Showing 51001 words to 54000 words out of 67181 words
Chapter 18 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx
sigaba
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 32 )
Koda binta taje wajen kanin mahaifinta tasanar masa tanaso ya wakilci ɗaurin aurenta ranar Litinin bai wani bi ba asiba saima murna dayayi ya buƙaci ta ara masa kuɗi daga cikin sadakinta zai sa jari sannan yayi mata jaje kan kama mahaifinta da akai, tunda suka taho a hanya tunani kala kala ya lullube binta tabbas batada zaɓi Amma bazata iya goge son fayez daga cikin rantaba, jamel kuwa ya lura binta gaba ɗaya ta sauya ba kamar farkon fara soyayyar su ba yanzu ko magana batayi sosai,
Adaran yau ummah taje ɗakin mama tasanar mata da komai game da Auren binta mama tayi murna sosai cikin jin daɗi tace, " alhamdulillah kinga munci riba biyu kenan gata fitowar musa gata aurar da binta kai wannan yarinyar malak babu abinda zamu ce mata sai godiya da fatan Allah ya biyata da gidan aljanna, itadai ummah shiru tayi dan a ƙasan ranta batasan aurennan saboda farincikin ƴarta kawai dai ta amince ne dan babu yarda zasuyi
*
A kiɗime ya shigo gida sai kwala mata kira yake tana kwance a doguwar kujera a falo tana jinsa bata amsaba har ya karaso ya tsaya a kanta sai ruwan bala i yake yana cewa, " wai malak kodai kin fara haukacewa ne ubanme kikai da kuɗi har 100 milion a yau?, malak bata tanka masaba ta cigaba da danne dannan wayar ta mom ce ta sakko tana kiran, " kunfara ko malik da girman ka kake daga mana murya haka mai ya faru ne,
Cikin takaici yace, " dazu naga alat ɗin cirar kuɗi har 100 milion a account dinmu na gidannan, rike baki mom tayi tana jinjina kai ta zaune tace, " kekwa malak mai kikai da kuɗi haka haba dan Allah yakamata ace kinsan tattali abin naki yafara yawa, itadai malak bata tanka musuba kawai saita dannawa papy kira tasa a speaker tace , " hello papy shin inaso kagayamin daman akwai shamaki tsakanina da dukiyar ka ne?, su mom sunajin papy muryarsa har rawa take wajen furta, " inji ubanwa ai duk abinda na mallaka nakine kiyi yadda kikeso dasu, ok tace ta katse wayar sannan ta watsa musu wani irin kallo tace, " kunji daga bakin mamallakin dukiyar dan haka banason surutu kodu na cinye bakuda yadda zaku dani musamman ma kai Malik, tafaɗa tana nunashi da yatsa ya fusata zai tanka mata mom ta hanashi malak kuwa taja tsaki tabar wajen,
Ranar Lahadi da daddare fayez ya kira binta daman tana cike da alhini da kewar rashin ganin kiransa har tsawan awa 24 , cikin sauri ta ɗaga ta kara wayar a kunne kalmar farko daya faɗa matace tasa ta hawaye, " da gaske bazaki aureni ba ?, shiru tayi haɗi da toshe bakinta da hannu ɗaya chan ya kuma cewa, " bazan takura mikiba binta watakil ke ba rabona bace na hakura dake kamar yadda kika nema kuma daga yau in Allah ya yarda bazan sake kiranki ba pls inaso kiyiwa wannan maganar kyakkyawar fahimta hakan ba yana nufin naji haushinki bane ko nadaina sanki aa ni mai kyaunarki ne inaso kisa aranki idan har zaki kira sunan wanda yake sonki fiye da komai a rayuwar sa to kikira sunana ni mai kyaunar ki ne har abada inai miki fatan nasara da salama a rayuwar ki binta Allah yabaki wanda zai kula da rayuwarki fiye da yadda hankali zai nazarta Ubangiji Allah yayiwa rayuwar ki albarka data ƴaƴan dazaki haifa Allah yarabaki da dukkan nin sharrin abinki ya sadaki da alkhairin sa , shiru yayi wanda shirin kanaji kasan kuka yake,
Wani irin zafi da radaɗi binta keji a ranta takasa jurewa jitake kamar ta wargatsa komai tazabi zama dashi saboda son da take mata, wani irin kukane ya kuma kwace mata wanda yasata kashe wayar ta kifa kanta akan cinya tafara rerashi da karfinta, ummah da gudu ta shigo ta zauna kusa da ita ta rungumota jikinta tana rarrashi, " ummah ina son fayez bazan iya jure rashinsa ba ummah zuciya ta zata fashe ummah yazanyi innalillahi Allah ka kawomin dauki , cikin tsananin tausayawa ummah take rarrashinta da cewa , " kiyi hakuri ki miƙa lamarinki ga Allah indai akwai zalinci zakiga sakamako kuma rabonka baya taba wuceka aduk inda kake ,
Ranar Litinin da safe kawu nuhu yazo karfe 7:30 sumama an chakare iyayen amarya kenan sai kai kawo take tanata bushasha da kudin da umma ta bata ayi abincin daurin auren yan unguwa zuwa yanzu duk sun sani mata sai shiga gidan suke suna kallon niki nikin kayan lefan da aka kawowa binta akwati shidane an cikasu da kaya
Binta tunda taga haka ta koma ɗaki ta kule zazzaɓi mai zafi ya rufeta tana ganin kiran wayar jamel takasa ɗagawa idanunta sun gaji da kuka Khadijah kawarta ce ta shigo dauke da sallama a bakinta ta zauna gefan gado tana kallon binta tace, " binta anya kuwa kina son aurennan ?, tashi binta tayi sai rawar sanyi take idonta sunyi jajir tace, " mekika gani?, Khadijah ta girgiza kai cike da tausayawa tace, " naji ance ba fayez zaki aureba kuma jifa yadda kika rame duk kim chanza binta duk wanda ya ganki yasan kina cikin damuwa, kuka binta ta fashe dashi mara sauti chan mama ta shigo ta tsaya tana zare ido cikin faɗa take cewa, " au wai kukan kike lallai ma to saikiyi da kyau harki gaji wato saboda kijawo mana abin faɗe kike kuka lokacin da baƙi suka taru Salan ace bakya so, wata jarka data tsumu da magani ta miko mata tace , " ungo maza sha kiban jarkar yanzu kuma ki tashi gamai gyaran jikinan zatai miki shaf shaf nayi magana da jamel yau dinnan za a kaiki kowa ya huta inyaso sauran gyare gyaran kya karasa agidan naki , karbar maganin binta tayi tasha tabata jarkar ta fice itadai khadija ta rike baki cike da mamaki tana tunanin mace kamar binta san kowa kin wanda ya rasa bai kamata ai mata irin wannan aurenba ,
Da wurwuri malak ta farka yau saboda ɗokin binta zatai aure ta bar mata fayez ɗinta, waya ta ciro ta kira jamel bayan sun gaisa tace, " ina fatan ba wata matsala komai yana tafiya dai dai?, " eh alhamdulillah ba wata matsala da mamanta cewa tayi na bari idan an ɗaura auren yau sai a kawota nanda kwana biyu nikuma nace aa yau nakeson a kawomin matata, murmushi malak tayi tace kayi kyan kai jamel, bayan sun gama wayar ta kira Ammee a waya suka dan taɓa hira sunata farin ciki tace, " yauwa Ammee nasan ba lallai fayez yaji labarin aurennan ba kifaɗa masa yaune kinji labari daga wajena , dariya Ammee tayi tace , " yanzu kuwa , sukai sallama ta kashe wayar ta tashi ta nufi ɗakinsa ,
A zaune ta sameshi yana jan charbi da alama tunda yayi sallar asuba bai tashiba , ƙarasawa tayi ta zaune tace, " good morning dear son, " kai ya gyada mata dan bayasan magana tayi murmushi tace, " fayez ashe yarinyar nan yaudarar mu tayi suka cinye mana kuɗin aure ashe tsohan saurayinta takeso yaune ma daurin aurensu, kasa fahimci yayi cikin mamaki yace, " wace?,
" binta mana , wata kwaran kwatsa yaji a zuciyar sa dan danan ya kuma ƙanƙame charbin hannunsa yana sallallami saida yayi shiru na sakanni sannan yace, " jamel zata aura kenan shiyasa tace bata sona tarabu dani, " uhm abin takaici shiyasa tun farko nace maka talaka tsinannan mutum ne azzaluma Allah yayi mata abinda tama Allah ya saka maka fayez,
" Ammee menene na tsine mata Ni bata min laifin komai ba rayuwar tace kamar yadda nabar malak na koma mata itama tabarni ta komawa saurayinta,
" Allah sarki fayez ko wannan abun ya isa ka gane duk duniyar nan babu wadda zata iyai maka son da malak take malak adai cikin soyayyar aure, shiru fayez yayi bai kara cewa komai ba,
✍🏻 mai alƙalamin zeenare
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf zeenariya
WhatsApp number
+218912472599
__________________________________
GARGAƊI
Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 33 )
Ammee na fita hawayen da suka taru a idon sa suka samu damar gangarowa ya sunkuyar da kansa yana sharesu shi kaɗai yasan irin wutar kaunar da yakewa binta amma babu yadda zaiyi batare da yasan daliliba ta rabu dashi, wayarsa ya ɗakko ya duba hotonta a hankali yake shafa fuskar wayar hawaye na ɗiga akai chan ya shiga wajen number ya duba lambar ta jiyake kamar ya kirata yayita yi mata magiya karta rabu dashi amma bazai iyaba dan bashida tabbacin zata tausaya masa, tunanin goge lambarta ne ya saukar masa kamar yadda tunanin cireta a zuciyar sa yazo wani ɓan gare na zuciyar sa yana dana sanin cusa soyayyar ta a ransa idan da ace yasan ba rabonsa bace da bazai batawa kansa lokaci akantaba bazai wahalar da kansaba tun farko dayabi kaddararsa wato malak , blocking din numbers dinta duka yayi a wayarsa sannan ya gogesu ,
*
Binta takasa jurewa jitake kamar zuciyar ta zata buga kuka take ba kakkautawa mara sauti hankalin Khadijah ya tashi cikin kiɗima take rarrashinta ta haɗi da tambayar, " wai duk mai yajawo wannan kukanne da damuwa haka binta karma ki kashe kanki a banza kifadamin mai yake faruwa ni nasandai bakida aminiya kamar ni duk da bakya shiga cikin kawaye amma ni bakya boyemin sirrinki kuma kinsan duk abinda kika fadan tamkar kinbarshi a cikinki ne dan ba mai ji , cikin wani irin yanayi har layi take saboda sarawar da kanta yake taje ta tura kofar dakin nata sannan ta dawo ta zauna tace, " Khadijah bazan boye mikiba banason aurennan na tsani Jamel ni fayez dina nakeso nayi rayuwar aure dashi , nan binta ta zauna tabawa Khadijah labarin haduwarta da fayez da kuma matsayinshi a wajen uwar dakinta malak da kuma yarjejeniyar da sukai a ta kaice, cikin matuƙar mamaki Khadijah tace, " binta karki yarda ki cuci kanki wlh karki bari wata banza chan ta sauya miki alkibilar rayuwa tasa ki ƙare rayuwar ki cikin kunci da damuwa,
" Khadijah ya zanyi yanzu karfe 8:23 kuma karfe 9:00 dai dai za a daura auren tayaya zan kuɓucewa wannan auren sannan baza a shiga kotuba sai 10:00 bayan an daura kenan , shiru Khadijah tayi tana tunanin chan tace , " ana samu abbanku ya fito to take zaki iya tarwatsa wannan maganar auren , kuma jim kaɗan tayi tana tunanin wazai taimaketa chan ta tuna da malik cikin sauri ta ɗau wayarta tana cewa , " na tuna na tunashi yayana ne kadai zaisan yadda zaiyi ya taimakeni, khadija na tambayar wanene binta bata iya bada amsaba dan ta dannawa malik kira ,
Yana ganin kiranta ya ɗauka ba batun gaisuwa tana kuka tasanar masa da yadda sukai da malak cikin mamaki yake, " kai har ita wacece zatai miki auren dole lallai ma yarinyar nan abin nata ya wuce yadda nake tunani towai ma meyasa baki faɗan tunda wuri ba?, cikin muryar kuka tace, " yaya inason Abbana ya shaƙi iskar yanci bazan iya jure ganinsa a gidan yariba, " ok kina jina karki damu karki wani tashi hankalin ki badai karfe 9:00 dai dai za a dauraba ba ni nasan mai zanyi baza a daura aurenba kuma malak bazata san ba a daura ba har sai mahaifinki ya fita, wani irin sanyi binta taji aranta batasan sanda ta tsugunna tanata gidiyaba kamar tamai sijjada ta waya, mamace ta banko ƙofa ɗauke da wani dan datsetsan leshi a hannun ta da akwatin kayan kwalliya dasu turare da sarkoki cikin mamaki tace, " dawa kike waya, kallon wayar binta tayi a tsorace bakinta yana rawa tace, " ya yaya ne, " wane yaya?, mama ta daka mata tsawa Haɗi da kwace wayar ta duba taga ansa yaya Malik taja wani dogon tsaki tace, " godiyar me kike masa?, Khadijah ce tayi saurin cewa, " lah mama kuɗi ya tura mata gudummawa shine take masa godiya, kayan ta ajiye akan bed tace " mai gyaran jikin bazata samu zuwaba maza gamai kwalliya tazo zatai miki ki shirya kisa kayan lokaci zai kure,
Ba musu ta karɓa dai dai lokacin da mai kwalliya tayi sallama sukace ta shigo ta samu waje ta zauna a gurguje binta ta watsa ruwa tazo ta zauna aka fara kwalliyar,
Sai duba agogo take kowane minti tare da bugun zuciyar ta yake tafiya dan gani take lokacin yana gudu kamar acire tara daga lissafin agogon duniya haka takeji,
*
Ammee na zaune a kujera ta kalli suhaima tace, " wai kwa malik ya kiraki a waya?, " hmmm Ammee har yanzu dai shiru kike ji nifa gani nake hajiyarsu kamar bataso, " taya zataso yar baƙin ciki nadaɗe da sanin hafsa bata kaunar a halina badan malak ba da ko haɗuwa mukai a hanya babu wanda zai tankawa wani saboda kiyayyar da take nuna mana , autace ta zauna kusa da Ammee tace, " wai kuwa Ammee bakyajin komai idan kikaga hafiza ta shafe watanni bata wai wayi gidaba?, Harara Ammee ta daka mata tace, " to uban me zanji tunda ta zabi zama da mutsiyacin mijinta ai bawani mai kima saishi taje chan ta karata,
Tara saura munti biyu jamel ya kirata lokacin sun gama shiryawa ita da Khadijah sunyi kyau abinsu kowa sai buɗa yake biki ya dau zafi kamar daman an shirya masa gida ya cika da mata makotansu, " hello ina jinka, tace murya a ɗan dashe, cikin walwala yace, " yauwa mun ƙaraso yanzu ma haka muna layinku motocin mu sunyi parking, wata iriyar faduwar gabace ta ziyarce ta cikin dauriya ta dake tace to, gidan tuni ya kachame da shewar ga ango yazo ,
Iyayen amarya da abokan arziki dana angone suka dunguma suka tafi babban masallacin dake unguwar nesa da gidansu binta kadan dan a ɗaura auren,
Basu da yawa sosai kasancewar litinince wasuma basu hallaraba sai tsegumi suke wannan wane irin aurene ran Litinin
Manya sun zazzauna liman ya iso anfara addu oi za a ɗaura Aure kenan akaji jiniyar motocin yan sanda sun karaɗe masallacin kan kace kwabo rundunar guda sun kutso cikin masallacin aka dakatar da komai aka sawa ango da wakilansa ankwa aka cusasu a motar yansanda haɗi da karbe wayoyinsu aka tafi, sallallami jama'a suketa yi wakilin binta Wato kanin babanta ya rike baki yama rasa ta cewa nan dai liman ya bawa mutane hakuri sannan ya sallami kowa,
Mutane sai tofa albarkacin bakinsu suke wasuma daga Wajen suka wuce gida yan tsirarine suka ƙarasa gidansu amarya mutane na ganinsu suka fara fito da abinci ana raba musu,
Kawun binta ne ya kira mama gefe dan ita yafi sabawa da ita ya gaya mata duk yadda akai awajen daurin auren cikin takaici tace, " duk yadda akai tuggun tsinanniyar yarinyar nan ne binta batasan auran shiyasa kasan mai zamuyi musu muce an ɗaura auren in yaso idan aka sakoshi daga hukumar sai a ɗaura a boye batare da ta saniba kuma koda ubanta ya fito an jima ace masa an daura, amsa mata kawu yayi tadau kuɗi dubu goma ta bashi sannan ta fidda kuɗi dubu hamsin tace ya bawa binta a matsayin sadakinta,
Binta na zaune cikin zullumi taji sallamar kawu cikin gidan yana ta kwala mata kira yana cewa, " Allah ya yarda alkhawarin Allah ya cika an ɗaura Auren Fatima binta da angonta Jamel, wani ras ras binta taji kirjinta na yi har tun tuɓe take ta fito tsakar gida tayi kasake ta kasa cewa komai kawai so take taji ya maimaita danta tabbatar da abinda kunnuwanta sukaji ,
Aikwa mai maitawa kawu yayi dan danan mata aka hau buɗa itadai gaba ɗaya taji kamar an zare mata laka kukanma ta kasa wani irin lagaf taji jikinta yayi mata kawai sautin an ɗaura ne keyi mata yawo a ka
Ƙarasowa kawu yayi yana washe baki yace, " mu shiga daga ciki yar albarka mu tattauna shiga tayi ya bita ɗaki ya zaro kuɗi dubu amsin ya danƙa mata yace sadakinta ne sai da ta ƙare musu kallo sannan ta raya aranta ta tabbata yanzu ita matar Jamel ce wani irin kuka mai ciwo ta fashe dashi har saida ummah ta shigo tana rarrashin ta sannan kawu ya sanar dasu an kama jamel amma bai faɗa musu harda waliyansa aka kama ba,
A gurguje mama ta shirya ta leko ɗakin binta taga Ummah na rungume da binta sai rarrashin ta take ta ƙaraso wajan su ta zauna tace, " nizan ƙarasa wajen shari ar nan idan Allah yasa wahalar mu ta ƙare zan dawo dashi, Ummah taso taje amma saboda baƙi ta fasa mama ta tafi,
✍🏻 mai alƙalamin zeenare
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf
zeenariya
__________________________________
GARGAƊI
Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page ( 34 )
Alhamdulillah zaman kotu yazo da sauki dan kiri kiri mrs Tahir tasa lauyanta ya janye kalamansa na nuna hujjojin da ba tabbas akan malam musu, kotu ta wanke mahaifin binta sannan take ta bawa ɓan garen mai ƙara umarnin su bawa malam musa 2 milion saboda ɓata masa lokacin da akai da kokarin liƙa masa abinda bai aikataba, take mrs Tahir ta bada kuɗin aka ƙarƙare shari ar aka sallami malam musa,
Cikin farin ciki Abba suka shigo gida binta