Showing 27001 words to 30000 words out of 67181 words
Chapter 10 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx
ta fito tana musu sannu da gida suka amsa daidai lokacin aka kwalla kiran sallar magriba kowa ya nufi sashinsa itama binta ta daura al wala,
Saida gari yafara duhu Abba ya shigo mama ta shimfiɗa tabarma aka kawo abin taɓawa ummah ta fito, bintama data dade da idar da Sallah tana kwance tana chatting da fayez taji Abba na kwada mata kira da sauri ta fito tazo ta zauna taga sai fara a suke dukansu ga kuɗi a gaban Abba yan dubu dubu a daure da kyauro, zama kawai binta tayi tana tattara nutsuwarta gu guda Abba yasha ruwa yayi hamdala ga Allah yace, " alhamdulillah gaskiya binta yarannan ya cika ɗan halak, binta na murmushi tace, " Abba wanene, Abba ya mance sunan kira yake, " ɗan gidan malam sani ai babansa tsohon abokinane tun muna dako lokacin ina saurayi ban aure koda ta kwararkiba gaskiya naji dadin wannan haɗin gashi ta dalilinsa naga tsohon abokina dana daɗe ban ganiba sama da shekaru kusan talatin yau gashi sanadin ƴata maganar aure ta kawosu,
Cikin mamaki da rashin fahimtar wani sashe na maganar Abba binta ta gyara zama tace, " Abba maganar auren wa?, ummah ce ta kalli binta tace, " aurenki mana ai ya turo iyayen sa sun kawo kuɗi Haɗi da tambaya kuma an bashi,
wani irin zabura binta tayi dan danan gumi yafara karyo mata cikin yanayi na tashin hankali tace, " Abba wa kuka bawa ni ?......
✍🏻 zeenariya
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf zeenariya
WhatsApp number
+218912472599
__________________________________
GARGAƊI
Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (17)
Fuskokin su Abbane suka sauya cikin daure fuska Ummah tace, " ban gane wa aka bakiba?, cikin ruɗewa binta tajuya ganinta ga Ummah tace, " ummah kiyiwa Allah ki faɗamin wanda yakawo kuɗin aurena?, ummah najin haka tabuɗe baki zatai magana kenan Abba ya dakatar da ita yace, " binta wa kika kawomin kikace kinaso kuma kikace ya shirya aurenki, binta najin haka takuma gigicewa zamanma taji ya gagareta ta durƙushe murya na rawa tace, " Abba kana nufin jamel?, kai Abba ya gyada mata tuni hawaye suka fara bin fuskar ta cikin wani irin yanayi jitake kamar ta ɗaga hannu tasa aka ta kurma uban ihu amma ba dama tashi tayi tana rike dakanta ko ganin hanya batayi sosai saboda hawayen dake fita a idonta ba kakkauta wa , tana isa ɗakinta ta rufe kofa ta nemi gu ta zauna a lokacin suyar da kirjinta yake mata ya karu sosai tarasa inda zatasa kanta dabarar sallalami ce tazo mata take tafara kiran innalillahi wa innah ilaihirraju un ,
Yanayin da binta ta shiga ya tabbatar wa dasu Abba akwai matsala musamman ma data tashi cikin yanayi na damuwa ummah ta kalli Abba tace, " kukafa naga tanayi to ko batason jamel ne?, Abba cikin yanayi na hassala yace, " oho mata ni mamaki ma nake nadaisan binta tun tana yarinya bata magana biyu, tsaki mama taja ta taɓe baki tace, " ku kirata kuji menene matsalar me takewa kuka aurenne bataso ko jamel din, jinjina kai Abba yayi yace, " kubari gobe zan zauna da ita zanji koma menene ,
A ɗaki kuwa binta tunanin kiran Jamel ne yazo mata ba shiri talalubi wayarta ta shiga danna masa kira cike da tsantsar ƙaguwa ya ɗaga sai dai har wayar tagama ringing bai ɗauka ba cikin fusata ta kuma kira tanata kai kawo takasa nutsuwa kamar daga sama taji ya ɗaga yace, " hello , jikinta yana rawa tace, " he hello jamel mai yasa mai yasa zakamin haka jamel kasan irin bala in da kakeson jefani kuwa ?, ata bangaren jamel yanajin haka yayi murmushi yace, " ni bana magana biyu shiyasa nayi miki haka kuma aure nidake wlh ba fashi tunda har manya suka shiga dankin ga namiki shiru a tunaninki zan bari wanchan tsohon dan iskan ya lalata miki rayuwa ne?,
Binta kuka ta fashe dashi chan ta zube kasa tana makale da wayar a kunnan ta tace, " dan Allah jamel kayi hakuri karabu dani wlh bazan iya aurenkaba tunda na amsa maka ina sonkane saboda tausayin ka dan Allah nima ka tausaya min ka rabu dani wlh bazan iya aurenka ba bana sonka jamel,
wata irin gigitacciyar tsawa jamel ya doka mata wadda tasa hanta cikinta kaɗawa da kakkausar murya yake mata kashedi haɗi da rantse rantse babu abinda zai hana aurensu, harya kashe wayar binta tsananin mamakine cunkus a ranta na jamel kanta kawai take tambaya daman haka yake masifaffene bai iya magana ba taya rayuwar ta zatazo dai dai da tasa,
Ƙwonƙwaso kofar taji anyi dai dai lokacin da kiran fayez ya shigo wayar ta ayanayin da take bazata iya ɗaga wayarba hakan yasata danne wayar gaba ɗaya ta kasheta dai dai lokacin da bugun ƙofar ya tsananta, da sauri ta mike taje ta buɗe Ummah ce tashigo ta tsaya tana ƙarewa binta kallo tace, " binta nakasa gane meyake faruwa faɗamin gaskiya bakida kamar ni duk duniya,
Zama binta tayi kan karamin bed ɗinta hawaye na surara a fuskarta hakika ummah tayi gaskiya bata chanchanci a ɓoye mata komai ba cikin yanayi na damuwa tace, " ummah bashi nakeso ba wlh raban dayayimin magana an kwana biyu harna fara mantawa dashi kwatsam sai yazo ya nemi aurena Abba kuma bai jira jinta bakinaba ya anshi kuɗin aurensu, jinjina kai ummah tayi tace, " babbar magana , zama tayi kusa da binta ta dafata tace, " haba binta yanzu saboda haka kika kulle kanki a ɗaki kiketa gursheken kuka wannan fa abu mai saukine Abbanki bazai taɓa yi miki auren doleba kinacewa bakyaso nasan mayar masu da kudinsu zaiyi ,
Wani irin sanyi binta taji aranta hakika uwa rahamace duk tsanani zata nema maka sauki cikin wani irin jin daɗi binta ta rungume ummah tana cewa, " nasan kina sona ummah ta bazaki bari amin auren doleba, ummah na shafa bayan binta alamar rarrashi tace, " indai kuwa ina numfashi,
*
Kira kan kira taketa masa baya ɗauka, sauke wayar tayi ƙasa tana cije baki hannu ta miƙa ta ɗauki cup glass ta ɗaga ta shenye ragowar lemon dake ciki ta aje kofin ta fito, a falo taga Malik zata fita yace, " ina zaki?, banzan kallo tayi masa ta yatsuna fuska tace, " ko ubana bai isa yayimin wannan banzar tambayar ba idanma yayimin to ba dolane saina bashi amsa ba,
Malik baiyi mamakin jin abinda tace ba hakan yasa ya tashi yana gyara rigar jikinsa yace, " Malak bantaba ganin yarinya irinki ba ina jiye miki tsoran yadda rayuwa zatai dake nan gaba wlh tallahi iyakarki tana daf da zuwa karshe, juyowa tayi ta kalleshi a fusace tace, " na daɗe da sanin kai makiyinane bari kaji har yanzu ban juyo kanka ba shiyasa kake abinda kakeso idan har na maida hankali akanka, tafaɗa tana nunashi ta jinjina kai ta cigaba da cewa , " zaka shiga tashin hankalin da zama gaban iyayenka sai ya gagareka, mom ce ta sakko tana cewa , " to tabba tacciya yayan naki kike faɗawa wannan kalmar malak kibi duniya a hankali fa, mom ta faɗa tana nuna ta,
Malak maida ganinta tayi ga mom ta saki murmushin takaici tace, " banida lokacin ku yanzu inada abinyi kuma babu yadda zakuyi dani dole sai gani sai hange, takareshe maganar tana tsaki ta juya tana wata irin tafiya ta rashin kunya jitake kamar ta tsaga kasa karan tsinin takalmin ta kawai ke tashi,
Dukansu kallon ta suke saida ta fice mom ta zauna tana ɗaukar rumot tace, " wani lokacin sai nadinga jin kamar bani na haifi malak ba saboda a bubuwan da takemin duk lalacewar ɗa bazaiwa iyayensa haka ba , cikin damuwa malik yace, " mom nifa duk papy nake dorawa lefin lalacewar yarin yar nan, " hmm Malik halin malak fa natane na ƙangin kanta bawai gatane yasata zama haka ba idan da dan gatan da papy yake nuna matane to da kaima irinta zaka zama kofiye da ita tunda kaine na fari irin gata dajin daɗin da muka nuna maka wlh malak bata sameshi ba, jinjina kai malik yayi yace, " gaskiya ne to Allah ya kyauta ya shirye ta,
Malak tana tuƙi tana kiran fayez bai ɗaukaba rannan nata a matukar ɓace kamar ta tashi sama haka takeji Allah Allah take taga takai inda ta nufa,
Awani katafaran guri daya kayatu da fitulu kala kala tayi fakin gurin tsit ba hayaniya sai daidaikun mutane yawanci yan mata da samarine, ciki sosai ta shiga wajen wani kayataccen falo ta zauna tayiwa ɗaya daga cikin ma ai katan wajen magana, chan aka kawo mata kwalaben giya guda biyu madai daita da glass cup sai ruwa da kayan marmari , ajiye wayarta tayi agefe ta zuba giyar a cup takafa a bakinta saida ta shanye tas takuma zubawa tasha
Gibtawa yayi zai shige ya hangota chak ya tsaya yanason tantancewa itace , jim kaɗan yayi yana nazarin ƙarasawa bayan ya tabbata itace, cikin nutsuwa ya ƙarasa kusa da ita ya zauna, juyowa tayi ta kalleshi duk da tana cikin damuwa hakan bai hanata cewa , " abokinmu , waheed har yanzu mamaki yake naganin tana shan giya cikin damuwa ya matsar da kwalaban daga kusa da ita yace , " wannan rayuwar bata dace da mace kamarki ba ,
Shiru malak tayi chan hawaye suka fara bin fuskar ta cikin dauriya da zafin da takeji a zuciyar ta tace, " yazan yi bana ganin rayuwata nada wani amfani indai bazan sameshi ba, kallon ta yayi cikin tausayinta yace, " kina nufin akan fayez zaki lalata rayuwar ki kefa musulmace yar musulmai, saurin ɗaga masa hannu tayi tana jinjina kai tace, " shi a binda yakemin dacewa ne ai duk abinda nayi damuwar sace tasa
✍🏻 zeenariya
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf zeenariya
WhatsApp number
+218912472599
__________________________________
GARGAƊI
Ban yarda a juyamin labari ta kowace sigaba
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (18)
Wutar kaunarsa kullum ƙara ruruwa take a zuciyata yayin da shi kuma wutar kiyayya ta take kuma ruruwa a zuciyarsa kullum rayuwa ta baya take komawa yayinda shikuma yake sake gina tasa rayuwar shin ka gayamin menene laifina danna nuna masa soyayyah ? menene kuskuran da zai hana fayez aurena ? shin a wane dalilin tun farko ya ginamin soyayyar sa nataso cikinta, tunda tafara magana waheed ya kafeta da ido yana fahimtar tsantsar damuwar da take ciki, ajiyar zuciya ya sauke yace, " malak hakika na fahimceki kuma shima na fahimceshi idan mukabi komai a tsanaki za a samu mafita amma dole saikin bani hadinkai dan nasan fayez yanada burin aurenki ,
*
Ummah nafita binta ta ɗaga hannu sama tayiwa Allah godiya, buta ta ɗauka tayi alwala ta dawo tayi sallah sai da ta shafa addu'a taja wayarta tana daga zaune cikin tausayinsa ta shiga message din da taga ya turo mata " ( zuciya ta bazata taɓa bawa ruhina damar nutsuwa ba idan banji muryarki ba, ina cike da kewarki ina cike da ɗokin san jin Muryar ki acikin kowace rana zun zurutun kaunarki ce take nunkuwa a raina fiye da yadda fatar bakina zata iya misaltawa zanso ki kasance cikin bani kulawa domin gujewa faɗawa wahalar so sannan inaso kisa a ranki ba zan taɓa chanza ra ayina akanki ba duk rintsi duk wuya nima dan Allah ki toshe kunnuwanki ki ƙara ƙarfafa zuciyar ki karki yadda ayi nasarar rabamu kota wace sigace , samunki a rayuwa tane ya fahimtar dani zahirin so, bissalam na barki lfy abincin ruhina ) wani irin tattausan murmushi tayi daidai lokacin da kwalla tasamu damar gangarowa kan kuncinta cikin yanayi na shaukin soyayyar sa ta danna masa kira,
Yana ɗaga wa yayi hamdala ga Allah yana mai furta, " ninasan bazaki taɓa iya bacci ba batare da kinji murya ta ba , murmushi tayi tace, " taya zan samu nutsuwa batare da tabbatar wa kana lfy ba kowane minti sai tinaninka yasamu damar kutsawa cikin ƙwaƙwalwa ta, duniyar soyayyah suka lulu sam Binta bata faɗa masa an kawo kuɗin aurenta ba dan batasan tashin hankalin sa,
*
A gogon hannun sa ya duba yaga ƙarfe ɗaya na dare, miƙewa tsaye yayi yace, " taso muje na kaiki gida inyaso gobe zan kiraki nasanar dake yadda mukai dashi, miƙe tayi a hankali duk da tafara buguwa saidai batai shawuwar dazata hargitse ba, sata yayi agaba tana tafe yana binta a baya saida sukazo wajen parking yace, " muje na ajiyeki a gida dasafe zansa akawo miki motar taki, girgiza masa kai tayi tace, " aa daka barshi ai zan iya tukin, kai ya girgiza mata alamar aa ya karbi mukullin hannun ta yaje ya hau tasa motar ya ƙaraso gabanta yayi parking ta shigo suka tafi,
Suna tafe suna hira har ya kaita ƙofar gidansu zata fita yace, " kin manta baki bani no din ba, murmushi tayi taɗan watsa gashin kanta dake kwance akan kafadunta ta mika masa hannu ya bata wayar tasa tasa masa number sukai sallama tashiga gida,
Washegari da safe binta ta shirya bayan ta karya Abba ya kirata ɗakinsa daga ita sai shi yace mata, " jiya nayi miki magana akan yaronnan daya kawo kuɗin aurenki banji kincemin komaiba mai kike nufi yanayinki ya nuna akwai matsala, binta jitai mummunan faɗuwar gaba cikin yanayi na tsoran yadda Abban nata zai karbi korafinta tace, " Abba banason jamel, saurin kallon ta Abba yayi sai yayi murmushi yace, " daman nasan haka zakice to fadamin dalilinki na cewa bakya sanshi bayan kuma ke kika gabatar min dashi da kanki,
Rasa mai binta zatace tayi chan ta buɗe baki dakyar murya kasa kasa tace, " Abba inada wanda nakeso, haɗe rai Abba yayi lokaci ɗaya kamar bashiba yace, " waye shi wanda kikeso ɗin, muryar binta na rawa tace, " fa fayez, jinjina kai Abba yayi yace, " to indai ni na haifeki na isa dake bazaki aureshi ba wanda na zaba miki Jamel ne kuma kisa a ranki mutuwa ce kawai zata iya rabaku, saurin dafe gefan zuciyar ta tayi tanajin yadda take mata bugu da karfi cikin tashin hankali ta fashe da kuka ta tashi daga zaunen da take ta tsugunna akan gwaiwowin ta tana haɗe hannaye alamar roƙi tace, " Abba na rokeka ka taimakamin ka barni na auri faye...., bata ida rufe baki ba taji ya wanketa da zazzafan mari, agigice ta tashi ta fice dagudu kai tsaye ɗakin ummanta taje ta durkushe tana sakin nannauyan kuka, Ummah dake kan gado da sauri ta sakko ta nufota tana cewa, " lafiya keda wa meyake faruwa ? , rungumeta Binta tayi tan cewa, " ummah ki taimaka min Abba zaimin Auren dole wlh bazan iya rayuwa da jamel ba, ummah najin haka tama rasa ta cewa kawai sai ta tashi ta fice, kai tsaye dakin Abba ta nufa tasameshi zaune itama ta zauna tace, " lafiya malam ya kukai da yarinyar nan, kwafa Abba yayi yace , " ina daukar binta mai hankali ashe wawuyace tayaya zata ɗorawa kanta abinda yafi ƙarfin ta wai wannan ɗan masu kuɗin takeso , rike baki ummah tayi tace , " eh gaskiya dole kayi faɗa tayayama za ai ayi wannan hadiyn bayan muda kanmu matsayin masu hankali munsan akwai matsala ,
Saida Ummah suka gama tattaunawa sannan tadawo tafara rarrashin binta acikin rarrashin nata batace za a fasa aurenba kuma batace baza a fasaba hakuri kawai taketa bawa binta da nasiha, shiru binta tayi chan taga lokaci na tafiya a sanyaye tace, " ummah bari natafi aikina kinga namakara, " toba matsala Allah yayi miki albarka, tashi tayi ta saɓi jakarta ta fice, abakin kofar gida taga mota tasan tagidansu malak ce sai dai batasan wanene a cikiba hakan yasata ƙarasawa batare data kwankwasa glass dinba aka bude , wani irin mugun kallo tayi masa tace , " meya kawoka ?, murmushi yayi yace , " nazo daukyar matatane koyau bazaki aikinba, kada kai kawai binta tayi chan kuma sai ta sake tunani batare datace komai ba ta buɗe motar ta shiga shima bai ce mata komai ba yaja motar,
Sun fara tafiya tace masa, " Jamel meyasa kakeson zamemin matsala a rayuwa ta ni bance ina sonka ba dan na aureka nafaɗa ne dan naragewa kaina raɗaɗin danakeji, shiru Jamel yayi batare daya kalletaba yace , " soyayyah ta dake itace mafi alkhairi sama da soyayyarki dashi , juyowa tayi tana kallonsa tace ," fayez bazai taɓa zamemin matsala ba saboda yana sona kuma ina sonshi, wata wawiyar tsawa ya daka mata yace , " idan ina tare dake karki kara ambatar sunansa banaso natsaneshi na tsani jin zanchansa , tsit binta tayi dan batada tacewa jamel gaba ɗaya ya chanza yakoma mara hakuri mara tausayi daɗaɗan kalaman dayake mata yanzu duk babu datayi magana sai tsawa kamar ya rufeta da duka,
Har cikin gidan yashiga yayi parking da sauri ta saɓi jakarta ta fito kanta a ƙasa tana goge hawaye jitai tayi karo da mutum lutayi zata faɗi taji an tareta cikin wani irin zafin nama idonta ta ƙanƙame chan hancinta yafara jiye mata ƙamshin sa da sauri ta buɗe idonta ta ganshi shima itan yake kallo wani irin daɗi yakeji a ransa, miƙewa tayi tana sunkuyar dakai fuskarta ta ɗauke da murmushi tace, " barka da safiya, kallon ta yayi shima yana murmushin yace, " barka dai , buɗe baki Binta tayi zatai magana sai taga malak tsaye a bayan fayez ta harɗe hannuwa, jakar hannunta ta ƙanƙame tazame jiki tabar wajen , jamel dake tsaye abayan bintane suka hada ido da fayez cikin tsantsar