Showing 15001 words to 18000 words out of 83501 words

Chapter 6 - DUHU DA HASKE Hausa Novels by Jiddah S Mapi.docx

19 Sep 2025

2232

ta kaita, koda zata shiga tayi mata kiss a goshi tace "na gode saina dawo"

gyaɗa kai tayi tace "please ki dawo da wuri sabida kinga ni kaɗaice a gida sai bana jin daɗi"

murmushi tayi tace "to ammi"

har suka tafi tana ɗaga mata hanu, saida suka fita ta haɗa rai ta juya tana tafiya, jin ammi take a cikin zuciyarta ko kaɗan batason abinda zai cutar mata da ita, ji take zata iya yin komai akan farin cikin ammi, koda tazo shiga suna ganinta suka mike saida ta shiga office kafin suka zazzauna.

_Jiddah Ce...✍️_

08144818849

[09/04 à 08:06] JIDDA MAPI: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*DUHU DA HASKE*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Na

*Jiddah S mapi*

*Chapter 5*

~Washe gari ammi ce ta fito da ɗan gudu daga ɗakinta tana kiran manal da waya a hanunta, manal wacce tayi masifaffen kyau cikin dogon riga red yana jan kasa sosai hanun dogo dogo ta ɗaura red veil a kanta sannan tasa bakin glass hanunta rike da jaka black ta shafa jan baki red tayi kyau sosai, kamshi take sosai tana kaɗa makullin mota a hanunta, kallon ammi take da fuskanta wanda babu fara'a harta karaso, mika mata wayan tayi tace "dadynki yanata nemanki a waya baisan wayarki ta lalace tun jiya da dare amma kinyi bacci"

murmushi tayi tace "no barshi Idan na dawo zamuyi magana"

rike hanunta ammi tayi ganin ta juya ta fara tafiya, tsayawa tayi ba tareda ta juyo ba tace "ina sauri fa"

ammi a gabanta ta tsaya tace "gashi fa yana jinki"

kallon ammin tayi na dan lokaci a ranta tace "shiyasa yake cutar dake sabida ya ganki very innocent, da kinsan da wanda kike tare da bazaki rinƙa haɗani dashi a waya ba"

karɓa tayi tace "hello dady ai nayi fushi da kai shiyasa naki amsa"

murmushi me sauti yayi sannan yace "my daughter kar kiyi fushi dani, me kikeso na kawo miki tsaraba gobe"

murmushi tayi tace "ai bakayi tafiya ba bale ka kawomin tsaraba"

da sauri yace "ban gane ba..."

murmushi me sauti tayi sannan tace "ina nufin ji nake kamar kana tare damu duba da yadda kake kiranmu a waya da har nayi zaton ka manta damu"

yace "habawa wane ni na manta da ƴata da matata wacce nafi sonta akan kowa"

murmushi ammi tayi jin abinda ya faɗa manal kuma kamar ana zuba mata wuta a ciki haka take ji, mikawa ammi wayar tayi tace "dady zan wuce aiki saina dawo"

yace "bye Allah tsare"

tace "Ameen"

fita tayi a fusace take tafiya harta isa wajen mota, shiga tayi ta direct hotel ɗin data gansu jiya can taje, koda ta sauke glass gateman ya ganta sannan ya barta ta wuce, tana shiga tasa facemask ɗinta sannan ta fito tana kallon ko ina na hotel ɗin, cikin rashin tsoro take tafiya dab zatayi kwana sukaci karo da yarinyar data gansu jiya tare, harara yarinyar tayi mata sannan tace "ke baki ganin hanya ne ko ke makauniya ce?"

murmushi tayi ta cikin facemask ɗin batayi magana ba, tsaki taja zata tafi manal ta damƙe hanunta, karan azaba tayi dan ji tayi kamar an ɓalla hanun, juyowa tayi tana kallon manal idanunta kawai take iya gani amma bata ganin fuskanta, idanunta kaɗai abin tsoro ne, kwace hanunta ta fara saide manal ko gezau batayi ba, cikin azaba tace "wacece ke?"

buɗe baki tayi zata bata amsa taji muryan dady yana cewa "my sweet"

sakin hanun tayi da sauri ta juya ta bar wajen, ita kuma ta rike hanunta tana hawaye, a lungu ta laɓe ta yadda ba zai ganta ba tana kallonsu, rike hanun yayi yana kallonta yace "meya sameki baby?"

cikin kuka tace "wata ce ta damƙe min hanu"

yace "wacece ita? tasan ke wacece da zatayi miki haka? ki gayamin koma wacece ita sai nasa an kulleta yau harda iyayenta"

dube dube ta fara ko zataga manal, waro ido tayi ganin manal ta cire facemask ɗin ta yadda zata ganta tana mata wani irin shaiɗanin murmushi, tsoro sosai taji ya ziyarceta kasa magana tayi, yace "ina take?"

tana kallon cikin idon manal kamar yadda manal take kallonta tace "ta tafi ban ganta ba"

killer smile manal tayi sannan ta maida facemask ɗin tazo ta gabansu ta wuce, motarta ta shiga ta wuce office, suna jin karan tekun takalminta duk suka tashi cikin girmamawa suka mika mata gaisuwa, hanu kawai ta ɗaga musu sannan ta wuce ta tafi office, saida ta shiga kafin suka zauna, akan kujera ta zauna ta kunna cctv footage dake gabanta ta fara kallon duk abinda ya faru kafin tazo, bayanta ta jingina da kujeran tasa yatsa ɗaya a goshi tana kallon duk wani motsin dake faruwa a company ɗin.

washe gari sai dare dady ya dawo yana ganinta yace "manal"

murmushi tayi tace "welcome dady"

ganin ta ɗauke kai yace "bakiyi farin cikin dawowa ta bane?"

zatayi magana taga ammi na kallonta a hankali tayi murmushi ta tashi da sauri ta rungumeshi, yace "na kawo miki sabon iPhone 16"

cikin jin daɗi tace "thank you"

zame jikinshi zaiyi yaji ta rikeshi da karfi, gabanshi ya faɗi, kara zamewa yayi ta kara kankameshi ko motsi ya kasa yi, zafi ya fara ji ya kara zamewa saide ko gezau batayi ba, banda wani irin murmushi babu abinda take yi, a hankali yace "ɗan sakeni"

cikin murmushin da ita kaɗai tasan meyasa tayi tace "no dady welcome nake maka we missed you"

a ɗan tsorace yace "to ai amminki ma so take tamin welcome"

tace "no"

ammi ganin kamar akwai matsala a tare dashi tace "to manal ni ba zaki barni nayi mishi welcome ba?"

sakinshi tayi tana kallonshi tana murmushi tace "to na barshi"

rungumeshi ammi tayi tana mishi sannu da zuwa, ɗakinshi ta rakashi yana tafiya yana juyawa ya kalli manal wacce take sanye da riga da wando me faɗi ta harɗe hanu a kirji tana girgiza kai kamar karamar yarinya tana kallonshi, bai gama tsorata ba saida sukazo cin abinci ci take tana kallonshi tana murmushin da ya kasa gane na menene, a hankali tace "dad"

yace "yes"

tace "menene hukuncin namiji me cutar da matarshi?"

wani irin faɗuwa gabanshi yayi da sauri yace "meyasa kikayi mishi wannan tambayan?"

tace "wani film nake kallo naga mijin yana cutar da matar kasan karshe meya faru?"

girgiza kai yayi, tashi tayi daga inda take ta ɗau fork ɗin da take cin chips dashi taje ta bayanshi kamar zata ɗau chips na gabanshi, gani yayi ta caka cokalin akan chips ɗin, a firgice ya kalleta, murmushi tayi mishi tace "ƴarsu ce ta kasheshi domin ba zata iya gani ana cutar da mamanta ba"

jikinshi ya fara rawa, tasa chips ɗin data ɗauko a plate nashi a baki ta fara tauna a hankali ta koma wajen zamanta ta zauna, ammi kam sai cin abincinta take, ganin ya gama tsorata ta kalleshi shima ya kalleta, gani yayi tana aika mishi wani kallo, kawar da abin tayi tace "dad?"

a tsorace yace "na'am"

tace "yaushe zakaje ka kara duba company ɗina yau nace musu dadyna zaizo ya kara dubani idan ya dawo"

sai yanzu yaji sanyi a ranshi yace "zanzo very soon my daughter"

tace "to dady amma bakacin komai why?"

a ranshi yace "ke kika tsorarani"

a fili kuma yace "zanci ai"

ɗauka tayi ta fara bashi a baki tana murmushi shima haka, koda suka gama tace "dady ammi zan tafi ɗaki domin zanyi aiki da laptop yau sosai"

ammi tace "saida safe kenan?"

tace "yes good night"

duk sukace "good night"

tafiya tayi dady ya kalli ammi yace "komai normal?"

ɗaga gira tayi tace "normal"

rike hanunta yayi yana murzawa a hankali yace "salma ina ɗaukin ranan da zamu haifi yara namu na kanmu, ina son ganin mun haifu tare, ranan da zan fara jin wannan labarin na tabbata bazan iya bacci ba dan farin ciki"

a hankali tayi murmushi itama tana shafa hanunshi dake kan nata tace "mu gode Allah a haka tunda ya bamu manal watakila haka kaddaranmu yake, nima ina fata da addu'a kullum Allah ya bamu haihuwa tare wannan shine babban burina a duniya"

manal dake tsaye a jikin window ta ɗaura hannayenta akan window tayi shiru tana kallonsu, bata jin abinda suke cewa amma tana iya ganin damuwa a fuskansu musamman ammi, sakin labulen tayi ta faɗa kan gadonta tace "inason ammi sosai banajin a duniya akwai abinda zanso bayan ita"

sauka tayi daga gadon taje wajen zanen dady da takeyi, stool ɗin ta janyo ta zauna a gaban hoton ta ɗaura duka kafafunta akai, fentin dake gefe ta ɗau baƙi ta fara shafawa a fuskanshi, saida ta tabbatar ta maida fuskanshi baki ƙirin ta yadda ba wanda zai gane wa ta zana kafin ta bige hoton ta tashi ta watsar da fentin duka akai ta juya ta koma kan gado ta ɗau laptop ta kwanta rub da ciki tana aiki, fuskanta kamar wacce aka aikawa saƙon mutuwa.

Kamar kullum yauma sanye take da riga da wando amma na pakistan, tayi kitsa gashinta kitso ɗaya har bayanta ta saki tasa guntun hijabi ta rataya jaka a bayanta sannan ta rungume takaddu a kirjinta, yanzu kenan tayi parking na motarta a kofan gidansu man, knocking ta fara kamar zata ɓalla kofan, Imran ne yazo ya buɗe, sexy eye's nata ta zuba mishi sannan ta ɗaga hanu tareda yimishi signal alaman meya faru?

kanshi ya sunkuyar kasa yace "ya Abdul baida lafiya"

waro ido tayi da sauri ta tureshi ta shiga gidan, umma dake shirin shiga ɗaki taga ta shigo da gudu tace "lafiya ameesha?"

batayi magana ba wuce ɗakin man, umma tsaki taja tace "Allah ka shiryamin wannan yarinyar"

tana shiga ta ganshi kwance akan gado ya rufu da bargo ya juya baya, da sauri ta karasa ta aje takaddun a gefe ta haye kan gadon, yaye bargon tayi tana ɗagoshi tace "man bakada lafiya meya sameka?"

a hankali ya buɗe lumsashun idanunshi wanda cikinsu yake brown kamar na cat, pinkish lip nashi ya cija cikin dauriya yace "zazzaɓi"

da sauri tace "sorry man"

ganin yadda ta rikice tana mishi sorry har hawaye ya fara taruwa a idonta yace "da sauki fa"

sajenshi ta shafa tace "babu sauki tunda kana kwance"

tashi tayi zata dira a gadon tace "bari naje na kira hamisu me chemistry yazo ya dubaka yayi maka allura"

da sauri ya rike hanunta yace "no ba sai an min allura ba inajin sauki"

Imran ya shigo ya tsaya a bakin kofa yana kallonsu yayi kalan tausayi, kallonshi tayi na tsawon minti biyu tace "bazan iya barinka haka ba kasan hankalina ba zai taɓa kwanciya ba"

hanunta ya rike ya tashi daga kwancen ya zauna ya jingina bayanshi da bangon gadon yana tauna lip nashi na kasa, hanu tasa ta gyara mishi gashin shi daya barbaje, yace "zan samu sauki ko kin kirashi babu enough money da zaiyi treating ɗina dasu"

da sauri tace "zan nema"

fuskanta ya nuna tsananin tausayinshi, girgiza kai yayi yace "no nasan kinada kokari zaki iya nema to amma ai ba aiki kike ba bale kice zaki biya daga baya"

kanta ta sunkuyar kasa hawaye yana bin kuncinta, kallon takaddun data aje yayi takaddunshi ne da nata na neman aiki, yace "zan kwanta na huta idan na samu sauki sai muje neman aikin ko?"

a hankali ta jijjiga kai, share mata hawayen yayi tana kallonshi ya girgiza mata kai alaman ta daina kuka, tashi tayi ta ɗauki takaddan tace "to zanje na siyo maka paracetamol duk da naji jikinka babu zafi"

Imran yace "dakin bari ki kawo kuɗin zai samu sauki"

harara tayi mishi tace "me zakayi da kuɗin?"

kaikaya kanshi yayi yace "ice cream"

kasa kasa yayi magana bata jishi ba, fita tayi daga ɗakin da niyan siyo mishi paracetamol, tana fita yacewa Imran "leka ta tafi?"

imran ya leka yace "ta tafi"

tsalle yayi ya diro daga gadon cikin waka yace "yau na huta da zuwa neman aiki, kullum saide tace sai munje neman aiki kuma bama samu, yau na huta da zuwa"

Imran ganin yana waka harda rawa ya fara kashe mishi ido tareda yi mishi alaman ya daina gata nan, idonshi a rufe yake yin waƙan yana juyawa kamar wani karamin yaro, kwankwaso ta rike tana kallonshi sai huci take, juyowa yayi yace "Imran yau ka tayani murna na huta da meee......"

shiru yayi lokacin da suka haɗa ido, dara daran idanunta ta zuba akanshi ko kyaftawa batayi, da sauri yayi kamar mara lafiyan gaske ya tako a hankali zai rike hanunta ta fizge, cikin ɓacin rai tace "kenan karya kayimin da rashin lafiya?"

a hankali yace "wallahi..."

tace "shiru"

tsit yayi, Imran sum sum ya juya zai fita tace "dakata"

tsayawa yayi tace "ku rasa abinda zakumin karya dashi sai rashin lafiya? kasan yadda naji a zuciyata kuwa? kasan yadda naji a lokacin dana ganka kwance babu lafiya?"

shiru yayi kanshi a kasa, cikin tsananin ɓacin rai tace "sabida ina nace maka kullum muje neman aiki shine zakayi karya da rashin lafiya? sanin kanku ne iyayenmu maza sun mutu, idan bamu nemi aiki ba wa zai taimaka mana? a kullum saina maimaita wannan kalman fiyeda a irga kaine babba kaine ya kamata ka samu aiki a cikinmu ka taimakemu, amma tunda bakaso ba zan kara maka maganan neman aiki ba"

watsar da takardun tayi ta fita daga ɗakin a fusace, da gudu ya bita yana cewa "meesha please, meesha...meesha"

umma tana ganinta yadda take a fusace ta dafa kirji tace "me sukayi mata ranta ya ɓaci haka?"

tace "Ameesha menene?"

tace "babu komai"

takalmi yasa yana binta yana cewa "wallahi ba zan kara ba, dan Allah kada kiyi fushi dani please and please and please, zanyi frog jump ma sabida punishing kaina, kin gani na rike kunnena am sorry, fita tayi daga gidan ta tura kofan ji kake gauuu saida umma ta toshe kunne, ko mashin nata bata hau ba tana tafiya tana share hawaye yana biye da ita, ganin taki tsayawa ya fara frog jump yana cewa "kin gani ina hukunta kaina"

har gida ya bita tana shiga ta wuce ɗakinta, Anty dake zaune akan sallaya tayi sallan walaha tace "Ameesha meya faru?"

tace "babu"

ɗakinsu da fahad ta shiga ɗan karami madaidaici da gadonsu kanana guda biyu, rufe kofa tayi a kanta tana jinshi yana bubbuga kofan taki buɗewa, idonshi ya cika da hawaye ya zauna a bakin kofan ya haɗa kai da gwiwa yayi shiru, Anty tashi tayi daga kan sallayan tazo wajenshi ta shafa kanshi tace "ban san meya haɗaku ba amma nasan kaine da laifi sabida nasan Ameesha tana kokarin ganin ta kiyaye abinda zai ɓata maka rai, koma sai menene kaje idan ta huce sai kazo tunda kun saba haka kuma ku shirya"

girgiza kai yayi yace "bazan iya tafiya na barta tana fushi ba"

tace "to shikenan"

tashi tayi ta barshi a wajen dan tasan halinshi ko me zatayi ba zai tashi anan ba sai ameesha ta sauko daga fushin koda kuwa kwana zaiyi, aikinta taje tana yi, koda fahad ya dawo yace "ya Abdul meya sameka?"

girgiza kai yayi yace "babu"

yace "a,a ya Abdul ka faɗamin meya sameka?"

a tsawace yace "nace babu"

shiru fahad yayi sannan ya tafi ya barshi a wajen, haka har dare salla kawai yake tashi yayi, ita kuma a cikin toilet na ɗakin take alwala tana salla, tana sane yana wajen so take ta hukuntashi kada ya kara mata karyan rashin lafiya, bata fito ba sai washe gari da safe, a lokacin ya idar da sallan asuba, tayi wanka tasa riga pink me sharara da wandon jinx tayi shocking ta bazo gashinta baya fuska haɗe ta fito daga ɗakin, yana ganinta ya ɗaura hanu akan kunnenshi yayi kalan tausayi cikin sanyin murya ya ƙaryar da wuya yace "am sorry"

tausayi ya bata kuma bata iya jure fushi dashi ta mika mishi hanu, rikewa yayi ya tashi, yace "am sorry bazan kara ba"

girgiza kai tayi tace "ya wuce"

Anty data fito daga kitchen tace "to ga karyawa sai kuzo kuyi idan kun gama fushin naku"

yana rike da hanunta suka zauna suka fara cin abincin, Imran ne ya shigo hanunshi rike dana fahad, yana ganin ameesha ya durkusa yace "kiyi hakuri ba zamu kara ba"

murmushi tayi taja kunnenshi tace "kai baka san ka wuce karya ba yanzu? ka kai 20years fa"

da sauri yace "na daina wallahi"

sakinshi tayi suka zauna da fahad wanda yake ɓata rai sabida man yayi mishi faɗa, man yace "fahad ba zaka gaisheni bane?"

yace 'ba kamin faɗa ba jiya"

yace "sorry kaji"

a hankali ya gyaɗa kai yace "to good morning"

murmushi yayi yace "morning my bro"

breakfast suka fara gwanin sha'awa, suna gamawa ameesha ta shiga ɗaki ta fito tayi rolling kanta da mayafi black tasa after dress black akan riga da wandon jikinta, takalmi flat a kafanta tayi kyau sosai musamman fuskanta da kullum yake ɗauke da murmushi dake kara mata kyau, rataya jaka tayi tace "muje"

duk suka kalleta sukace "ina?"

tace "neman aiki mana"

Abdul da Imran suka haɗa ido, a ran Abdul yace "wayyo Allah na ba zata taɓa barina na huta ba"

tashi yayi ba dan yaso ba suka jera suna tafiya kamar yayi kuka, gidansu sukaje ta gaida umma kamar ba itace ta fita jiya ranta a ɓace ba, umma ma ta nuna kamar bata san jiya sunyi faɗa ba tace "ya kike ameesha?"

tace "lafiya"

zama tayi kusada umma suna hira shi kuma ya shiga ciki yayi wanka, ya jima sosai bai fito ba, tashi tayi tace "bara na dubashi"

umma tace '"to"

shiga ciki tayi da sallama a bakinta, ganinshi tayi zaune a bakin gado yayi shiru, murmushi tayi mishi time ɗin daya ɗago suka haɗa ido, da hanu tayi mishi alaman kayi kyau, tashi yayi yace "mu tafi"

tace "wait first"

tsayawa yayi, ta ɗauko mataji ta taje mishi gashin shi ta kwantar, style tayi mishi me kyau tace "wow kayi kyau sosai"

yace "thank

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login