Showing 3001 words to 6000 words out of 67181 words

Chapter 2 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx

ana biyan naira dubu ɗari biyar kuma aikin babu yawa abinda yasama tayi mana tayin sunce suna bukatar matashiya mai tsabta da hankali mai ilimin boko, Abba najin haka yace, " kina nufin aikatau to maganar aurenfa, usaina zata kuma magana kenan Hajiya fatima ta tari numfashinta da cewa, " bintan da ko saurayi batadashi abi komai a hankali idan aikin ya chanchanta saitayi kafin auren tunda nema nemane duk inda yake, mahaifiyar binta wato usaina taƙara da cewa, " maganar gaskiya ni nafiso naga binta tasamu aikinnan dan Hajiya halima ta tabbatar min babu wata matsala kuma suna biya da tsoka da zaman banzan nan dazata dingayi tunda tayi boko tayi arabi tayi aikinta koda na wata biyarne inyaso sai tasa jari ta gina kanta kaga an taimakawa Hajiya fatima da wasu ɗawainiyar gidan nan, nisawa abban Binta yayi yace , " eh wannan maganar gaskiya ce to badamuwa awane gidane , " gidan Alhaji khabeer muhd , umman binta tabashi amsa riƙe baki abba yayi yace, " anya zan bar yarinyar nan tayi aikinnan kuwa wannan gidan inajin labarinsu basa kaunar talaka karfa wani abun yafaru da ƴata kwalli daya rafkin,

Hajiya fatima ce taƙara dacewa , " wai wane khabeer din kadde wanda nasani , " eh shifa dai abokin yayanki omar, rike baki tayi cike da fargaba dazata iya tabbas data hana binta wannan aikin amma babu yadda zatai kar usaina taga kamar baƙin ciki take musu,

Ranar laraba binta tafita kasuwa siyayyar kayan miya tanata Allah Allah tayi takoma gida dawuri, a gaggauce tagama siyan komai tafito titi tanata tsaida abin hawa sunki tsayawa hakan yasa taga kamar zata ɓatawa kanta lokaci sai tayi yanke ta wani layi da niyar ta fita babban titi tasamu abin hawa, tana tafe riƙe da ledodin kayan miyan taji ana mata hon a baya dayake layin bashida faɗi sosai sai taƙi matsawa aranta sai mita take tana cewa, " su waɗannan masu motar sun raina masu yawo a ƙafa wlh, jitai an kuma hondin a hassale ta juyo cike da tsiwa tace, " to sarkin rashin hakuri sai a jira nasamu wajen faka ƙafafuna mana,

Yana daga cikin motar yaji abinda tace baisan sanda ya saki dariya mara sautiba ya ƙaraso daidai da ita yasauke gilashin motar, binta naganin shi tayi mutuwar tsaye aranta tace, " na shiga uku wannan balaraben na faɗawa magana Allah yasa bai jiniba, kauda kai tayi taɗan ƙara saurinta shima rage gudun motar yayi yana tafe yana kallon ta aransa yana yaba tsantsar baiwar kyau da Allah yabawa yarinyar dayake baisaba ganin mace haka kurin yayi mata maganaba sai yayi shiru duk da zuciyar sa tana so tayi mata magana, ahaka suke tafiya suka fito babban titi ta tsaya tana neman abin hawa ganin hakan yabashi damar matso da jibgegiyar motarsa kusa da ita yayi parking yace, " yan mata kizo na rage miki hanya akwai rana ga kaya a hannunki, kallo ɗaya tayi masa kawai ta kauda kai, ganin bata ce masa komaiba yasashi jin kamar yayi tafiyarsa sai kuma yaji yakasa da daddaɗar muryarsa ya kuma cemata , " ban taɓa tare mace ahanya nace zan rage mata hanyaba kece ta farko kuma gashi zaki watsan kasa a ido , nisawa binta tayi tace , " nima ba,a taɓa cewa za,a ragen hanyaba sai yau kayi hakuri bazan iya shigaba , " tsoro kike karna yanke miki kai , yafaɗa yana kallonta kanta a sunkuye tayi dariya tace , " aa ,

" kinaso nan gaba idan naga wata tana buƙatar taimako karna taimaka mata kenan saboda abinda kikai min??, girgiza kai tayi takuma kallon sa yanada kamala baya siffa da mutanan banza gashi haɗaɗɗe batai tunaninma yanajin hausaba, shiga tayi gaban motar tanajin yadda sassanyan kamshin turarensa haɗi dana AC ya gauraye motar, aranta tayiwa Allah godiya dan kuwa rana tafara buɗewa gashi zafi ake,

Sun fara tafiya yace mata, " ina zan saukeki, " a hanakali tafaɗa masa sunan unguwar, har suka ƙarasa unguwar babu wanda yaƙara cewa wani ƙala, binta kafin ta fita tace, " Nagode sosai Allah yasaka maka da alkhairi, murmushi ya sakar mata yace to nima nagode sosai, " godiyar me kakemin ?, Binta tafaɗa tana kallon sa , " godiyar barina da kikai nasamu ladan rage miki hanya

✍🏼 zeenariya

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

__________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (3)

Sai dai gashi zaki tafi bansan sunan kiba,

" sunana fatima ana kirana da binta, jinjina kai yayi yace, " wow nice name nikuma sunana Dr fayez, cikin mamaki tace, " ashema likitane ne haba shiyasa kakeda tausayi, " zigani kike?, yafaɗi maganar cikin jin daɗin yadda yake tattaunawa da ita

" aa gaskiya nafada ai, nan dai sukai sallahma ma tawuce gida shima yaja motarsa yatafi,

Binta nashiga ciki ta tadda mama zaune a bakin get abba yana wanke mata mota, ƙarasawa tayi tana cewa, " Abba sannu da aiki mama sannu da hutawa, " yauwa sannu kindawo naga yau kinyi sauri, cewar mama kenan, " eh nasamu abin hawa dawurine, tashi binta tayi tawuce sashin ummanta bacci ta taddah ummah nayi bata tashetaba tawuce ɗakinta tasa kayan tsakar gida tajawo wayarta ta tashiga latsawa sallahma taji abakin ƙofar tata tagane muryar wacece baki a washe tace, " shigo ramlah, Ramlah na shigowa tace," ashe kin ɗau murya hutawa kikene?, " eh wlh kinga yanzu nadawo daga kasuwa, zama Ramlah tayi abakin bed ɗin tace, " gaskiya kawata yau kinbawa yan unguwar nan mamaki, tashi zaune binta tayi cikin mamaki tace," ban gane nabada mamakiba menayi,

" hmmm daman kowa cewa yake bakya kula talakawa saboda ke matar manya ce sai kuwa gashi nan yau munganki da wani kamar ma bajinsin hausawa ba ga kyau ga kuɗi, rike baki binta tayi tace, " dan Allah waya faɗa miki kai mutane ba,a iya musu,

Da dariya lamrah taƙara da faɗin, " wlh wankima nake suhailat tazo tace anty kinga motar saurayin anty binta kuwa gashi haɗaɗɗe kamar balarabe, dafata binta tayi tana dariya tace, "kai suhailat badai iya tsaigumi ba wlh toba saurayi na bane ragemin hanya kawai yayi, nan suka ja hirarsu ta kawaye

*

Tunda yaje office ya zaune yake tunaninta karo na farko kenan bayan malak dayaji wata ƴa mace ta burgeshi dukda akwai masu cewa suna sonsa haɗaɗɗun mata malak ce tayi musu zarrah yau kuma gawata wadda bama takama kafarsu ba tana ƙoƙarin shigewa chan chikin zuciyar sa, shikaɗai yake sakin murmushi yanajin inama ya amshi number ta,

Kirane ya shigo wayarsa yana dubawa yaga mai kiran cikin hanzari ya ɗauka

" hello madam

Sassanyar ajiyar zuciya yaji tasauke tace, " ykk ya aikin?, " ina lfy kefa?,

" fine dama nakiraka ne nafaɗa maka yau zamu fita da daddare, jinjina kai yayi yace, " misalin karfe nawa?, " Eight o'clock at night , " okay ina zamu?, yakuma jefo mata tambaya, " why are you asking such a question fayez kasandai bazai wuce restaurant ba muci abincin dare achan, a fusace take maganar hakan yasa shima ya fusata amma bai nuna mataba saboda yafita hakuri kuma yanada kauda kai, " okay bye zanzo anjiman ki kulamin da kanki, " bye , tabashi amsa takashe wayar ,

*

Asalin su

Malam Muhammad mutum ne da Allah yayi masa tarin dukiyar da baisan iyakar taba ɗan kasuwa ne babbah kuma ya taɓayin shugaban ƙasa a Nigeria azamanin mulkinsa yagina adalci mutane suna matukar sonshi kuma suna alfahari dashi har yayi mulkinsa ya gama

Yanada mata Aminatu dayara uku biyu maza ɗaya mace khabeer muhd shine babbah wato papyn malak sai ayman muhd shine mai biye masa wato Abban fayez machan itace hafiza wadda Allah yayiwa rasuwa rana ɗaya da mahaifinta sanadin hatsarin mota, mahaifiyar su aminatu ita tacigaba da kula dasu biyun har suka kammalah karatun secondary suka fita kasar waje yin jami,a bayan shekara uku ayman yadawo gida lokacin ya tadda mahaifiyarsu a asibiti ba lafiya nan ya kira ɗan uwanshi khabeer yazo koda na sati ne saiya koma kemai mai khabeer yaƙi zuwa har Allah yayiwa ameenatu rasuwa lokacin khabeer yanada shekara ashirin shi kuma ayman yanada 18 , bayan rasuwar mahaifiyarsa ragamar dukiyar gidan takoma hannun ayman dayake yarone a lokacin sai yayi wasarere da ita aka dinga damfararsa ana kwasa ƴan uwan mahaifinsa duk saida suka zama masu arziki haka na mahaifiyar suma marasa tsoron Allah acikin su sunci dukiyar mai isarsu kwanci tashi komai yalalace dukiya ta zabge saboda an daina juyata kuma kullum ɗiba ake hadda mutanen mahaifinsa duk sun kwasa sun gudu

Ahaka ayman ya jajirce ganin zata ƙare yasa aka raba musu shida ɗan uwansa, kasan ayman yazuba kasuwanci dasu kuma yacigaba da karatunsa a Nigeria kason khabeer kuwa mahaifin budurwarsa yabawa yayi masa kasuwanci dasu dayake malam sani mai amanane ya riƙe dukiya tsakani da Allah har khabeer yadawo ya amshi abarsa yacigaba da juyawa

Bayan shekara biyar ayman yayi Aure lokacin ya buɗe katafar hospital dayake likita ya karanta bayan shekara guda da auren Allah ya azurtasu da samun da namiji kowa na murna aka samasa Muhammad ake kiransa da fayez saida suka shekara biyar suka sake haihuwar hafiza , bayan yin Auren ayman da shekaru 8 khabeer shima yayi Aure da hafsat sani

A yanzu haka suna zaune a , nasarawa GRA gidan su a layi ɗaya yake manya manya Hajiya zainab da Alhaji ayman ƴaƴansu huɗu fayez da hafiza sai suhaima da siyama, Hajiya Hafsah da Alhaji khabeer sunada ƴaƴa biyu Malik shine babban mai shekaru 24 sai malak mai shekaru 22

Ba karamin so wannan family sukewa junansu ba hakan yasa suka daɗa ƙarfafa zumuncin su ta hanyar haɗa Auren fayez da malak,

Mun dawo cikin labarin,

----

Yamma nayi fayez yabar office kai tsaye inda ya ajiye binta da safe ya nufa yana zuwa unguwar yayi parking a gefan titi ya shigo kan layin daya ga tashiga wasu samari dasuka kwalalo masa ido tun shigowarsa layin ya nufa yayi musu sallahma har rige rigen amsawa suke ya gaishesu suka amsa kam shinsa duk ya gauraye gurin yara da manya masu wucewa sai kallon sa suke kamar sunga baƙon halitta cikin sassanyar muryarsa mara hayaniya yace musu, " dan Allah tambaya nake, " Allah yasa munsani,

" gidansu wata yarinya nake nema fatima ana kiranta da binta, wani mai ɗan hankaline cikin samarin yace, " ranka yadaɗe akwai masu suna matima dayawa a layin nan kuma bintama haka don ko gidanmu akwai binta sai dai ka misalta mana kamanninta kozamu gane, iska fayez yaɗan hurar a bakinsa yace, " zaka ganta farace sol mai tsayi tanada siririn hanci da manyan ido ga cikakkun gashin gira miskila miskila haka , murmushi saurayin yayi yace , " naganeta yarinyar nan yar gidan Hajiya fatima dabaka kwatantamin fasalintaba bazan ganeba dan yarinyar bata kula kowa akwai miskilanci kam kaga wanchan gidan mai bene mai fenti ruwan toka nan ne gidansu , godiya fayez yayi yasa hannu a aljihu yaciro kuɗi yan dubu dubu masu yasa bai irgaba yabasu yace suraba , nan samarin suka shiga godiya yayi musu sallahma ya wuce

Kai tsaye ƙofar gidan ya nufa ya tsaya ya kwankwasa madai daicin get din bajimawa malam musu ya fito ganin fayez yasashi tunani zaton sa ko ƴan uwan Hajiya fatima ne

Fayez aransa yaji kamar wannan dattijon babantane cikin ladabi ya rusuna ya gaisheshi shima abban cikin girmamawa ya amsa tare da faɗin, " wajen Hajiya kazo sai dai kash tafita yanzu yanzu, sun kuyar dakai fayez yayi yace " nazo wajen bintane, cikin mamaki Abba ya maimai ta binta aransa yake cewa karo na farko kenan da akazo zance wajen binta , " to ba damuwa bari na faɗa mata ,

Binta na kitchen tana feraye doya Abba yashigo yace, " kije ana sallahma dake awaje, to binta tace Abba yakuma fita yayi masa masauki a palon baki na waje,

cikin mamaki tanaso ta tambaya wanene amma bazata iyaba dan koma wanene tasan ba mutumin banza bane tunda abbanta ne yace tazo maibima da izinin sa yazo, ɗaki tafada ta shiga toilet tawanke hannunta sanna taje bakin mirror taɗan gyaggyara fuskarta sama sama tasa hijab har kasa tafito waige waige tadingayi a harabar gidan bataga kowaba ƙofar ɗakin batki tagani a hangame ta hango haɗaɗɗan takalmansa sauciki kana gani kasan ba karamin mai kudine yake sasuba, ɗan rakuɓewa tayi abakin ƙofar tanajin kamar karta shiga sai kuma ta dake tayi sallamah kanta a sunkuye batare data ɗago ta kalleshi ba tagaidashi muryar dataji ce tasata ɗaga kai ga mamakinta kuwa shine murmushi yasakar mata yace , " binta kinyi mamaki ko

Jinjina kai tayi alamar eh tazauna a kujerar dake kallon tasa tace , " meya kawoka wajena daga ragin hanya,

" inason zamu ɗan tattauna dakene tun dazun dana kawoki naso hakan sai kuma naga rashin dacewar nayi maki magana a titi, jinjina kai tayi tace ," eh hakane to wace magana zakai dani ,

Gashin kansa dayaji gyara ya shafa yace , " kinada saurayi ko a'a ?, " meyasa katambaya ?, " saboda maganar dazamu tattauna tanada alaƙa da hakan , " hmmm to bani da shi , kayataccen murmushi yayi mata ya gyara zama yana sake kurawa fuskarta ido yace , " ina sonki Binta kuma so bana wasaba tunda naganki nakasa sukuni yau ko aikin kirki banyi a office ba inata tunani tare da fatan Allah yasa nasamu karɓuwa , shiru Binta tayi tace , " daga haɗuwa ɗazu shikkenan saika kasa sukuni?, dariya yayi yace, " Binta mebi ke yau kika fara ganina amma ni na dade dafara ganinki, zaro kyawawan idonta tayi cikin mamaki tace," a ina kaganni?, " bazaki gane kwatancen ba tunda ke baki ganniba a lokacin,

" ina fatan zan samu karɓuwa a wajenki?, shiru tayi chan tanisa tace , " inada bukatar lokaci danyin tunani akanka kuma inada bukatar sanin wasu abubuwan agame dakai dannah gane da wa zanyi soyayya,

" kinyi gaskiya binta dafarko dai kamar yaddah nafaɗa miki sunanah fayez ayman muhd ni maaikachin lafiyane Ammee na da Abba na suna raye inada kanne mata uku hafiza suhaima siyama hafiza tana da Aure da yara biyu shekaru na 30 , binta taji daɗin bayanin kansa dayayi mata, " harda abinda bannemi sanibama ka sanar dani nagode tom, " bakomai girmanki ne kisan komai , " gaskiya ne nima yadace nasanar dakai wani abin game dani sunana Fatima nanne gidanmu ina ruwa da mahaifina sai ummah na da kuma mamana , takareshe tana masa dariya shima dariyar yayi yace kwai kwayata zaki , nan suka shiga hira kamar wanda suka daɗe da sanin juna sunjima sannan binta taje takawo masa ruwa da lemo sai wajen magriba sukai sallahmah yatafi bayan sunyi musanyan numbar

✍🏼 zeenariya

🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️

( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )

story and writing by

zainab ahmed Yusuf zeenariya

__________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد

𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (4)

Fayez yana komawa gidan tundaga haraba yajiyo hayani yana tsaki ya shiga gidan,

a palo ya taddasu a zazzaune Ammee na cewa,

" haka kika zaɓa kuma a haka zaki ƙare kinadai kallon yan uwanki zasu auri manyan masu kuɗi ke kuma kin ƙare da talaka babu abinda Auren talaka yake tsinanawa sai tsiya da asara dashegen yawan sex ba dare ba rana bakida hutu daga ciki sai goyo idan yagama kasheki yatara miki ƴaƴa ya tabbatar koya sakeki ba wanda zai aureki sai ya shiga gana miki azaba yana miki kora da hali,

subhanallah fayez ya furta a fili ya kalli kanwar tasa hafiza daduk wannan ruwan Bala,in Ammee da ita take , awani sheƙeƙe Ammee ta kalleshi tace, " ai daman kai kake zugata kaida abban ku dole kace subhanallah fayez sam baka biyo jininaba wlh , zama fayez yayi yace ,

" haba Ammee arzikifa nufine na Allah abinda kukewa hafiza bakwa kyauta mata itamafa ƴarkice menene lefinta danta auri wanda takeso kuma muma kafin mubata shi saida muka tabbatar nura mutumin kirkine pls dan Allah Ammee kudaina mata haka intazo,

siyama ce tace, " gara da Allah ya kawoka yaya kawaifa dan dady ƙarami ya taɓawa anty suhaima waya shikkenan tasa USB tazaneshi harsaida jikinsa ya fashe, ran fayez ne yakuma ɓachi ya kalli suhaima dake gefan Ammee yace, " idan ɗanki tayiwa haka zakiji daɗi to wlh daga yau karna sakejin hafiza tazo da ƴaƴan ta wani yadakesu, Ammee ce ta tari numfashinsa dacewa, " wlh fayez baka isaba daga kai har hafizar nina haifeku baku kuka haifeniba idan tasan batason yaran suyi lefi ta daina zuwa dasu mana wannan ƴan iskan ƴaƴan nata fitinannu badama ka aje abu sai sun taɓa,

kai kawai fayez ya jinjina yatashi yace hafiza ta biyoshi ɗakinsa, miƙewa tayi taja hannun yaranta dady karami da anam suka nufi ɗakin fayez suna shiga suhaima tayi tsaki tace , " aibataga komaiba indai zata dinga zuwa maula gidannan,

siyama kamar tayi kuka tace , " Ammee idan bakyasan hafiza mai yasa kika haifeta ?, nisawa Ammee tayi tace, " wlh auta bawai bana sonta bane inason ƴata sonnema yasa nake mata haka dan ta haƙura da wannan jarababban mijin nata tabashi ƴaƴan sa tazo tayi rayuwa kamar da ta goge ta auri hamsaƙin mai kuɗi wanda ba raini duk family zamuyi alfahari da ita, shuru siyama tayi tana tunanin bakar zuciya irinta mahaifiyar tata sam bata kaunar talaka kuma itama asalinta talakawan ne fitik lokacin da Abban su ya auretane tagoge tazama hamshakiya wannan dalilin yasa bata zumunci da talaka a family ɗinta indai kaga taje wani sha a ni nasu tosai dai idan na masu kuɗi familyn ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login