Showing 6001 words to 9000 words out of 83501 words

Chapter 3 - DUHU DA HASKE Hausa Novels by Jiddah S Mapi.docx

19 Sep 2025

2238

sosai ganin taki yin kuka, saida ammi ta karɓeta da kyar, har suka isa gida babu wanda ya kara magana, suna shiga ta wuce ɗakinta wanda suka tsara mata da kayan alfarma na yara rufewa tayi ta kwanta akan gado sai yanzu ta fara kuka, zama yayi akan sofa yace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un"

ammi tana shafa kanshi tace "karka damu dan Allah yaranta ne"

yace "mace da wannan taurin zuciyan?"

tace "ba komai zata daina har yanzu yarinya ce batasan komai ba"

shiru yayi.

har dare bata fito ba tana ɗaki da wando da riga na uniform ɗin a jikinta, knocking Ammi tayi cikin sanyin muryanta tace "manal ɗin ammi buɗe kofa muje muci abinci dady na jiranmu a dining"

shiru tayi bata amsa ba, tace "manal? idan baki buɗe ba yau zanyi tafiya na barki"

da sauri ta tashi taje ta buɗe, murmushi tayi ta rungumeta tace "kiyi hakuri kinji?"

a hankali ta gyaɗa kai kawai amma har yanzu ranta a ɓace, da haka har suka isa dining, zama tayi bayan ammi ta zuba mata abincin ta ɗauko attarugu dake gefe an yayyanka domin sawa a salat ta fara ci haka ba tareda ta haɗa da komai ba, ci take da alama tana cikin tsananin ɓacin rai, Ammi ta kalli dady a tsorace, shima ya kalleta, ruwan sanyi ta zuba a cup da sauri ta mika mata, matsar da ruwan tayi taci gaba da cin attaruhu da haka harta koshi tace "na koshi"

kiss ta yiwa ammi a goshi sannan ta yiwa dady wanda ya kasa kai koda loma ɗaya na abinci a bakinshi, suna kallonta har ta bar wajen ta koma ɗaki, Ammi cikin kallon mamakin ta juyo da kanta zuwa dady yace "salma anya bamu ɗiuko abinda zai damemu ba?"

da sauri tace "dan Allah kada ka kara wannan maganan, ita ɗin ƴarmu ce koma me take yi saide muyi mata addu'a"

yana kallonta yace "salma na tsorata kuma har yanzu a tsorace nake"

tace "ni kaina a tsorace nake amma ya zamuyi? ya zama dole mu kula da ita domin mune iyayenta"

dafa kai yayi, shiru yana kallon plate na abincin ta, attaruhu da koda rabi kaci saiya dameka shine zata cinye wannan duka?"

itama Ammi kasa cin komai tayi.

tana shiga ɗaki ta wuce toilet da gudu ta kunna ruwa ta ciro harshenta da yake raɗaɗi ruwan yana zuba akai, runtse ido tayi ganin bai daina zafi ba, tace "na hukunta harshena sabida ya bada hakuri yau"

da haka harta gama primary ta shiga secondary, duk wani abinda take so tana samu bata rasa komai ba, wani abu da ita shine idan tana son abu koda a wajen waye saita kwace, sannan idan taga zata rasa saide duka su rasa, wannan shine abinda ta taso dashi a ranta hakan yasa ba zata rasa komai ba, koda ta rasa saide su rasa tare da me abin, da haka har ta kai 20years a lokacin take ajin karshe na secondary, batada kawa batada aboki bata shiga cikin mutane bata kula kowa, bata dariya sannan Allah ya bata ilimi sosai, ta iya zane ta iya zana duk wani abinda ta gani.

zaune take a ɗakinta wanda dady ya maidashi kamar masarauta, komai na ɗakin irin na sarauta ne sannan gadonta ma kamar na sarakuna, tana sanye da farin wando me laushi yanada faɗi sosai, sannan farin vest a jikinta kasancewar akwai zafi sosai yau, gashin kanta har yana taɓo hips nata, bayanta fari sol tana zaune akan table yayinda ta aje abinda take tane kamar black boat a gabanta, hankalinta gaba ɗaya akan zanen da take yi, yayinda take zana hoton dady tana murmushi sosai, kyakkyawan hanunta ɗauke da jan lalle yayinda ta rike alkalamin zanen, knocking akayi kafin aka turo kofan, Ammi ce tayi kyau sosai cikin riga silk me adon leshi a hanu da kuma wuyan, blue dress yayi mata kyau sosai idan ka ganta hutu da arziki ya zauna a jikinta, a hankali ta karasa inda take ta rungumeta ta baya tana kallon zanen da take yi, sakinta tayi tace "manal ya kamata ki bar zanen nan kizo kici abinci dare yanayi kuma gobe kinada school kin manta kuna zana jarabawan gama secondary?"

aje alkalamin tayi sannan ta juyo tana murmushi

"masha Allah tsarki ya kara tabbata ga ubangijin da yayi wannan halitta"

ashe juya bayanta da tayi ya ɓoye asalin kyawunta saida ta juyo asalin kyawun ya bayyana, idanunta sun kara girma shape nasu kamar kwai, yayinda karamin bakinta ya kara zama pink sosai, gashin idanunta sun zama zara zara harma sunfi lokacin da take karama, breast nata a cike fam, jikinta ya samu hutu asalin kalanta ya kara bayyana ammi a kullum tana yiwa manal kallon balarabiya domin haka taga mamanta kuma babu abinda ya rabata da maman, murmushi ta kuma yiwa ammi wanda ya lotsar da dimple nata da suka kara fitowa sosai, kafa ɗaya lankwasa akan kujeran ɗaya ta aje a kasa, cikin zazzaƙan murya tace "Ammi am trying my best to see na gama zana hoton dady but kowane rana kara san Abba a raina karuwa yake hakan yasa nake kara zana shi ya fito fes ko bakiso na zana miki love of your life yayi kyau ne?"

jan kunnenta ammi tayi cikin wasa tace "yaran zamani bakuda kunya"

dariya tayi tace "wash ammi da zafi am sorry"

ammi tana rike da kunnenta tace "tashi muje muci abinci anjima kya karasa"

zatayi magana Ammi ta ɗago da ita tace "oya muje"

turata take suna tafiya, hips nata cike da wandon duk da wandon yanada faɗi hakan bai hana hips nata fitowa ba, har suka fita zuwa dining dady na zaune sanye da jallabiya yana cin abinci, yana ganinsu ya rufe yayi kamar baya ci, turo baki manal tayi tace "laaa wallahi dady na kamaka yau kana cin abinci babu ni"

da sauri ya haɗiye abincin bakinshi yace "A,a manal banci komai ba kinga jiranki nake"

make kafaɗa tayi "niban yadda ba"

hanu yasa a kunne yace "am sorry"

kallonshi tayi tace "na yafe tunda ina sonka"

murmushi ammi tayi tasa musu abinci suka fara ci, dady yace "Alhmdllh, manal me kikeso kiyi idan kin gama school?"

tace "dady inaso na zama fashion designer, so nake na rinƙa zana hotunan abubuwan fashion da kuma ɗaukan nauyin kowane manyan event, sannan inaso na rinƙa decorating na wajen da za'ayi event"

murmushi yayi yace "good girl kinada basira sosai, zan buɗe miki babban company na fashion designing sannan zaki samo ma'aikata kwararru waɗanda zasu kawowa company ɗinki cigaba, kece c.e.o"

da gudu ta tashi ta rungumeshi tayi mishi kiss a gefen fuska tace "you are the best dad in the world, dady bazan iya haɗaka da kowa ba, kuma bazan yadda na haɗu da wani akanka ba"

murmushi yayi yace "kece kaɗai ƴata da Allah ya bani ya zama dole na baki duk abinda kikeso"

murmushi tayi tace "thank you"

washe gari, ta shirya cikin uniform nasu domin tana zana jarabawan gama secondary, tafiya take a cikin gidan cikin takunta na nutsuwa da kasaita, uniform yayi mata kyau sosai, tunawa tayi da takaddanta tsaki taja ta juya zata koma sukayi karo da mai aiki tana rike da shara a hanu ya zube a jikinta, waro manyan idanunta tayi a fusace ta wanketa da mari, cikin zafin rai ta kalli kayan jijinta daya ɓaci da datti tace "you are fired"

cikin tsananin bukatan aiki matar tace "dan girman Allah kiyi hakuri"

ko jinta bata tsaya yi ba ta koma cikin gida ranta a ɓace ta cire uniform tasa kayan gida abaya light purple da mayafi siriri, wayarta ta ɗauka ta fita daga ɗakin, mota ta shiga driver ya jata zuwa school, fita tayi kowa yana kallonta da kayan gida da tazo, bata ko kallesu ba ta zauna a wajen zamanta tana jiran a bata question paper, da mamakinsu sukaga ta samu question paper harma ta gama ta fita daga class ta koma mota ta tafi.

*Jiddah Ce...✍🏻*

08144818849

[09/04 à 08:05] JIDDA MAPI: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*DUHU DA HASKE*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Na

*Jiddah S mapi*

*Chapter 3*

~Yau ake shirya gagarumin taro domin murnan kammala secondary school na manal umar maidawa, duk cikin school ɗin anyi decoration kuma da taimakon manal akayi hakan domin itace take tsara musu yadda zasuyi, bayan an gama guri yayi kyau sai masha Allah, fari da baƙi shine kalan uniform nasu hakan yasa sukayi ƙayata wajen da kayan ado fari da baƙi har zuwa wajen saukan manyan manyan baƙi, bayan ta gama gida ta koma domin yin shiri yau cikin murna take domin dady yayi mata alƙawarin zai mata manya manyan surprise a yau ɗinnan, towel ne ɗaure a kirjinta yayinda ta bazo gashinta da yasha gyara har zuwa tsayin towel ɗin da bai gama rufe cinyarta bama, daga wanka ta fito hakan yasa take ɗan kankame jiki, gaban mirror ta zauna akan stool tana kallon kanta a madubi, murmushi tayi tace "manal babu abinda kika rasa a rayuwa ke kanki kyau kike yiwa kanki bale wa mutane"

shafa fuskanta tayi tace "yau zanyi adon da ban taɓa yin irinshi ba"

kiran wayan Ammi ne ya shigo a hankali ta ɗaga tana shafa mai tasa a handsfree tace "hello Ammi na"

Ammi cikin murnan ganin ƴarta ta girma tace "manal mun tafi da dadynki da fatan idan kin shirya zaki fito da wuri domin dadynki ya aje miki surprise na tsadadden motarki a kofan gida wanda a ciki muke so kizo muci wajen taron karɓan takaddan kammala secondary ɗinki"

cikin jin daɗi tayi murmushi tace "thank you so much mom and dad"

katse wayan ammi tayi, da sauri tayi kwalliya wanda bai fito sosai ba, bayan ta shafa powder ta shafa mascara akan zara zaran eyelashes nata sannan ta shafa lipbalm akan lips nata, gashinta ta kame da ribbon fari sannan ta tashi tana shafa turaren jiki, kayan dake kan tamfatsetsen bed nata ta ɗauko farin riga ne kamar wedding gown da takalminshi me tsini, sawa tayi ta kalli lalle baki da ja dake kwance akan tafin hanunta da bayan hanun, murmushi tayi wanda tana jimawa bata yi ba, idan kaga tayi murmushi to tana tareda ammi ko dady, agogon hanu tasa wanda dady ya siya mata tsadadden rolex ne, ɗankunne da sarka duk na gold Ammi ta siya mata sabida wannan ranan, turare ta fara jiƙa jikinta dashi, ta ɗauko crown ɗin da Ammi ta bata tasa a saman kanta, kallon kanta tayi a madubi tace "wow wow wow kece miss world manal"

wayar da dady ya siya mata iPhone 16 da cover fari ta rike a hanunta kafin ta ɗauko karamin jakan dake ɗauke da adon duwatsu fari mai ɗaukan ido ta rike, fitowa tayi daga ɗakin fuska babu fara'a domin bata saba ba, tafiya take kamar boss, masu aiki sai bata hanya suke tana tafiya bayan riganta yana binta.

a unguwan tudun anan wata kyakkyawar budurwa ta tsaya akan mashin nata me ƙafa biyu, sanye take da riga da wando, wandon a buɗe yake sosai kamar skirt da riga baƙi me ratsin pink a hanu da wuya, hanun rigan a yanke yake, ta ɗaura bakin rigan sanyi a waist nata, gyara baƙin mayafinta take a daidai lokacin ta juyo da kyakkyawar fuskanta, masha Allah wannan yarinyar karshe ce wajen kyau, fara ce sal, ɗaga murya tayi ta buɗe karamin bakinta, da karfi tace "MAAAAAAAAN"

ganin bai leƙo kamar yadda ya saba ba ta ɓata tare tareda turo karamin bakinta ta kuma buɗe murya tace "maaaaaaaaaan"

sau uku tana kiranshi bai amsa ba kuma be fito ba, a yadda suka saba kullum da safe idan tazo nan ɗaukanshi akan mashin nata zai amsa ko kuma ya leƙo, wani ma riganshi a hanu yana sawa yake fitowa, sauka tayi akan mashin ɗin kamar zatayi kuka, fuska a shagwaɓe da gajiyan da takeji ta fara bubbuga kofan gidansu, da alama ta saba da wannan ihun idan zata kirasu tace "man ka buɗe kofa mana kazo zamuyi late"

ji tayi an buɗe kofan kallon matar dake tsaye tana mata murmushi tayi, tasa kafa cikin saurin data saba tace "umma man wai har yanzu bacci yake?"

wacce aka kira da umma kyakkyawar mata ce ta manyanta kaɗan, tana hamma tace "to AMEESHA ai dole yanzu ya tashi tunda kinzo irin wannan buga kofan naki kamar ana yaki ba dole yanzu ya tashi ba"

tana tafiya tana cewa "ai man baya ɗaukan komai serious bai damu da neman aiki ba nice na damu"

bankaɗe kofar ɗakinshi tayi ta shiga, tsayawa tayi tana kallonshi yana bacci ya rungume pillow ya cusa kanshi a cikin pillow, hannu ta ɗaura akan kwankwasonta dake ɗaure da rigan sanyi tana tuna ya zata fara tashin shi a baccin nan, da sauri tayi dariya sannan ta fita ta ɗauko roba a tsakar gidan, ruwa me sanyi ta ɗibo a randa ta ɗaura akanta da kyar ta kama hanyan shiga, wani matashin kyakkyawan yaro da ba zai wuce 20years ba ya fito daga wanka yana tsane jikinshi da towel, ganinta da bokitin ruwa ya buɗe baki zaiyi magana tasa yatsa a baki tareda waro mishi manyan idanunta alaman yayi shiru, cikin sanɗa ta shiga ɗakin taje inda yake kwance akan karamin gadonshi dake gefen na kaninshi ruwan ta juye akanshi, a firgice ya tashi daga baccin yana goge ruwan dake fuskanshi, ido ya zuba mata, subhanallah ashe duk wani me kyau a duniya akwai wanda ya fishi, wannan shine asalin kyau, gashin kanshi a kwance sosai luf, ya kara kwanciya sabida ruwan daya jiƙashi, gashin idonshi kuwa ba'a magana domin baƙi ƙirin kuma a kwance, karami baki ne dashi, idonshi yafi komai ɗaukan hankali a fuskanshi, kallon jikinshi yayi yanda ya jike har zuwa kan gadon, armless ne a jikinshi da wando three quarter, tana rike da waist da hanu ɗaya ɗayan hanun kuma tana nunashi dashi tana dariya kamar zata faɗi kasa, wanda yake tsaye a bakin kofan yasa hanu a baki shima yana toshe dariya, ganin bata daina dariyan ba yaji wani irin haushi, fizgota yayi da karfi ya wurgata kan gadon, waro ido tayi tace "dan Allah...dan Allah...dan"

ragowan ruwan dake cikin bokitin ya juye akanta, ihu tayi tace "sanyi wayyo umma"

tashi yayi yana cire rigan, faffaɗan kirjinshi ɗauke da kwantaccen gashi, yana gama cire rigan ya shiga toilet baiyi magana ba, tashi tayi tana turo baki tace "IMRAN bani riganka"

yana shafa mai yace "a cikin wardrobe"

buɗe wardrobe tayi ta ɗau riganshi me kyau longsleev ta fita, ɗakin umma tayi sallama sannan ta shige a time ɗin umma tana haɗa musu breakfast, da sauri ta fara cire bottle na gaban riganta tace "umma kinga man ya watsa min ruwan sanyi banyi mishi komai ba ko?"

umma tace "na sanki da neman tsokana fa ameesha anya ba kece kika watsa mishi ba?"

turo baki tayi a time ɗin ta cire rigan tasa na imran, ya mata kyau sosai ta bazo gashinta daya jiƙe tana so ya bushe kafin su tafi, umma ganin tayi fushi tace "yi hakuri nasan laifinshi ne, ai tun kuna kanana yake yawan tsokananki"

sai yanzu tayi dariya, fitowa tayi ta koma ɗakinsu bata kame gashin ba, zama tayi a bakin gadon Imran tana ganinshi yana shiryawa tace "man kasan me?"

girgiza kai yayi

tace "yau naji labarin wani company wai suna neman masu aiki shiyasa kaga na fito da wuri"

yana gyara suman kanshi ya lumshe ido a hankali ya kuma buɗewa sannan yace "kullum bakya barina nayi bacci sai zancen aiki aiki aiki"

murmushi tayi fuskanta ya koma serious tace "man ya zama dole ka neme aiki duba da iyayenmu maza basa raye, Abbana da Abbanka abokai ne tun suna yara, abotansu yasa har yanzu muke tare mun zama kamar family ɗaya, sun mutu rana ɗaya sanadin hatsarin mota, Allah bai basu kuɗi ba hakan yasa dole sai mun nema zamu taimaki iyayenmu mata, ka taimaki kaninmu Imran sannan na taimaki kanina farhan da ummanka da mamana, shiyasa kullum nake taƙura maka akan neman aiki"

kallonta yake ta cikin madubi yadda take hawaye tana magana tareda murza yatsanta, girgiza kai kawai yayi baiyi magana ba saida ya gama abinda zaiyi ya ɗauko takaddun school nashi yazo inda take, zama yayi a gefenta ya riko hanunta yana murzawa yace "my meesha ba gashi na ɗauko takaddun zamu tafi ba?"

a hankali ta jijjiga kai idonta yana kara cika da hawaye, kwaɓe kyakkyawan face nashi yayi sannan yace "to ina zanji farin ciki babbar kawata da muka taso tare tun muna yara tana kuka?"

a hankali tayi murmushi kanta kasa, tashi yayi yace "muje na gyara miki gashinki saimu tafi ko?"

share mata hawayen yayi da tafin hanunshi ya kaita gaban mirror, zaunar da ita yayi a gefen gadon Imran dake facing mirror ɗin, yana kallonta ta cikin madubi yana gyara mata gashin, cikin muryanshi me kashe zuciya yace "duk wanda ya auri wannan kyakkyawar kawar tawa gaskiya ya auri rigima"

duka ta kai mishi ya kauce yana dariya, Imran ya shirya tsaf cikin uniform ya rataya jaka saide fuska babu annuri, kallonshi tayi lokacin da zasu fita tace "ya dai? kake haɗa fuska lafiya?"

cikin ɓacin rai kamar zaiyi kuka yace "banida ko biyar a hanuna kuma nasan ya ABDUL ma baida kuɗi da zai bani"

murmushi tayi tasa hanu a aljihun wandonta tace "ga kuɗin mashin naka ga kuma kuɗin kashewanka sai kayi manage kasan tunda wannan rakwaɓaɓɓen motan man ɗin ya ɓaci muka fara tafiya akan mashin ɗina dan nasan motan ba zai taɓa gyaruwa ba"

dariya yayi ya rungumeta yace "thank you Ameesha"

shafa kanshi tayi tace "don't mind"

umma ta fito musu da breakfast tace "Abdul ka tsaya kuci abinci kada ku tafi da yunwa"

zaiyi magana ameesha tace "no ki barshi kawai saimun dawo"

cikin jin haushin aikin data dameshi saiya nema yace "nifa yunwa nakeji"

tace "umma sa mana a flaks"

juye musu tayi a flaks Imran kuma yana tsaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login