Showing 45001 words to 48000 words out of 83501 words
miki, ko dai bada jinin hanuna ya kamata nayi ba?"
ganin ammi tayi shiru tana kallonta a tsorace ta tashi ta nuna kirjinta tace "ammi da jinin zuciyata na ya kamata na zana hoton abdool ko?"
rezan ta ɗauka sannan ta ɗaga rigan jikinta daya gama ɓaci da jini da fenti tasa reza a kirji zata tsaga da wani irin gudu ammi ta rungumeta ta kwace rezan ta wurgar
shiru tayi tana kallon bayan ammi, hawaye ammi ta fara
cikin tsoro tace "yayi kyau a haka manal karki illata kanki dayawa"
murmushi tayi me sanyi sannan tace "karki damu ammi koda zuciyata yace na cire na bashi zan bashi"
ammi ta kankameta tace "dan Allah manal ki daina wannan maganan ina tsoro"
sakinta tayi a hankali ta zaunar da ita a bakin gadon
first-aid box ta ɗauko ta fara tsayar da jinin da yake zuba, ɗago ido tayi a hankali ta kalli manal ɗin gani tayi gashinta ya zubo ya rufe mata fuska ga wani murmushi me kama da dariya da takeyi, ga wani masifaffen kyawun da tayi, kallon cikin idonta tayi masu ɗaukan hankali, a hankali ta kuma maida kanta kasa tana cigaba da wanke mata ciwon, saida ta gama ta tashi a hankali ta fara gyara mata tulin gashinta me tsantsi tana mayarwa baya, jiki a mace ta riketa tace "muje kiyi wanka jikinki duk ya ɓaci"
towel ta ɗauko mata, a hankali ta cire kayan ta ɗaura towel ɗin, kayan ammi ta kwashe ta fita dasu, a washing machine tasa sannan ta dawo ta goge jinin daya ɓata tile ɗin, ta buɗe wardrobe ta ciro mata riga dogo me taushi ta aje mata akan gado, kallon hoton data zana tayi a hankali tace "na shiga uku, Allah kasa babu wacce yake so take sanahi ina hango musu gagarumin matsala a tare dasu matukar manal ta shiga rayuwarsu"
cikin sanyin jiki ta kwashe fentin duk ta kai wajen zamansu sannan tasa hanu a hoton zata matsar gefe, turo kofan toilet tayi da sauri tace "wait ammi"
tsayawa tayi tana kallonta, farin fatarta ya kara bayyana tana wani irin glowing, towel pink dake ɗaure a kirjinta ya bayyana rabin cikakkun boobs nata a waje, bai kuma gama rufe mata cinya ba, ta wanke gashinta hakan yasa ya zubo har zuwa hips nata dake ɓam, ta karaso ta zame hanun ammi daga hoton tace "ammi wannan hoton ban yadda kowa ya taɓa ba"
ammi nuna kanta da yatsa tace "harda ni?"
jijjiga kai tayi kana ta mannawa hoton kiss ta manna a kirjinta tace "harda ke, kinfi kowa sanin idan inason abu bana haɗawa da kowa"
ammi banda kallonta ba abinda take yi, a cikin ranta ta karasa maganan tace "idan kuma kinga zaki rasa saide kowa ya rasa"
murmushi tayi ta kyasta hanu ta rungume ammi ta baya tayi mata kiss a kumatu tace "yes ashe ammi na kin sani gashi kin faɗa"
ammi batasan maganan ya fito fili ba, sakinta tayi ammi ta jingina da jikin bango tana kallon manal wacce take sa kaya tana murmushi leɓenta na kasa cikin bakinta.
Ameesha wacce take cike da damuwa zaune akan kujera man yana kwance kusa da ita ya ɗaura kanshi a cinyarta, hanunta a kanshi tana shafa lallausan gashinshi tace "inaso ka fahimta kai namiji ne ba zaka gane me nake nufi ba, wannan manal ɗin babu alkhairi a tare da ita"
yana zana hoto ya ɗaura plain shit ɗin akan kafarshi ya aje hoton ya lumshe ido yana jin daɗin yadda take shafa kanshi yace "babu komai fa kawai batada magana ne kuma tanada izza amma kin ganta batada matsala"
zanen da yake ta wurgar a fusace sannan ta ture kanshi akan cinyarta cikin ɓacin rai tace "ka fahimta mana abdool"
shima tashi yayi ranshi ya fara ɓaci yace "wai yaushe kika zama haka ne meesha? ban sanki da yiwa mutum mummunan zato ba na sanki da yiwa kowa kyakkyawan zato...."
"to ai tunda ka santa da yiwa kowa kyakkyawan zato saika duba wannan watakila ta hango matsala ne"
cewar Imran wanda ya shigo yanzu, da hanu ta nunawa Imran wajen zama a gefenta tace "yawwa Imran dan Allah bakaga abinda na gani a tare da ita ba?"
Imran ya zauna zai yi magana man ya tashi cikin jin haushi ya kwashe takaddanshi ya fara tafiya tace "man"
fita yayi daga gidan da alama gida zai tafi, Anty wacce take jinsu tun ɗazu tazo ta zauna kusa dasu tace "ameesha"
a hankali tace "na'am anty"
tace "sau dayawa maza basa gane asalin halin mace sai sun zauna da ita, sannan shi namiji abinda ya gani shi yake aiki dashi kuma yake yadda dashi, tunda kikace tazo har gida dan ta baki hakuri hakan yasa yaga tanada kirki dan ba kowace boss bace zata zo har gida ta baki hakuri ina ganin ki share wannan zancen ya wuce ki bar abinda zai faru ya faru, wani lokaci idan muna hana abu ya faru karfi da yaji to kamar munaso mu hana ƙaddara ne, idan Allah ya ƙaddara zata shigo rayuwarku dole zata shigo babu wanda ya isa ya hana, ke dai kawai addu'a zakiyi dan ba yadda za'ayi ace haka zakuci gaba da rayuwa dole watarana zakiyi aure shima kuma zaiyi aure"
shiru tayi a ranta tace "ba zaku gane me nakeji bane idan na ganshi kusa da wata macen"
a fili kuma tace "to anty"
Imran dake kusa da ita yace "Ameesha kada ki damu nima wallahi wannan manal ɗin ko kallonta nake sai naji kamar akwai wani mugun abu a tare da ita"
anty tace "na haneku da yiwa mutum mummunan zato"
yace "to anty"
washe gari ya riga ameesha shiri yana tsaye a kanta ita kuma tana durkushe tana ɗaure igiyan takalminta, ya kalli agogo yace "kinga kinsa munyi late ko? tun ɗazu kike ɗaura takalmi har yanzu baki gama ba? wallahi zan tafi na barki"
a fusace tace "to ka tafi mana ba sai na tafi da kafa ba, nasan ma ba zaka iya tafiya ka barni ba"
Imran da suke hutu ya fito yana mika yana hamma yace "Unty Ameesha"
cikin ɗaure takalmin tace "nasan idan kasa unty a gaban sunana to wani abin kakeso, kada ma ka fara dan banda ko biyar"
turo baki yayi, durkusawa man yayi ya rike hanunta ya ɗaura a kafaɗanshi ya fara ɗaure mata takalmin murmushi take tana kallonshi, hon sukaji a kofar gida, duk suka kalli juna, yaci gaba da ɗaurewa suka kara jin hon, man yace "imran jeka duba waye da mota a kofa?"
tafiya yayi domin dubawa, tana ganinshi ta sauke glass tareda yi mishi murmushi ta ɗaga mishi hanu, da mamaki yake kallonta, saiya ɗaga mata hanu shima, tace "Abdool fa?"
ya kasa magana kawai ya nuna mata ciki, yana gaba tana biye dashi a baya yana cewa "yau kin ɓata mana lokaci shashasha kawai"
tace "niba shashasha ba sai de......"
shiru tayi tana kallon manal wacce take aika musu kyautan murmushi ta cikin tsadadden motarta da take ciki, tayi kyau da ɗaurin ɗankwalin atamfa, hanu ta ɗaga musu, abdool ya ɗaga mata hanu, fitowa tayi tana gyara karamin mayafin daya rufe rigan jikinta dake sanye da fited gown, takalmi me tsayi ne a kafarta kafin ta karaso kamshin turarenta ya karaso, cikin murmushi take tafiya tana kallon cikin idon ameesha, a gabansu ta tsaya tace "barka da safiya"
cikin rainin wayo tace "Ameesha"
da kyar ta haɗe yawu tace "barka"
tace "sannu Abdool"
kallon agogo tayi tace "kasan kayi late sosai? kuma yau akwai manyan baƙi da zasu zo ina bukatarka kusa dani"
yace "okay kije zamu biyoki a baya yanzu"
girgiza kai tayi tace "ban yadda da driving ɗinka ba da alama baka sauri nice zan kaika"
yace "no saina aje ameesha a wajen aikinta kafin nake tafiya"
murmushi tayi idonta akan ameesha tace "me zai hana ka nema mata me daidaita sahu ko kuma ni zan nema mata driver sabida wajen aikinmu yana bukatarka da wuri"
shiru sukayi, ameesha tace "no bana bukatan napep ko wani driver zan iya zuwa da kafata karki damu kanki wannan huruminmu ne ba naki ba..."
da sauri man yayi mata alaman tayi shiru, manal kallon agogon dake hanunta ta kuma yi tace "muje saina ajeki kafin mu wuce dashi"
girgiza kai tayi tace "a,a tunda kuna sauri kuje kawai ni zan shiga napep"
man ya rike hanunta yace "saimun ajeki kafin mu wuce ba zan iya ganinki ki shiga napep inanan lafiya ba"
zatayi magana ya rufe bakinta ya jata zuwa cikin motan, shi ya zauna a gaba ita kuma ameesha tana baya manal ta zauna a mazaunin driver, Imran yana tsaye a jikin kofa yana kallonsu, haka kawai yaji wani kala sai yaji babu daɗi a ranshi, su biyu idan sun tafi yafi mishi kwanciyan hankali, shiga ciki yayi umma tace "Imran ya na ganka cikin damuwa?"
yace "umma wannan manal ɗince tazo har kofa"
da sauri tace "me tazo yi?"
yace "wai ɗaukan ya Abdool sun tafi tare da ameesha a motarta ina ganin fuskan ameesha ba dan taso ba ta bisu"
umma tace "Innalillahi to wai ita zuwan nan na lafiya kuwa? gaskiya idan man yazo saina tambayeshi me yasa take zuwa"
yace "gaskiya kam"
tafiya suke akan titi idonta duk akan ameesha ta cikin madubi take kallonta, ameesha data ɗaga kai saita haɗa ido da ita, murmushi tayi tace "Ameesha kinyi shiru"
itama murmushin yaƙe tayi tace "ba komai"
man yana duba sakonni a wayanshi saida ya gama yasa wayan a aljihu ya juya baya ta wajen ameesha ya bada attention ɗinshi duka wa ita yace "my darling, my meeesha, my princess"
yana faɗan haka ne sabida yaga tana cikin fushi, kwaɓe face yayi yace "please ki saki jiki"
wani mugun kallo manal tayi mata, rike hanun Ameesha yayi yana wasa dashi, yana kallon kyakkyawan fuskanta, ganin haka manal ta zuba mata cat eye's nata masu ɗaukan hankali, kwacewa kan motan yayi daga hanunta, da karfi ta juyar da motan ta wajen ameesha ta kife akan titin, ihu ameesha tayi jin azaban daya ziyarci kata, manal ta waro ido, man yace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un"
mutane suka taru da kyar suka ɗaga motan lokacin Ameesha harta daina ihun azaba tayi shiru, buɗe motan yayi da gudu ya fito baibi ta kan manal ba wacce take cewa hanunta, ciro ameesha yayi idonta a rufe jini yana zuba yana ɓata goshinta, cire rigan jikinshi yayi a yaga ya ɗaure mata kanta dashi yana tashinta yana kiranta "meesha? meesha?"
ɗagata yayi cak ya ɗaura ta a kafaɗanshi ya fara gudu zuwa inda zai samu mota, manal dake zaune a wajen ta kalleshi ta cikin madubin motan, baima san ko tana raye ko ta mutu ba burinshi yaga ya tseratar da Ameesha, dunƙule hanu tayi ta buga jikin madubin take ya fashe, buɗe marfin motan tayi da taimakon mutane ta fito domin yayi kaca kaca motan, binsu tayi a baya saida ta isa inda suke kafin tace "ameesha ki buɗe idonki dan Allah"
da kyar ya samu ya tsaida wani mota ko magana baiyi ba ya buɗe ya shiga ya daura ameesha a cinyarshi yana tashinta gaba ɗaya ya fita a hayyacinshi, manal ta shiga motar tayi shiru tana kallonshi, hawaye ta gani a idonshi ji tayi tana jin zafin ganin hawayen, a hankali ta ɗaura hanunta akan nashi ta girgiza mishi kai alaman ya daina kuka, city hospital ya kaisu da sauri ya ɗauketa manal tana biye dasu ya kaita, a ɗakin da masu accident suke zama aka kwantar da ita, yana waje ya goya hanu a baya yana safa da marwa kana ganinshi zaka san yana cikin tashin hankali, a hankali tazo wajenshi ta dafashi tace "Abdool ka....."
cikin wani irin tsawa yace "stay away from me"
baya tayi jikinta yana rawa, makalewa tayi a jikin bango tana kallonshi da tsoro a ranta, hawaye ya fara wanke mata fuska tayi shiru tana ɓoye fuskanta daga kallonshi, jikinshi ne yayi mugun sanyi ganin halin data shiga, a ranshi yace "ƙaddara ce ba itace tayi ba Allah ne ya ƙaddara zakuyi accident"
cikin sanyin jiki ya rike hanunta ya zaunar da ita akan kujera ya durkusa a gabanta cikin damuwa ya ɗaura kanshi a kafarta yayi shiru, jim kaɗan taji yana shesheƙan kuka, a hankali tasa hanu akanshi ta shafa lallausan gashinshi tace "please"
cikin kuka yace "da nine naji wannan ciwon banason ganin ameesha cikin ciwo"
ji tayi kirjinta ya buga jikinta ya fara rawa, a hankali tace "ka daina kuka babu abinda zai sameta"
dr ne ya fito da sauri ya tashi yace "Dr tana lafiya?"
manal a ranta tace "Allah yasa ta mutu"
dr yayi murmushi yace "kwarai tana lafiya yanzu ma bacci take sabida ta ɗan bugu ne kaɗan ba wani ciwo bane sosai, sannan zuciyanta ne ya tsinke shiyasa ta suma"
murmushi yayi ya share hawayen ya kalli manal hanu ya ɗaga ya mika mata alaman su tafa, tafa hanunta tayi cikin nashi yace "ameesha is safe"
murmushin yaƙe tayi tace "thank god"
shiga ciki sukayi suka zauna kusa da ita, a hankali ta fara buɗe ido saurin rufewa tayi ganin sun haɗa ido da manal tana aika mata wani irin kallon data kasa fassarawa, yace "buɗe ido gani nan my meesha"
buɗe ido tayi ta kalleshi tayi murmushi tace "babu abinda ya sameka?"
cikin jin daɗin tambayan yace "ba komai sannu kinji?"
tace "to"
saida ta huta kafin dr yace ya sallameta man yace "manal mu sai gobe zamu fito"
tace "to amma.."
yace "please kije gobe zan fito yanzu koda naje ba zan iya aikin komai ba"
jijjiga kai tayi ta kalli ameesha tace "Allah kawo sauki"
a hankali tace "ameen"
yana rike da ita suka shiga napep, kallon manal tayi itama tana aika mata wani mugun kallo har suka tafi, driver ta kira yazo ya ɗauketa, a hanya sai sannu yake mata har suka isa gida, Imran ne ya fara ganinsu yace "yaya meya faru?"
yayi magana yana kallon ameesha dake ɗaure da bandage a saman kanta, kallonshi tayi basuyi magana ba, koda suka shiga ciki umma tace "kunyi accident ko?"
da mamaki yace "eh umma"
tace "to meyasa ameesha ce kaɗai taji ciwo ita wacce tazo ta ɗaukeku bataji ba?"
yace "umma ƙaddara ce fa"
tace "ku kiyaye ba kowa ake yadda dashi ba"
rike ameesha tayi ta zaunar da ita akan kujera tace "sannu ƴata kinji?"
a hankali tace "to"
kwanciya tayi ta rufe ido, so take tayi bacci amma manal take gani idan ta rufe ido, ta kasa gane wani irin kallo take mata.
saida yayi kwana biyu basa fita yace dole saita huta kafin suka fara fita aiki, zuwa yanzu manal ta fara nuna mishi so gadan gadan bata bari komai ya sameshi a office, ya ɗau hakan a matsayin abota, wani lokaci tana zaune a office zata aika a kirashi ta zuba mishi ido tana murmushi tana kallanshi idan yana bata labari, koda ta koma gida da dare zata kirashi tace ya faɗa mata kalolin zanen da zatayi amfani dasu akan sabon zanenta, idan yaji haka saiya saki jiki yana faɗa mata, Abdool yana yin hakan ne ya biye mata yana bata nishaɗi sabida abinda dr ya faɗa, sannan ya kula tana yawan zama lonely, batada yawan surutu, sai idan tana tare dashi zakaga tana dariya saɓanin haka fuska kamar wuta haka take zama babu ko murmushi bale dariya, ammi a kullum addu'a take Allah ya ragewa manal son abu a rai idan ta fara, yadda take nuna son Abdool har tausayi take bata, wani lokaci zata rungume hotonshi data zana tana kuka a kasa har tayi bacci, soyayya me zafi take mishi, har ammi bata yadda ta yabeshi domin tsananin kishi take sosai dashi.
_wait please i have a question, you know I love you ko? why are you guy's following me privately and asking me whether littafin paid ne ko free? ga wanda suka saba karanta littafina ai idan na gama free pages kun san tsayawa nake da posting sai wanda yayi payment yake samun complete, so please and please idan kin san you can't make your payment idan na gama free kada kiyi nisa, domin yanzu na fara littafin akwai sauran tafiya sosai_
*Jiddah Ce...*
08144818849
[09/04 à 08:06] JIDDA MAPI: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*DUHU DA HASKE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 14*
~Ameesha ce take kula da umma har ta samu sauki da taimakon man da kuma anty wato mahaifiyar ameesha, an sallamesu sun koma gida bayan ta samu sauƙi, Ameesha bata kara ɗagowa man maganan ba hakan yasa suka fara zama lafiya kamar da, yanzu ma haka yau weekend ne ya fita da ita shopping ta siyo kayan sawa wasu Imran da fahad, nasu umma kuma atamfa ta siya musu tace zata kai ɗinki, hira suke yi yana bata labarin meeting ɗin da sukayi jiya wajen gyara sai tace ba haka zakayi ba canjawa zakayi, da haka suka isa gida suka baje kayan a falo, Imran yana gani ya ɗauki nashi, hira sosai sukeyi kamar zasu tada falon, umma tashi tayi tace "zan kwanta nikam bakwa rabo da hayaniya"
tana tafiya ameesha ta kalli Imran yana cin chocolate ɗin da suka siyo kwacewa tayi ya ɓata rai yace "ki bani abuna"
tace "ba zan bayar ba"
tashi yayi zai kwace ta tashi da gudu suna zagaya ɗakin idan taga zai kamata saita ɗale kan kujera ta dira ta baya, man yana chatting a wayanshi shida faruk faɗawa kanshi ameesha tayi ta rikeshi gam tana ɓoye chocolate ɗin, ido ya zuba mata ganin tana dariya bama tasan a jikinshi take ba, gashin dake kwace a gaban goshinta yana mishi kyau koda yaushe kallo yake, a hankali yasa hanu yana kara kwantar mata, aje wayan yayi yana kallonta sosai, a kullum saiya ganta kuma yasan ita kyakkyawa ce ajin karshe amma bai taɓa ganin kyawunta kamar na yau ba, ko