Showing 54001 words to 57000 words out of 67181 words
Chapter 19 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx
najin shigowarsu ta fito da gudu ta rungume shi tana sakin kuka mai tsuma rai, " na godewa Allah ya wankemin Abbana alhamdulillah, Abba ganin tsirarin mutane da alamar anyi taro ga binta da kwalliya yace, " mai yake faruwa ne agidannan ban ganeba?, jin jina kai Ummah tayi tace, " dogon labarine muje daga ciki kayi wanka kaci abinci,
Haka kuwa akai Abba ya shiga yayi wanka ya gyara kansa yayi aski ya fito yayi shimfiɗa a tsakar gida lokacin yan biki duk an watse daman yan cin warane kuma tunda ta kare aka watse, gidan ashare yake kakal ummah da mama suka fito aka zazzauna binta na kwance a daki zazzaɓi yaki sauka Abba yasa aka kira masa ita ya soma tambayar su mai yake faruwa, mamace ta zauna tafaɗa masa duk abinda yake faruwa tana zuwa inda tace an daura auren binta yayi wata irin ɗagowa ya kalleta yace, " what bakuda hankali saboda kawai ina daure zakuyi mata irin wannan wula kanci ku ƙaƙaba mata wanda bata so kunfa san komai saboda farincikin ta na wargatsa maganar aurensu wanchan karan na haɗata da wanda take so shine yanzu dan ba idona kuka aikata haka, faɗa Abba yake sosai ta inda yake shiga batanan yake fitaba, mama cikin hassala tace, " ai bamu muka kar zomanba ita bintan ita ta yarda zata aureshi idan uwar ɗakinta ta amince tasa baki aka fidda ka , hannu ya ɗagawa mama sannan ya kalli ummah yace, " banga amfaninki ba usaina idan ita fatima batasan zafin haihuwaba ai ke kinsani dazaki bar yarki ɗaya kwallintal ta auri wanda bataso, mama najin haka tahau masifa tana ɗaga murya wai ance mata juya sosai take ruwan bala i hakan ba ƙaramin ɓatawa Abba rai yayiba, binta ganin sunata cece kuce hankalin ta ya tashi tace, " dan Allah Abba kuyi hakuri ni na amshi kaddarata zan zaune dashi, mama najin hakan tayi saurin cewa, " ai dolenki ne tunda an riga an daura babu wanda zai hanaki zama da jamel shegiya tsinanniya jinin masifa uwar san kuɗi wlh nayi nadamar barin mijina ya auri uwarki gashi duk kun birkitamin shi yau ni yakecewa juya akan wannan karuwar yarinyar,
Kalaman mama binta jinsu take kamar mashi dan bata taɓa tunanin mama zata jefeta da irin wannan kalaman ba Abba kuwa kokarin dakatar da ita yake taki yin shiru muryar ta sama da tasa ummah kuma sai kuka take ta sunkuyar dakai chan ta tashi ta wuce dakinta,
Da sauri binta ta bita ta sameta a zaune tayi tagumi tana hawaye, ƙarasawa binta tayi ta durkushe kusa da ita tana kuka tace, " Ummah dan Allah kiyi hakuri, kallon ta ummah tayi tace, " binta ke kika jamin tun farko kece kikaja dabaki tubure bazaki auri Jamel ba da yanzu anyi aurenki cikin lalama da nutsuwa,
" Ummah kiyi hakuri wlh na hakura da fayez zan zauna da jamel kiyi hakuri ummah dan Allah, ta karashe tana sakin kuka, " halacci ɗaya zaki nunamin binta shine ki zauna da jamel karnaji karna gani idan kuma kikaki wlh zan zare hannuna daga kanki bani baki..., Ummah bata ida rufe baki ba binta tasa hannun ta akan baƙin ummah tana kuka tace, " na yarda ummah na amince zan zauna dashi bazan taɓa aikata abinda aurena zai samu matsala ba,
*
Zazzaune suke a office din DPO jamel ya gaji da tambayar mai sukai anki basu amsa da suka matsa da tambayoyi DPO yayi musu barazana ɗan banzan duka hakan yasa sukai shiru, kiran wayane ya shigo wayar DPO ya ɗaga yana washe baki chan yace, " eh yallaɓai to a sakesu eh karfe 11:00 yanzu to Nagode sosai za a sakesun, yana katse wayar ya kira wani dan sanda yace a basu wayoyinsu su faɗi inda za a kaisu a kaisu shikkenan, tashi Jamel yayi cikin ɓacin rai dan yaga kamar ƙarfin haline abin sasu akai yace, " wai mekuke nufine yallaɓai wlh zan shigar daku kara ya ana tsakiya da daurin aurena kuzo ku kamamu kuma wai daga baya kusakemu bamu muku lefin komaiba kun rusamin ranar farin cikina , darayi officer yayi yace , " nagama nawa saura yarage naka kayi duk yadda kakejin yamaka daidai kaficemin daga nan idan ba hakaba zan maka kullewa mai hujja , dattijan da suke tare da jamel ne yajashi suka fita ,
Wayoyinsa ya kunna lokacin da suka hau a dai daita yana kunnawa kiran kawun binta ya shigo ya ɗaga bayan sun gaisa yake tambayarshi mai ya faru aka kamasu jamel ya bada amsa babu komai chan kawu yace, " to mahaifinta ya fito yau kuma mun san baya san aurenka da ƴarsa shiyasa muka ce an riga an daura inaso duk yadda zakai kayi ka ɓoye gaskiyar ba a ɗaura ba idan da hali karka bari iyayenka su gana da mahaifinta idan har kasan kana santa kaje a shawarce kace yabaka matarka idan yabaka ita kukaje kuka samu kamar sati biyu sai a bayyana ba a ɗaura ba kaga dole ya yarda ayi ɗaurin auren gasken dan gudun abin kunya, shiru Jamel yayi yana nazari chan yace , " toba matsala kawu Nagode ,ya kashe wayar ,
Yana kashewa ya kira malak bayan sun gaisa yake faɗa mata abinda yafaru sannan ya faɗa mata dabarar da kawun ya shirya chan tace, " wannan dabarar tayi Jamel idan har baka bitaba to bakada rabo a aurenta yazama dole idan kana sonta ka yarda ka rufe maganar ba a ɗaura aureba kai idan da so samune ma kayi mata ciki kafin gaskiya ta bayyana hakan shizai sa abaka ita dole idan kuma ba hakaba kanaji kana gani fayez zai aureta, jin jina kai Jamel yayi cikin samun kwarin gwaiwa yace , " alfarma daya nake nema ranki ya dade wajen zama na sirri wanda ba wanda zaisan inda na kaita , dariya tayi a fili tace , " inada gida keɓantacce kazo ka karbi mukullin akwai komai a ciki kasata , sallama sukayi ta kashe wayar ,
Binta na zaune tana aikin kukan daya zame mata jiki a kwanan nan jamel ya kirata a waya ta ɗaga da sanyin murya yace mata ta shirya da magriba zai zo ya dauketa baya bukatar gayyar yan ɗaukar amarya daga baya duk Mai son zuwa yaje, amsa masa tayi dato saida ya kashe wayar taji hankalin ta ya kuma tashi kamar ansa mata ranar mituwarta tama rasa ina zata tsoma rayuwar ta taji daɗi kota ina ba sauki gashi Abba na fishi da ummanta sannan mama na gayan bakaken magan ganu saboda ita ga tunanin fayez da halin dayake ciki ya cunkushe a zuciyar ta ji take inama ta mutu a yanzu ta huta,
Tashi tayi taje ta tsugunna gaban Abba da mama tace, " Abba kayafemin idan nayi kuskure dan Allah Abba kasaki ranka da magriba jamel zai zo yatafi dani idan baka yafemin ba bazan samu nutsuwaba, kauda kai Abba yayi chan ya juyo fuskarsa babu wal wala yace, " kin bani mamaki binta amma babu komai tunda haka kika zabarwa kanki kije Allah yabaku zaman lafiya yasa albarka a auren, kallon mama tayi tace, " mama kema kiyafemin nasan yau ranki ya bachi sosai saboda ni har kin gayawa ummana maganar da bantaɓa ji kinfaɗa ba dan Allah ki yafemin insha'Allah bazan kuma saku a damuwaba wannan shine na karshe , kwafa mama tayi chan ta sassauta ranta tace , " maganar dana faɗa na faɗane saboda babanki daya cemin juya amma ni idan ba hakaba babu wani laifin da kikaimin ko a da ɗinma saboda fayez da kika likewa ne yasa nadaina shiga shirginki , godiya binta tayi ta tashi ta shiga dakin ummah ,
Tunda ummah taji ance da magriba jamel zai zo ya tafi da ita sai taji hankalin ta ya tashi tarasa ina zatasa ranta zafin rabuwa da binta ne ke nukurkusar ta ta rungume binta sunata kuka an rasa mai rarrashin wani chan dai ta daure tayi mata nasiha dai dai gwargwado,
Bayan magriba kamar yadda ya faɗa yazo gidansu binta a motar gidansu malak bayan ya gana da Abba ya jaddada masa amanar yarsa ɗaya tilo ya danƙa masa ita akasa akwatinan ta a mota suka tafi,
Tunda ta shiga motar ta sunkuyar da kanta tanata kuka, shikam Jamel bai ce mata uffanba dan akwai maganganun da suke masa yawo aka wanda malak ta faɗa masa game da binta sanda yaje karbar mukulli,
Abakin restaurant yayi parking yaje yasai musu abinci bayan ya shigo binta ta karewa Wajen kallo ta ɗago ta kalleshi da jajayan idonta tace, " Jamel nan hanyar inane naga munaki kusan 1 awa muna tafiya kuma gidan da kace zamu zauna baifi tafiyar 15 minit ba, cigaba yayi da tukinsa yace , " sabon gida na sauya nan da 10 minit zamu ƙarasa , shiru tamai kawai ta cigaba da kukanta ,
Abinda ya bawa binta mamaki shine rantsar tsiyar unguwar da jamel ya shiga bata kara shiga mamaki ba saida taga gidan da ya tsaya ya buɗe get sannan ya shiga da motar ya fito yace ta sakko cikin wutar mamaki ta sakko tana ƙarewa gidan kallo sannan ta kalleshi tace, " Jamel nan ba gidanka babe bakata kuɗin kama wannan gidan ka faɗamin gaskiya, hararar daya galla matace tabata mamaki chan yace, " ai bai kamata ki tuhumeni akan wannan gidan ba tunda daman harkar kuɗi kikeso kuma sune sukasa kika liƙewa fayez babban gidane gashi nan na saki a cikinsa ina fatan hankalinki zai kwanta ,
Shiru tayi ya buɗe gidan yace ta shiga ta shiga shikuma ya fita yashigo da jakun kuna,
A falo ta zauna tana kallon falon ƙanshin da takeji agidanne ya tabbatar mata da gidan malak ne dan ƙamshin ɗakin malak ne kaɗai keyin sa , gidan bawani babba bane sosai amma ya tsaru,
Wani daki jamel ya shiga da akwatinan sannan ya fito falo ya zauna ya kalli binta yace, " bani wayoyin ki, kallonsa tayi tace, " mai zakai da wayoyina, tsawa ya daka mata, " bani nace, yaƙare yana miƙo hannu da sauri binta jiki na rawa ta miƙa masa ga mamakin ta sai taga ya cire layikan ya karya ya cillo mata wayar, wani irin kukan takaici ne ya kwace mata ta fuskanci kamar jamel ba zaman daɗi yakeso suyiba yana son cuzgunawa rayuwar ta saboda biyewa malak,
Dur ƙusawa tayi ta haɗe hannayen ta tana rokonsa tace, " Jamel nifa matarka ce dan Allah karka sauya min soyayyar da kakemin bansan kowaba anan sai kai dan Allah ka yarda muyi zaman amana da gaskiya, kallon ta yayi a wani sashin na zuciyar sa yana jin tausayinta amma kawai saiya dake yace, " ni wane irin roƙone ban mikiba inaji ina gani kika dinga azabtar min da zuciyata akan fayez , " kenan ramawa zakai jamel ?, tafaɗa tana kallon sa , tsaki yayi ya tashi ya shiga wani ɗaki,
Naɗe ƙafa binta tayi kamar marainiya ta cure waje ɗaya tayi shiru tanata tunanin ummanta, chan wajen minti biyar ya fito da jallabiya da alama ruwa ya watsa yazo ya nemi waje ya zauna ya buɗe abubuwan daya siyo yafara ci abinsa, baicewa binta uffanba,
Itama tashi tayi dan tanaso tayi sallar isha tace masa inane bedroom ya nuna mata Dakin dayakai kayansu ta shiga taga bedroom din ya cika da kawatattun kayan daki masu kyau akwatinan ta ta buɗe ta fito da kayan bacci da hijabi ta shiga toilet tayi wanka sannan tayi alwala ta fito tasa hijabi tayi sallah bayan ta idar ta jin gina da jikin bed tayi shiru tana cigaba da tunanin yadda rayuwar ta da Jamel zata gudana a wannan gidan
✍🏻 mai alƙalamin zeenare
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf
zeenariya
💁🏼♀️
Masu cewa na gyara sunan littafin HUDUD ba yana nufin iyaka bane iyakoki yake ɗauka a larafcin saudiya to ina mai baku hakuri nasan da hakan dan nima na karanci larabcin Saudiyar sai dai badashi nake amfani ba dan ba a Saudiya nakeda zamaba kunsan larabci kala kalane kowace ƙasa da yadda suke faɗin abubuwa kamar dai hausace ta Nigeria ta ban banta data Niger hakama ta gana tasha banban to dai a taƙaice bazan iya sauyawa ba dan nasan da hakan nasa masa HUDUD tun farko , na barku lafiya Allah bada lada 🥰🙏
__________________________________
GARGAƊI
Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 35 )
Shiru dakin babu abinda kakeji sai sanyin Ac haɗi da sassanyan kamshin turaren ɗakin bacci barawo dan danan ya kwashi binta ta kife a wajen,
Mamaki ne ya ishi Jamel ganin bata fito ta nemi abinci ba chan daya gama abinda yake wajen, 12:00 ya tashi ya shiga ɗakin tsayawa yayi chak yana kallonta cikin takaici wato ta ɗaukeshi shashasha baccima take dan danan zuciyarshi ta harzuƙa ya daka mata wata gigitacciyar tsawa Haɗi da dukan ƙafarta , binta a razane ta tashi tama rasa inda zatai jikinta sai tsuma yake ya ƙare mata kallo yana wani zaro ido yace , " binta bafa zanɗau wannan iskancin ba ya ina zaune ina jiranki zaki wani shigo ki kwanta , kallonsa tayi cikin mamaki tace , " jamel ya kake nema ka sauya daga jamel din dana sanka ne wai mainai maka kakemin haka ?, jinjina kai yayi yana kuma turɓune fuska yace , " kima daina marai raicewa binta bazan tausaya mikiba dan nima baki tausaya minba, yafaɗi yana jan dogon tsaki ya zauna a gefan gado, dafe kai tayi ta saki kuka mai ciwo tana tunanin mai yake shirin faruwa da itane takasa gane mai yajawo hakan ace amarya a daran farkonta miji ya dinga haka neman fitina kala kala,
Yana zaune akan bed ita kuma tana tsaye babu wanda yayi magana chan ya tashi ya kashe light haɗi dace mata, " kinga kin dameni da kukafa banaso, tana ganin ya kwanta ta fice falo ta zauna tayi tagumi ko zataji sassauci a zuciyar ta chan ya fito kamar wani zaki yana huci yazo ya kama hannunta ya figota ya shigo da ita bedroom ya tankaɗata kan bed a rashin sa a hannunta ya daki bango ta bige cikin wata irin murya ta saki ƙara dan azaba, ba tausayi yasa hannunsa abaki alamar tayi shiru sannan yace, " mahaukaci kika ɗauke ni ina miki magana matsayina na mijinki zaki fita falo ki barni, cikin muryar kuka tace, " jamel nafahimta yanzu kwangilar kasheni ka karɓa kenan shiyasa ka chanza min gida inda babu wanda yasani, kuma fusata yayi babu alamar tausayi yazo ya cukumi fuskar binta datai jajir saboda kuka yace , " dana barki ki auri fayez gara na kashekin daman da gaske malak take bazaki taba yimin biyayyaba saboda kinaso narabu dake ki auri shi ,
binta ganin idan ta cigaba da tanka masa zai lahantata yasata tayi shiru sai shashsheƙar kuka take tanaji tana gani yasoma shafa jikinta yana nishi harya cire mata hijabin dake jikinta yasoma lasar tundaga wuyanta har kan leɓanta yana kai hannayensa kan kirjinta , faɗuwar gabace ta kwacewa binta saida ta rike gefan zuciyar ta saboda wani irin bugu taji tanayi da sauri da sauri saboda tsoro chan taji ya chabki harshenta yana kai hannunsa kasan mararta jitai bazata iya jurewaba ta tureshi da iya karfinta tana kuka tace , " dan Allah kayi hakuri jamel bana cikin yanayin nutsuwar dazan iya wannan yanzu dan Allah kamin afuwa ka kyaleni , idonsa kamar na yan maye yake kallonta chan ya cije baki yanufota tayi saurin zillewa dagudu tayi bakin ƙofar ɗakin ta fice
da gudu ya tusata tana zuwa taga kofar fita daga falon a rufe , hannu ta ɗora akai tana kuka dan gani take Jamel wulakantata kawai yakeson yi babu yadda batayiba ta zille masa ta kasa haka ya riketa ya mannata da jikinsa ya shigar da ita bedroom rigar dake jikinsa ya cire yarage daga shi sai gajeran wando yasawa ƙofar key yadawo ya kuma figota ya shiga yaga kayan jikinta ta karfin tsiya saida ya yagesu tas, binta na ganin haka hankalin ta yakuma tashi tadage sai ihu take tana cizonsa tana ya ƙushinsa amma kamar mai jikin karfe yaƙi cikata chan dayaga zata ɓata masa lokaci sai ya cire boxer ɗinsa ya kwantar da ita ta karfi ya haye kanta yafara ƙoƙarin neman hanyarsa ,
Binta kowace addu'a ce tazo bakinta kawai yi take tana jinsa yana ƙoƙarin tsagata sai fasa ihu take tana kiran sunan uwarta da ubanta chan ta soma kiran sunan fayez tana cewa ya ceceta shikuma jamel yanajin haka yakuma tunzura cikin rashin imani yayi mata tsagwaran rashin imani da gayya da mugunta ya kachachchalata yadda yaga dama tun tana ihun saida ta daina har yaji yasamu cikakkiyar gamsuwa sannan ya sauka a kanta yanata mita yana zage zake yana gani bata motsawa amma baibi ta kantaba ya kwanta a gefe yana faɗin , " ina gama hutawa zan ɗora daga inda na tsaya sai muga ko fayez ɗin zai iya zuwa ya ceceki ,
*
Malik na kwance yanata kiran lambarta akashe duka layikanta biyun gaba daya hankalin sa ya kasa kwanciya dan yaga Jamel yazo wajen malak sun daɗe suna tattaunawa sosai Malik ya tsorata chan dai ya yanke shawarar dasafe zaije ya duba gidansu ko lafiya,
Washegari da sassafe Malik ya shirya ya tafi gidansu binta dan har a lokacin ma yanata kiran wayarta akashe, a kofar gidansu yayi parking ya ja ya tsyaa chan yakira wani almajiri yace yayi masa sallama da binta almajirin ya shiga ya fito ya ce wai inji wa malik yayi murmushin jin dadi yazata tana nan yace ace nata Malik ne