Showing 1 words to 3000 words out of 83501 words

Chapter 1 - DUHU DA HASKE Hausa Novels by Jiddah S Mapi.docx

19 Sep 2025

480

[09/04 à 08:05] JIDDA MAPI: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*DUHU DA HASKE*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Na

*Jiddah S mapi*

*Chapter 1*

~Cikin garin kaduna yau an tashi da zafi sosai tsananin zafin rana da kuma rashin iska me sanyaya jikin ɗan adam, duk wanda ka ganshi akan hanya sai kaga zufa a jikinshi, wani kango ne me ɗauke da ɗan karamin bola mutane suka taru a wajen kowa yana kallon cikin kangon, yara da manya tsaye amma da alama idanunsu cike yake da tausayi, wata mata ce take nishi sosai tana runtse ido a lokaci ɗaya kuma tana rike da ciki tana cije baki, babban ciki ne a jikinta wanda da alama naƙuda take, kyakkyawar mata ce duk da tulin datti da haukan da take fama dashi bai hana kyawunta bayyana ba, fara ce sal amma jikinta wani wajen yayi baƙi sabida dattin da take tare dashi na biye biyen bola, tulin gashi ne baƙi ƙirin a kanta, idanunta manya manya sai kallon mutanen wajen take dasu, gashin yayi datti sosai yana rufe mata fuska cikin ciwo take mayar da gashin baya, da alama ita kanta batasan me yake damunta ba, hawaye ne ya fara bin fuskanta ganin ciwon yaki karewa tace "ku bani ruwa"

duk mutanen suka kalli juna kowa yana tsoron zuwa wajenta domin tana faɗa sosai wani lokaci ta kan kama mutum ta daka kuma tayi dariya idan taga yana kula, wani mutum da alama matafiyi ne yace "ku bata ruwa mana naƙuda fa take kada ta mutu anan"

wani dake gefenshi yace "malam wannan da kake ganinta kowa dake wannan unguwan ya santa ta kai shida anan hakan baisa ta saba da kowa ba duk ranan da haukanta ya tashi saita kama mutum tayi ta duka kamar zata kaishi lahira, gata da karfi wallahi kana isowa wajenta idan ta kamaka ba zaka iya kwatan kanka ba, da alama bayan haukan asali tana da karfi"

mutumin yace "subhanallah kana nufin ta kai shekara shida anan? kenan anan ta samu cikin?"

jijjiga kai yayi shima cikin jin zafin abinda aka yiwa mahaukaciyan yace "tabbas anan ta samu cikin kasan mutanen yanzu babu imani, son duniya yanasa mutum ya aikata duk abinda yaga dama, gashi ciki har wa mahaukaciya wacce bata san me take ciki ba"

share hawaye mutumin yayi kana yace "Allah ya saka mata amma duk wanda yayi mata wannan abin Allah ba zai barshi ba, ba zaiji daɗin duniya ba, mahaukaciya amma zaka kusanceta harma ta samu ciki? wasu bokayensu ke sasu saduwa da mahaukata domin neman abin duniya, amma yanzu mu samu mu bata ruwa kota yaya"

mutumin yace "to shikenan bari mu jarraba"

tafiya yayi zuwa gida da shike basu da nisa, ya dawo da ruwan ha zuwa lokacin ta fara birgima a kasa tana ihu, hanunta akan cikinta fuskanta zufa yana wanke duk wani baƙi baƙin daya ɓata mata, farin fatarta yana kara bayyana, hakoranta da suke baƙi ƙirin ta haɗa waje ɗaya tana danne bakinta, da alama tana jin ciwon sosai, yaran dake wucewa sun taso daga islamiya suka fara mata ihun da suka saba kullum idan suka taso, idan suna mata tana rawa wani kuma ta bisu su ruga a guje "balarabiyan mahaukaciya taci tuwo bata koshi, ta daki malam idi"

kullum wannan wakan suke mata, tun ranan data yiwa wani duka a unguwan sunanshi malam ido yazo da niyan yin lalata da ita da kyar aka kwaceshi a hanunta, suke mata wannan waƙan, yau jin tayi shiru yasa jikinsu yayi sanyi suka tsaya suna kallonta tana kuka da murƙususu, wata yarinya karama tace "baba haihuwa zatayi?"

wanda ruwan yake hanunshi yace "eh A'isha haihuwa zatayi"

tace "baba kawo ruwan nayi mata addu'a malaminmu yace me haihuwa ana mishi addu'a a cikin ruwa"

bata ruwan yayi, tayi addu'a sosai sannan ta mikawa sauran yaran sukayi duk addu'an da suka iya, cikin dauriya mutumin ya karasa inda take da ruwan a hanunshi, aje mata yayi sannan ya juya da sauri ya bar wajenta, cikin ciwo taja jiki ta ɗauko ruwan, kafawa tayi a baki saida ta shanye tas kafin ta wurgar da kofin, a lokacin ta fara sabon ihu alaman haihuwan yazo gadan gadan, mutumin yace "duk kowa ya matsa anan abar matan kawai mazan duk su watse, hakan kuwa akayi kowa ya watse aka bar mata manya kawai a wajen, yaye zanin dake jikinta me uban datti tayi sannan ta runtse ido ta ciza ɗan karamin bakinta tayi wani irin nishi, ji sukayi kukan jariri ya karaɗe kunnuwansu, dukkansu dake hawaye atake suka fara murmushi, baba lami itace macen da tafi su girma duk a wajen, cikin dauriya ta isa inda take ta ɗago jariri ta yanke cibi sannan ta kalleta cikin murmushi tace "ƴa mace aka samu"

duk suka ce "Alhmdllh"

tana kwance a kasa kan bolan tana nishi sosai har yanzu da alama bata dawo hayyacinta ba, baba lami tace "ya kamata mu samo ruwan zafi kafin ta dawo hayyacinta muyi mata wanka"

matar dake kusa da ita tace "to"

da sauri taje gida cikin tausayi ta kawo ruwan zafi sosai tazo dashi a cikin baho, dukansu matan suka ɗaukota daga kan bolan suka sata a ruwan sukayi mata wanka sannan suka sa jaririyar ma suka wanketa, kunu suka bata tasha kafin suka sawa jaririyan nono a baki sai kuka take tayi tunda taji nono a baki tayi shiru.

suna zaune a wajen kowa ya kasa tafiya sai sharan hawaye suke, babban abinda yake ɗaga musu hankali shine basu san wani mugun ne ya aikata wannan laifin na yiwa mahaukaciya ciki ba, wannan yarinyar wani rayuwa zata yi? gashi wannan mahauciyar ba ƴar nigeria bace dan kana ganinta kaga asalin balarabiya, babu baki a jikinta ko kaɗan sannan kyawun da kuma gashin duk na larabawa ne, baba lami ta kalli matan dake kewaye dasu tace "amma anya ba zamu ɗauke wannan yarinyar ba? kada yarinyar tayi girman wahala? ba lalle tasan ta haihu ba"

duk sukace "kwarai ya kamata mu ɗauketa kada ma tasan ta haihu domin yarinyar zata girma akan bola kamar yadda itama take rayuwa anan"

tashi tayi zata ɗauke yarinyar yaji an damƙe hanunta gam, waro ido tayi tana kallonta, buɗe manyan idanunta tayi tana ganin baba lami ta washe hakoranta dake ɗauke da datti, tace "satamin yarinya zakiyi? yarinyan dana siyo a kasuwa jiya?"

girgiza kai baba lami tayi tace "A,a gyara miki ita zanyi"

murɗa hanunta tayi, saida tayi karan azaba tace "sacemin ita zakiyi"

da kyar matan suka kwace ta a hanunta, tace "duk wanda ya taɓamin ita saina karya hanunshi"

duk suka watse a wajen dan sun san halinta, tun daga wannan rana bata kara yadda yarinyar ta matsa kusa da ita koda na minti ɗaya bane, idan yarinyar tana kuka saita zuba mata ido tana dariya har ta gaji tayi shiru, nono kuma ta koyi bata dan kullum sai tasha nono, idan ta gaji da bata nono saita kamo akuya acan cikin unguwa tazo ta bawa yarinyar nonon akuyan, da haka har ta fara girma, duk sanda yara suka ganta saisu fara cewa "ƴar balarabiyan mahaukaciya, ga ƴar mahaukaciya"

karama ce sai tayi ta dariya tana rawa idan sunayi itama maman tayi ta rawa, akan wannan bolan suke rayuwansu zata kwantar da yarinyar taje ta nemo abinci me datti akan bola ta kawo musu suci, tunda baba lami ta gane tana zuwa neman abinci idan ta tafi sai tazo ta yiwa yarinyar wanka ta bata abinci kafin ta dawo, yarinyar tana girma tana kama da maman sosai, domin kuwa babu abinda ta bari a halittan mamanta.

watarana ta fita neman abinci bata dawo ba har dare, yarinyar kwance akan bola tana kuka sosai, da alama batada lafiya domin jikinta yayi zafi tana ta rawa ɗari, kankame jiki tayi waje ɗaya tana kuka me sauti, ganin babu wanda yazo wajenta ta fara bacci, da haka har gari ya waye mamanta bata dawo ba, babu wanda ya kula da hakan domin suna ɗan nesa da mutane, abinci take nema ta samu taci babu, cikin kuka ta fara cewa "mama? mama? abinci"

tana cikin kuka wani tsadadden mota yayi parking a inda take, da sauri matar ta fito daga motan tana neme neme, kyakkyawar mata ce ajin karshe a kyau, tasa farin leshi da farin siririn glass a idonta, daga ganinta kasan ta karantu sannan taji kuɗi, ganin yarinyar tana kuka ta leka cikin motar tace "my umar ka ganta wallahi tana kama sosai da wacce muka bige"

da sauri ya fito yana sa tsadadden wayarshi a aljihu, ido ya zubawa yarinyar yace "gaskiya wannan itace ƴarta Allah sarki"

atare suka karasa inda take, hanu ya buɗe mata yace "zo"

maƙe kafaɗa tayi tana kuka cikin magananta na yara da baya fita tace "mama! abinci"

hawaye ne ya cika idon matar da sauri ta share tace "ki gafarcemu mun bige mamanki a rashin sani mun kaita hospital domin a duba lafiyarta bataji wani ciwo ba, bayan anyi mata allura kowa ya fita domin ta samu hutu tana tashi ta gudu ta bar hospital ɗin, bayan mun dawo muna nemanta muka rasa inda ta shiga gateman ya bamu tabbacin ta gudu, wani muka samu yace mana yasan inda take zama harma da ƴarta yayi mana kwatance amma gashi har yau bata nan da alama ta tafi wani wajen ko kuma taji ciwo a ciki ciki ta mutu a wajen"

hanunta ya rike yace "dan Allah ki daina faɗan haka bata mutu ba insha Allah tana raye, kuma zamu mika mata ƴarta a hanunta insha Allah"

hanu ta mikawa yarinyar tace "zo"

a hankali ta fara takawa da tafiyarta wanda bai gama fita ba ta faɗa jikinta, bata damu da farin leshin dake jikinta ba dattin dake jikin yarinyar kasancewar daga kan bola take bata damu ta ɓata mata jiki ba, rungumeta tayi sai kuma taji yarinyar tayi shiru ta daina kukan kiran mama, kallon mijinta tayi wanda yake kallon yarinyar cike da tausayi tace "zamu jira ta zuwa dare idan bata dawo ba to fa wani abin ya sameta ba zata dawo ba, domin mahaukaci duk inda yake baya manta wajen kwananshi kuma baya manta ɗanshi"

zama sukayi a gefen bolan yarinyar tana jikinta, suna wajen har dare bata dawo ba, kallon mijinta da yayi alwala tayi sannan tace "bata dawo ba hakan ya nuna ta tafi wani wajen"

shima cikin gajiya da jin warin wajen yace "to ya zamuyi salma?"

a hankali tace "me zai hana mu tafi da ita tunda bamu da ɗa ko kuma ƴa mu tafi da ita ta zama ƴarmu"

kallon yarinyar yadda ta rungumeta tana bacci yayi, sai yaji tausayin salma a ranshi yasan tana son yara kuma Allah bai bata ba, a hankali yace "to shikenan mu tafi da ita ta zama ƴarmu mu bata kulawa kamar yadda zamu baiwa ƴar da muka haifa"

cikin sanyin murya da tausayin kansu tace "Allah ya bamu tarin dukiyan da ko mu kanmu bamu san iyakanshi ba, Allah ya bamu arziki da ilimi da duk wani abinda ɗan Adam yake buƙata a rayuwa saide Allah bai bamu ɗa ko ƴa ba, inada tabbacin ya bamu wannan yarinyar ne domin ta zamo ƴa a wajenmu, ya bamu ita ne domin ya share mana hawayen rashin yara da muke yi a kullum, ni da kai tare muke zama a ɗaki cikin tarin dukiyan da Allah ya bamu muyi kuka muyi addu'a Allah ya kwashe dukiyan ma kawai ya bamu koda yaro ɗaya ne, yau gashi Allah yayi mana kyauta da kyakkyawar yarinya balarabiya kamar mahaifiyarta ina fatan kada mahaifiyarta ta dawo ta kwaceta a hanunmu, ina fatan ta koma can wani waje ta warke da ciwon haukan kuma kada ta waiwayo bale tasan ta haifi yarinya akan bola"

murmushi yayi ya shafa gefen fuskanta yace "hakurinki yasa nake kara sanki a kullum, ina alfahari dake, da kuma ƴar da Allah ya bamu"

ɗaukanta tayi ta mika mishi ita tace "kasa mata suna"

karɓanta yayi yace "masha Allah kyawunta sosai yake kamar kece kika haifeta domin da kaɗan ta fiki hasken fata, sunanta MANAL"

murmushi tayi ta shafa fuskan yarinyar da take bacci tace "MANAL Allah yasa ki zamo alkhairi a rayuwarmu da kuma rayuwar kowa da kowa"

tashi sukayi zasu bar wajen hadari ya haɗu baƙi ƙirin atake gari ya fara iska me karfi, bolan dake wajen ya fara ɓata musu jiki, rungume yarinyar yayi a kirjinshi yana rufe ido yace "muje mota salma"

da gudu suka nufi hanyan motan, nan take ruwan sama ya sauko sai tsawa ake da karfi da kuma walƙiya me tsoratarwa, buɗe motan yayi suka shiga da kyar suka rufe marfin motan suna addu'a, ruwa aka fara kamar da bakin kwarya har aka gama ruwan kafin suka ja motan suka tafi, tunda suka hau kan titi idon salma akan yarinyar murmushi take sosai domin ta kasa ɓoye farin cikin da take ciki, da haka suka isa unguwa me kyau me ɗauke da manyan gidaje, da ganin unguwan zaka san ba kananan mutane bane a cikinta, a kofan wani tamfatsetsen gate suka tsaya, yayi hon sau biyu kafin gateman ya buɗe musu, hanu ya ɗaga mishi "barka da dawowa alhajin Allah"

cikin murmushi ya ɗaga mishi hanu shima, rufe gate ɗin zaiyi sulɓi ya jashi faɗuwa yayi kafanshi ya bugu da jikin gate ɗin, babban mutum ne hakan bai hanashi yin karan azaba ba, yace "wayyoo Allah kafata"

da sauri Alhaji umar ya buɗe marfin motan ya fito, gudu yayi zuwa wajenshi domin akwai nisa tsakanin compound da kuma gate ɗin, taimaka mishi yayi ya ɗagashi saide ya kasa taka ƙafan, cikin dauriya ya cije baki yace "Alhaji kafata kamar bata jikina"

da sauri ya kalli inda salma take rungume da yarinyar yace "ki shiga da ita ciki zan kaishi wajen gyaran kafa"

cikin sanyin da takeji da ruwan sama daya jikata ta karaso wajen ta yiwa malam sani sannu kafin ta rungume manal sosai ta shiga cikin tamfatsetsen gidansu na alfarma, shi kuma Alhaji umar ya rike malam sani suka shiga mota, wajen gyaran kafa ya kaishi sunyi sa'a mutumin yana gida yana dubawa yace ƙafan ya samu matsala dole sai anyi gyara, hakan kuwa akayi Alhaji umar ya biya kuɗi aka gyara ƙafan aka ɗaure da kyau kafin suka tafi, gidanshi ya kaishi domin ya huta, juya motan yayi zuwa gida cikin jin tausayin malam sani, bai taɓa jin ciwo ba tunda ya fara wannan aikin sai yau, har ya koma gida ya samu salma ta yiwa manal wanka ta canja mata kaya me kyau da rigan sanyi na yara, madara take bata yarinyar tayi shiru tana kallonta a hankali kuma tana shan madaran, zama yayi a gefenta kan white sofa, cikin damuwa tace "ya kafar malam sani?"

cire hulan kanshi yayi sannan yace "kafarshi ya samu matsala harma an gyara"

tace "subhanallah Allah ya bashi lafiya"

a hankali yace "ameen"

kallon manal yake itama tana kallonshi, murmushi yayi mata yace "zo nan ƴata"

taɓe baki tayi kamar zatayi kuka tana kallon salma, murmushi salma tayi sannan tayi mishi gwalo tace "batason Abba Amminta take so"

ɓata rai yayi yace "shikenan dama ai mata sun fi son mata ƴan uwansu ni kuma maraya ne an barni ni kaɗai"

cikin sanyin murya ta matso kusa dashi sosai, hanunshi ta rike tana murzawa, a hankali ta rungumeshi tareda manal tace "babu wanda zai kika sabida kai mutumin kirki ne, haƙiƙa manal ta samu uba na gari"

yace "salma inaso mu yiwa juna alkawari"

jijjiga kai tayi kanta a kirjinshi tace "alƙawarin me?"

yace "duk wuya duk rintsi ba zamu taɓa cewa manal ba ɗiyarmu bace koda mun samu yara anan gaba"

hanunshi ta damke cikin nata kana tace "nayi alkawarin manal koda na haifi yara sama da dubu ba zasu taɓa sanin ba mune muka haifeta ba"

a hankali yace "nima nayi alƙawari"

*Jiddah Ce...✍🏻*

08144818849

[09/04 à 08:05] JIDDA MAPI: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*DUHU DA HASKE*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Na

*Jiddah S mapi*

*Chapter 2*

~FM academic wani makaranta ne da yaran masu hanu da shuni da kuma ƴaƴan manyan siyasa suke ciki, school ne wanda akwai branch nashi a kasar london, sun kawo nan nigeria domin yara su samu sauƙin karatu, tsadadden school ne na gaske, a kofan school ɗin sukayi parking na motarsu fitowa Alhaji umar yayi hanunshi rike dana manal, tayi kyau ta kara kyau akan kyaun da take dashi, pink na wando ne a jikinta da farin riga sai headband pink da aka kame mata tulin gashinta ta baya, fara ce sal harma ta fara komawa yellow, gashinta kuwa baƙi ƙirin, hancinta me tsini yanada tsawo sosai da ɗan karamin bakinta da pinkish lips, hajiya salma ta buɗe motan ta fito, cikin ɗaga murya tace "manal ba zaki jirani bane?"

kallonshi manal tayi tace "Dady mu jira Ammi"

murmushi yayi mata yace "mu rama abinda tayi mana jiya mu tafi"

dariya ta fara sosai tana biye dashi suka shiga cikin school ɗin, kallon ko ina take da manyan idanunta masu kalan madara tace "dady wannan school ɗin yana da kyau sosai"

yace "shiyasa zan saki a ciki ai sabida kema kinada kyau"

tace "dady idan na girma kasan me zanyi?"

girgiza kai yayi, tace "zan siya maka jirgi"

dariya yayi yace "to shikenan manal amma kafin ki siyamin nayi alkawarin zan siya miki private jet a matsayin gift na gama secondary school ɗinki"

tsalle tayi tace "yeeee zan zamo nice ta farko a cikin sa'annina wacce zata fara hawa jet nata na kanta?"

gyaɗa kai yayi, tareda ammi suka shiga office na headmaster, akan kujera ya zauna itama manal ta zauna akan kujera tana kallon headmaster ko gaisuwa batayi mishi ba, hanu dady ya mika mishi suka gaisa kana yace "good morning"

amsawa yayi itama ammi ta gaisheshi ya amsa, kallon manal yayi yace "ba zaki gaisheshi ba?"

a takaice tace "good morning"

daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login