Showing 48001 words to 51000 words out of 83501 words

Chapter 17 - DUHU DA HASKE Hausa Novels by Jiddah S Mapi.docx

19 Sep 2025

2247

kyafta ido baya yi ita kuma bata kula da hakan ba sai dariya take yiwa Imran wanda ya ɓata rai kamar zaiyi kuka, fararen hakoranta suka bayyana, kallon man tayi ta ɗaga mishi gira tareda kashe ido tace "ya dai malam kallon fa?"

murmushi yayi ya zameta daga jikinshi ya tashi ya bar wajen, taɓe baki tayi ta ɗau chocolate ɗin ta mikawa imran tace "gashi ba dan halinka ba"

yace "banso"

tace "to"

ci zatayi ya kwace tayi dariya sosai tace "kana ganin zan lallashe ka ne?"

yace "amma ai idan ya man ne yayi fushi kina lallashinshi"

a ranta tace "sabida shi ɗin na daban ne a zuciyata"

a fili kuma tace "sabida nima yana lallashi na"

man aje wayan yayi a saman gadonshi ya kwanta ya janyo pillow ya rungume, lumshe ido yayi yana ganinta tana dariyanta da ta riga ta saba koda yaushe tana cikin dariya, wayarshi ce ta fara ringing kamar ba zai ɗauka ba yaji kiran yayi yawa, ɗauka yayi yaga sunan manal yana yawo ɗauka yayi yasa a kunne yace "hello"

cikin tashin hankali ammi tace "Abdool kai kaɗai nake dashi wanda nasan zai iya taimakamin, Abdool manal ta bushe bata motsi tun ɗazu tayi aman jini har ta gaji abdool...."

kuka take yi kamar ranta zai fita, Abdool da sauri ya tashi yace "kuna gida?"

tace "eh"

yace "ki kaita hospital mana"

tace "har gara a gida idan munje hospital karuwa ma nakega ciwon yake"

yana jin zafin kukan da take yi yace "ki shafa mata ruwa a fuska ina zuwa"

tashi yayi ya cire kayan jikinshi yasa jallabiya fari, wayarshi ya ɗauka da sauri ya fito yana ɗauka makullin mota, ameesha da Imran ganinshi a rikice sukace "meya faru?"

yace "nemana ake yanzu ina zuwa"

fita yayi suna cewa "waye?"

bai amsa musu ba, motarshi ya shiga da mugun speed ya bar area.

ammi tashi tayi ta ɗauko ruwa a bowl ta rame sosai ta kara yin fara, ruwan tazo dashi ta shafawa manal dake kwance a gado, a hankali taja dogon numfashi ta buɗe ido, cikin sanyin murya tace "ammi zan mutu da wuri ko?"

girgiza kai tayi hawaye suna wanke mata fuska tace "no manal zamu rayu tare ba zaki mutu da wuri ba, ba zaki tafi ki barni ba"

riko hanun ammi tayi ta kalli hoton abdool dake ɗakin tace "ammi inason abdool amma nasan da wuya na sameshi, ammi so nake na rayu da abdool, ki taimaka min ki nemamin soyayyarshi"

tausayi ta bata sosai tace "ba komai zan tayaki manal"

cikin kuka tace "kimin alkawari"

tace "na.miki alkwari"

murmushi tayi, sallama yayi ammi tayi mishi iso, da sauri ya shigo yana kallonta, tana kwance a inda take tana mishi murmushi, a hankali tace "kazo?"

gyaɗa kai yayi yace "ya jikin?"

tace "da sauki"

ammi tace "zauna mana"

zama yayi akan kujeran yayi shiru, ammi tace "manal tun tana karama take fama da ciwo a zuciya, ya taɓa tashi mata sau ɗaya amma tunda muka kaita asibiti aka bata magani ya daina, babanta yace ba komai, bai kara tashi mata ba saida ta girma, bayan dr ya gwadata yace tanada cancer a zuciya kuma babban illa zaiyi a rayuwar ta muddin bata samun farin ciki wannan ciwon zaici gaba da girma, gashi yanzu ya gama girma...."

kuka take sosai, a hankali ya kalleta murmushi tayi mishi hawaye yana cika mata ido, a hankali ta juyar da kai ta yadda ba zaiga tana kuka ba, yana ganinta yaga tana share hawayen, kafin su kara wani magana dr ya shigo ya fara dubata, kallon ammi yayi yace "wai meyasa take sa abu a ranta ne? wannan ciwon ina gudun wani stage da zai kai labarin ba zaiyi daɗi ba, zan bata magani masu karfi a wannan karon ba zai kara tashi mata ba da yaddan Allah idan dai ba gama cinye zuciyarta cutan yayi ba"

ammi tana hawaye ta karɓi maganin, tafiya zaiyi ya kalli man, alama yayi mishi da ya biyoshi idan ya fita, gyaɗa kai man yayi, yana fita yace "ina zuwa"

bin bayanshi yayi, saida sukayi nesa yace "inason magana da kai muje motata idan ba damuwa"

a hankali yace "to"

shiga motan dr sukayi, ya zauna yayi shiru yana jiran yaji me zaice, dr habib yayi gyaran murya sannan ya cire siririn glass na idonshi yace "Abdool"

da mamaki ya kalleshi yace "kana mamakin ya akayi nasan sunanka ko?"

shiru yayi, dr yace "a bakin manal nasan sunanka, akwai wata rana da batada lafiya an kirani koda nazo nayi ta sallama basu jini ba sai kawai na yanke shawaran shiga kasan me naji?"

girgiza kai yayi, yace "manal tana faɗawa amminta cewar tana sanka amma babu yadda zatayi ta nuna maka ka kasa fahimta, manal tace tana burin aurenka amma har sai idan kai ka buɗe baki kace mata kana son aurenta kafin ta aure ka"

da mamaki Abdool ya kalleshi yace "so?"

gyaɗa kai yayi yace "kwarai Abdool, kuma akwai wani sirri da nakeso na faɗa maka wannan sirrin ko mahaifiyar manal bata sani ba daga ni sai kai zamu sani"

kallonshi yake da mamaki yace "wani sirri ne?"

hawaye ya gani a idon dr habib, ya share hawayen sannan yace "manal saura mata shekara biyar a duniya, ciwon kansa dake zuciyarta saura kaɗan ya gama cinye zuciyar kuma kowane shekara yana karuwa da ɗigon ɗaya, saura biyar ya cinye zuciyar daga nan ba zata kara numfashi ba, a halin yanzu ma idan ya kara tashi mata dole sai anyi amfani da Iskan shaƙa na oxygen kafin a ceto rayuwarta"

man yace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, babu mafita? ko wani hanyan da zata samu sauki?"

yace "shine dalilin da yasa na kiraka nan"

gyara zama yayi cikin tashin hankali yace "ka faɗamin menene mafitan?"

yace "ka auri manal"

a razane ya kalleshi, jijjiga kai yayi yace "kwarai aurenka da manal zai rage mata kaso hamsin a cikin kaso ɗari na ciwonta sabida naga idan kana kusa da ita tana zama cikin farin ciki, kai kaɗai zaka iya wannan, shekara biyar daya rage mata ta yishi cikin farin ciki, idan ba haka ba zata kareshi kwance da oxygen a fuska"

shiru yayi yace "bayan wannan babu wani hanya?"

yace "wannan shine hanya ko ina zakuje za'a faɗa muku idan kana ganin ba gaskiya bane zaka iya ɗaukanta zuwa wani asibiti daga kai sai ita"

shiru yayi, dr yace "kaje kayi shawara da zuciyarka"

jikinshi a sanyaye ya buɗe motan zai fita dr yace "Abdool"

tsayawa yayi bai buɗe ba, yace "zaka iya aurenta a ɓoye sabida ba zatayi tsawon rayuwa ba, dan ceton rai zakayi auren da kareta daga wahala badan sonka ba"

a hankali ya buɗe motan ya fita, bai shiga ciki ba kawai ya shiga motarshi ya fita daga gidan, shima dr tafiya yayi, man sai maimaita kalman yake "dole wannan shine hanya saura mata shekara biyar a duniya"

da haka ya isa gida, su ameesha suna zaune ya shigo jikinshi a mace, tare sukace "ka dawo?"

a takaice yace "eh"

tafiya ya fara zuwa ɗaki ameesha da sauri ta tashi ta bishi, yana shiga ɗakin yasa sakata ya rufe, tace "man kana lafiya?"

umma ce tayi mata alaman ta kyaleshi, barin shi tayi ta koma ta zauna duk sukayi shiru domin yanayinshi ya nuna baya mood me daɗi, kan gado ya faɗa ya janyo pillow ya rufe fuskanshi dashi, duk maganan dr yana kara yawo akanshi, a hankali ya fara tunano duk abinda yake faruwa da yadda take aman jini idan cutan ya tashi, amma da yaje wajen take sakewa ta fara murmushi, rufe ido yayi a hankali, muryan ameesha yaji tana cewa "banaso ina ganinshi cikin damuwa"

tashi yayi daga kwancen ya zauna yayi shiru, shine bai fito ba har dare , ameesha tareda Imran suka tafi gidansu, koda safe bai yadda ya bawa ameesha fuskan tambayanshi meya faru ba, yadda suka saba haka ya kaita wajen aiki ya wuce shima, yana shiga su faruk suka mishi sannu da isowa, hanu kawai ya ɗaga musu, zai wuce ita kuma manal ta fito daga office tana waya, karo sukayi da sauri tayi baya, kallonta yayi itama tana kallonshi ta rame ta kara zama fara kalanta na balarabiya ya fito, tace "ina zuwa"

sauke wayan tayi ganin yanayinshi tace "kana lafiya?"

a hankali yace "ina lafiya"

murmushi tayi tace "ya gajiyanka?"

girgiza kai yayi yace "babu"

tafiya zaiyi tace "Abdool"

tsayawa yayi tace "akwai abinda ya ɓata maka rai ne?"

yace "no"

tace "to zanje na karɓo saƙo a wajen abokin dady na yace naje akwai makullin store da dady ya bashi cike da kayan abinci wai zai rabawa mutane amma ya mutu kafin lokacin"

a hankali yace "sai kin dawo"

tace "to ko zamuje?"

girgiza kai kawai yayi ya wuce, binshi tayi da kallo har ya shiga office kafin ta taɓe baki da ɗaga kafaɗa alaman ko me ya sameshi oho, tafiya tayi tana kiran waya tace "yes gani nan zuwa yanzu"

yana shiga ya zauna a kujeranshi ya fara jujjuyawa yasa hanu a sajenshi dake kwance luf yayi shiru yana kallon sama, jiya gaba ɗaya baiyi bacci ba ya rasa ta inda zai fara kawo maganan ma.

a kofan wani katafaren gida ta tsaya, ta kira tace "nazo"

iso security's sukayi mata ta shiga har ciki da glass nata a ido tana takunta na izza bakinta da cingum tana ci tana karewa wajen kallo, ya haɗu sosai, tana shiga taga wani mutum tsaye da alama shine ya kirata, da hanu tayi mishi alaman kaine?

gyaɗa mata kai yayi, murmushin gefen baki tayi sannan ta zauna a kujeran da taga shine na saukan baki, kamar koda yaushe kafa ɗaya kan ɗaya ta ɗaura sannan tace "ina jinka meke tafe da kai?"

zama yayi kusa da ita yana kallon cikin idonta yace "sign nakeso kiyi akan store ɗinnan ya zama nawa"

tace "idan naki fa?"

dariyan mugaye yayi sannan yace "zan tona miki asiri"

gyara zama tayi ta ɗau cup goran ruwan dake gefe sannan ta buɗe ta kafa a bakinta saida ta shanye duka ta wurgar da goran a gabanshi, murmushin gefen baki tayi tace "akan me?"

wayanshi ya ciro daga aljihu ya nuna mata video ɗin motar da taje ta ture dady da kuma lokacin da taje hotel tasa zee ta kashe kanta, yace "wallahi saina yaɗawa duniya kowa yasan kece kika kashe mahaifinki"

dariya yaga ta fara harda rike ciki, tace "okay kafin ka yaɗa nima bari na nuna maka wani abu"

buɗe wayanta tayi ta shiga wani video data ɓoye a waje me nisa ta nuna mishi, saurin tashi yayi akan kujeran ganinshi da budurwa babu kaya a jikinsu suna baɗala, zai karɓi wayan a hankali cikin rainin wayo ta komar bayanta tace "ban gama nuna maka ba ai Alhaji yusuf"

wani video ta kuma nuna mishi wannan yafi wancan muni domin luwaɗi yake yi da wani ɗan karamin yaro, yaron yana kuka ya rufe mishi baki, a firgice ya kalli manal wacce take mishi murmushi, a shagwaɓe tace "koma ka zauna mana ya naga duk ka ruɗe kana zufa?"

yana tsaye zaiyi magana ta nuna mishi wani number tace "wannan shine numbern matarka Rabi'atu"

ta nuna mishi wani number tace "wannan kuma na ƴarka farida, sannan wannan video bani kaɗai nake dashi ba"

nuna mishi tayi yaga mutane uku ta turawa batayi saving number ɗinsu da suna ba, tace "kaga waɗannan idan nace su goge wannan video zasu goge, idan kuma sukaga na mutu ina nufin ka kasheni to fa zasu yaɗa"

zaiyi magana tayi playing mishi voice ɗin da tayi recording tun daga zuwanta har yanzu tace "kaga harma na tura musu conversation namu"

gira ta ɗaga mishi kana tasa lips na kasa a bakinta tayi kamar karamar yarinya tace "relax mana Alhaji yusuf be a man"

da sauri jikinshi yana rawa ya bata wayanshi yace "ki goge video ɗinki da kanki, dan girman Allah kiyi hakuri wallahi babu wanda zai san kece kika kashe umar maidawa"

murmushi tayi sannan tace "ba nice nayi ba sabida haka ba nice zan goge ba"

tashi tayi tasa glass nata tace "idan kaga dama ka goge idan kaga dama ka bari sani ya ragewa me shiga rijiya ta baya na barka lafiya"

kafin yayi magana ta tafi, motarta ta tashi cikin iyawa take driving har ta isa company.

tana shiga ta wuce office bata kula kowa ba, jingina tayi da jikin kofan bayan ta rufe a hankali ta runtse ido, tace "dady why? meyasa kayi abinda ka fusatani har na kashe ka?"

ji tayi ance "manal"

da sauri ta fara kalle kalle a tsorace, zuwa tayi ta zauna akan kujeran ta fara jin ana kiran sunanta kuma muryan dady take ji, a kullum idan anyi mata magananshi tana jin hakan, toshe kunne tayi a take ta fara rawan ɗari, kifa kanta tayi a table na gabanta, ciwonta ya tashi ta fara jan numfashi da kyar tana haƙi, amai ta fara na jini kirjinta ya riketa, faɗuwa tayi kasa ta fara rike kirji tana cigaba da amai, take ya ɓata farin tiles ɗin dake office ɗinta, man wanda ya jima yana tunani a hankali ya tashi yana goge zufa, har aka tashi baima san an tashi ba yana zaune akan kujera kowa ya watse, karan wayarshi ya dawo dashi hayyacinshi, da sauri ya kara a kunne ganin sunan my meesha yana yawo, ya ɗaga cikin sanyin murya yace "sweetheart ya akayi?"

da sauri tace "man jikin umma fa ya kara tashi mun kira me chemist zaizo yayi mata allura"

yace "okay gani nan zuwa yanzu"

tsshi yayi ya fara tattara takaddun da baiyi aikin komai akansu ba yasa a drower, fita yayi ya rufe office ɗin, gani yayi lokaci yaja sosai gashi kowa ya watse babu kowa a company har me gadi babu, makullin hanunshi ya cire zai rufe kofan company idonshi ya kai kan office na manal, gani yayi a buɗe da mamaki yace "meyasa bata rufe office nata ba?"

tsaki yaja cikin sauri yaje zaija kofan ya ganta kwance a bakin kofa da alama da birgima ta iso wajen domin duk ta ɓata cikin office ɗin da jini, jikinta duk a ɓace, zaro ido yayi yace "manal"

hanu ta ɗaga a wahale ta mika mishi tana buɗe baki tanaso tayi magana, sai kuma taja numfashi da kyar, da wani irin gudu ya ɗauketa ya fita da ita, ganin babu kowa yasa ya buɗe gate da kanshi bayan ya sata a motarshi, fita yayi ya kulle gate ɗin sannan da mugun gudu ya tafi asibiti da ita, well care hospital ya kaita aka karɓeta da sauri aka shiga emergency room da ita, safa da marwa ya fara a bakin kofan, wayanta da yake hanunshi aka kira ya kalli sunan yaga ansa sweet mom, da sauri ya ɗaga ammi tace "manal hankalina ya tashi baki dawo ba har yanzu kuma lokaci ya tafi sosai"

yace "nine"

tace "Abdool? ina manal ɗin?"

yace "muna well care hospital"

zatayi magana ya kashe dan bai san amsan da zai bata ba, ammi a ruɗe tasa hijabi akan rigan jikinta bata kula yayi guntu ba kawai tasa takalmi kamar zata faɗi ta fito, da hanu ta yiwa driver alama tama kasa magana saida ta shiga motan tace "well care hospital"

da sauri suka fita, a hanya sai addu'a take a fili da kuma a zuciya da haka suka isa asibitin kafin ya gama yin parking ta buɗe ta fito kamar zata faɗi ta shiga ciki, man yana bakin kofa emergency yana tsaye yana kallonsu ta cikin glass fari na kofan, kokarin ceto rayuwarta suke saide bata motsi zuwa yanzu, buɗe kofan likitocin sukayi kowa ya fito cikin karaya, ammi tace "ta mutu ko?"

man ya kasa magana sai kallon Dr yake, cikin sanyin jiki yace "saide kuyi hakuri"

hanu biyu ammi ta ɗaura aka, ta saki wani irin ihu, man ne ya daure yazo ya riketa, rungumeshi tayi tace "shikenan na rasata, na rasa ƴata ɗaya tilo, shikenan tabi mahaifinta, Abdool na rasa manal dama tace watarana zata tafi ta barni"

hawaye yaji yana sauka daga idanunshi, a hankali yace "kiyi hakuri"

ɗagata yayi yana hawaye yana tafiya da ita zuwa mota dan yasan ba zata jure ganin gawan ba, ji sukayi tayi tari da kyar ta buɗe ido ta kuma rufewa, da sauri yace "dr tanada rai"

duk sukayo kanta suka fara dubata, gani sukayi ta fara numfashi amma a halin yanzu tana buƙatan oxygen, sa mata sukayi nan take ta fara shaƙan numfashi a hankali ta buɗe ido, akan gadon suka turata zuwa ɗakin da suke kwantar da patients, cikin kuka da dariya ammi tace "Allah na gode maka, Allah kada ka ɗaukemin manal a wannan rayuwan, a matsayina na mahaifiyarta ina fatan tayi tsawon rai"

Abdool cikin tausayi yace "ameen"

shiga inda take sukayi suka zauna kusa da ita, fuskanta ɗauke da oxygen tana shaƙan numfashi ta ciki, hanunta ɗaure da drip kana ganinta zaka san tana cikin mawuyacin hali, ya tashi yace "zan tafi ammi amma zan dawo"

tace "to Abdool na gode"

tafiya zaiyi sai kuma yaji ba zai iya tafiya ba, gara umma yasan tana tareda ameesha dasu Anty da kuma Imran harma da fahad ita kuma manal fa?

kallon ammi yayi yaga tana gyangyaɗi alaman ta gaji ta zama weak, kuma da alama batada karfin zuciya, a hankali ya dawo tace "ka fasa ne?"

a hankali ya gyaɗa kai, kyawawan sexy eye's nashi suka cika da hawayen tausayi.

dr ne ya shigo hanunshi rike da file ya tsaya a kansu ya kalli ammi yace "amma kin san cewa ƴarki ba zatayi...."

alama man yayi mishi da yayi shiru, shiru yayi man yace "mun san ba zatayi komai ba zatayi rai kuma mun gode da taimakonku"

murmushi yayi yace "mu gode Allah, amma da so samune ace ta samu kyakkyawan labari idan ta farka hakan zaisa ciwon yayi saurin lafawa harma a cire mata wannan oxygen ɗin, idan tana samun farin ciki ranta baya ɓaci to zata iya warkewa sosai, saɓanin haka saide a kiyaye magana mara daɗi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login