Showing 15001 words to 18000 words out of 67181 words

Chapter 6 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx

zeenariya

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (10)

Tun ranar da lailah taga binta da fayez ta ɗana tarko duk wani motsin binta a gidan nan yana kan idonta, itama binta tunda ta fuskanci lailah tasa mata ido ta chanza taku kwata kwata bata yarda ko ganin fayez tayi ta nuna tasanshi indai agidanne ko alayin shima fayez ɗin haka amma tabayan fage sunata zuba soyayyar su kusan kullum sai yaje zance bafashi,

Ayaune binta ta kwantanta zanan takalmi mai kyau saida taɗau tsawan kwana biyu tana zanashi kuma ta tsaya ta nutsu ta zurfafa tunani zanene dabata taɓa ganin kalar takalmin akafar waniba duk da takalmi ta kalmime amma kowanne da irin tsarin adonshi cikin farinciki da fatan Allah yasa malak ta karɓa binta tazo aiki yau, bayan tagama aikinta taje tasamu malak a falo tana zaune tana danna wayar ta Binta ta rusuna ta gaisheta ta amsa sannan tace, " badam daman maganace nakeso muyi hannu malak ta ɗaga mata dai dai lokacin da wata farar mata kana ganinta kaga Hajiya ta shigo, dafara a malak ta tashi ta rungume ta suka karaso suka zauna matar tace, " aini nazaci harkin gaji da jirana kintafi, malak cike da walwala a fuskarta tace , " haba Ammee ai ɗoki bazai bari natafi batare da kinban albishirin ba,

" Kwarai kuwa to albishir ɗin dazan miki shine jiya dadyn fayez ya titsiye shi kan maganar aurenku babu yadda yaronnan yayi saida yabawa mahaifinsa amanna asa ranar aurenku nan da wata guda,

Binta dake tsugunna a gefe wani ɗufff taji kunnuwanta da zuciyar ta sunmata batasan sanda ta dafe kirjiba tanajin numfashinta yana barazanar tsayawa, malak kuwa munna ba a magana, kallon su kawai binta take sai a wannan lokacin tafara tunanin matsayin ta awajen fayez hawaye ne suka shiga siraro mata da sauri tasharesu ta tashi zata bar wajen malak ta kalleta tace, " ke ina zaki, binta da duk yanayin ta ya chanza daker ta iya cewa ɗaki zani, " wace magana zaki faɗan, binta ta kaddun da suke hannun ta ta kallah sai tachanza shawara a fili tafurta , " eh ah kawai daman na nafito ne na tambayeki kokinada bukatar wani abun , kallon junansu sukai tsakanin Ammee da malak Ammee tana taɓe baki tace ," wannan kuma mai kama da fulanin jejin ina kika samota ?, tsaki malak taja tace , " yar wanke wankece , alama tayiwa Binta da hannu tatashi ta tafi

Binta na shiga ɗakin lailah ta tsugunna tana sakin kuka mai ciwo wayarta tazaro ajaka ta danna masa kira kamar ita yake jira ya ɗauka kuka mai cin rai tasaki tana cewa, " meyasa zakamin haka fayez mai yasa zaka yaudare ni, lailah datazo giftawa ce ta tsaya bakin ƙofar dayake binta ta juya baya tana tsugunne,

" kayimin shiru banason jin wani uzurinka kacuceni ka dasamin soyayyarka gashi yanzu nafaɗa tarko adaidai lokacin daya kamata nasan iyakar soyayyar da kakemin, kashe wayar tayi tajuyo ganin lailah a tsaye yasata jin sabuwar faduwar gaba lailah tashigo tana murmushin mugunta tace, " Allah yayi asirinki ya tonu zargin da nake miki ya tabbata, share hawayenta tayi cikin muryar neman agaji tace , " lailah dani dake duk matsayinmu ɗaya kuma nasan bazakiso kishiga matsalar danake cikiba dan Allah kirufan asiri karki bari malak tasan wannan zanchan, wani far lailah tayi da ido tace abu mai sauki ne indai kinaso zamu daidaita amma kafin nan inaso nasanar dake mugwayen abubuwan dazasu faru dake idan har malak tasani zata tarwatsa miki rayuwa saikinji kintsani kanki da rayuwar wannan duniyar kuma bazata taba bari ya aurekiba ,

Binta najin haka taki wani sabon tsoro ya darsu a ranta cikin tsananin son samun mafita tace , " lailah wlh banaso hakan tafaru zan rabu dashi rabuwa ta har abada nikaina nasan fayez ba ajina bane kuma ban chanchanci nace zan goga kirji da malak ba har muyi kishi, ɗaga kafaɗa lailah tayi alamar ba ruwanta sannan ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tace ," aiki kankani zakimin na rufa miki asiri idan kuma kinki natona miki asiri kai harda karin gishiri zanyi dan miya tayi zaki ,

" indai abinda zaki sani bai sabaywa Allah ba na amince zanyi,

" ok tom sonake kitaya ni yakin sato zuciyar malik akwai filan ɗin danake haɗa masa inaso kizama tsani idan kika yarda muka gudanar da shirinmu nima zan san yadda zanyi natayaki yakinki kuma ina mai tabbatar miki zaki samu yafez cikin sauki sannan babu abinda malak zata iya miki sai kallo, kallon ta binta tayi ta jinjina kai tace, " menene ribarki idan kika aikata haka wai ma kina tunanin akwai wani shirin dazaki kisa Malik yace yana sanki ?, yar dariya lailah tayi tace, " akwai yarinta a kanki binta bari kiji nidin nan cikakkiyar yar duniya ce dole ne kuma abinda nahada yayi aiki kedai kawai kiyi duk abinda nasaki karki sake kiwuce iyakarki,

Kai kawai binta ta jinjina har cikin zuciyar ta bata yarda da lailah ba kawai zata bita da eh saboda tasan cikekken shirinta akan malik sannan a hankali ta warware yadda lailah bazata ganeba bare ta tona mata asiri

*

Shikadai ne zaune a office chair dinshi wayer dake kan table ya kurawa ido aransa yana nanata kalmar da Binta tafaɗa masa na yacuceta , sosai yafaɗa duniyar tunani da neman mufita baiyi auneba yaji sallama akansa cikin yanayi na bazata yaɗago yaga wanda ke tsaye, take fara a tawanzu a fuskarsa yace , " waheed kaine yaushe kashigo kasar , bashi hannu yayi suka tafa sannan yazauna yana cewa ," daman cewa nayi bazata zan maka tunda nayi nayi kazo ziyara kaki , yar dariya fayez yayi yace , " kasar takuce ba dyadi kanata koɗa siriya tunda naje najiyota tafita raina ,

" fayez nafasan halinka kawai dai zinariyar matance tatashi hankalinka saida kadawo gudun karkaga wata yar balarabiyar ta kwace ka , murmushi kawai fayez yayi yace, " duk ba wannan ba ya kayi aurene?, girgiza kai waheed yayi yace," inanan dai ina dubawa har yanzu da saura kaifa ai nasan yanzu dai kunshiga daga ciki kaida mutuniyar ?, karamar iska fayez yafitar abakinshi yana sosa kai yace, " har yanzu dai muna nan, rike baki waheed yayi yakuma cewa, " fayez mai kuma kuke jira lokaci yanata ja yanzu fa kai ba irin kananan samarin nan bane yan 23 dazaka tsaya wasa,

Cikin bayyana damuwa a fuskar fayez yace, " waheed Allah ya kawoka alokacin daya dace, nan fayez yazauna ya zayyanewa abokin nasa duk abinda yake faruwa, cikin matuƙar jimami waheed yace , " gaskiya lamarinnan akwai rikitarwa fayez inama ace binta bata san malak ba kwata kwata dakomai zaizo da sauki ,

" babu yadda zanyi waheed inason binta sonda bantaɓa yiwa wata ƴa maceba itakuma malak tazamenin tamkar ƙaddara wadda Allah ne kaydai zai iya kawo iyakar abin, nan suka cigaba da tattaunawa kota wane bangare suka kurɗa ba mufita dolece tasasu yanke shawarar auren binta da malak alokaci ɗaya,

Koda dare yayi fayez yaje har gida yasamu binta bayan ta fito ta tsaya ta haɗe rai tamkar ba bintan daya sani daba, cikin nuna alama takosawa da ganinsa tace ,

" fayez ashe har kanada idon dazaka zo ka kalleni dashi wlh badan kar su Abba sugane akwai matsala ba dabazan fito ba, rausaya kai yayi cikin muryar rarrashi yace, " yakike so nayi da rayuwa ta bazan taɓa iya rabuwa dakeba, wani irin kallo ta ɗago kai tayi masa sannan tasaki murmushin takaici tace, " mekake nufi fayez dolefa saidai kazaɓi daya koni ko malak kaga daganan kowa saiya san iyakar sa ,



" taya kike tunanin zan iya daukar daya nabar ɗaya a cikinku ketamkar rayuwa ta kike indai inaso nasamu farinciki a rayuwar aurena kece wadda yadace na aura ita kuma malak tamkar sarƙar wutace da aka ratayamin a wuyana tana konani kuma tanamin radaɗi gacin naman jikina sukuma iyayena Ammee da dady tamkar ankwa ne da aka dauremin hannuna ta baya ta yadda babu yadda za ai na iya cire sarƙar wutannan har sai idan na auri malak,

Ya karashe maganar yana kallon ta tana hawaye yace, " tayaya zan iya cire wannan tarkon na kuɓucewa auren malak iyayena sune katangun karfen da suka hanani gujewa auren malak kuma ina kokarin yimusu biyayyah shiyasa har yanzu nakasa bijire musu, saurin ɗaga masa hannu binta tayi tace, " ya isa haka fayez banason jin komai taya kake tunanin malak zata yarda ta zauna da yar talakawa wadda tayi matukar rainawa yar aikinta a matsayin kishiya nafahimci kai kawai sanranka kake biyewa baka duba abinda zai faru idan ka aureni ka auri malak,

gyaran murya yayi cikin kwantar da harshe yace, " ninasan wacece malak babu abinda zata miki saboda tana tsorona fiye da yadda take tsoran iyayenta duk abinda nayi mata iyaka dashi bata taɓa bijirewa , kallonsa kawai binta tayi ta girgiza kai alamar aa ta ƙara da cewa, " na hakura dakai fayez hakuri nahar abada , tana gama faɗin haka tajuya tashige gida tabarshi a tsaye yana kallanota

Saida ta ɓace masa dagani ya naushi bango cikin wata iriyar muguwar fusata kai kawo kawai yake a ƙofar gidan chan yahau motarshi sai gida yana zuwa afusace yayi parking ba inda ake aje motocin ba

Yana huci yashigo falo Ammee batanan sai suhaima da siyama awani kidime yace ina Ammee siyama bakinta narawa tace tana dakinta, kai tsaye bedroom din nata yashiga yaganta zaune bakin gado tana danna waya ganin yadda yashigo mata a hargitsa yasata mikewa kanya ƙarasa tanufoshi tana cewa, " subhanallah fayez lfy wanene ya mutu ?, girgiza mata kai yayi kawai sai hawaye suka fara kwaranya a idonshi cikin yanayin neman agajinta ya dafa kafadunta yana cewa, " dan Allah kitaimaka min ki warware haɗin auren nan tsakanina da malak wlh bana san aurenta inada wadda zan aura, yakare maganar yana rungume Ammee sosai taji tausayin ɗan nata amma saita dake a fili ta chanza fuska tana ɓan ɓareshi daga jikinta tace, " fayez kayi haukane akan wata banza mace kazo kanamin kuka kamar karamin yaro,

Tsaki taja ta zauna kan doguwar kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana banka masa harara, jiki a matukar sanyaye ya ƙaraso kusa da ita ya zauna ya rungume kafafunta yace,

" Ammee inada wadda nakeso nifa namijine bai kamata a cusamin wadda banajinta arainaba dan Allah kiduba wannan lamarin, kallon sa tayi a wannan karon cikin tausasa murya tace, " kamar yadda kake cikin wannan halin na ɗimuwa da zafin soyayyar wata haka malak take kullum da irin wannan raɗaɗin take kwana take tashi a matsayin ta na mace kai zaka iya auren mata hudyu idan kanaso amma ita namiji ɗaya takeda yancin Aure idan an fasa aurenku taje ta auri wanda bataso yakake tunanin rayuwar yarinyar nan zata kasance malak abin tausayice fayez kayi tunani kai kanka kakasa jurewa bare ita mace macenma karamar yarinya, shiru kawai fayez yayi yana rungume da kafarta, hannu tasa tana shafa lallausar sumar kansa tace, " shekara da shekaru kuna soyayyah katsam sai kace kafasa aurenta bayan kasa tayimaka sonda bazai taɓa fitaba sai mutuwa kayi tunani mai kyau ɗana idan kafasa Auren malak dadynka tsinema zai dan kai zaka kawo karshen zumuncin sa da ɗan uwansa kuma nima kaina bazan yafe makaba dan ka cuceni kasa nazama makaryaciya a idon yarinyar da iyayenta,

Tsit fayez yayi sosai wannan magana ta taɓa masa zuciya yanzu tunaninsa ya karkasu, dady ne yashigo ɗakin yagan su a haka yar dariya yasaki yace, " aa fayez kuma yau kaunar ce tatashi akazo aka maƙale Ammee haka tamkar wani karamin yaro, itama dariya Ammee tayi cikin nuna kamar ba wata magana sukeba tace, " nasiha nake masa kasan yakusa zama ango nanda wata ɗaya,

Zeenariya ✍🏼

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

_________________________________

sacrifice

I dedicate this page to my relatives Zeyad Suraj Ahmed Abdullah Maryam I send you pure and unparalleled love

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (11)

Zama dady yayi yana cewa, " to ai fayez ba yaro bane a shekarun sa yanzu shi mai yiwa wasu faɗa ne , tashi fayez yayi yana shafa ido bayason dady ya fuskanci maganar a kan bayasan aurenne shiyasa bai tsaya ba yana gaisheshi ya fice,

Ajiyar zuciya Ammee tayi tace, " wai kuwa ya maganar siyarda hospital ɗin, zama dady yayi yana maida kallon sa gareta yace, " inason saimun tattauna da fayez kinsan shine yake kula da komai na hospital ɗin bazai taɓa jin daɗiba idan yaji zan siyar ban shawarce shiba, Ammee aranta bataji daɗiba tana yamutsa fuska tace, " haba dan Allah saikace shiya haifeka bakai ka haifeshi ba hospital ɗin nanfa idanma an siyar shizai cigaba dajan ragamarsa tunda naji malak tana cewa idan babanta yasiya ita zai bawa ita kuma ta dan ƙawa mijinta wato fayez idan anyi Auren, jinjina kai kawai dady yayi yace, " nifa barikiji wlh banason siyar da wannan hospital ɗin bawai dan kuɗin da ake samu acikinsa ba saidan kawai nasan fayez yana matuƙar san wannan hospital ɗin da kuma ka sancewar sa shugaba a kan kowane ɓangare idan na siyarwa khabeer yaran nan bazaiji daɗiba,

" haba dadyn su ya kakeso ka maida hannun agogo baya wannan fa hospital ɗin yana nan a matsayin sa na fayez tunda ubansa ne zai siya kuma sirikinsa kaga idan aka bada kuɗin hospital ɗin sai yabude duk kalar kasuwancin dayake so riba biyu kenan,

Koda binta tashiga gida kai tsaye ɗakinta tawuce tana zuwa tafaɗa kan gadonta tana sakin wani kuka mai cinrai ita kaɗai tasan irin azabar datakeji gaba ɗaya ruhin jikinta yaƙi bata hadinkai ta manta da fayez tayi watsi dashi duk lokacin da suka samu matsala wata sabuwar a zabtarciyar soyayyarsa ce take damunta, ummah ce tashigo ta tsaya akanta takusa kaiwa minti biyar tana kallonta chan tace, " Binta, firgigit binta ta ɗago kai azabure ganin uwar tata yasata ƙoƙarin share hawayenta, zama mahaifiyar tata tayi tace, " daman nasan ba lafiya ba binta duk kinchanza mai yake damunki mai akai miki mai yake faruwane?, kallon ta binta tayi chan tasaki wani sabon kukan tace, " ummah ina cikin matsala Ummah ina san fayez amma yafi karfina ba sa an aurena bane Ummah bazan taɓa samun fayez matsayin mijiba, nan binta ta kwashe labarin duk abinda yake faruwa ta faɗawa ummah, sosai ummah ta jinjina wannan al'amari matsayin ta namai hankali tace, " binta shawarar dazan baki a matsayina na mahaifiyarki shine ki hakura da yaranan babu yadda za ai abarshi ya aureki kuma uwar ɗakin nan taki tafiki gaskiya tunda itace wadda yakeso tun asali kicire zuciyarki daga kansa kiyi hakuri kicigaba da zuwa aikinki har Allah yakawo miki wani wanda yake daidai dake , binta cikin raunin zuciya tace, " ummah aikinma sonake na daina zuwa inaso na yenke duk wata alaƙa ta dasu zuciya ta bazata taɓa iya jure ganin fayez da malak ba, murmushi Ummah tayi ta ce, " binta bazaki taɓa barin wannan aikinba saboda a yanzu haka dashi muka dogara nida babanki , cikin rashin fahimta binta ta kalli umman tata tace, " dashi kuka gogara kuma?, lumshe ido ummah tayi taja numfashi tace, " banso na sanar mikiba amma yanzu yazama dole nasanar miki kwanakin baya farko farkon fara aikinki mamanki ta dage sai abbanku ya hanaki yin aiki a wannan gidan shikuma abbanki yaki yadda dan yasan idan ya hana cewa zanyi mugunta ce dan anga zamu dinga samu shinefa tace masa indai bazai hanakiba zata jenye duk wani taimako datake mana kodededa na gass ne tadaina bayarwa , cikin matuƙar nuna rashin jin daɗi binta tace, " ummah daman kuna haka a tsakaninki da mama ?,

"Eh muna haka wannan shine karo na biyu idan ta faɗi abu bamubi ba nida babanki takan jenye mana komai babanki yayita shan wahala kuma Duk da haka idan yanemo koda garin kwakine sai anraba da ita, " bari na takaice miki zance binta albashin farko dakika dauka dubu dari biyar kikabada a ajiye babanki ya amshesu yayi biyan bashi sauran kuma yasai mana abinci ,

" ba matsala insha Allahu zan cigaba da neman kuɗina ,

" yauwa Yar albarka nagode amma dan Allah karki sake kirike matar babanki a zuciya wannan maganar ki ɗauka tamkar banyi miki itaba koba komai tayi kokari kuma tana kanyi itace ta aurawa babanki ni kuma itace tayi ɗawainiya da cikinki ke hatta haihuwarki a babban asibitin yayanta dake Abuja takaini na haihu a chan saboda ance haihuwar zatazo da matsala kinga kuwa dole mucigaba da mu tuntata, riƙe hannun mahaifiyar tata binta tayi tace, " ummah baki koyan wannan tarbiyyar ba na ɗauki mama kamar ke dakika haifeni kuma ina sonta har yau har gobe acikin arzikin ta muke rayuwa kuma zancigaba da neman kudi dan dawainiyar gidannan,

Bayan sati ɗaya

Yana buɗe kofar office din yaganta a zaune ƙarasowa yayi ya zauna a kujera yace , " yau kuma kece a hospital ɗin nan , murmushi tayi tace, " kawai naji ina sha awar zuwa nazo naganka ne , jinjina kai yayi yace , " ykk ya aiki , " ina lfy,

" Fayez nikuwa na tambayeka mana , kallonta kawai yayi ta gyara zama tace , " har yanzu baka nunamin gidan dazaka ajiyeni ba kuma kullum aurenmu matsowa yake , batare da ya kalletaba yana haɗa takaddu yace, " banshirya inda zan zaunaba za a kuma karamin koda wata biyune na kimtsa cikin nutsuwa, wani irin kallo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login