Showing 21001 words to 24000 words out of 83501 words
ɗaya akan ɗaya tana kallonta har saida ta rataye kanta taga bata numfashi kafin tasa hanunta a handglove ta ɗau wayarta ta turawa police text cewar "nice zee nice na kashe Alhaji umar maidawa domin na kwashe kuɗinshi amma dana dawo sai naji labarin kuna nemana shiyasa na kashe kaina"
tana gama turawa ta wurga wayan akan gado ta cire handglove ɗin, ba tareda ta taɓa ta ba tasa mata a hanunta sannan ta fice daga ɗakin, motarta ta shiga ta wuce gida, a bakin kofa ta tsaya tayi shiru, a hankali ta tura kofan ta shiga jikinta a mace, gani tayi ammi ta taso a haukace idanunta sun kumbura sunyi jajur ga hawaye dake wanke fuskanta, ta riketa da karfi tace "manal ina waya da dadynki naji yayi wani kara daga nan naji mutane suna ihu wai wuta, ina jinshi yana nishin azaba da ihu har nazo naji yayi shiru, manal ya dadynki ya mutu ne? manal dan Allah ki tasheni daga baccin da nake, shi kaɗai nake dashi shi kaɗai ya ragemin a duniya, manal Allah yasa mafarki nake"
shiru tayi tana kallonta a lokaci ɗaya ta zama karamar mahaukaciya, tana cikin kuka da ihu taji kiran waya, da sauri ta ɗauka cikin ruɗewa tace "hello my love kaine ko ka kirani da wani number domin ka tabbatarmin bada gaske abinda nake tunani ba ko?"
ji tayi ɗan sanda yace "hajiya muna me baki hakuri mijinki ya mutu sannan mun samu gawan wacce ta kasheshi a hotel zamu tura miki abinda ta rubuta ki karanta da kanki"
kashe wayan yayi ammi ta bushe ko motsi batayi, wayanta yayi kara alaman sako ya shigo, tana duba taga abinda aka rubuta, kasa take shirin faɗuwa manal ta riketa, gani tayi ta suma a jikinta idonta rufe, da karfi tace "ammi ki tashi, ammi ki tashi mana"
ji tayi an fara hayaniya a kofar gidansu, kwantar da ammi tayi a gefe ta fita domin ganin meke faruwa, gani tayi mutane sunata faɗan maganganu marasa daɗi "dama ɗan iska ne karuwa ce ta kasheshi"
komawa ciki tayi ta watsawa ammi ruwa a jiki, numfashi me tsayi taja sannan ta buɗe ido a wahale, tace "bacci nake ko manal? mafarki nake ko?"
girgiza kai tayi idonta fam da hawaye tace "da gaske ne ammi dady ya tafi ya barmu"
jin abinda mutanen suke faɗa ammi tayi, a hankali ta tashi jikinta kamar an zare laka, lekawa tayi kofa domin gani da idonta, ji tayi suna faɗan magananganu marasa daɗi, komawa ciki tayi tana shiga falon ta zube kasa a sume, manal ce ta ɗagata ta kwantar da ita akan sofa ta kira dr A'isha, tana zuwa ta fara dubata alluarai tayi mata sannan ta ɗaura mata drip ta tafi, saida ta jima tana bacci a hankali ta fara buɗe idanunta da sukayi nauyi ganin drip a hanunta ta fizge zata tashi tace "ina umar yake? ina yake manal?"
cikin tsawan da yasa jikin ammi rawa manal tace "will you please shout up your mouth"
tsit ko numfashin kirki bata kara yi ba, sai kallon manal ɗin da take a mugun tsorace, idanunta sunyi jajur cikin huci tace "kina ji akace miki a macen da suke zama a hotel tare ta kasheshi, hakan ya nuna bama tafiya yayi ba yana can tare da mace yana cutar dake, kina neman haukata kanki sabida maci amana"
a hankali tace "manal ba...."
a tsawace tace "shiru!!!!!!"
jikin ammi ya fara rawa dan bata taɓa ganinta cikin ɓacin rai haka ba, rungumeta manal tayi ganin jikinta yana rawa, shafa bayanta tayi a hankali alaman lallashi tace "ki koyi rayuwa babu shi, kada naji koda wasa kin kira sunanshi, sannan duk wani abinda kikasan ya shafeshi ki tabbatar kin kona ko kuma kinyi kyauta dasu"
shiru tayi tana jinta, tashi tayi ta shiga ciki, daga kan hotonsu ta fara harma da zanenshi da takeyi, zuwa kayanshi ta fito dasu, ammi tana ganinta tace "manal me zakiyi?"
a tsakiyan falon ta aje taje kitchen ta ɗauko fetur da ashana tazo a gaban ammi tasa wuta, waro ido ammi tayi tasa hanu a baki tana kallonta, zagaye kayan take ta goya hanu a baya tana kallon yadda yake ci da wuta, ammi ganin hoton da suka ɗauka ranan aurensu yana konewa da wuta taje da gudu zatasa hanu ta cire manal ta fizgota, a haukace tace "manal hotona da umar nefa ki barni naje na cire"
kankameta tayi duk dukan da ammi take mata bata ko girgiza ba har saida komai ya kone kurmus kafin ta saketa, faɗuwa kasa ammi tayi akan gwiwanta har yanzu hanunta a baki tana kallon tokan hawaye yana bin kuncinta yana zuba zuwa hanunta, cikin zafin rai tace "to idan kin kona komai cikinshi dake jikina kuma fa manal?"
fuskanta a ɗaure ta kalli ammi sai kuma ta shiga ciki batayi magana ba, akan gado ta faɗa tayi shiru ta rufe ido.
har dare ya ratsa ammi tana wajen bata motsa ba, saida bacci ɓarawo ya saceta manal tazo ta ɗagata ta kaita kan gadonta, zama tayi kusa da ita ta ɗan kishingiɗa akan gadon tana kallon kyakkyawan fuskan amminta, hawaye yana bin fuskanta da haka har bacci ya ɗauketa itama, washe gari ammi ce ta fara buɗe idonta da sukayi mata nauyi, ganin manal kwance a jikinta taji wani irin tausayin kansu ya kamata, manal batada kowa sai ita, itama batada kowa sai manal da kuma umar gashi ya mutu ya barta, share hawaye tayi a hankali ta fara zame jikinta domin zuwa yin alwala, buɗe ido manal tayi a hankali tana kallonta cikin sanyin murya tace "ammi na kin tashi?"
share hawaye tayi tace "na tashi manal"
riketa tayi ta kaita toilet, saida tayi wanka sannan tayi alwala koda ta fito manal ta cire mata kayan da zata sa marar nauyi da mayafi, sawa tayi bata damu data shafa mai ba ta shinfiɗa sallaya ta tada salla, addu'a take tayi tana kuka da haka har tayi sallama ta zauna shiru da carbi a hanunta, manal tazo ta kwantar da kanta a cinyarta tayi shiru.
da haka tayi kwana uku bata cin komai sai ruwan zafi take sha shima sai manal ta tsawata mata kafin take sha, haka suke zaune a gidan shiru babu hira babu komai, dama manal bata hira sai kuma abinda ya faru ya kara sa ta zama miskila domin idan ta zauna bata magana da kowa saide ta haɗa rai kamar yadda ta saba, gara da idan taga dama tana murmushi amma yanzu zata iya wuni ta kwana ta tashi batayi murmushi ba, komai ta maidashi serious, bata wasa bata kallo bata yin wani abu da zaisa taji daɗi a rayuwarta wannan ɗabi'an kuma tun tana yarinya haka take, yau tayi niyan zuwa aiki tun safe ta gama shiryawa ammi komai na buƙata domin bataso idan ta tashi daga bacci ta wahala, bayan ta shirya cikin hijab baki da siririn mayafi tafi gane sa takalmin me tsini, ta fito daga ɗakinta ta shiga ɗakin ammi dake bacci, murmushi tayi ta shafa gefen face nata tace "bye"
juyawa tayi zata tafi sai kuma ta juyo tana kallon ammin, kallon cikinta tayi sai taji gabanta ya faɗi, a ranta tace "wannan cikin be kamata ya zauna ba ya zama dole na zubar dashi"
murmushin gefen baki tayi sannan ta fita, tana fita ammi ta buɗe ido, a hankali tace "alhmdllh tunda ta fita yau zan iya kallon hoton umar ko zanji daɗi a raina"
hotonshi ta ciro daga ƙarƙashin gadon data ɓoye ta fara kallo tana murmushi tana hawaye, tana shafa cikinta tace "baka nan amma ina jinka a jikina, wannan cikin kaɗai nake gani ina jin daɗi kuma ina ganin baka barni ba, koba komai zan haifi ɗan da kaine ka samar dashi, zan haifu mana Umar abinda mukayi Shekara da shekaru muna nema, duk da abinda kayi na yafe maka duniya da lahira domin baka taɓa cutar dani ba a zamanmu da kai, koda sau ɗaya baka taɓa cutar dani ba, nasan kowane mutum da irin ƙaddaranshi kaima Allah ya kaddara maka hakan ne amma nasan ba halinka bane, koda kayi hakan to nasan sabida ni kayi, kanason mace amma kana jin kunyan karamin kishiya sabida na rabu da iyayena domin kai, kuma na tabbata wannan itace kaɗai macen da kake bi, nasan halinka umar nasan abinda zaka iya da wanda ba zaka iya ba, Allah ya yafe maka nasan sabida ni ka shiga wannan halin amma kai ba mazinaci bane nice shaida, kuma nayi alkawarin kula da duk abinda na haifa zan bashi tarbiyya irin yadda kake cewa zaka bawa ƴaƴanka idan muka haifa.
manal koda taje office ta wuni tana plan ɗin yadda zata zubar da cikin, bayan ta tashi daga aiki da yamma taje chemist tana shiga bata kula da mazan dake cikin chemistry ɗin ba ta ciro kuɗi masu yawa ta aje tace "abani maganin abortion"
duk suka kalleta bata kulasu ba tace "akwai ko babu?"
meshi ya kalli kuɗin data aje mishi yace "akwai"
bata yayi ya nuna mata yadda zatayi, ɗauka tayi ta fita daga wajen bata yiwa kowa kallo sau biyu ba, ɓoyewa tayi a jakanta lokacin data shiga gida ta samu ammi tayi musu girki, daɗi taji a ranta ganin ammin tana zaune akan sofa tana kallo, murmushi tayi mata tace "sannu ammi"
cikin murmushin tace "yawwa kin dawo?"
gyaɗa kai tayi ta wuce saida ta canja kaya zuwa na shan iska kafin ta fito ta kwanta kusa da ita ta ɗaura kanta a cinyarta itama tana kallo, a hankali ammi take shafa kanta, ji tayi cikinta yayi motsi tace "manal?"
cikin sanyin murya tace "umm"
tace "naji cikina yana motsi tun ɗazu inata addu'a Allah yasa namiji zan haifa"
bataso ta gano komai tace "Ameen"
murmushi ammi tayi tace "idan na haifi namji zansa mishi suna faruk"
tace "okay Allah ya kawoshi"
tace "ameen manal"
*Jiddah Ce....✍️*
08144818849
[09/04 à 08:06] JIDDA MAPI: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*DUHU DA HASKE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 7*
https://chat.whatsapp.com/CGf8vl2tuAo75eBYR6Yl7h
~Da sassafe ta tashi da kanta ta shiga kitchen tana girki, bata iya komai ba sai indomie data jiƙa ta zuba a cikin plate ta rufe ta kai dining, juice ta juye na gora a cikin cup guda biyu kala ɗaya, saida tasa shaida a jikin cup ɗin ta yadda zata gane nata da wuri, ciro maganin da aka bata tayi ta zuba a cikin juice ɗin, juyawa tayi saida ya narke ta fito dashi a hanu tana murmushi, a kusa da abincin ta aje ta juya zuwa ɗakin ammi fuskanta fal murmushi, knocking tayi kana ta shigo, ammi na zaune abakin gado tasa hanu a cikinta tana shafawa yayinda idanunta suke kan hoton dady, ganin bata san ma ta shigo ba ta tafa hanu kamar karamar yarinya ta maida face nata tace "Ammiiii"
a firgice ammi ta ɓoye hoton karkashin pillow tayi saurin share hawaye tace "manal"
takawa take tana yi kamar me rawa har ta isa inda take, faɗawa kan gadon tayi ta kwanta tana kallon pop na ɗakin, kafafunta a kasan gadon tace "ammi tun ɗazu nake jiranki na gama breakfast"
murmushi tayi cikin innocent face nata tace "to manal muje dama yunwa nake ji"
tashi tayi ta rike hanunta suka fito, kallonta take tana kallon cikin daya fara nuna kanshi, akan kujera ta zaunar da ita kana ta matso da abincin gabanta tace "eat"
kallo tayi da ganin indomie kasan bai dahu ba, tace "to manal"
ci ta fara itama manal ta zauna suna ci tare, ammi zata ɗau goran ruwa tayi saurin tura mata cup na juice, ɗauka tayi tasha, suna haɗa ido manal tayi mata murmushi itama ta mayar mata, da haka har suka gaba cin abincin, saida ta tabbatar ta shanye juice ɗin duka kafin itama ta shanye nata, tashi tayi tana tafiya tana cewa "yau zan tafi aiki ina fatan ba zaki zauna kina kuka a gida ba"
tace "ba zanyi kuka ba"
tace "okay"
ɗakinta ta shiga, kayan jikinta ta cire sannan ta ɗaura towel ta kwance gashinta domin zata wanke, zata shiga toilet ta dawo da baya tana kallon kanta a madubi, murmushi ta yiwa kanta tace "nice manal"
shiga tayi ta fara wanka da tsadaddun sabulanta da shower gel, gashinta ta zuba shampoo me kamshi wanda dady ya dawo mata dashi daga kasar paris, yana kamshi sosai kuma yana maida gashi baki ƙirin da laushi, ta jima tana wankan kafin ta fito ta ɗaura towel a kirji santala santalan cinyoyinta farare tas suka bayyana domin karami ne towel ɗin, ɗayan pink towel ɗin kuma karami ta ɗaura a kanta tana tsane ruwan, wajen mirror, gaban mirror cike fam da kayan mayuka da turaruka, zama tayi ta ɗauko dryer ɗinta da dady ya siya mata shima a paris, busar da kanta tayi sannan ta fara shafa mayuka, saida ta ɗau lokaci a wajen kafin ta tashi ta buɗe wardrobe, kayanta a jere suna kamshi zaɓo wani yadin larabawa tayi yana sheƙi ammi ta siya mata a makka, dogon riga fited gown ne baƙi ya zauna a jikinta ya fitar da duk wani shape nata, yanada ado sosai a jikin domin sheƙi yake yana walƙi, takalmi me tsini tasa baƙi ta yafa karamin mayafi akan gashinta da tayi parking, kallon fuskanta tayi idan ma batayi kwalliya ba tafi kyau, fesa turaren tayi sannan ta buɗe drower tana kallon tulin gilasanta, ɗauko babban cikinsu tayi half face tasa a idonta, jakanta baƙi kiran gucci ta rike a hanu ta ɗau makullin mota tana tafiya tana karkaɗa makullin tana hura fito da ɗan karamin bakinta, wani irin smiling da yake kara mata kyau ta yiwa ammi ganin tana kwance tana kallo, itama ammi murmushi tayi sannan ta ɗaga hanu tayi mata alaman kinyi kyau, tace "ammi na tafi"
tace "saikin dawo Allah ya tsaremin ke"
tace "ameen"
tafiya take tana fito har ta isa wajen motarta, shiga tayi cikin natsuwa take driving, me gadi yace "fuska kullum babu dariya kamar me ɗaukan rai"
tana shiga company tayi parking, makullin motar a hanu tana kaɗawa tana fito duk wanda ta gani yana durkusawa ya gaisheta hanu kawai take ɗaga musu idan taga dama tana cigaba da fito harta shiga ciki, duk suka daina aiki da computer ɗin gabansu suka tashi daga zaunen da suke suna mika mata gaisuwa, tsayawa tayi tana karewa kowa kallo a cikinsu, gani tayi kujeran mutum ɗaya babu kowa, sunan dake jikin kujeran ta kalla tace "ina rahma husain?"
sukace "bata zo ba"
jijjiga kai tayi tace "meyasa?"
a takaice take yin magana bata yadda magana yayi mata tsayi, wani daga cikinsu wanda aka rubuta kamal a jikin kujeranshi yace "babanta baida lafiya"
tace "shiyasa bata zo ba?"
duk suka kalli juna jin abinda ta faɗa, tace "shiyasa bata zo ba"
a hankali yace "eh"
tace "okay"
zuwa tayi wajen kujeran ta cire daga cikin masu zama a wajen, waje ta fitar da kujeran sannan ta ɗauke laptop ɗinta bata yiwa kowa magana ba ta wuce office nata.
wayan office aka kira tana ɗauka akace "muna magana da c.e.o ɗin companyn m.u.m ne?"
tace "eh kuna magana da manal umar maidawa"
daga ɗayan ɓangaren akace "munga zanen da akayi daga company ɗinki sannan mun fitar da sabbin kaya irinshi, munaso mu haɗa hannu da company ɗinki zamu baki contract ɗin zana mana sabbin kayan da zamu fitar a sabon shekara"
tana juyi akan kujera a takaice tace "kamar guda nawa?"
yace "munaso kamar kala dubu biyar"
shiru tayi tana nazari sai kuma tace "okay zaku iya zuwa ku aje kuɗinku aiki zai kammala bada jimawa ba"
yace "akwai account number ɗinku na m.u.m a wajena zansa naira biliyan goma idan an gama aiki zan cika Biliyan uku sabida daga china aka bada order kuma kasashe da dama suna jiran sabon kayan da za'a fitar"
cikin kakkausan murya tace "idan kasa biliyan goma sha uku duka a account zaka samu aiki idan kuma ka rage koda naira biyar ne a ciki ba zanyi aikin ba"
zata kashe wayan yace "tsaya zansa duka"
tace "okay"
tana zaune taji karan message alaman kuɗin ya shigo account ɗin m.u.m murmushi tayi ta tashi daga zaunen ta fita zuwa waje, suna ganinta suka tashi, goya hanu tayi a baya tana zagayesu ta fara magana "an bamu aikin zane guda dubu biyar kuma kunsan ba karamin aiki bane, inason kara girmar da company ɗin m.u.m fashion designing ta yadda daga ƙasashen waje kawai zamu rinƙa karɓan aiki, to amma hakan na zai faru ba domin naga baku da kwarewan da nakeso a zane, wannan dalilin yasa dole mu nemi kwararre wanda ya kware wajen zana zane hakan zaisa mu kara samun mutane dayawa susa hannun jari da company ɗinmu, mu rinƙa karɓan manya manyan contract daga manyan kasashen duniya, kunga wannan?"
takadda ta nuna musu na neman kwararren me zane, tace "photocopy ɗinshi zakuyi kamar guda ɗari ku manna a kowane bango da kuka san zai janyo hankalin mutane, sannan a social media kowa yayi posting cewar company ɗin m.u.m fashion designing suna neman ƙwararren me zane, a yadda na kware a zane ba lalle a samu wanda ya kaini ba, nasan nice kaɗai a nigeria nake iya zana duk abinda naga dama kuma ya fito fes, hakan yasa kowa yakeson ganin manal tayi mishi zane, nasan ba za'a samu wanda ya kaini ba amma may be a samu wanda ya kware ina fatan kun fahimceni?"
a tare sukace "yes madam"
tace "okay a fara yanzu yanzu"
duk suka buɗe laptop daga tsayen sun kai su goma sha biyu suka fara posting a social media ta yadda zai tafi viral, farko a account ɗin m.u.m suka fara posting kafin sukayi da sauran personal account nasu, me photocopy kuma yana gefe yana copy ɗin saida yayi guda ɗari ya raba musu suka fita domin mannawa, manal wayarta aka kira ta amsa "ammi"
cikin jin ciwo tace "manal an kirani a