwa papy ya kalli malik yace, " ka Kira hukuma su tafi da ita su bincike ta babu ruwana a wannan maganar, malik najin haka ya ɗaga waya yayiwa yan sandan izinin shigowa nan danan sukazo suka sa mata ankwa idon malak yayi fiki fiki cikin ɓacin rai tace, " yanzu papy kana gani zazu tafi dani daman baka sona ?, banza papy yayi mata ta maida ganinta ga mom tafara magiya tana cewa , " mom dan Allah kice karsu tafi dani nibansan komai ba akai kinsan malik baya sona saboda yarinyar nan, banza mom tayi mata duk da zuciyarta batasoba tanaji tana gani aka tafi da malak ,

*

A hankali ta buɗe idonta ta kalli saman ɗakin chan tafara tuno abinya yake faruwa ta kalli hannunta taga ruwane ta yunkura duk da azabar da takeji ta cire ruwan daga jikinta ta zauna tayi shiru tana kallon ɗakin chan tafara tunani a ranta wai yanzu ace mijinta na sunna ne zai mata wannan cin zarafin da rashin imanin kamar babu soyayya sai ɗaukar fansa, bata rufe bakinta ba ya turo kofa tana ganinshi tafara jada baya tana hawaye, tsayawa yayi daga inda yake yace, "kinga ki kwantar da hankalin ki wlh babu abinda zan miki kinji , kallonsa tayi kawai ta saki kuka ta sunkuyar da kanta ƙasa

✍🏻 Mai alƙalamin zeenare

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

WhatsApp number

+218912472599

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 36 )

Jikinsa ne yakuma yin sanyi cikin nadama ya jingina da bango yana cewa, " wlh binta nayi nadamar abinda nayi miki dan Allah kice kin yafemin ko naji sassauci a zuciya ta, kallon sa tayi cikin mamaki sai kuma ta share hawayen ta tace, " babu komai jamel kaifa mijinane, ƙarasowa yayi kusa da bed din yace, " inason na faɗa miki wata gaskiya, " ina jinka, tafadi tana kallonsa ,

" binta maganar gaskiya niba mijinki bane baa daura mana aureba, binta najin haka ta ware ido cikin rudani tace, " jamel mai kake cewane ban fahimta ba kayini yadda zan gane, kuka ya fashe dashi yace, " ki yafemin nayi abinda ban taɓa aikata waba wlh ba a ɗaura aurenmu ba na aikata zina dake innalillahi na cuci kai na nabiyewa son zuciya na cutar dake ki yafemin sonki da kishin kar wani yasameki ne yasa nayi miki haka, binta na sauraren haka ta mike da kyar cikin kiɗima tace, " ba a ɗaura auren muba kace?,

" ba a dauraba kawunki ne yace nacewa mahaifinki an ɗaura idan ba haka ba zai aurawa fayez ke dan yafi son ki auri fayez shine na faɗa masa hakan, " innalillahi wa innah ilaihirraju un ka cuceni jamel Allah ya isa bazan taɓa yafe makaba ka zalince ni ban taɓa tunanin zan samu ga mutumin banza irinka ba azzalumi macuci fasiki, kukane mai karfi ya kwace mata ta tashi tana jan kafa da kyar saboda ciwan jikinta tanufi hanyar fita da sauri yaje yasha gabanta ya tsugunna yanna bata hakuri yace, " dan Allah karki barni wlh ina sanki bazan taɓa bari kibar hannuna ba dan Allah ki zauna tare dani muyi rayuwa cikin aminci....., wankeshi da mari tayi tana huci tace, " la a nannan Allah mutsiyaci wace iriyar rayuwar aminci zanyi kai wani irin dabbane wai Jamel, kuma riƙe mata ƙafa yayi yana cewa, " na yarda ki kirani da koma menene binta wlh bazan iya rabuwa dake ba dan yanzu nasan mahimmancin ki a gareni , juyawa tayi kamar zata shige ɗakin yana tashi ta zille da sauri tana rintse ido saboda azabar da takeji ta nufi kofar fita daga falon ,

*

An fito da malak kofar gida za a cusata a motar yan sanda mota tayi parking a gaban ta yan sandan dan danan malak ta shiga zare ido cike da fatan Allah yasa ba fayez bane,

dadyn fayez ne ya fito daga motar ya ƙaraso ya miƙawa ɗan sandan hannu suka gaisa yace, " mai yake faruwa ne?, malak naganin haka ta marairaice fuska zatai magana ɗan sandan ya daka mata tsawa yace, " karki sake naji bakinki anan, dakatar dashi dady yayi da kuma tambayar mai yake faruwa,

" muna zargin tane da haɗa baki da direbanta jamel su sace yar aikinta binta, jin jina kai dady yayi ya kalli malak sannan yace, " to ina mai rokon afuwa kubani ita yanzu na tafi da ita a motata namuku alkawarin zaku samu haɗin kai daga gare dari bisa dari mu gudanar da duk wata tuhumar amma bamaso atafi da ita a motar ku saboda yan jarida da sauran mutane, officer to ya amsawa dady dan yasan manyan mutane nesu,

Motar yan sandan ce tafara gaba dady yaja hancin motarsa ya bisu a baya suna tafiya ya kalli malak dake kusa dashi yace, " my daughter mai yasa zaki jagoranci babban laifi irin wannan ina ganinki mai hankali?, ma rairaicewa tayi tace, " uncle I swear I don't know anything about this statement kawai dan Malik baya sonane shiyasa ya ɗoramin laifin kumafa da sukace min zasuyi aure ita da shi Jamel ɗin nina basu gidan zama nayi mata lefe nabashi sadaki a matsayinsu na yan aikina,

Jinjina kai dady yayi yace, " bazan karyataki ba amma inada yaƙinin ɗan uwanki malik bazai taɓa yarda a tuhumeki akan abinda yasan baki da hannu akai ba kinga my daughter zan baki shawara idan har bakyaso ki ɓata mana suna a idon duniya to kifaɗi gaskiya a game da wannan lamarin maganar nan ba ƙarama bace batune na sace mutun yan adawa suna sani zasu zuzuta abun yazama sular zubewar darajar mu sannan duk ɗan familyn mu bazai shiga cikin mutane ya sakata ya walaba , shiru malak tayi tana nazarin maganar dady tabbas gaskiya ya faɗa amma taya zatai kirari ta dabawa kanta wuka bayan binta ita kadaice matsalarta a yanzu ,

Suna ƙarasawa police station aka sata a ɗakin tuhuma inda ake tuhumar manyan masu laifi, wata yar sanda ce mara imani tazo zatayiwa malak tambayoyi , gaba ɗaya malak ta gama tsorata da ganin matarnan dan babu alamar ɗugon tsoro ko sassauci a tattare da ita cikin hanzari tazo ta zauna akan table ta ƙarewa malak kallo na wasu sakanni sannan tace , " menene alakarki da wadda ta ɓatan ?,

Daker malak tace, " yar aikinace,

" ko, matar tace sannan ta kafe malak da ido tace , " ance itace wadda saurayinki zai aura haka ne?,

" yes,

" sannan kuma ance direbanki ma yana sonta dan har daga baya data yarda zata aureshi ke kika ɗau nauyin komai na auren bayan kuma kowa ya shaida bakya santa,

" bincike ya tabbatar mana kece ta ƙarshe wadda jamel ya haɗu da ita kafin yaɗau binta sannan kuma munsamu rahoton cewa ɗaya daga cikin motocin da kike hawa ya hau kuma a tsarin doka na aikinki bakiyar da yaɗau motarku ta kwana a wajeba saidai idan da izinin ki?,

Idan malak ne yakuma yin zuru zuru dan danan tafara zufa tana numfashi da sauri da sauri murmushi yar sandar tayi mata ta miƙa mata ruwa dan danan malak ta karɓa tafara kwankwada saida ta gama yar sandar ta kuma jefo mata magana, " kenake saurare yi bayani, yadda malak tayi firgigit ne ya kuma tabbatar wa da wadda take tuhumar tata batada gaskiya malak na ƙin ƙina tace, " batun mota ninace ya ɗauka dan nazaci an ɗaura auren da gaske, shiru malak takumayi tana riƙe hannun ta sai karkarwa suke yar sandar takumai mata wani irin kallo nake nake saurare dan danan malak ta kuma cewa, " shikuma zuwan dayayi yazone akan nabashi hutun sati guda saboda yayi sabon aure,

*

Mama na zaune a ɗaki sai zufa take Abba ya shigo ya tsaya akanta abinda ya razanata shine taga ɓacin ran dabata taɓa ganiba a fuskar sa da kakkausar murya yace, " Fatima ki faɗamin dalilin dayasa kikace acemana an ɗaura auren bayan kuma ba a ɗaura ba, dafe kirji mama tayi tana cewa, " wa ni ? au sharrin daza amin kenan yaushe nace ace nina...., katseta yayi ta hanyar ɗauketa da gigitaccen mari wanda ya tilasta mata rufe baki dan danan cikin wutar mamaki,

" kin zalince ni kin cuceni mutuniyar banza mutuniyar hofi an gaya miki bansan komai ba to naje har kauye na titsiye habu ya gayamin kece kikace yacewa su binta an ɗaura auren sannan kika bashi dubu amsin yabata sadaki kuma ke kikasa acewa jamel yazo yadau matarsa a matsayin an ɗaura , mama najin haka ta fashe da kuka takasa cewa komai ummace ta shigo dakin tana cewa , " ban taɓa tunanin koda kina cutaba zaki iya cutar da rayuwar binta nida ƴata muna binki sauda ƙafa sharaɗin da kika gindaya shi muke bi yarinyar nan uwa ta ɗaukeki tun tana ƙarama take kiranki da mamanta ni haihuwar ta kawai nayi amma komai ke kike zartarwa akanta saboda Allah a tsawan rayuwar ta dake wane laifi tayi miki mai tsaurin dazai iya sawa ki hukuntata ta hanyar kassara mata rayuwa , kukane ya kwacewa ummah Abba cikin tsananin tausayin iyalin nasa yace , " fatima kije na sakeki saki daya , amma najin haka ta dafe kirji cikin ɗaga murya tace , " ka sakeni malam kasan mai kake faɗa kuwa sakinafa kace kayi ?," eh sakinki nayi ko bakiji ba na maimaita, tsugunnawa tayi tana riƙe gefan rigarsa cikin tashin hankali take basa hakuri tana neman yafiya, ficewa ummah tayi Abba ma ya fuzge rikon datai masa yabi bayan Ummah yana rarrashin ta,

*

Banko ƙofa tayi tana ƙwala masa kira a kiɗime ya nufota yana kiran, " Ammee lafiya mai yake faruwa, riƙe masa kafaɗu tayi tana cewa, " malak malak ce yan sanda suka kamata wai ana tuhumar ta yanzu nagani a TV,

" tuhuma kuma tamai?, fayez ya faɗa cikin mamaki Ammee cikin ɗimuwa tace, " akan waccan yar iskar yarinyar mana Binta wai tabi saurayi sun gudu shine iyayenta suka shigar da ƙara wai malak ce tasa aka saceta, " what? , ya furta bakinsa har cijewa yake yace, " wai kina nufin binta aka nema aka rasa?, kai ta gyaɗa masa alamar eh ai bai wani tsaya jiraba ya dauki wayarsa da mukullin mota ya fice, jikin Ammee ne yayi sanyi dan tasan wannan gigicewar dayayi ba saboda malak bane,

Kai kawo papy yake cikin tsananin fusata ya doka rimot ɗin hannun sa da ƙasa yana cewa, " ya akai daga kama malak yanzu yanzun nan har yan jarida sun samu labari sun wallafa karya akai, mom ce cikin takaici tace, " wlh bana tausayin malak nafi tausayin binta dan ba asan a wane hali take ciki ba, huci kawai papy yake mom ta ƙaraso kusa dashi ta dafa kafaɗunsa tace , " my man kowane iyaye sunasan yayansu kamar yadda mukeson tamu yar wlh nida kunnena naji lokacin da jamel yazo suke tattaunawa nazo zan gifta naje kitchen naji tana ce masa karya sake ya rabu da Binta idanba hakaba yanaji yana gani zata auri fayez sannan dana kuma giftawa na foto daga kitchen naji tana faɗin kabari har saita samu ciki zaka bayyana gaskiya kaga da cikin fayez bazai taba aurentaba dan tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login