Showing 72001 words to 75000 words out of 83501 words
yana rike da akwatin suka fito, zaro ido tayi ganin motan police zagaye da gidansu, salati ta fara Imran ya tsaya a bayanta ya rungumeta ya ɓoye fuskanshi a jikinta ko a hanya baison ganin police yana matukar jin tsoron masu uniform, cikin rawan jiki yace "ki taimakeni karki bari su tafi dani"
_*make your payment free pages saura kaɗan is 400 via 6037523268 Hauwa shuaibumapi keystone, evidence via 08144818849*_
*Jiddah Ce....✍️*
[09/04 à 08:06] JIDDA MAPI: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*DUHU DA HASKE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 19*
~Man ne ya fito daga motan police ɗaya tareda police suka fara zuwa har gabansu, cikin ɗauke kai yace "shine wannan"
police ya ciro ankwa yace "you are under arrest"
ameesha ta shiga tsakaninsu tace "babu wanda ya isa ya tafi dashi domin bai aikata komai ba"
man yace "ki matsa"
tace "ba zan matsa ba"
yace "ki matsa"
tace "babu inda zanje"
fahad daya dawo daga school yaga polisawa a kofan gidansu da sauri yazo wajen ameesha dake tsaye tana fuskantan police da man tana cewa babu inda za'aje da Imran, wurgi yayi da ita faduwa tayi a gefe, yace "ku kamashi shine"
Imran yace "ameesha zasu tafi dani wallahi banyi komai ba"
sa mishi ankwa sukayi suka fara janshi yana tirjewa, da gudu ameesha taje tana janshi daga wajensu tana kuka tana cewa "sharri ne ku sakeshi babu inda zakuje da shi"
wurgi sukayi da ita, ta faɗi kasa da rarrafe ta isa wajen motan ta ɗau dutse ta fara harbin man tace "ka haukace ne? kayi hauka ne? kana ganin za'a tafi da kaninka kana tsaye?"
ganin yana shirin shiga motan da akasa Imran a bayan motan tareda ƴan sanda suna tsare dashi, taja kafanshi ya sauko kasa, takalminta ta cire ta fara dukanshi dashi, wurgi tayi da takalmin duk abinda ta samu a wajen ɗauka take tana dukanshi dashi, cikin kakkausan murya tace "na tsaneka, man na tsaneka, nayi dana sanin saninka a rayuwata, i hate you"
shiga motan yayi ta zauna daram a kasa tana kuka Imran yana kallonta har aka fara tafiya dashi, tashi tayi ta fara binsu da gudu kamar mahaukaciya, mama ce ta riketa tana fizgewa mama ta kaita gida, numfashinta yana yankewa tace "mama kina gani? kina gani fa man ne yazo dasu suka tafi dashi?"
mama tace "ki daina wannan kukan ameesha komai zaiyi daidai"
numfashinta har yankewa yake, ganin man take yi yana shiga motan, watsi ta fara da kayan ɗakin tace "i hate you man, i hate you"
da kyar mama ta lallasheta shiru tayi mama tana rungume da ita itama tayi shiru, cikin shesheƙan kuka tace "mama?"
a hankali tace "na'am ameesha"
tace "na tsani man, na tsaneshi"
shiru mama tayi basu kara magana ba.
police station aka kaishi sukace ya cire duk kayan jikinshi yasa uniform, cirewa yayi yasa uniform, da ankwa a hanunshi suka sashi a gaba zuwa ɗakin prison da cewar gobe zasu je kotu, ameesha da mama tare suka zo man ya juya baya bai kallesu ba, tana ganinshi ta fara huci mama tace "ki nutsu ameesha"
hijabi ne a jikinta tana kallonshi yayi sign zai tafi, cikin ɗaga murya tace "butulu mara imani, wanda baisan haƙƙin uwa ba bale na ƙani, wanda ya watsar da farin cikinshi dana mahaifiyarshi dana kaninshi sabida mace, wanda ko kaɗan baya tuna baya"
har cikin ranshi yaji maganan amma yayi shiru zai fita taji zuciyanta yana tafasa ta kasa daurewa tace "kai baka jin kunyan kanka? baka jin kunya ace haifanka akayi? kai ai kamata ace kana zaune a gidan zoo tareda ƴan uwanka dabbobi..."
a fusace yace "meesha?"
itama cikin fusata da son ganin ta kuntata mishi
tace "Abdulrahman tabbas kai dabba ne, harma wasu dabbobin sun fika tunani"
fita yayi tace "kaji kunya man, na tsaneka, wallahi na tsaneka man ko ganinka banson yi, man nayi dana sanin saninka a rayuwata"
shiga mota yayi ya haɗa kanshi da stairy ya fashe da kuka me sauti kamar yaro, ya rame ya fita hayyacinshi daga ka ganshi zaka san baya cikin hayyacinshi, har ya isa gida yana sharan hawaye, koda yaje a hankali yake tafiya kamar ba jini a jikinshi ya shiga ciki, ammi ya gani tana zaune akan wheelchair, yana ganinta ya fara hawaye a hankali ya karasa wajenta ya kwantar da kanshi a kafarta bayan ya zauna kasa, hawayenshi ya fara ɗiga akan kayan jikinta, cikin sanyin murya yace "ammi ina baki hakuri a madadin kanina, kuma nayi miki alkawarin zan tabbatar an hukuntashi, sannan nayi alkawarin kula dake har ranan da ɗayanmu zai koma ga ubangijinshi ko ni ko ke, ammi nasan kin cutu amma ki yafemin ki yafewa kanina yanzu haka an kamashi gobe za'a shiga kutu dashi, idan ya amsa kaifinshi za'a sassauta mishi hukunci, idan bai amsa ba zasu mishi hukunci me tsanani...."
kuka yake yi sosai, a hankali take shafa kanshi, ji yayi hawaye ya ɗiga akan hanunshi, ɗago kai yayi idonshi kamar barkono yace "insha Allah kin daina kuka daga yau ammi"
share mata hawayen yayi, a hankali take girgiza mishi kai alaman akwai abinda takeson faɗa mishi amma bai gane ba.
manal zaune a gaban mirror tana kallon kanta, fuskanta a kumbure hanunta rike da hoton Abdool wanda ta zana, hawaye masu zafi suna sauka daga manyan eye's nata suna wanke kyakkyawan fuskanta daya koma jajur, cikin kuka tace "manal meyasa? me yasa kike haka?"
a hankali ta kalli hotonshi tace "soyayya ce, tun ina karama na yadda da wannan maganan idan inason abu babu wanda zan gaɗa dashi, idan naga zan rasa to fa saide mu rasa duka"
share zazzafan hawayen tayi tace "kiyi hakuri ameesha, amma duk ranan da naga Abdool ya koma miki to saide mu duka mu rasa"
kallon kanta take kuma yi a madubin tana jin tsanan kanta da kanta, maruka masu zafi take yiwa kanta tana kuka, a hankali ya turo kofan ya shigo, ganin tana kuka tana marin kanta yaje da gudu yana riketa, kuka ta fashe dashi, yace "an kai Imran prison gobe zamuje kotu zai amsa laifinshi"
cikin kuka tace "ban taɓa tsammanin zaka ɗau mataki ba Abdool"
yana hawaye yace "nayi alkawarin ɗaukan mataki ba zan bari aci zarafinku a banza ba"
tace "na gode"
riketa yayi suka zauna a kasa tana kankame da hotonshi data zana.
Ameesha duk yadda taso su barta taga Imran sun hana, sunce sai gobe idan aka kaishi kotu da karfe biyu na rana zata ganshi, tana kuka tace "to shikenan"
tare da mama suka tafi, tana komawa gida ta fara ciro hotuna da duk abinda tasan ya shafi man ta ɗaure a cikin buhu ta kai bayan gidansu ta wurgar a inda suke aje abubuwa mara amfani, komawa ɗaki tayi wajen mama ta kwanta tayi shiru, mama sai hawaye take fahad kam yayi kuka har ya gaji yayi bacci, yadda taga rana haka taga dare, data gaji tayi alwala tazo ta shimfiɗa sallaya tayi salla, addu'a ta fara a fili tana kuka tana rokon Allah ya sassauta musu wannan abin, a wajen ta kwana.
man yadda yaga rana shima haka yaga dare, daga karshe sallaya ya shinfiɗa ya fara salla baima tuna yayi alwala ba, manal dake kwance ta tashi da sauri tace "man bakayi alwala bafa"
sallama yayi, a hankali ya tashi yace "na manta"
shiga ciki yayi domin yin alwala, hawaye ya cika mata ido a hankali ta share ta tashi daga kan gadon ta sauka, alwala yayi ya fito yaci gaba da salla, ɗakin ammi taje ta kunna wuta, da mamakinta taga ammi zaune akan gadon idonta biyu, kallon ammi tayi sannan ta sunkuyar da kanta ganin Ammin tana kallonta, a hankali ta karasa bakin gadon ta zauna kusa da ita, kwanciya tayi ta rungume ƙafafuwan ammi tace "ammina nazo na baki hakuri, ammi ki yafewa ƴarki wallahi banida yadda zanyi ne, wallahi inason abdool ammi bazan iya rabuwa dashi ba"
tashi tayi taga ko motsi batayi ba, tace "na gommace na rabu da kowa na rayu dashi"
murmushi tayi haɗe da hawaye sannan tace "ammi ko yanzu naga zaki faɗawa Abdool gaskiya ki gafarceni zan kara illataki, koda shike bakida bakin magana ba yadda zaki iya faɗa mishi ko ammi?"
tana magana tana ciza pink lip nata na kasa, kame gashin ta tayi ta baya ta rike Ammin tace "yawwa bari na baki maganinki"
ɗauko mata maganin tayi ta bata da ruwa ta buɗe mata bakin tasa mata, tace "yawwa ammina kwanta kiyi bacci"
kwantar da ita tayi sannan ta rufata da blanket tayi mata kiss a goshi tace "good night"
kashe mata wutan tayi sannan ta tafi, cikin iya tafiya take taku, har ta shiga ɗakin taga ya idar da sallan yana zaune kawai, a hankali ta rungumeshi ta baya tana shafa fuskanta akan sajenshi tace "ka daina damuwa komai zaiyi daidai"
tashi yayi da ita a jikinshi ya tafi da ita zuwa bed, kwantar da ita ya fara sannan shima ya kwanta yayi shiru, itace ta samu bacci shi har gari ya waye idonshi biyu.
Ameesha har gari ya waye tayi sallan asuba kafin bacci ya ɗauketa akan sallayan.
a firgice ta tashi jin mama na kiran sunanta, mama tace "ki nutsu mana breakfast na kawo miki"
karɓa tayi taci kaɗan ta juye sauran a flaks ta shirya da sauri tace "mama yau za'a je kotu da karfe biyu yanzu har sha biyu yayi zan tafi ki sameni acan"
mama tace "to ameesha"
da sauri tasa takalmi flat shoe tasa hijabi ta tafi, mashin nata ta hau dashi ta tafi, tana zuwa sukayi checking nata suka sata ɗana abinci kafin ta shiga ciki, sunyi mata iso zuwa wajenshi tana rike da kulan abincin suka buɗe mata, shiga tayi taga har ya fita a hayyacinshi kwana ɗaya kacal, abincin ta buɗe tace "kayi salla?"
yace "eh"
abincin ta fara bashi a baki, a hankali yace karɓa yana hawaye yana ci, ruwa ta bashi tace "karka damu ina tare da kai koma me zai faru ba zan barka ba ina tare da kai sannan idan anje kotu ko zasu kasheka kada ka karɓi laifin daba naka bane kaji?"
a hankali yace "to"
abincin taci gaba da bashi, man ne ya shigo sanye da kananan kaya, akwai tambayoyin da akeso Imran ya amsa kafin su tafi kotu shiyasa suka kirashi, tare dashi suka karasa wajen kofan, tun daga nesa yake kallonta tana bashi abincin tana lallaɓashi da alama karfin gwiwa take kara mishi, wani irin sanyi yaji a ranshi, yasan matukar ameesha tana waje to Imran zai samu sauƙin komai, , gyaran murya police yayi yace "zamu fita dashi zai amsa tambayoyi kafin a wuce kotu"
tana bashi abincin tace "bari ya gama cin abinci"
cikin tsawa police yace "mu zaki gayawa bari ya gama cin abinci?"
tashi tayi tace "ka faɗamin a wace dokar kasa akace abar wanda yake kulle da yunwa?"
shiru yayi, bata kalli ko inda man yake ba taci gaba da bashi saida ta gama ta rufe flask ɗin ta wuce man dasu ta fita, akan kujera ta zauna tana kallonsu har aka fito dashi, waje suka bashi ya zauna man ma ya zauna suka fara mishi tambayoyi, amsawa yake man ma yana bada amsa, kuka Imran ya fashe dashi ganin man ya bada shaidan tabbas ya aikata, cikin kukan yace "ameeeshaaa"
tashi tayi tazo ta rungume kanshi tace "karka damu Allah yana tare da me gaskiya, makaryaci kuma ko aina yake sai Allah ya ƙona shi sai Allah ya hanashi zaman lafiya da kwanciyan hankali, Imran duk wanda babu tausayi a zuciyarshi ba zai taɓa jin daɗin komai ba a duniya, tunda kanada albarkan uwa babu abinda zai sameka, uwarka ta mutu kana kusa da ita mace bata hanaka zuwa kusa da uwarka ba, insha Allah wannan abin kaɗai ya isa ya cireka daga masifa"
tana magana tana kallon man, bai yadda sun haɗa ido ba.
da haka har lokacin tafiya kotu yayi, tana biye dasu akan mashin nata har zuwa kotun, abin mamaki mutane sun cika makil suna jiran zuwanshi, abinda basu sani ba shine manal ta bawa ƴan gidan jarida maƙudan kuɗaɗen akan su yaɗa labarin amma su ɓoye cewar itace ta basu, har man saida yayi mamakin tarin mutanen dake kotun, Imran yana sanye da ankwa aka kaishi gaban kotu ya tsaya, ameesha ta samu waje ta zauna, man zai zauna yaga manal tazo da ammi tana turata akan keken guragu, da sauri yaje ya rike ɗayan gefen ita kuma tayi kyau cikin riga da wando da baƙin after dress a saman, ta rufe aninin after dress ɗin tasa bakin mayafi siriri da takalmi me tsini a kafarta, kallo ɗaya ameesha tayi musu ta ɗauke kai, wajen zama suka samu suka zazzauna a gaba kamar yadda ameesha take gaba amma suna da nisa, juyowa tayi suka haɗa ido da manal, kashe mata ido manal tayi sannan tayi mata murmushin data saba da mugunta, ɗauke kai tayi alkala yazo kowa ya tashi saida ya zauna suka zazzauna, ya kalli Imran yace "ina lauyan me kare wanda akayi kara da lauyan wanda yayi kara?"
lauya ɗaya ne ya tashi wanda manal ta biyashi makudan kuɗaɗen akan yayi duk yadda zaiyi a yiwa Imran hukuncin kisa, yace "sunana barrister fadeel nine lauyan me kara"
Alkali yace "ina lauyan dake kare wanda akayi kara?"
shiru akayi a wajen, Imran kanshi a kasa, Ameesha ta ɗaga hanu tace "a bamu dama mu ɗau lauya yanzu"
yace "an baki dama kuma an baku minti ishirin"
kallon wani lauya da yake zaune tayi, da alama yanada mutunci domin a nitse yake, taje tayi mishi alama su fita waje mana, tashi yayi aka bisu da police ɗaya suka fita, kuka ta fashe dashi bayan sun fita ta fara bashi labarin abinda ya faru sannan tace "dan girman Allah ka taimakemu"
yace "karki damu insha Allah"
komawa ciki sukayi ya tsaya yace "sunana barrister sadeek nine lauyan me kare wanda akayi kara"
alkali yace "malam Imran anyi karanka ka yiwa matar yayanka fyaɗe sannan ka kusa kashe mahaifiyar ta dan zata faɗi gaskiya shin ka amince da laifinka ko baka yadda ba?"
a hankali ya girgiza kai yace "ban aikata ba"
take suka fara gudanar da shari'a lauyanshi yana kokari domin ya kusa gano bakin zaren, manal wacce take kallonshi ta kasan ido ta kalli ameesha, murmushi ameesha tayi mata ganin zasuyi nasara, lauyanta yace "ya mai girma me shari'a idan babu damuwa zanso na kira yayanshi domin ya bada shaida"
yace "an baka"
yace "Abdulrahman bismilla"
tashi man yayi yaje ya tsaya a inda aka nuna mishi yana fuskantar kowa, alkali yace "malam Abdulrahman kace kaga kaninka da idonka a lokacin daya aikata laifin da ake tuhumanshi dashi munaso ka bada shaida"
a hankali yace "eh na ganshi da idona a lokacin dana dawo gida ina jin sautin ihunta yayinda shi kuma yake kokarin rufe mata baki, bayan na fara dukanshi ya fita a guje shine ya ture mahaifiyar matata"
kotun tayi tsit sai kukan man akeji, lauya yace "zaka iya komawa ka zauna"
lauyan imran ya tashi yace "shin ka ganshi ido da ido ko kuma zargi kake?"
yace "ba zargi nake ba ido da ido na ganshi"
lauyanta yace "idan babu damuwa zanso na kira wacce aka yiwa laifin tazo nan gaban kotu ta bada shaida"
alkali yace "an baka dama"
yace "manal"
tashi tayi tana tafiya a hankali har ta isa inda aka nuna mata, alkali yace "wannan shine karshen shaidan da zamu karɓa shin wani shaida zaki bawa kotu domin tabbatar da an aikata miki wannan laifin"
cikin magananta me sanyi tace "shaidana na farko itace Ammi na"
zuwa tayi ta fara tura ammi har gaban alkali tace "wannan itace shaida ta"
alkali yace "shin da gaske ne shine ya aikata miki hakan?"
a hankali ta kalli manal taga tayi mata murmushin da ita tasan idan tayi akwai matsala, a hankali ta gyaɗa kai, alkali yace "maidata"
mayar da ita tayi sannan tazo ta tsaya a gaban alkali tace "sai shaida na uku bayan wanda mijina ya bayar"
gani sukayi ta fara cire aninin gaban riganta, ɗauke kai sukayi ganin ta cire after dress ɗin ta wurgar a kasa, rigan jikinta ta cire ya rage daga ita sai bra, sannan ta fara zame wandon, ganin sukayi duk jikinta yakushi da kuma tabo ne kuma da alama na jiya ne domin yayi jajur, ameesha sunkuyar da kai tayi, manal zata cire wandon Abdool yazo da gudu ya hanata, kuka ta fashe dashi ya rungumeta ya kaita wajen zamansu, alkali yace "duba da shaidun da muka samu daga wacce tayi kara kotu ta ɗaga wannan karan daga nan zuwa shekara huɗu masu zuwa, a farkon shekara kwana ta biyu za'a karasa wannan case ɗin, wanda ake tuhuma da wannan laifin zaiyi zaman prison na tsawon shakeru huɗu babu beli har sai ranan da muka kara dawowa, kotu ta bashi daman neman lauya"
ameesha kasa tashi tayi tana gani zasu fita da Imran yana kuka yace "ameesha kina gani zasu tafi dani? shekara huɗu zanyi babu ku? shekara huɗu fa ameesha kafin a yankemin hukunci, ameesha"
ɗauke kai tayi daga kallonshi, kowa ya watse a kotu ita kaɗai ta rage duk yadda mama tayi da ita taki tashi, a hankali ya juya ya kalleta yaga kanta a kasa, cigaba yayi da tura keken ammi, manal kuma tana sharan hawaye suka tafi, saida taci awa ɗaya a zaune kafin ta tashi a hankali take tafiya kamar zata faɗi, napep ta shiga zuwa gida, an bawa Imran uniform na prison sannan aka turashi prison ɗin, tana shiga gida ta zauna akan kujera tayi shiru.
"ameesha sai bayan shekara huɗu ma kafin zasu yankemin hukunci? kina gani zasu tafi dani?"
toshe kunne tayi domin wannan sautin ya hanata nutsuwa, har dare batayi magana ba a hankali ta tashi ta fita ta hau mashin taje prison, tayi ta rokonsu harda durkusawa kasa kafin suka yadda ta shiga inda yake,