Showing 63001 words to 66000 words out of 67181 words
Chapter 22 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx
ya fito daga gidan yari ko cikakkiyar lafiya bashi da ita, ɗaga mata hannu mama tayi tace, " bansa dakeba keda kike yawan karuwanci wajen ƴaƴan masu kuɗi ga malik ga fayez koda wasuma Allah ne masani to kije susai muku gidan da zaku zauna wai kodai ma basa biyanki kuɗi kyau ta kike raba musu gindin sunaci saboda kyawawane su, tuntsirewa da dariya sukai ita da aminiyar ta Hajiya zezah
Ran ummah ne ya baci duk da bata magana saida tace, " gwara ni na haifi yar dazataje ta saida gindin tabiya buƙatun ta ke faɗa mana ina taki yar wacce zata iya tsaya miki idan matsala ta sameki koda dededa karuwancin ne tayi, mama cikin mamaki ta bude baki tana kiran , " kai ka kai butulu ina kika samu bakin magana kin manta daga kauyen dana samokine kina fama da cin hatsi babu dare babu rana wato kin kile kin manta wacece ke ko , ummah najin haka ta buɗe baki zata kuma magana binta ta dagatar da ita sannan ta share hawayenta tace , " mama niba karuwa bace fayez wanda yake neman aurena ne shikuma malik tamkar dan uwa na ɗaukeshi dan Allah idan zakici zarafina ki tozartani kimin ni kadai amma banda su ,
Dogon tsaki mama taja tana shirin cewa wani abu Abba ya shigo ya sassauta murya yace, " dan Allah na rokeki kibani lokaci ƙalilan na samu aiki na kama mana haya mubar miki gidanki cikin salama basai kin tozarta mu ba, wani irin kallon galala tamai taɗan saki dogon tsaki tace, " sainayi tunani, ummah najin haka tace, " amma Abban binta kabani mamaki nazaci zakace mu kwaso kayanmu mubar mata tsiyarta a yau shine kake rokonta afuwa , juyowa mama tayi tace, " to sheɗaniya wayasa dake tauraruwa mai wutsiya bakar kadara amiki rana kiyi dare kai kuma jani talau saika biye mata ku tattara ku koma ƙauye da zama abaku bukka dan nasan ko arzikin ɗaki bazaku samuba ,
Hakuri Abba yayita bata da kyar taja kawarta suka shiga ɗaki suna shigewa sukai dariya ƙasa ƙasa suka tafa Hajiya zezah tace, " ai dama nagaya miki binsu kina kuka kina basu hakuri bashi zai sa ya dawodake ba tunda kuwa kinada makami kawai ki murza kambunki kina zaune zaizo yace ya dawo dake, murmushi mama tayi tace, " zezah bazan taɓa mantawa dakeba ke kike buɗan ƙwaƙwalwa aduk lokacin data toshe Allah yayi miki albarka shirin farko ya afku saura na biyu,
Abba ne ya taya ummah maida kaya ba yadda binta bataiba suka hanata tayasu saboda jikinta bayan an gama shigar da kayan suka shiga ɗaki suka zauna binta ta kalli Abbanta adan tsoro ce tace, " Abba ko nayiwa fayez maganar bamuda gurin zama yadan taimaka yasai mana gida tunda yanada kuɗin, murmushi Abba yayi yace , " binta bazan taɓa yarda da wannan ba kuma ban baki izinin kifaɗa masa ba ni namiji ne kuma alhamdulillah da sauran karfina zansan yadda zanyi na nema amma banyi lalacewar da sirikina zai saimin gurin zamaba wannan shizai hana ki samun zaman lafiya daga danginsa zasu rainaki kuma su raina iyayen ki gwara mu riƙe mutumcin kanmu,
" gaskiya ne maganar ka, cewar ummah kenan,
Shiru binta tayi tasan dama ba lallai Abba ya yarda da hakanba,
*
A kwanakin nan papy ya matsawa Malik da maganar aure hakan yasashi tilastawa kanwa zuwa yaga suhaima su tattauna ya fahimceta dan ba lallai yadda yake tunanin ta takasance hakaba duba da yadda hafiza ta fita daman ita da fayez rikon addini son gaskiya dabin ta yarda da rukon amana,
Yana zaune a haɗaɗɗan falonsu da aka wadatashi da turarukan kamshi masu daɗi gabansa an jere masa kayan ciye ciye kala kala wanda tunda yayi musu kallo ɗaya bai kuma kallon suba ya tisa wayar sa da danne danne ƙarƙashin zuciyar sa cike da fatan Allah yasa suhaima ta zama irin yayarta hafiza,
Sakkowar ta yaji daga saman bene har yafara jin kamshin turarenta da alama itace dan yaji kamshin daf dashi amma bai dago kaiba saida yaji sallamarta da zazzaƙar murya, yana ɗagowa sukai ido hutu ya fara kallon fuskarta ta sha kwalliya babu laifi itama kyakkyawa ce duk da yasanta sai yaga takuma girma bin jikinta yayi da kallo a tsanake abinta ya ɓata masa rai kallon kanta ba ɗan kwali tasaki gashi ya zubo mata gashi wata doguwar riga datasa bata kai mata ƙasa ba sannan rigar irin mai hannu ɗaya ce kusan rabin kirjinta a waje hannunta da zakwa zakwan farata sunsha finti da duwatsu takalminta mai shegen tsini a taƙaice dai irin shigarsu ɗaya da malak kamar ƴaƴan arna,
Wata iriyar ajiyar zuciya ya sauke ta takaici ya kauda kai haɗi da amsa sallamar zama tayi kusa dashi ta yadda suke iya shaƙar ƙamshin junansu ta ɗan karkato ta harɗe ƙafarta ɗaya kan ɗaya cikin siga maijan hankali
✍🏻 zeenariya
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf zeenariya
__________________________________
GARGAƊI
Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 39 )
Gaisheshi tayi dakyar ya amsa dan sosai ranshi yayi matukar bachi tunani yake ga gida ga gida yaushe suhaima tayi wannan lalacewar bai sani ba kuma fayez yana kallonta , ƙofa yayi lokacin da wata zuciyar tace masa yoga yar uwarka malak nan itama ai akan idanku ta lalace , suhaima lura tayi yafaɗa duniyar tunani sai tasa hannu taɗan dafa kafaɗar sa da sauri ya juyo yana mata wani irin kallo cikin takaici yace, " ke ɗauke hannun ki ni sa ankine zaki dafani?,
Marai raice fuska tayi tace, " haba mijina naga kamar ranka a ɓace yake mai yake damunka, wani irin kallon raini yayi mata yace, " na tsani abincin daya gamashan iska shiyasa idan na ganshi raina yake baci take, cikin mamaki ta kalli kayan abinciccikan dake kusa dashi tace, " a rufe duk suke ai,
" ba abinci nake nufi ba ke nake nufi , yafaɗa yana miƙewa tsaye itama ta mike dan danan idonta suka kawo ruwa tace, " haba ya Malik wlh da gaske ni sanka nake dan Allah ka yarda ka aureni , ɗaga mata hannu yayi yace, " ni bance bazan aureki ba amma indai kinada bukatar samun soyayyata saikin koyi sitirta jikinki kinsan daman ana sha awar auren macene saboda abin da suke suturce to ke kinzomin kusan tsirara ina ganinki naji baki dace daniba kodama na aureki sai dai kizama mai wankemin kaya, yana gama faɗin haka ya fice, wani irin kuka suhaima ta fashe dashi dai dai lokacin da Ammee ta fito tana tafa hannaye suhaima na shirin faɗa mata abinda yafaru tace, " duk najishi gaskiya akwai aiki ni ina tunanin yana ganinki zai gigice yace adaura aurenku nanda sati biyu shikenan kuma sai ya kyamace ki , siyama ce tafito tana dariya hadda rike ciki tace , " ai dama na gaya miki kisa kayan mutumci shine zakiyi saurin siye zuciyarsa amma kikaƙi ji, Ammee ce takai mata duka da sauri ta gudu sannan taja hannun suhaima dake kuka suka shiga daki ,
Malik na fitowa suka haɗu da fayez yabashi hannu suka gaisa yace, " ashedai zakazo da gaske yau dai sanadin mace ya kawoka gidanmu, murmushi kawai malik yayi yace, " bazan ɓoye makaba fayez akwai gyara a lamarin yarinyar nan, " malik kenan ai shi yasa tun farko nace bata dace dakai ba kai kuma kace kana kunyar mahaifanmu tunda na guji malak to wlh kaima kayi gaggawar zamewa Auren suhaima dan halayyarsu ɗaya gashi basasan addini har gwara siyama da ta isa aure ita yakamata ka nema, dafe kai malik yayi cike da takaici yasan gaskiya fayez ya gaya masa dan tsakaninsu babu boye boye,
" ina tunanin zan iya chanzata tunda bawata babba bace kuma na fahimci tana sona zata iya duk abinda nasata, kwafa fayez yayi yace, " ni dai bazan daina baka shawara ba tunkan magana tayi nisa kazame gwara kaje kasamu binta tasamoma yarinyar kirki mai tarbiyya ka aura shizaifi kwanciyar hankali, " abokina idan nayi hakan kamar na kunna wutar dabazata kasuba ita bintan ma saidai muyi mata fatan samun sa ada a family namu bawai mu karo wataba abin yazama biyu, " na sani gaskiya ne to Allah yazaba mana abinda yafi alkhairi yasa ta shiryu tunkan aurenku, ameen malik ya amsa sukai sallama,
*
Kamar yadda Abba yace zai nemi aiki haka yayita yawo bai samuba gashi na abinci ma nema yake ya gagaresu binta ta faɗa damuwa dan batasan ta wace hanya zata nemi kuɗi ta taimaki iyayenta ba kwatsam sai maganar zane ta fado mata da sauri ta ɗakko sabuwar wayar da fayez ya siya mata da sabon layi ta duba littafin da take ajiye muhimman lambobi ta dubo lambar Aisha, kira ɗaya biyu ta ɗaga bayan sun gaisa take sanar mata itace binta mai zane sosai Aisha tayi mura ta shaida mata ina ta shiga shiru bata ƙara magana akan zaneba , nan binta take faɗa mata ," wlh nadan shiga busy ne ya maganar zane kuna siya nakawo muku , cewa tayi a yanzu sun siyi zanika da yawa a hannin wasu sai dai tabari nanda wata biyu zasu kuma siya saisu kirata ,
Kashe wayar tayi tanata tunanin hanyar dazatabi tasamu kuɗi ummah ta shigo ta zaune tayi tagumi binta ta kalleta tace ,"ummah lafiya ?,
" yanzu ladi tazo take faɗamin wai matarnan tabi ta yaɗa bin maza kike anata zanchan a unguwa kowa ya yarda da hakan saboda masu kuɗin da suke sintiri a gidannan , dafe kai binta tayi tace, " to Ummah menene na damuwa abinda munkusa tashi daga unguwar ma gaba ɗaya ,
" binta maganar tashi babu ita abbanki ya maida matarsa jiya ma a ɗakinta ya kwana kinga har yanzu bai ko leko tsakar gidaba, dafe kirji binta tayi cike da mamaki tace, " anya ba wani abin taiwa Abba ba kuwa?,
" Allah masani binta maibi asirine mai bi kuma halin matsin dayake cikine yasashi koma mata, shiru binta tayi kawai dan batada tacewa,
Yau da yamma fayez yazo zance bayan sun gaisa yace, " wai kuwa kinashan maganinki,
" eh mai kagani?,
" ganinki nayi kamar baki warware ba ba irin fara a da hira kamar da,
Ɗan shiru tayi tana wasa da hannun ta chan ta dago tace , " fayez zaka iya zaman aure dani duk da kasan yanzu niba budurwa bace ?, alamar damuwa ce ta bayyana a fuskar sa yace, " banji daɗin wannan maganar ba binta ba fata nake mikiba koda abinda yafi wannan ne yafaru dake nizan aureki na zauna dake ki rayu cikin samun kyakkawar soyayya da kulawa saboda ni bawai jikinki ne yasani sonki ba kawai hakurinki da juriya kauda kai addini tsoran Allah gaskiya rukon amana tausayi sanyin taimako biyayyar iyaye ke komai ma kin haɗa,
Murmushin jin daɗi tayi tace, " tayaya kagane ina da hakuri?,
" tun ganinki danayi na farko a lokacin da muka kusa takeki da mota kuma malak ta fito ta cimiki mutumci baki tanka mata ba tundaga lokacin naji inama na tsaya na tambayeki gidanku danni kalar matar da nakeso kenan,
Dariya binta tayi tace, " fayez azahirin gaskiya banida hakuri sai dai faɗa na bawai inayinshi akan komai bane nafi nuna ɓacin raina idan akai kokarin tabamin mutumcina ko kuma iyayena,
" okay su Abba kawai zaki iyayin faɗa akansu banda ni ashema bakya sona, dariya tayi tace, " ai kai kwa yakamata ma nafi yin faɗa akanka sai dai ganin yadda malak tafini hakikicewa ne yasa na shafawa kaina ruwa bazan zaƙeba har sai munyi aure za a gane banida sauki akan mijina, dariya fayez yayi har ransa yaji daɗin abinda tace
Chan da hirarsu taɗau dadi tace masa , " fayez dan Allah na roƙeƙa wata alfarma ɗaya, maida hankalinsa yayi gareta yace, " ina jinki my wife,
" dan Allah kada kabari akai jamel kotu tunda ba laifin sa bane idan aka hukuntashi shi kaɗai an zalinceshi kayi tunanin da kawuna bai cemasa yace an ɗaura aurenmu ba aida babu yadda za ai Jamel yazo yayi karyar hakan kuma da ace malak bata bashi gidan zama da motaba aida bazai taɓa yin tunanin yazo ya ɗauke niba ,
Fayez najin haka ransa ya bacci yayi saurin dakatar da ita dacewa, " naji amma ni kozan iya yafewa kowa shidai bazan yafe masaba saboda fyaden dayayi miki ya wahalar min ke sannan yasa rayuwarki a haɗari wlh yanzun ma sa arsa ɗaya raunin dake jikinsa da tuni yana gidan maza,
" fayez shimafa fyaɗen sashi akai yayimin ,
" Toshi dabbane da komai aka sashi zai aikata tsakaninsa da malak wanene babba dazaki dingamin maganar na kyaleshi , sosai jikin binta yayi sanyi kawai sai tasa kuka, hakuri fayez yadinga bata yana rarrashin ta chan tayi shiru tace, " komai muƙaddiri ne daga Allah nayi imanin kaddaratace haka Allah ya rubuta za amin fyaɗe amma duk da haka bazan bari azalinci kowaba yazama dole jamel ya fita kodan raunin dayayiwa kansa kuma iyayensa talakawa ne dashi suka dogara idan aka kulleshi an zalincesu,
" binta dan Allah mubar maganar jamel raina bachi yake, shiru tayi masa ta kauda kai chan ya busar da iska daga bakinsa yace, " naji zan fiddashi shikkenan magana ta wuce ko?, murmushin jin daɗi tayi ta dinga masa godiya sannan yace, " amma fa dole sainasa yan sanda sun kafa masa sharadin babu shi babu ke,
" na amince wlh na yarda, tafaɗi cikin jin daɗi maganar soyayya suka faɗa data aurensu daya tashi tafiya yabata kuɗi masu yawa dubu ɗari biyar yace tasa kati, sosai tayi murna tasan bana kati bane kawai dai yabata ne dan yasan ziro take,
*
Da daddare dady suna zaune shida Ammee suna hira fayez yazo ya zauna ya gaishesu ganin farin ciki washa washa a fuskar sa yasa dady cewa, " alhamdulillah wal wala tadawo tunda yarinyar chan tayi free kaketa wani washewa kwanan nan duk ka chanza ka koma kamar fayez dinka nada , murmushin jin dadi fayez yayi yace, " ai dady babu abinda zamu cewa Allah sai godiya yanzu shirye shiryen gidan dana nuna maka na siya nake inaso na zuba komai basai tazo da koda chokali ba,
" Masha Allah gaskiya ka kyauta Allah yayi maka albarka, amen fayez ya amsa yana kallon Ammee data ƙufula sai hura hanci take suna haɗa ido tace masa, " kai yanzu ko kunyi bakaji fayez wai kai wane irin shashasha ne yarinyar da wani yagama kacha kacha da ita zaka aure yarinyar datasha furta maka batasonka ita kakewa rawar ƙafa yar mutsiyatan kakecewa zaka cika mata gida da kaya ,
✍🏻 mai alƙalamin zeenare
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf zeenariya
WhatsApp number
+218912472599
__________________________________
GARGAƊI
Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 40 )
" ke ke ya isa haka wannan wane irin rainin hankali ne naga da yardarki ya nemi auranta, dady yayi magana chikin bachin rai, ƙwafa Ammee tayi tace, " I'm tired bazan iya jure ganinsa haka ba haba dan Allah haka ake rayuwa adakeni kuma a hanani kuka fayez gudan jininane duk abinda na kyamata to ba alkhairi bane a gareshi , tafaɗi tana kauda kai dady yace , " ke harkin isa kisan goben mutum I warn you with a loud voice ki fita daga harkar aurensa kibarshi yasarara , tashi kawai Ammee tayi tabar wajen fayez ya kalli dady yace, " karka damu dady ƙawarta take tayawa kishi, dariya dady yayi yabawa ɗan nasa hannu suka gaisa,
A kowace rana malak tunanin abinda zatai ta bakantawa kowa take tarasa hanya tana zaune kamar yarda tasaba kullum aɗaki tunda abinnan ya faru sai dai akai mata abinci bata fita ko parlour kuma ta dainayiwa kowa magana, hawayene yaketa bin fuskar ta chan ta zabura ta tashi kamar wadda aka tsikara ta shiga neman File chan ta samoshi ta duba ta tabbar shine sai ta saki wani ƙayataccen murmushi ta dau wayarta ta danna kira bayan an ɗauka tace , " inaso a nemomin dillalai gobe suzo office dina 10:00 zanzo, tana gama faɗin haka ta kashe wayar tana sakin wani shakiyin murmushi ,
Yayi wanka yana ƙoƙarin saka kaya kira ya shigo masa ya duba yaga mai kiran ɗauke da fara a ya ɗaga bayan sun gaisa yake tambayar ta ," ya jikin naki ina fatan ba wata matsala ?,
" alhamdulillah yaya jiki yayi sauki yau aka kwanchan dinkin,
" sannu Allah yaƙara sauki kiyi hakuri bankuma zuwa na dubaki ba tunda natafi ,
" bakomai yaya ai ni ya kamata nazo nayi muku godiya har gida kaida Hajiya mom,
" Amma danaji dadi dan har cewa tayi zatazo gida ta dubaki to sai kuma wani uzirin ya hana,
" ayya wlh bama sai tazoba ni zanzo dan Allah ka gaishemin ita,
" okay zataji nima ki gaishemin da abba da mama insha Allah zanzo na kuma dubaki, godiya tamai sukai sallama , cikin fara a yasa riga yana shirin sa dogon wando yaji ana kwankwasa masa ƙofa ya ajiye dogon wandon yazo ya buɗe a zatanshi mom ce ko papy kawai saiyaga suhaima cikin mamaki yace , " ke lafiya ?, shigo wa tayi tazo ta zauna akan sofa tana gaishe shi amsawa yayi ciki ciki ya tsaya yana kallon ta yau kam da ɗan mutumcin dan abaya tasa da mayafi sai dai duk rabin gashinta a waje, " tambayar ki nake lafiya?, yafaɗa cikin haɗe rai kamar bashiba
" lafiya kalau mom nazo gaisarwa,
" to nan ne ɗakin