Showing 18001 words to 21000 words out of 83501 words

Chapter 7 - DUHU DA HASKE Hausa Novels by Jiddah S Mapi.docx

19 Sep 2025

2236

you amma baki kishin wata ta kwace miki best friend naki?"

tace "na yadda da best friend nawa nasan koda wata zata kwaceshi ba zai kwatu ba sabida ina nan nashi"

tayi magana tana nuna faffaɗan kirjinshi, murmushi yayi yace "na sani ai baki damuwa sabida kinfi yadda dani fiye da kanki"

fita sukayi, sallama sukawa umma tayi musu fatan alkhairi kafin suka tafi, itace ta fara hawa mashin, ya harɗe hanu a kirji yana kallon gefe ya ɓata rai, kallonshi tayi bayan ta tada mashin ɗin tace "hau mana"

yace "kullum kinasa ana kallonmu ace nine me barin mace tana jana a mashin gaskiya saide ni na jamu"

tace "kai kanka kasan na fika kwarewa a tuka mashin domin ni tun ina yarinya hawan mashin nake kai kuma tsoron mashin kake sabida haka ka hau mu tafi ko kuma na tafi na barka"

yace "saide ki tafi"

ranta ɓace tace "wallahi ba zan hau ka zubar damu ba"

ganin yana ɓata musu lokaci tasan haɗe da bayason zuwa neman aiki ne tace "my darling man?"

ɓata rai ya kuma yi, tace "hau mu tafi kada muyi late kaga fa time yayi kafin a gyara maka motarka mu fara tafiya a ciki ko? kayi hakuri kaji?"

da kyar ta lallaɓashi ya hau, tafiya ta fara dasu cikin kwarewa, tace "rikeni kada ka faɗi nasan halinka"

shiru yayi mata tasa hulan tuƙinta na mashin kawai taci gaba da tafiya, sunyi tafiya me nisa kamar zasu bar garin kafin yaga ta tsaya a kofan wani waje me kama da company, kallonta yake zai yi magana ta rufe mishi baki tace "shii"

aje mashin ɗin tayi suka shiga tare, murmushi tayi mishi ganin babu mutane daya na interview, zama sukayi akan dutse tana bashi labari yana jinta yayi shiru yana kallonta har lokacin da akace su shigo, tare suka shiga office ɗin zafi sosai, me interview yana zaune akan kujera yana da jiki sosai ga tumbi, yana ganinsu yace "have a seat zanje na dawo yanzu"

zama sukayi a kujera cikin nutsuwa, yana fita ameesha ta kwashe da dariya dama man ya lura tana ɓoye dariya tunda taga mutumin, tace "man kaga wani kato dashi, wannan tumbin nashi kamar zai haihu yau ko gobe, da gani da kuɗin haram ya cika tumbin" tashi tayi ta fara gwada tafiyan mutumin, man shiru yayi yana kallonta ta kwaikwayi muryanshi tace "have a seat bari naje yanzu zan da...."

waro ido tayi ta kasa karasa maganan ganin mutumin tsaye a bakin kofa yana kallonta, kuma da alama yaji duk abinda ta faɗa, a hankali cike da tsoro ta fara yin baya, a bayan Abdul ta tsaya ta kasa cewa komai sai rarraba ido, Abdul ne ya tashi yace "sorry...." hanu mutumin ya ɗaga mishi, a hankali tayi mishi raɗa cikin tsoro tace "mu tafi, mu tafi, mu tafi"

mutumin yace "ku ficemin da gani"

kafin ya kara magana sum sum suka fita daga office ɗin, da sauri ta kunna mashin ɗinta tace "hau hau da sauri"

hawa yayi taja da gudu ta bar wajen, a hanya ta rufe ido tace "ya Allah bakina babu control bana sanin lokacin da nake wani magana gashi yauma bamu samu aiki ba, Allah yaushe zaka bamu aiki?"

man ya ranƙwashi kanta yace "kin gani ko bakinki ya janyo an koremu"

tace "sorry man"

suna isa gida Imran yana ganinsu ya taɓe baki yace "yauma kamar kullum basu samu komai ba haka suka dawo gida marasa sa'a"

ameesha tace "me kace?"

yace "ba abinda nace"

tace "da yafi maka"

*_jiddah ce...✍️_*

08144818849

[09/04 à 08:06] JIDDA MAPI: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*DUHU DA HASKE*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Na

*Jiddah S mapi*

*Chapter 6*

~Manal meyasa zaki tafi da wuri baki bari na tashi a bacci ba?"

murmushi tayi tace "sorry Ammi akwai abinda zanyi ne yau a company an sani zane kuma yau akeso ya zama dole na zana kalan kayan a gaban maids ɗina domin su fahimci yadda ake fitar da sabon designing na kaya"

driving take hankali kwance tana waya, tayi kyau sosai cikin riga da wando baƙi na suit ba karamin kyau yayi mata ba, kasancewar yau tanada yin zane shiyasa tasa wannan dressing ɗin, tayi rolling kanta da baƙin jessy veil karami, ta fito sak balarabiya goran ruwa ta buɗe tana sha, ammi tace "har yanzu na kasa tashi manal a cikin kwanakinnan ina jin nauyin jiki gaba ɗaya jikina babu daɗi ga shegen cin abinci dana koya kamar hauka, ko banson cin abinci sai naci kuma dama na ɓoye miki ne sabida kada hankalinki ya tashi amma da naci abinci nake amarwa"

da sauri tace "haba ammi shine zaki ɓoyemin rashin lafiyanki bari ina zuwa"

katse wayan tayi ta kira Dr Aisha tace "kije gida yanzu ammi babu lafiya ki dubata"

katse wayan tayi tace "na kira dr A'isha zata zo yanzu ta dubaki"

a hankali tace "to manal saikin dawo bye"

tace "love you ammi"

ammi tace "love you too"

koda ta isa company bata tsaya ɓata lokaci ba cikin action nata tace "kowa ya shirya zamu fara program yanzu"

duk suka nutsu tsit suna kallonta, babban black boat da tarin fentin zane aka kawo mata, stool ta janyo ta zauna, takalmin kafarta me tsini ne sosai, tasa aka kashe wuta wani abu kamar tv ta kunna a jikin bango kato sosai, ta kawo fentin ta fara zane duk abinda ta zana suna gani a jikin tv ɗin, rigan amarya ta zana me kyaun gaske tayi fentin kalan yayi kyau domin kuwa matured color ta zaɓo wato dark purple da adon black a jiki, color ɗaya ne ya rage ta kara ajiki ta juya fuskanta kamar kullum tace "a cikinku waye zai cika mana sauran kala ɗaya daya rage?"

duk sukayi shiru suna tsoron amsawa dan zata iya koran mutum idan ya faɗi abinda be mata ba, cikin ɓacin rai tace "waye zai cika mana ɗayan color daya rage?"

tsit ko tari bakaji, ranta yayi mummunan ɓaci cikin daka tsawan da yasa duk jikinsu ya fara rawa tace "kuna nufin a haka zakuyi aiki dani baku san komai ba akan zane? idan bana nan aka kawo aiki waye zaiyi a cikinku? ta ya zan zauna babu wanda ya kware a zane kamar yadda na kware?"

cikin ɓacin rai ta kashe tv sannan ta ture black boat ɗin tana huci tace "banga amfanin yi a gabanku ba jahilan banza marasa tunani"

fita tayi a fusace take tafiya kamar zata tashi sama, tana fita suka saki numfashi me kyau domin duk jinin jikinsu ya tsaya da aiki, manal nada kwarjinin da ko wani namijin baida shi, musamman idan ranta a ɓace ko fuskanta ka gani ba zaka iya mata magana ba, gaba ɗayanta fusatacciya ce, zata wuce waje taga me mopping tana cigaba da aiki bata tsaya ba, wani irin mugun kallo ta aika mata da sauri ta durkusa kasa tace "sorry madam"

cikin fusatan da take ciki taje inda take tsaye da sandan mopping da roban ruwan ta kalleta sama da kasa, kanta kasa jikinta yana rawa tace "sorry madam"

itafa babu abinda yake kona mata rai kamar taji ance mata sorry, ta tsani a bata hakuri, roban ruwan ta ɗauka tana cigaba da kallon fuskan yarinyar, ɗaga roban tayi sama daidai kan yarinyar ta fara tsiyaya mata ruwan, kankame jiki tayi tana jin masifan sanyin ruwan kamar daga frij aka ciro, rufe ido tayi tana hawaye, saida ta juye ruwan duka a jikinta sannan ta kifa mata roban akanta ya rufe fuskanta ta juya ta bar wajen, tana fita wayarta ya fara ringing dubawa tayi taga ammi, ɗauka tayi cikin kakkausan muryanta da babu tsoro ko wani shakka tace "ammi na"

cikin murna ammi tace "ki dawo gida yanzu akwai good news"

zatayi magana ammi tace "please manal this is the first time da zan rokeki kibar aikinki ki dawo gida"

a hankali tace "okay ina zuwa"

kallon agogo tayi taga lokaci bai tafi sosai ba, daga inda take ta buɗe motarta da remote, tana zuwa ta shiga ciki ta zauna, ɗaga glass tayi gateman da gudu ya buɗe gate ta fita, gida ta nufa tayi parking a compound ta fito tana tafiya cike da yanga da kasaita, da hanu ta kira wata me share cikin gidan, a tsorace tazo ta durkusa kasa babbar mata ce ta manyanta sosai, tace "gani hajiya"

cike da rashin walwala tace "dr A'isha tazo?"

da sauri tace "eh tazo hajiya"

bata ƙara magana ba ta tafi zuwa ciki, tun a kofan main parlour taga ammi tazo da gudu ta rungumeta, tsananin murna ne akan fuskanta da alama akwai abin farin cikin daya sameta wanda bata taɓa jin irinshi ba, cikin jin daɗi ta ɗaga manal tana juyi da ita, manal murmushi take tana kallonta, saida ta sauketa tace "ammi meya faru kike wannan farin cikin?"

hanunta ta rike ta zaunar da ita akan sofa, itama zama tayi bata saki hanunta ba tace "manal wannan shine karon farko a duniya da uwa zata fara faɗawa ƴarta wannan labarin"

cikin rashin fahimta tace "ammi menene?"

cikin jin daɗi tace "manal I'm pregnant"

kirjin manal ya bada sautin dum dum dum

idanunta suka kara girma tana kallon ammi kamar gunki, jinta da ganinta suka ɗauke a lokaci guda, ammi tayi shiru tana kallon yanayinta, jikinta yayi sanyi tace "manal?"

ganin jikin ammin yayi sanyi tace "wow am shocked, ammi kenan za samu kani ko kanwa?"

ammi tace "yes manal zaki samu ƙani ko kanwa by god grace"

a ranta tace "kenan zamu zama mu biyu da wata ko wani akan ammi da dady?"

a fili kuma tace "wow congratulations bari na kira dady na faɗa mishi duk da yayi tafiya"

rike wayan tayi tana girgiza kai tace "ba yau ba, gobe zai dawo daga tafiya da yamma kamar karfe huɗu ni da kaina zan sanar mishi kuma zanso kiyi min decoration na gidannan yayi kyau sosai domin nafi son nayi celebration wajen faɗa mishi kuma kema ki tayamu"

murmushi tayi tace "to ammi zan tayaki gobe da kaina zan shirya gidannan domin nasan dady zai fiki farin ciki"

rungumeta ammi tayi tace "manal farin cikin da nake ciki bazan iya misaltawa ba"

hawaye ne ya zubo mata, da sauri ta share mata hawayen tace "please don't cry"

murmushi tayi tace "ina cikin farin ciki"

tace "ammi banda kuka please"

a ranta sam bataji daɗi ba, babu abinda ta tsana kamar haɗa abinta da wani, idan tanada abu tafi son ta zauna da abin ita kaɗai babu wanda zai taɓa, yanzu gani take cikin ammi zai iya shiga tsakaninta da ammi da dady, kawar da tunanin tayi, bata koma wajen aiki ba kuma tayi niyan gobe ma ba zata je ba.

washe gari tana tsaye akan kujera hanunta ɗauke da igiya me yalƙi tana ɗaurawa akan labulen ɗakin, dogon riga ne a jikinta roba roba mara hanu, tayi kyau sosai da hulan net ta cusa gashinta a ciki, cikin ɗakin yayi kyau sai yalƙi ke tashi ta ko ina, ƙamshi ne yake tashi tako ina, ammi ta fito daga ɗaki rike da waya tace "manal gashi dadynki"

tana daga tsaye ta karɓa ta kara a kunne tace "dadyyyy"

yace "yes ya kuke? yau zan dawo"

murmushi tayi tace "to dady saika dawo"

hira sukayi kaɗan kafin ta baiwa ammi tana kallonta tana murmushi tana yin wayan, da sauri ta ɗauke kai taci gaba da aikinta, ammi bayan ta kashe wayan ta kalli ɗakin tace "wow manal kin iya shirya ɗaki You are the best decorator in the world"

murmushi tayi tace "thank you"

leshi ne me tsada a jikin ammi peach color, sai glowing take kana ganinta kage me ciki domin tayi kiɓa sosai basu ankara bane domin har cikinta ya ɗan fito kaɗan, ta zauna akan sofa tace "manal sauko ki huta"

saukowa tayi tana rike bayanta alaman ta gaji, kallon dining tayi yadda ammi ta shirya warmer's ɗin data yiwa dady zazzafan girki ga juice kala kala data haɗa mishi, kallon ammi tayi taga sai kallon hoton dady take yi, tace "ammi bari naje na karɓo cake ɗin dan tamin saƙo ta gama baking"

buɗe wayanta tayi ta nunawa ammi hoton tace "kin gani"

murmushi ne fal a fuskanta ganin an rubuta "happy anniversary to you umar maidawa"

Ammi ce tasa aka rubuta hakan domin kuwa yau anniversary ɗinsu ne suna shekara 28 da aure, tace "yayi kyau sosai nasan idan dadynki ya gani zaiji daɗi sannan na dafa mishi favorite food nashi kiyi sauri kije ki ɗauko kafin ma yaje airport ya zama komai ya kammala"

da sauri ta shiga ɗakinta ta ɗauko wani guntun hijabi tasa, fitowa tayi tana danna remote na motarta tace "bye ammi"

ammi dake fesa turare tace "saikin dawo"

fita tayi da sauri take driving domin taji tana son cin cake, sunada nisa tsakaninsu da me baking ɗin tayi tafiya sosai kafin ta isa gidan, a kofa ta tsaya tana hon bata fito ba kuma bata daina hon ba, ranta ya ɓaci ganin matar bata kawo mata ba a fusace ta juya zata tafi taga matar ta fito da sauri, sauke glass tayi tana kallonta harta karaso wajenta, tace "kiyi hakuri na tsaya neman....."

karɓa tayi kawai taja motar bata tsaya jin me zatace ba, matar da kallo ta bita har ta fita a layin, driving take tana kallon cake ɗin a sama an rubuta sunan dady, ɗago kai tayi tana maida hankali kan hanya, da sauri ta koma baya ganin kamar motar budurwa dady ne a fake gefen hanya, nesa dasu tayi sannan tayi parking tana kallonsu ta cikin tinted glass, gani tayi dady ya sauke glass yana wurgar da ɓawon ayaba, runtse ido tayi ganin yarinyar ta shafa jikinshi tana kissing nashi tako ina tun kafin ya ɗaga glass ɗin har ya ɗaga, buɗe ido tayi a hankali, waya ta ɗaga tayi kira, ana ɗauka tace "nice nazo hotel naku rannan na baka miliyan ɗaya sabida kamin bincike na musamman"

shiru tayi sai kuma tace "ina jinka"

cikin kasa da murya yace "ko jiya suna tare domin anan ya kwana"

murmushin gefen baki tayi lokacin da taga ta fito daga motar tana gyara skirt ɗin dake jikinta sannan daga can gefe me gyaran takalmi ne da alama wanke mata takalmi yake, a hankali tace "thank you"

kashe wayan tayi ta kalli cake ɗin dake hanunta, daidai inda aka rubuta sunanshi tasa hannu ta dama ta watsar a waje, saida taga idon mutane babu dayawa sannan babu motoci a gefen titin ita kuma wacce akace mata sunanta zee tana can hankalinta akan me gyaran takalmi ta kunna motarta da mugun speed ta nufi motar da yake ciki gadan gadan, ganin bishiyan dake gaba dashi kaɗan ta kara gudun, bige motan tayi da karfi ta tura saida taga ya fara gangara kafin ta juya da gudu tayi nesa dasu ta yadda babu wanda zai ganta, ido ta zuba mishi tana ganin alaman hanunshi yana bubbuga jikin glass, hankalin zee ya dawo kanshi ihu tayi ganin motar zata bugu da bishiyan, rufe ido tayi lokacin da motan ya bugu da jikin bishiya atake ya tarwatse ya kama da wuta, ihu zee take yi tana neman taimakon jama'a, mutane suka taru makil a wajen suna kallon yadda motan yake ci da wuta, kowa yana kokarin kashewa amma abin yayi nisa domin har bishiyan saida ya fara ci da wuta, tana zaune daga cikin motan tana murza yatsun hanunta idanunta akan motar har ya zama toka, rufe ido tayi ganin ƴan sanda sunzo wajen zee ta gani ta silale ta gudu sabida tasan dole saita amsa tambayoyin ƴan sanda, murmushin gefen baki manal tayi ganin ta shiga mashin tada motan tayi ta fara binta har zuwa hotel ɗin, facemask manal tasa lokacin da zata shiga ciki, tana ganin zee ta shiga ɗakin hotel zata rufe kofa tasa hanu ta damƙe kofan, a tsorace ta kalleta, murmushi tayi ta cikin facemask taki yadda ta cire sabida tasan ba'a rasa cctv camera, duk yadda taso ta rufe kofan ta gagara, shigowa manal tayi ta rufe kofan gam, jikin zee ya fara rawa domin ta gane itace rannan ta rike mata hanu, a bakin gado ta zauna ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tace "zee zee zee ya naga duk a tsorace kike kamar kin aikata wani laifi?"

shiru tayi tana neman hanyan gudu amma kofa yaki buɗuwa, tace "laa ko dai kinyi kisa ne kin ture mutumin dake cikin mota ya gangara ya bugu da jikin bishiya motar ta kone?"

zaro ido tayi cike da tsoro tace "wacece ke?"

dariya tayi sosai tace "sunana MANAL UMAR MAIDAWA"

idanunta a waje tace "kenan ke ƴar Alhaji ce?"

gyaɗa kai tayi tace "yes ni ƴarshi ce ke kuma fa?"

shiru tayi, tace "kema ƴarshi ce? ko matarshi?"

jin tayi shiru tace "ko dai karuwarshi?"

cikin tsoro tace "dan girman Allah kiyi hakuri ki fita a ɗakinnan bansan komai akan mutuwanshi ba"

dariya tayi sosai tace "to ai nazo ne na kuɓutar dake daga ƴan sanda, kinga wannan video?"

nuna mata video time ɗin da suke cikin mota da kuma time ɗin data fita tayi, sai tace "kinga kin kasheshi sabida ki kwashe komai nashi ciki harda wannan atm ɗin dake hanunki"

sai yanzu ta kula akwai atm a hanunta tace "wallahi talla...."

cikin tsawa tace "shiru"

tsit tayi, tazo gabanta ta tsaya, kwance mayafinta tayi tace "karɓi wannan mayafin naki"

karɓa tayi tace "so nake ki rataye kanki idan kuma ba haka ba sajna kira ƴan sanda na nuna musu wannan video sannan na bada manyan kuɗaɗe a lalatamin rayuwarki"

durkusawa kasa tayi tace "amma kinsan kuskure kike aikatawa na kisan kai? ke ki kashe mahaifinki da hanunki?"

cikin zafin rai tace "zaki aikata abinda nace ko saina kira ƴan sanda kinyi rayuwan crack?"

ganin ta ɗau waya ta karɓi mayafin ta kalli fanka dake ɗakin, ɗaurawa tayi ta runtse ido ta ɗau stool, tana kuka tana rokonta manal ta ɗaura kafa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login