Showing 45001 words to 48000 words out of 67181 words

Chapter 16 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx

dai abin yaci tura matar ta shiga ta fita akan mijinta kuma sun tara ƙarai rayin hujjoji masu tarin yawa akan babana dan Allah kimin rai idan kikai silar kuɓutar mahaifina kin gaman komai,

" hmmmm okay ba damuwa kije kiyi aikinki zuwa yamma ki jirani zan faɗa miki matsayar dana yanke kinsan ni bana shiga zantuttuka irin wannan ajina ya wuce ace kamar ni ina shiga, kai binta ta gyada tayi godiya ta tashi ta haura sama malak na ganin kulewar ta tasaki dariya matsaƙai ciya ta tafa hannu ta ɗaga waya ta danna kira,

Ammee na ɗagawa tace, " albishirin ki?, cikin zumuɗi malak ta ƙara da faɗin, " yau yar magen data tsone mana ido ta shigo hannu,

Shewa Ammee ta saki tace, " bani insha ya akai,

Sosai malak ta tsaya tayiwa Ammee bayani dallah dalla Ammee najin haka tace, " kinga shikkenan mun samu hanyar rabata da fayez yazama dole kafin ki taimaka mata kuyi dawajewar ba ita ba fayez ,

Murmushin malak tayi tace, " Ammee wannan tan tiriyar yarinya dazarar taga ubanta ya kuɓuta zata kuma liƙewa fayez sai dai ni inada dabara kwaya ɗaya dazata rabata da fayez har abada,

Murmushin jin dadi Ammee tayi tace," ina jinki ƴata?,

Ta buɗe baki zatai magana kenan taga sakkowar malik ya ƙaraso zai wuceta tayi saurin cewa , " inada magana dakai , kallonta yayi a wani shekeke yace, " ina jinki, wayar hannunta ta kashe ta maida hankali kansa tanai masa nuni da kujera ya zauna itama ta zauna ta harɗe kafa ɗaya kan ɗaya tamkar itace sama dashi tace,

" Bai dace muna yan uwa mu dinga nunama junanmu ƙiyayya a idon duniya ba ?, ɗago kai yayi ya kalleta batare dayace komai ba ta cigaba da cewa, " ina nufin a gidan jarida da akai hira dai game da kasuwancin fashion and designer akai maka tambaya akai na kayi shiru bakace komai ba hakan ya kawo cece kuce a midiya wasu suna alaƙanta hakan da rashin jituwar mu , mikewar da malik yayi tsayene yana gyara rigarsa yasa malak tasan tafiya zaiyi

A kausashe yace, " har yanzu ke yarinya ce malak shiyasa mugwayen halayanki suka girmama dan sun haɗu da yarinya kinata wani ciki kina batsewa a matsayinki na mace mahaifinmu ya ɗoraki akomai na dukiyarsa , yayi kwafa ya nunata da yatsa yace, " duk tsiya duk abinda zaki ɗiba karshe dai dole idan za a raba gado rabonki bazai kai nawaba idan ma tunanin ki wayewa ce hakan to ba wayewa bane faɗuwace mace agidan miji aka santa mata irinsu binta sune mata ba matan da suke juya kuɗi suna chakuɗuwa da mazaba kisake tunani ki nemi miji kiyi aure shine kika amsa sunanmi mace, yana kaiwa nan a maganar sa ya fice ,

Wannan maganar ba karamin baƙanta ran malak tayiba saida taji inama batai masa magana ba , iska ta furzar a bakinta lokacin data tuna matsalar ta takusa ƙarewa zatai aure kuma shima da yake gadarar gadonsa zaifi nata zatasan yadda za ai ta zaɓar masa matar da kanta ta yadda duk tsiya zata cigaba da juyasu shida dukiyar tasa da matar,

Fita tayi bakin harabar gidan ta karɓi mukulli a hannun jamel dan da kanta takesan tukin ta hau kan titi tanata tunani sai dai maganar malik ce tafi damunta dan duk abinda yafada gaskiya ne a fili ta furta, " tayaya zan bari yaje ya aure bare ta haifa masa ƴaƴa sucinye dukiyar dani na jujjiya ta kuma nakeda muradin ganin na mallaketa duk kasarnan su shaida ni ce jigon kasuwan cin gidanmu, shiru tayi ta faɗa duniyar tunanin kawai chan sai ta juya kan motarta izuwa Company su papy,

Tana isa kai tsaye ta wuce office dinsa yana ganinta ya washe baki yanuna mata mazauni ta zauna chan bayan sun ɗan taɓa hira tafaɗa masa muhimmiyar magana ce ke tafe da ita sai da ya bata hankalin sa yana sauraron ta tace,

" papy kaga kaida ɗan uwanka kunason junanku sosai kuma naga tunda maganar aurena da fayez ta rushe kakejin haushinsa kayi hakuri papy ɗan uwanka yana sonka inaso muƙara kullah wani kyakkyawan zumuncin ta hanyar haɗa Malik da suhaima Aure,

Cikin mamaki papy yace, " ikon Allah kaga yarinya mai basira da kyan kai gaskiya kin kawo shawara babbah shiyasa nake sanki Allah yayi miki albarka wannan abu nasan ayman zaiji farin ciki sosai dan babban burinsa bai wuce yaga ƴaƴanmu sunyi aura tayyaba ayi tuwona mai na,

Murmushin samun nasara tayi tana daɗa hasaso yadda shirinta yaketa tafiya dai dai yadda ta tsara ( Ni kuwa yar mutan Libya da sauran makaranta mukace komai nisan jifa kasa zai dawo muna nan muna zuba idon ganin yadda HUDUD dinki zai zo )

✍🏻 zeenariya

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

WhatsApp number

+218912472599

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 29 )

Cikin farin ciki ta kira Ammee a waya tace zatazo gidanta yanzu, a mintina ƙalilan ta isa bayan sun zauna tace, " Ammee ina suhaima, ?, " tana ciki, Ammee ta bata amsa, malak tayi yake tace, " a kirawomin ita wannan zuwan natane , washe baki Ammee tayi dan tasan koma menene alkhairin yarta zata samu , cikin hanzara ta buɗe maƙogaro tasoma kwararawa siyama kira bayan ta fito tace da ita tayi sauri ta kira mata suhaima , cikin sakanni kaɗan saiga suhaima ta ƙaraso tana ganin malak ta saki fara ar data ƙarawa fuskarta kyau ta zauna tana cewa , " aa yau babbar yayace agidan namu ,

" ykk, malak ta faɗa a takaice suhaima ta bata amsa malak ta kalli Ammee tace, " Ammee yau abune mai muhimmanci ya kawoni gidannan magana ce akan Auren ɗan uwana malik idan ba damu ina mai shawartar suhaima ta amince a haɗa aurensu nizan tsaya mata zata samu duk wani alkhairi amma abisa sharaɗi ɗaya, tunkan Malak ta gama magana bakin Ammee da suhaima yaƙi rufuwa dan murna har malak takai inda ta tsaya Ammee tace, " Masha Allah alhamdulillah ashedai bazan mutuba sai naga anyi wannan auren zumuncin danake muradi wato gaskiya malak babu abinda zance miki sai godiya kin nuna min soyayya mara iyaka nida ƴaƴana nagode nagode kuma ki faɗan sharaɗin a shirya muke mubi,

Murmushin ta na ƙasaita data sabayi aduk lokacin da aka yabeta tayi ta maida ganinta ga suhaima tana nunata tace, " kenake jira naji ta bakinki tukunna kin yarda zaki auri malik?,

" haba anty wazai ki handsome kamar Malik ai ni nadaɗe da fara sonshi a cikin zuciya ta kawai dan naga kamar yafi karfin ajina yasa ban tsauwala ba,

lumshe ido malak tayi ta ƙara da cewa, " sharaɗin auren Malik shine kisa aranki tamkar zamana kike a gidansa duk umarnin dana baki shi zaki bi idan kikai haka zaki samu zaman lafiya idan kuma kika bijire kinfi kowa sanin wacece malak, Ammee ce tayi charab da cewa, " ai malak basai kin ɓata bakinki wajen yimata gargaɗi ba suhaima kanwarki ce koda bata auri malik ba zatai miki biyayya akan duk wani abu da kika sata dannima kinaimin biyayya kinajin magana ta shiyasa girma da darajarki da kimarki tafi ƙarfin tunani a wajena da ƴaƴana,

Mikewa malak tayi tace, " nasani Ammee na bari zan tafi naga yamma tafarayi sauri nake ke kuma suhaima ki kwan da shirin zanchan aurenku zai taso cikin satinnan sauran yadda zaki shawo kansa kuma yarage naki, malak na gama faɗin haka ta fice, wani uban tsallan murna suhaima ta daka ta rungume Ammee sosai sukewa Allah godiya

*

Binta ce zaune a ɗakin lailah ta gama aikin tun awa biyu da suka wuce tayi ta gumi ita kaɗai sai tunani take kala kala lailah ta shigo tace mata , " kije oganniya na kiranki, tashi kawai tayi ta fita a dakin malak ta sameta a zaune ta ƙarasa sim sim tai mata sannu da zuwa sannan ta rakuɓe gefan kujera ta zauna a kan lallausan kafet ɗin ɗakin, kallon ta malak tayi tace, " nayi tunani kuma na yanke shawarar zan shiga maganar mahaifinki a kwaceshi dan har nayi magana da police ɗin da suka turasu kotu kuma sun bani address ɗin mrs Tahir zanje na sameta gobe amma inada sharaɗi da kuma ƴar yar jejeniya kafin na shiga maganar ,

gaban bintane yayi mummunar faɗuwa cikin fargaba tace, " ina jinki insha'Allah zanyi biyayya, murmushi tayi mata ta ƙara da cewa , " sharaɗi na farko shine zaki rabu da fayez rabuwa ta har abada babuke babu shi kuma amayar masa da dukuyar aurensa kuɗin aurenma karki damu nizan baki yanzu dan nasan kun kashe na wajenku sai a gaggauta gobe asa tsofaffin da suka amsa su mayar masa ,

Hawaye ne suka gan garo a fuskar binta hawayen tsananin tsabar raɗaɗin rabuwa dashine shikkenan zata rasa namijin da takewa so mara iyaka, cikin shashsheƙa tace, " na amince , kai Malak ta girgiza alamar tausayi chan kuma ta washe baki cike da fara a dajin daɗi tace , " ayya karki damu nasan shi mutum ne mai shiga rai am sorry ba mijin aurenki bane dole ki rabu dashi " yar jejeniyar kuma itace zaki maida aurenki da jamel dole ku kuma karɓar kuɗin aurensa asa nanda sati biyu a ɗaura wannan umarnina ne bawai shawara ba dole ki auri jamel idan kinaso babanki ya cigaba da shaƙar iskar ƴanci, saurin ɗago kai binta tayi ta kalli malak cikin wani irin mawuyacin yanayi na tsantsar tashin hankali ta durƙusa akan gwaiwoyin ta tace, " dan suturar da Allah yayi miki kibarni na rayu cikin salama banason Jamel ni banason aurenma gaba ɗaya kuma namiki alkhawarin rabuwa da fayez har abada zan fita daga rayuwar sa kamar yadda kika gindaya min ,

wani banzan kallo tayiwa binta dan danan ta sauya fuska kamar ba itaba cikin ɓacin rai tace , " binta ke munafuka ce bazaki iya rabuwa da fayez ba keyama zama dole idan kinason rayuwar mahaifinki ki auri jamel nanda kwana uku za a shiga koti ƙarfe goma inason kafin a shiga kotun ƙarfe tara da rabi a ɗaura miki aure da jamel,

Sunkuyar dakai binta tayi tana dafe da gefan zuciyar ta dake mata wata irin fuzga Cikin sauri tace, " na amince, ajiyar zuciya malak ta sauke ta miƙe tsaye tana kai koma chan taɗau wayarta ta danna kira bayan an daga tace, " maza kazo parlour ka jirani , tana ajiye wayar ta waiga ta kalli binta tace , " tashi muje , ba musu binta ta tashi ta bita zuwa babban falon ƙasa ,

Tare suka isa falon dashi malak ta zauna binta ma ta zauna a ƙasa shima ya ƙaraso ya zauna a ƙasa daga chan gefe ya gaisheta ta amsa sannan ta fara magana da cewa, " na kiraka ne dalilin binta inaso ka faɗamin har yanzu kana sonta kuma zaka aureta ?, cikin mamaki ya saki fara a yace, " ranki shi daɗe har abada bazan daina san binta ba kuma ko yanzu tace zata aureni a shirye nake na aureta, gyaɗa kai malak tayi ta kalli binta dake rakuɓe a gefe kanta a sunkuye tace mata, " to kinji abinda yace ke yanzu kina sonsa kuma kin shirya aurenshi, kai kawai binta ta gyaɗa mata alamar eh sannan malak tace, " to alhamdulillah tunda kunason junanku ku rubutan duk abinda kuke buƙata kai jamel koda bakada gidan zama nizan baka ke kuma duk abinda kikeso na lefe ki rubuta zan kawo miki idan kuma kuɗin kikeso kiyi magana in sa miki inaso aurennan a ɗaurashi nanda kwana uku ranar Litinin kenan karfe tara da rabi na safe daidai naji labarin kun zama mata da miki , jamel najin haka ya duka take yayi sujudul shukhuri ya ɗago yanata yiwa Allah godiya saida ya gama ya fara sanbaɗawa malak godiya yama rasa mai zaice dan daɗi yau gashi binta tace zata aureshi da bakinta kuma malak taɗau nauyin komai na auren , binta kuwa kasa danne zuciyar ta tayi ta ɗago kai suka haɗa ido da malak cikin kasaita ta sakarwa binta murmushin mugunta tace, " bari na tashi nabaku waje ku tattauna, tana fadin haka ta tashi ta haye sama Jamel kuma ya matso kusa da binta ya zauna akan kujera yace , " hakika banida abinda zancewa Allah sai godiya ashedai Binta rabonace ke, uhm kawai tace masa chan daya fara cikata da surutu ta tashi tace gida zata ta haye sama ta ɗakko jaka ta fito

Ba kowa a harabar ai kwa dan danan ta soma sanɗa zata wuce sai ga baƙar mota ta nufota daga wajen parking aran binta tayi tunanin jamel ne ga mamakinta sai taga malik a fili ta saki ajiyar zuciya shikuma ya buɗe mata murfin motar yace ta shigo,

Sun fara tafiya a titi ya kalleta yace, " yadai kanwata, " lfy kalau yaya Malik, " Masha Allah ya zanen anatayi ko?, kai kawai ta gyada masa dan ita harma ta manta da zanan saboda bata cikin nutsuwa,

Har ƙofar gida ya sauketa abin mamaki fayez yana kallon su ta cikin mota itama binta ta ganshi sam sai ta nuna kamar bataga motar tasaba ta shige gida, bayan shigarta da mintina kaɗan ya kirata a waya tazo ta bude motar tasa ta shiga ta zauna tayi tagumi shiru babu wanda yacewa kowa komai chan fayez ya buɗe baki yace mata, " ashe kinsan malik har shaƙuwarku takai ya kawoki gida ko ? , kallon fayez kawai tayi da idanunta chan ta lumshesu hawaye na kokarin gangarowa tace , " fayez nafasa aurenka gobe kazo ka karɓi kuɗin da kuka kawo idanma bakazo ka karɓa ba zansa akawo maka gida ,

✍🏻 zeenariya

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

WhatsApp number

+218912472599

__________________________________

GARGAƊI

Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 30 )

Wani irin kallo yayi mata cike da mamaki yace, " binta kinsan mai kike faɗa kuwa?, " nasani fayez cewa nayi na fasa aurenka za a dawo muku da kuɗinku, fayez najin abinda ta mai maita ya dunƙule hannu ya naushi mudubin motar na gefan da take zaune dan danan mudubin ya tsatstsage binta ta cure waje ɗaya ta sunkuyar da kanta tana kuka a tsorace ta bayar ita zai nausa , wani irin huci fayez yake cikin zafin nama ya kama kanta da karfi ya ɗago dashi suka fuskanci juna ido cikin ido yafara magana cikin wata iriyar rikitacciyar murya da tsawa wadda batasan yana da itaba , " meyasa meyasa zakiyimin wasa da zuciya kifaɗamin tun farko meyasa kika yarda kina sona , yadda jikinsa ke tsumane ya kuma furgita binta sai zare ido take tana kuka sotake ta faɗa masa gaskiya amma babu hali saboda yarjejeniyar su da malak cikin tashin hankali tace , " fayez na roƙeƙa ka fita daga rayuwata ada nace ina sonka yanzu kuma nace banaso dan Allah kasa aranka tamƙar baka taɓa saninaba ka manta dani fayez ka mantani a rayuwar ka , kallonta kawai fayez yake sai a wannan karon hawaye yasamu damar gangarowa a fuskarsa cikin wani irin yanayi kawai ya sauke hannayensa daga riƙon da yayiwa kuncinta yana kallo ta buɗe motar ta fice da gudu,

Binta na gursheƙen kuka ta faɗa jikin ummah tana cigaba da rairawa sosai hankalin ummah ya tashi saida tayi da gaske sannan binta ta zauna tabata labarin duk yadda sukai da malak sosai ummah ta jinjina rashin imani irin na malak kuma ta tausayawa yar tata cikin matsananciyar damuwa tace, " binta ganganci ne ki kassara rayuwarki haka , ɗagawa binta tayi tace , " ummah kun gamamin komai keda abba saboda ku zan iya jure kowane ƙalubale naja ɗamarar yaƙi da zuciyata wajen jure rashin abinda takeso , ummah na tsananin tausayin binta amma babu yadda zatai ta hanata saboda Abba kuma saboda tanaso alakarta da fayez ta kare hakan shizai sama mata salama a rayuwarta

*

A daran malak tasa aka nemo mata gidan mrs Tahir ta hanyar yan sandan da suke bincike akan shari ar,

bayan ta samu adireshin ta kira ɗaya daga cikin yan aikenta ta aikasu gidansu binta da kuɗi dai dai adadin yadda fayez yakai na auren,

Papy ne zaune kan bed yana danna waya mom kuma tana gaban mirror tana shafe shafe yace mata, " ki kiramin yaronki maza yanzu inason yin magana dashi, to kawai tace ta dau wayarta ta kirashi cikin mintuna ƙalilan yazo dan dama yana gidan, a kujera ya zauna daga gefe papy ya ziro kafafunshi kasan gadon ya zauna sosai sannan yace, " malik wai yaushe zaka fara maganar aurene yakamata kasanfa lokacin ka yana ƙurewa, mom najin haka ta juyo cikin jin daɗi tace, " wlh khabeer karigani a fili narigaka a zuciya tun tuni nakeson yi masa wannan maganar ashe kaima tana ranka,

Yar dariya malik yayi yace, " mom and papy ku kwantar da hankalinku zan duba wadda ta dace sai nasanar muku ayi magana , jinjina kai papy yayi yace , " ai batun zaɓima ka kwantar da hankalin ka yar uwarka ta zaɓa maka matar aure , malik najin haka take walwalarsa ta gushe shida mom cikin mamaki yace , " papy kana nufin malak ce zata zaɓan wadda zan aura ?,

" ai Bama zata zaɓa maka bane tama zaɓama suhaima yar gidan uncle dinka ayman, wani irin kallo mom tayiwa papy tace, " haba khabeer meyasa kake haka ne ina Malik ina suhaima dududu yarinyar nawa take ko gaisuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login