Showing 12001 words to 15000 words out of 67181 words
Chapter 5 - HUDUD (iyaka) Book Complete By Zainab Ahmed Yusuf Zeenariya.docx
tafashe da kuka tacigaba da cewa,
" banason hantara kuma banason kyara tsoran danakeji ɗaya ne karnaje na tadda irin wannan matsalar a family dinka wlh Allah yasan ina sanka amma bazan taba iya jure wulaƙanci ba kuma dayawan ku kumasu kuɗi haka kuke, innalillahi ya furta ya miƙe tsaye cike da takaici yace, " awane gida akai mike haka kuma wacece yarinyar datai miki haka?,
Itama binta mikewa tayi tace, " sanin hakan bashi da wani amfani awajenka, ƙoƙarin haɗiye fishinsa yayi ya ce, " okay naji zauna muyi magana, zama tayi shima ya zauna yace, " ki kwantar da hankalinki kiyi zamanki agida nibana bukatar komai na hidima daga gareki duk abinda kikeso nizan miki amma dan Allah kidaina zuwa aikinnan mace kamar ke bata chan chanci yawon aikiba har asamu mai wulakanta min ke, girgiza kai binta tayi tace,
" bana bukatar komai daga gareka fayez ni ba kuɗi nakeso ba kai nakeso dakuma samun zaman lfy da ingan tacciyar soyayyah daga gareka,
Nan hirar tasu ta koma ta zunzurutun soyayyah cike da shaukin juna, sosai fayez yake nuna mata irin masifaffiyar kaunar da yake mata aranshi yaso yau yabata labari gameda yadda yayiwa malak alkawarin aurenta tunkan yasan binta sannan ya nusar da ita hanyar dazasubi ta salama sushawo kan iyayensa suyarda yafara auren binta, sai tsoro da fargabar yadda zata fahimci maganar ya hanashi sanar da ita bayaso ta saɓawa fahimtar sa tayi tunanin ko bazai auretaba yaudararta yakeson yi tunda iyayensa basu aminceba sun zaɓa masa mata, tunanin hakan ne yasa fayez ya danne damuwarsa bai sanar mataba har sukai sallama yatafi
Yau da daddare bayan su Abba sun dawo ana zazzaune a tsakar gida anashan iska binta take bawa su Abba labarin malak uwar dakinta duk da ta boye muguntar da take mata saboda kar iyayen nata suhanata zuwa aikin, ummah dake kishingide ce tayi dariya tace, " ai binta kece baki saniba duk masu kudin nan haka suke kallon talaka kedai fatan danake miki Allah yasa wannan mai kuɗin da kika samu da gaske yake azo ayi aurennan da wuri kema kije naki gidan ki baza mulki yadda ranki yakeso, karamin tsaki Abba yaja yace, " nifa yaronnan yafara suremin kusan kullum saiyazo zance idan da gaske yake ya fito mana, kallon shi mama tayi tace, " yo banda abinka malam dududu yaushe aka fara soyayyar dazaka matsu ya fito kofa sati uku basukaiba mebi wasu yan shirye shiryen sa yake ,
" wane shiri kuma wannan zaiyi yaronfa ba irin kananan samarin nan bane da girmansa ni nayi mamaki ma dayace bai taɓa aureba dan wannan kina ganinsa yayi talatin, cewar Abba kenan mama da ummah suka tuntsire da dariya ummah tace, " banda abinka malam ai ƴaƴan masu kuɗi haka suke basa aure da wuri sai angaji da karatun ankama aikinyi angaji da tara dukiya tsurfa iri iri sannan daga baya sai ace aure, binta nagefe tanajin tattaunawar tasu akan aurenta ta wani ɓangaren dadi duk ya lullubeta dan ta fuskanci iyayen nata sunason fayez kuma a shirye suke su aura mata shi ,
____________
Bayan sati biyu
Soyayya da shakuwa mai karfi ta daɗa kulluwa tsakanin binta da fayez, ata ɓangaran aikinta harta saba da wulakancin malak tadaina damuwa da duk abinda zatai mata kuma tana takatsan tsan da aikinta abinda oganniya malak takeso shi take mata momin malak sosai take nunawa binta ƙauna harkayan kwalliya da kyautar kuɗi take mata haka papyn malak ma mutum ne mai san jama'a gason a girmamashi sannan ganin yadda takewa yarsa biyayya da kankantar dakai yasa yake sakar mata fuska suyi wasa da dariya yana kiranta da yarsa , ta ɓangaren Malik ma mutumin kirkine yana matukar girmama binta sau tari yakan kaita har gida da kansa hakan yasa binta take kiransa da yaya Malik
_
Yau tun da safe malak take kiran fayez yaki ɗagawa zuwa wannan lokacin a matukar fusace take hakan yasa koda binta tashigo batabi ta kanta ba tana gaisheta bama ta amsaba,
Tsab binta tagama aikinta ta fita zuwa ɗakin datake zama na lailah kacha kacha yau ta taddashi ganin bata gajiba yasata ƙoƙarin gyarawa saidai batasan mazaunin wasu kayanba kawai dai tasasu a inda take ganin yadace bayan ta gyara tsab ta zauna taɗau wayarta tana dannawa lailah tashigo tana zuwa taga dakin a gyare taje gefan gado tazauna tana taɓe baki ta mike inda take aje turarenta taga bata ganiba kamar jiran kadan take tace, " kutumar ubanchan ke ina turarena ko an dauka za akai gidan to wlh bazata saɓuba maza maza fitomin da abina,
Cikin tsantsar mamaki binta ta tashi tsaye ta ƙarasa kusa da ita tace, " ke ai bakida abinda zangani nayi sha,awarsa kazama irinki idan kina chin ƙasa ki kiyayi ta shuri bar ganin uwar dakinki tana cimin mutumci ina kyalewa nima kyallece , binta takarashe magar tana tsaki taje tabude Durowa tafito da turaren ta wula mata kan bed haɗi da cewa," ga tsiyarki nan, tsaki lailah taja tace,
" binta bar ganin shishshigin ki yasa kinyi sabo da yan gidannan wlh tallahi rana ɗaya madam zata juyo kanki sai kin tsani duk wani mai hannu da shuni na duniyar nan , dariya binta tayi tace, " to uwar hassada na lura daman bakinciki kike da yadda nake mu amala da mutanan gidannan to bari kiji babu yadda zaki iya dani dole kigani ki kyale kuma da kikemin fatan malak ta wulakanta ni akan me menayi mata da har hakan zata faru ke mai mugun halima da kike shiga abinda ba ruwanki malak batai miki rashin mutumcin ba sai ni ?, harara kawai lailah ta bankawa binta ta ɗau turarenta ta fesa ta fice,
Buɗe data binta tai tabawa fayez amsar message dinsa tana murmushi ganin yana online bai maido mataba yasata tunanin aiki yake kuma tasan baya kashe data, kashe tata datar tayi ta kira kawarta khady sukasha hirar duniya sannan ta katse lokacin data duba agogo taga sha biyun rana tayi tashi binta tayi da ɗan hanzarinta dayake yanayin zafine tasan a daidai wannan lokacin idan malak tana gida lemo mai sanyi ake kai mata, kitchen ta wuce ta dakko glas cup dadan kyakkyawar silver ta ɗorawa mai ruwan gold tana nufo ƙofar ɗakin taji malak na cewa,
" bazan laminci wannan ba saboda kai na ɓata lokaci na nakori masu sona da gaske sai yanzu zakazo kana gayamin wasu banzayan maganganu mace kamar ni malak khabeer muhd namiji zai wulakanta, binta najin haka takarasa bakim ƙofar a hankali ta tsaya batare data taɓa ƙofarba ta kasa kunne sosai da alama malak yau ta kwabe da saurayin nata wanda akeji dashi kamar tsoka daya amiya,
" babu abinda zan saurara wlh indai ban aurekaba babu wata ya mace data isata aureka dagani har kai saidai mumutu ba aure ɗan hakal kafasa nidakai da tsinanniyar tauraruwa mai wutsiyar dakeson rabani dakai, binta najin haka tarike baki cikin jimami aranta tace lallai wannan budurwar saurayin madam malak ta ɗebo ruwan dafa kanta,
Alamar tafiyar da Binta tajine yasata saurin tura kofar dakin da sallama abakinta daidai lokacin da malak tayi wurgi da wayar hannunta cikin tsananin ɓachin rai da fusata, binta jidai kamar ita aka buga da bango dan tsoro yau taga malak a yanayin fishin da bata taɓa ganinta cikiba fuskarnan harda hawaye, wani bangaren na zuciyar binta tausayin malak yakamu dashi ta saisaita murya haɗi da ƙarasawa kusa da malak cikin sigar rarrashi ta dafa kafaɗar malak tace, " haba uwar ɗakina hakuri zaki kefa jarumar mace ce mai aji dan Allah ki kwantar da hankalinki, cikin mamaki malak ta ɗago jajayen idonta ta kalli binta sannan takalli kafaɗarta data rike , binta naganin irin kallon da malak tayi mata dasauri ta cire hannunta daga dafen datai mata sannan tabata hakuri, halin da malak kecikine yahanata kartawa binta rashin mutumci,
Wunin yau gaba ɗaya malak bata fitaba itadai binta tagama aikinta tsab da yamma takama hanya ta tafi gida
Washegari da safe da wurwuri binta tazo tafara aikinta yanayin dataga malak yau yasha banban dana jiya yau tana cikin farin ciki ta tsantsara kwalliya kamar yadda tasaba tasa kaya masu kyau riga da sike wanda bai kai kasaba yadai rife gwaiwarta, tana cikin gyara kwalliyar fuskar tatane wayarta taɗau ringing tasaki wani kayataccen murmushi ta dau hawar cikin murya mai jan hankali tace, " kashigo ?, " to kakaraso dakina ina jiran ka , tana gama wayar ta juyo ta kalli binta tace, " ke jeki dakin lailah zanyi bako bayan minti goma kikawo mana shayi, to binta tace cikin girmamawa ta fice,
Kai tsaye fayez ɗakin malak yawuce ba laifi tayi kyau cikin tsananin nuna soyayya ta tarfeshi suka zauna a kujera suka fara tattaunawa ,
Bayan minti goma kamar yadda malak ta faɗa haka binta taje ta haɗo shayi tanufo bakim kofar dakin kamshin turaren dataji dakuma sautin muryar ne yasata tsayawa chak tanason gasgata abinda kunnuwan ta suke jiye mata
" ina mai matukar baki hakuri akan abinda yafaru jiya hakika idan namiki haka ban miki adalciba ina sonki malak kuma na amince zan aureki, wani ras ras kirjin Binta yasoma bugu da sauri ta girgiza kai tana karyata kunnuwanta wannan muryar bata fayez ɗinta bace, da karfin gwaiwa binta ta tura kofar dakin dan ta tabbatar wa da idonta zahiri
Zeenariya ✍🏼
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf zeenariya
__________________________________
GARGAƊI
Banyarda a juyamin labari ta kowace sigaba
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى الله وسلم على خير الخلق سيدنا محمد
𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 page (9)
Tana tura ƙofar idonta yakai kansa yajuya yana fuskantar malak , binta jitai kafafunta sunyi nauyi daker take jansu harta ƙarasa gabansu batare data ɗago ta kalleshi ba ta ajiye shayin a table dake gabansu ta ɗago kai a hankali ta sauke idanunta a kansa, wata muguwar jijjiga zuciyar ta tayi lokacin data gama tabbatar wa dakanta fayez ɗinta ne
Shima fayez yana cikin magana yajuyo ya kalleta chak bakinsa yarike yakasa ƙarasa abinda zai furta,
wani irin kallon mamaki malak take binsu dashi a ranta taji ta tsargu da kallon da sukewa junansu gyaran muryar da tayine yasa binta saurin dawowa hayyacinta duk da nutsuwarta bata tare da ita da sauri ta juya ta nufi hanyar fita batakai ga ƙofarba taji malak tace mata ,
" saikizo ki miƙo mana shayin, dawowa binta tayi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki hannun ta yana karkarwa ta miƙawa malak sannan shima ta miƙa masa ta fice,
Tana ƙarasawa ɗakin binta tasaki wani irin kuka mai ciwo haɗi da toshe bakinta da tafin hannayen ta biyun gudun kar a jita,
a ɗakin malak kuwa yafez kasa cewa komai yayi yalula duniyar tunanin kallon da binta zatai masa a yanzu, malak ce tayi magana taji yayi mata shiru hankalin sa yana wani wajen hannunta dake ɗauke da zakwa zakwan farcina ta kyasta masa a fuska yayi saurin kallon ta tace masa ," yadai, fuskarsa ya shafa cikin bayyana matuƙar damuwa a fuskar sa yace,
" ina kika samo wannan yarinyar? , murmushi malak tasakar masa taɗau shayi ta kurba sannan tace,
" yar aikinace takai wata tana aiki agidannan kagane ta ko? , girgiza mata kai yayi alamar aa ita kuma ta ƙara dacewa, " itace yarinyar daka kusa kaɗewa wata rana munfita nida kai har kake cemin Allah yazuba mata kyau, kwafa malak tayi tana murmushin mugunta tace, " ina fatan yanzu kafahimci duk wata mace mai kyau bazata ɗara darajata ba gadaishi nan wadda kayaba itace mai min goge goge da haɗan ruwan wanka,
saurin kallon ta yayi rannan nasa a matukar ɓace yace, " idan na fahimceki daman kin ɗauketa aikine dan kinunamin darajarki tafi tata?, Yar dariya tayi tana kallon jikinta tace, " eh mana kalleni da kyau taya zaka haɗa darajata data yar mutsiyata , kallon ta kawai yayi a matukar fusace yamike yafice, kafaɗa malak ta ɗaga irin ko a jikinnan nata ,
Binta wunin yau guda batayishi cikin walwala ba idanunta sunyi jajir zazzaɓi mai zafi dan danan yarufeta, koda takoma gida batacewa kowa komai ba a daddafe tayi sallah abincin ma kasa ci tayi ta kwanta, tanaji fayez yanata kiranta taƙi ɗagawa chan dai data gaji ta ɗauka tana cewa, " bakada abinda zaka gayamin fayez ka raunata zuciya ta rauni mafi ciwo ashe daman kanada matar dazaka aure kazo kayimin alkawarin aure?,
" wlh binta ban yaudareki ba abinda naketa son sanar dake kenan tsoro ya hanani Allah ya sani ina sonki malak tamkar matar cushe haka take a wajena ada na yarda da aurenta ne saboda banida wadda naji inaso yanzu kuma dana haɗu dake naji bazan iya rayuwa da watankiba, kuka sosai binta take daker tace,
" kanaso kajamin bala i fayez bazan taɓa iya kishi da malak ba batada imani zata salwantar min da rayuwata na haƙura nabar mata kai kaje ka aureta, nan fa hankalin fayez yakuma tashi
amfani yayi da raunin zuciyar binta ya tausheta ta hanyar faɗa mata maganganu masu sosa rai yabata hakuri yanemi yafiyar ta sannan ya faɗa mata duk abinda yake tsakaninsa da malak,
Ajiyar zuciya binta ta sauke duk da ta gamsu da bayanan sa amma zuciyarta takasa samun sukuni saboda tsoron abinda kaje ya dawo ganin babu yadda zatai saidai ta hakura tayi masa Afuwa tunda tana sansa,
Sosai fayez yaji daɗin shawo kanta sukai sallama, a wannan daren binta sam batai baccin kirki ba tsoranta yana yawaita idan ta tuna fayez da malak ƴan uwan junane kuma iyayensu ma ra,ayi ɗaya garesu nasan hada Auren malak da fayez,
Washegari da safe binta tatashi duk wani iri da ita ba wal wala dukansu suna zaune a dining suna karya wa suna hira jefi jefi ita takasa sa baki saɓanin kullum da a irin wannan lokacin take hira dasu suyi wasa suyi dariya,
Bayan tagama komai ta shirya tsaf fayez yakirata awaya yace zaizo ya kaita saida tace masa ba sai yazo ba amma yaki, bayan ya ɗauketa sunfara tafiya a mota yace mata, " binta mai zai hana ki hakura da aikinnan konawa kikeso zan baki, kallon sa tayi tace, " banaso ya zamana da bazarka nake rawa kabari kawai nanemi kuɗina zaifi, shiru yayi mata bai sake cewa komai ba har suka isa bakin get yayi parking ta fito wadda tagani a tsaye bakin get ce yasata kamewa cikin yanayi na tsoro da rashin gaskiya, lailah dake tsaye itama kallon mamaki take bin binta dashi ganinta a dalleliyar mota,
fayez neya fito daga motar hankalin sa yanakan binta yace, " wai har yanzu fishin kike ko Sallama bazaki min ba, a kidime binta tawaigo ta kalleshi kawai saita wuce cikin gidan batare datace komai ba, lailah cikin ruwan mamaki tayi tagumi tana jinjina girman abinda ta gani, shikuma fayez baiko bi takanta ba yaja motarsa yatafi, lailah da fita zatai saita fasa ta sallami mai adaidaitan nata takoma ciki, kai tsaye ɗakinta ta nufa tasan binta tanachan zata ajiye jakar ta, lailah nashiga tafara tafi tana cewa,
" yayi kyau sosai binta, saurin juyowa binta tayi ta kalleta tace, " lailah mekike nufi?, yar dariya lailah tayi ta ƙaraso tanawa binta wani irin mugun kallo na tuhuma tace,
" menene haɗinki da fayez mijin da madam malak zata aura ?,
Yar ajiyar zuciya binta ta sauke tarike hannayen lailah tana kallonta tace, " lailah bafa wani abin bane yaganni ne yaragen hanya dayake yaganeni yar aikin masoyiyar sace, taɓe baki lailah tayi tacire hannun ta daga na binta tace," ok naji to, daga haka tafice, wani daɗi binta taji aranta da lailah bata fahimci komai ba zama binta tayi haɗi da buga tagumi gaba ɗaya yanzu fayez bata tsoro yake idan ta tuna saurayin malak ne sai ta dinga ganin kamar yafi ƙarfin aurenta wasa da hankalinta kawai zaiyi,
Lailah tana fita daga ɗakin tayi dariya afili tafurta nasamu hanyar dazan fidda binta daga gidannan indai zargina ya tabbata akwai alakar dake tsakanin binta da fayez nice ta farkon wadda zan kaiwa malak albishir,
Bayan binta tagama aikinta taɗan fito harabar gidan dan tabawa idonta abinci sosai take ƙarewa harabar gidan kallo aranta tace ba shakka wannan gida irinsu ake kira da aldannar duniya
a tafkekiyar rumfar data ƙawatu da ado ta hango malik yana ganinta yayi mata alama da hannu takawo masa ruwa, komawa ciki tayi ta ɗakko ruwan da cup ta fito da sallama ta ƙarasa cikin girmamawa ta ajiye masa ruwan batare daya d
ɗagoba yayi mata godiya, zane taganshi yanayi na kananan kaya na maza binta tana matukar son fashion and design hakan yasata zama kusada shi tace, " lah yaya daman ka iya fashion and design?, kallon ta yayi yana murmushi yace, " eh ai sana ata kenan idan nazana sai Companyn papy dake America su buga kayan arabasu a sauran ƙasashe ,
" wow gaskiya wannan abu yayi kyau yaya nima inason nakoyi irin wannan zanen, ɗaukar wayarsa yayi yace bari ya nuna mata wani zane, nan takuma matsawa kusa dashi ya nuna mata sarƙoƙi kala kala lokacin da aka zana da bayan an bugasu haka takalma da rigunan mata dogwaye, rike baki binta tayi cikin al,ajabi tanajin inama itace take zanawa ana bugawa da kakarta ta yenke saƙa,
" kuma yaya wannan zanan kana ganin nima zan iya, rufe wayar sa yayi yana murmushi yace, " abin fikirane kuma babban kasuwanci ne dakowa yake burin yi uwar ɗakinki ma ai abinda takesonyi kenan ta kasa idan zaki iya ki kwatanta sai ki bata ta dinga siya tana biyanki,
wani daɗi binta taji aranta ta ƙudire a ranta zata gwada tagani,
Zeenariya ✍🏼
🕯️𝐇𝐔𝐃𝐔𝐃 🕯️
( 𝐢𝐲𝐚𝐤𝐚 )
story and writing by
zainab ahmed Yusuf