Showing 69001 words to 72000 words out of 83501 words
skirt ne yayi kyau ɗinkin ya zauna a jikinta, ta shafa powder tayi kwalliya me kyau ta juya ta kalli Anty tace "nayi kyau?"
gyaɗa kai tayi tace "kinyi kyau sosai"
tace "na gode mama"
jikinta yayi sanyi dan rabon data kirata da mama har ta manta, tsaban yadda suka saba da umma yasa tun ameesha tana karama bata iya ce mata mama saide ta kira umma da umma ko kuma mama, a hankali tace "ameesha ki kula da kanki"
tace "to mama"
makullin mashin nata ta ɗauka, tace "a,a ameesha zan baki kuɗi ki hau napep banda mashin yau kam sabida kinyi kyau sosai"
murmushi tayi ta karɓi kuɗin data bata tace "na gode"
takalmi tasa me kyau sannan ta fesa turare me kamshi ta yafa mayafi green tayi kyau sosai, ta ɗau wayarta sa karamin jaka tace "na tafi"
tafiya tayi a hankali take tafiya akan titin so take taga napep ta tsayar saide yau da alama zata wahala kafin ta samu, tafiya take a nitse sabida ɗinkin tana ji yana taƙurata abinka da rashin sabo, ishi ta fara ji bayan tayi nisa da tafiyan da alama da kafa zata isa, wani shago ta hango daga nesa tayi hamdala domin ruwa take son siya, cikin siririn muryanta tayi sallama wani dake tsaye a shagon ya kalleta ya amsa sallaman, murmushi tayi mishi shima ya mayar mata, yace "baiwar Allah kinyi kyau masha Allah na jima banga kyakkyawa kamar ke ba"
a hankali tace "na gode"
tace "me shago a bani ruwa"
kuɗin ta mika mishi meshi yace "ki bari zan biya"
girgiza kai tayi, yace "ba dan komai zan biya ba"
jin haka tace "to na gode"
ruwa aka bata me sanyi guda uku a gora, sallama akayi muryan da ko bacci take idan taji ba zai ɓata mata ba taji, man yace "akwai gum?"
me shago yace "eh akwai"
bayanta ya kalla ko aina yaga wannan bayan ba zata taɓa ɓata mishi ba, a hankali yasa hanu a aljihu ya ciro kuɗi yace "abani babban"
itama a hankali ta juyo tana rike da ruwan, kallonta yayi yaga ko kallonshi batayi ba ta raɓa ta gefenshi ta wuce, matsa mata yayi a hanya kanta kasa ta fita daga shagon, har tayi nisa bai daina kallonta ba ita kuma bata juyo ba ta rike ruwan tana tafiya abinta, mika mishi gum akayi ya karɓa ya fita, bai ganta ba, jikinshi a mace ya shiga motan yayi shiru, ya jima a haka kafin ya tafi.
da kyar ameesha ta samu napep ta shiga aka karasa da ita, Imran yana ganinta ya ɗaga mata hannu yana zaune akan stage ɗin da ɗaliban da suke gama school ɗin suke zaune, itama hanu ta ɗaga mishi, ta zauna kusa da fahad wanda yayi kyau cikin shadda, yace "welcome unty Ameesha"
tace "ya dai komai yana tafiya daidai?"
yace "yes"
suna wajen aka fara basu result ɗaya bayan ɗaya, har akazo kan Imran aka bashi mic yayi godiya ga malamansu da iyayenshi, rike da certificate ɗin ya riƙe mic yace "da farko zan fara godiya ga wacce ta tsayamin a rayuwa ta bada gudunmawa me girma a rayuwata ta kuma tabbatar na gama secondary ba tareda ta bari na lalace ba, ina mika godiya ga yayata Ameesha"
tafi akayi, headmaster ya karɓi mic yace "wacece ameesha? zamu so ki tashi mu ganki domin duk student na nan wajen iyayensu suka yiwa godiya da farko sannan malamansu amma shi yayarshi ya godewa hakika ke yaya ce ta gari kin cancanci mu ganki"
tana hawaye ta tashi tsaye, tafi sukayi mata, yace "zaki iya karasowa ki tayashi karɓan result?"
a hankali ta fito daga inda take zaune taje ta karɓi result ɗin, rungumeta Imran yayi itama ta rikeshi kuka yake yi tun tana lallashinshi har itama ta kasa daurewa kukan ta fara, lallashin kansu sukayi a hankali ta zameshi daga jikinta ta rike hanunshi suka koma mazauninsu, sun sa mutane dayawa kuka har aka tashi daga taron suka tafi gida mama tasa mishi albarka, haka suke rayuwarsu yanzu sun maida hankali akan karatun fahad ne da kuma abincin da zasu rinƙa siya.
watarana yana kwace a ɗaki tareda fahad suna baccin rana yaji wayarshi tayi kara, a hankali ya tashi ya duba sabida yana yawan duba message yayi apply ɗin aiki da yawa ko Allah zaisa ya samu, sabon number ya gani anyi rubutu kamar haka _barka da rana Imran yayanka ne Abdool ina fatan ka faɗawa ameesha ta fita harkata idan ba haka ba zan kashe ta_
sauka yayi daga gadon ya fita zuwa falo, dubata ya fara bata nan, yaji karan kanuka a kitchen da alama girki take, ya shiga da sallama ta amsa, tana yin miya tana ganinshi tayi murmushi me sauti tace "Imran ya akayi? ka fasa baccin ne?"
yace "eh"
da sauri tace "meya faru?"
yace "Inaso ki faɗamin gaskiya"
tace "ina jinka"
yace "ya kukayi da ya Abdool ranan da kikaje?"
shiru tayi, ya karaso yace "kinaso na fara zargin wani abin ne?"
girgiza kai tayi, batason tuna wancan ranan ko a mafarki, a hankali ta rungumeshi tana kuka sosai ta fara irga mishi yadda sukayi, zuciyanshi kamar wuta ya kara kallon text ɗin ya karanta, a hankali ya zameta yace "to yanzu kukan me kike?"
tace "abin yana cin raina Imran"
yace "karki damu ina tare dake babu komai da kanshi zai dawo kinji?"
tace "to"
yace "ci gaba dayi mana girki zan koma na kwanta"
tace "to"
cigaba tayi da girkin, ta yadda ba zata ganshi ba ya ɗau karamin wuƙan dake cikin kwando yasa a aljihun wandonshi ya fita, fita yayi daga gidan ya ɗau mashin na ameesha bata sani ba saida yayi nisa kafin ya kunna mashin ɗin ya hau ya tafi, har kofan gidansu manal yaje ya wurgar da mashin ɗin ya shiga, megadi yace "waye kai? Ina zakaje?"
yace "sunana Imran haruna lamiɗo kanin abdool"
yace "laaa kace babban baƙo mukayi maraba da zuwa aiko gashi kuna kama sosai"
a takaice yace "zan iya shiga ciki?"
yace "ka shiga"
kai tsaye ya wuce inda yaga kofa ya buɗe ya shiga baiyi sallama ba, da karfi ya buɗe murya yace "Abdool? Abdool? Abdool? ina kake? ka fito"
manal tana ɗaki taji muryanshi, wani killer smile tayi tace "good message ya tafi, sannan na goge a wayan Abdool ba zai taɓa sanin nice na aika ba"
ammi ce ta fito daga ɗakinta tana murza ido domin bacci take taji ana kiran Abdool, tana kallonshi tace "lafiya?"
yace "ina Abdool?"
ganin suna kama dashi tace "kaine Imran?"
yace "eh ina Abdool?"
ta nuna mishi ɗakin manal tace "may be yana ɗakin ka dubashi ina bacci ban san ko ya fita ba"
kafin ta karasa maganan ya shiga a fusace, tsayawa tayi tana mamakin yadda yake huci, yana shiga ta rufe kofan da makulli, yace "ina Abdool?"
murmushi tayi tace "na ɓoyeshi"
kan gado ta zauna tana latsa waya, yace "ina Abdool?"
tace "na ɓoyeshi"
kallon kofan yayi yace "ki bani makulli"
tace "no abinda ya shigo da kai shi zamuyi"
cikin tsawa yace "ki bani makulli abdool nake nema"
tace "a,a sai kamin cikin da ameesha ta zubar kafin na barka ka fita kanin mijina"
kukan kura yayi ya shaƙe wuyanta, cikin zafin rai da raɗaɗi ya danneta a gadon yana faɗan duk abinda tayi musu yana kuka, kakari ta fara tana kwace wuyanta, yace "ki bani makulli ko kuma na kashe ki"
ihu ta fara bayan ta kwace wuyanta tace "Imran kada kayi haka, nifa matar yayanka ce, kada kamin fyaɗe Imran"
da mugun mamakin abinda take faɗa yace "fyaɗe? ki bani makulli nace"
ihu tayi tace "Imran dan Allah ka bari"
yaga riganta tayi kirjinta dake cike fam cikin baƙin bra ya bayyana, saurin rufe ido yayi yace "Auzubillahi minashaiɗanirrajeem"
hanunshi ta ɗaura akan kirjinta ta latsa, da karfi tace "Imran me kakeyi haka? Imran dan Allah kada kamin haka Imran yayanka ba zai taɓa yafe maka ba"
kwace hanunshi ya fara amma fa manal ba daga nan ba wajen karfi, kokawa suka fara akan gadon, yana gani ta yage wandon jikinta ta zame pant ɗin tayi wurgi dashi, janyoshi jikinta tayi, shi kuma burinshi ya ɗauki makulli ya fita, da karfi tace "Abdool Imran yana min fyaɗe"
ammi dake jikin kofa ta fara bubbugawa da iya karfinta tana cewa "manal? manal?"
man ne ya shigo yana waya, da sauri ya kashe ganin ammi tana bugun kofa kamar ta haukace, da gudu ya hau stair ɗin yana cewa "ammi me ya faru?"
jin muryanshi yasa manal tace "Abdool ka taimakeni Imran yana min fyaɗe"
da karfi tace "wayyo ku taimakeni jama'a zan mutu Imran kayi hakuri na tuba, dan Allah kayi hakuri ka barni Imran kaifa kanina ne"
zaro manyan idanunshi yayi cikin tashin hankali yace "Imran me kakeyi? me nakeji haka Imran? ka buɗe kofan, ka buɗe kofannan imran"
Imran cikin tashin hankalin da tunda umma ta haifeshi bai taɓa shiga ba ya buɗe baki yace "wallahi..."
danne bakinshi tayi suna kokawa akan gadon saida ta tabbatar tayi kasa da wandon dake jikinshi, dira tayi akan gadon cikin rarrafe kafin ta buɗe kofan ta wanke fuskanta da zazzafan mari har sau uku, take fuskan yayi jajur yayi shatin mari, farcenta dake da tsayi ta fara yagunin jikinta dashi, buɗe kofan tayi tana haƙi ta kalli man dake zaune daram a kasa cikin shocking, kallon Imran yayi wanda yake jan wandonshi sama yana girgiza kai, faɗawa jikinshi tayi ta fashe da kuka tace "naso na hanashi amma yafi karfina Abdool, yace wai sai yamin cikin da nace ameesha ta zubar, yana ganin sharri na yiwa Ameesha, Abdool kaine shaida, na yiwa Ameesha sharri? nayi mata sharri ne? ba a idonka abin ya faru ba? dan Allah ka sakeni yanzu Abdool"
share hawaye tayi ta kalli Imran wanda ba zaka iya gane wani hali yake ciki bama tace "inace nice matsalan family ɗinku ko Imran? to bari zan kashe kaina zan barku ku huta nima na huta"
riketa man yayi ganin tana shirin zuwa kitchen, yace "idan kika kashe kanki nima zan mutu kuma nasan bakison jin kalman mutuwa a bakina"
turus ta tsaya, shiga ɗakin yayi yana kallon Imran, ammi cikin dagulewan lissafi ta fara tafiya zata sauka daga kan stair duhu duhu take gani, jiri take ji, manal tace "ammi?"
tsayawa tayi ta juyo, manal ganin ammi tana aika mata wani kallo ta karasa wajenta a hankali tace "ammi me yasa bakiyi magana ba?"
ammi idanunta suka rine, bakinta yana rawa kamar yadda jikinta yake rawa tace "manal anya ke mutum ce? na gama tsorata dake, mutum ce ke kuwa?"
tace "ammi meyasa kike min wannan tambayan?"
cikin hawaye ammi tace "duk abinda ya faru naji, amma ki sani kin shiga tsakanin uwa da ɗanta manal Allah ba zai barki ba"
murmushi tayi tace "kenan kin san komai? kuma kin yadda?"
jijjiga kai ammi tayi tace "Imran ne da gaskiya naji duk abinda ya faru kuma wallahi saina faɗawa Abdool komai, saina tona miki asiri yasan ke ɗin asalin wacece yau ɗinnan sai abdool yasan gaskiya sai yasan komai saina faɗa mishi wacece manal"
juyawa tayi zata je ɗakin, manal tayi murmushi kafa tasa mata zaro ido ammi jin manal ta harɗe kafanta a cikin nata ta faɗi ƙasa akan stair a take ta fara gangara tana buguwa da stair case ɗin cikin azaba, take numfashinta ya fara ɗaukewa, daidai lokacin Imran ya ture man dake dukanshi ya fita da gudun ceton rai, manal tana ganin haka ta ƙwala ihu tace "Ammiiiiiiiii"
cikin firgici tace "Abdooool Imran ya ture ammi akan stair case"
man da yake ɗakin yaji jiri yana shirin kadashi kasa, jingina bango yayi ya fita daga ɗakin, gani yayi ammi tana gangara imran yana tsaye cikin shock yana kallonta, minal kuma ta ɗaura hanu a kanta tana ƙwala ihun da duk gidan saida ya amsa, ammi tana gama gangara idanunta suka rufe bata kara motsi ba duk jikinta jini sabida stair nasu yanada tsayi, man yana kallon imran yana girgiza kai, da gudu Imran yaje zai ɗagata manal ta tureshi, cikin ɓacin rai tace "stay away from my mother, kuma wallahi idan ta mutu kaima saina kasheka"
man da kyar ya karaso wajen yana daddafa bango, a gaban ammi ya zauna yasa hanunshi a nata yaji hanunta yana harbawa, kallon Imran yayi zai tashi Imran ya fita da gudu dan yasan zai iya illatashi kafin yasan gaskiyan abinda ya faru
manal tace "ka taimakeni mu kai ammina asibiti kar ta mutu"
waya ya ɗauko ya kira numbern dr habib yace mishi yazo emergency ne, ɗaukan ammi yayi ya kaita kan sofa, ya zauna akasa ya ɗaura kanshi jikin sofan yayi shiru, lura tayi jikinshi yana rawa, a hankali ta zauna kusa dashi ta dafa shi, juyowa yayi ya rungumeta ya fashe da wani irin ɗan marayan kuka, shafa kanshi take a hankali tace "kaje gida abdool zan iya handling ɗina da Ammi, banso ƴan uwanka suna cutar dani nasan ranka zai ɓaci, banason ranka ya ɓaci dan Allah tashi kaje kaji? tashi Abdool"
gani yayi ta zama kamar sabuwar mahaukaciya, ya riketa gam yace "ko me zai faru ina tare dake"
shiru tayi yana kuka yace "ina so ki bani amsa ɗaya"
idonta a kumbure haka fuskanta yayi jajur shatin marin da Imran yayi mata ya fito sosai
tace "amsan me?"
cikin hawaye da jin zafin abinda Imran yayi yace "kin san umma na ta rasu?"
girgiza kai tayi tace "umma kuma? yaushe?"
cikin kuka yace "ta mutu basu faɗamin ba sun ɓoyemin, ameesha ta ɓoyemin mutuwan ummana"
rungumeshi tayi tana lallashinshi, cikin kuka yace "gashi Imran ya ture ammi idan ta mutu shima kasheshi za'ayi"
da sauri ta girgiza kai tace "ba zata mutu ba"
fuskanshi yayi jajur tsaban kuka yace "ki bani wani amsan"
tace "na me?"
yace "Imran yayi rel**se a jikinki?"
kuka takeyi, yace "please manal"
a hankali ta girgiza kai tace "na tureshi na gudu"
dr habib ne ya shigo basuda nutsuwa su duka, fara duba ammi yayi yace "kai ba zan iya wannan ni kaɗai ba saina kira dr jamal"
kiran waya yayi ya faɗawa dr jamal ɗin yanayin jikin, yace "ina zuwa"
babu jimawa yabi address ɗin sai gashi a gidan yana sallama, dr habib ne yayi mishi iso, babban doctor ne yayi karatu a kasar India tareda dr habib amma shi yafi dr habib zurfin karatu, kallonsu yayi yaga man rungume da manal da gani kasan suna cikin tashin hankali, dubata ya fara, saida ya gama yace "ta samu mummunan rauni a spinal cord ɗinta, ba zata iya tafiya ba sannan ba zata iya magana ba domin jijiyan kanta zuwa na bakin da kirjinta sun samu matsala, da wuya ta iya kara magana a rayuwarta, tayi mummunan accident wanda yin rai da tayi ma Allah ne yayi zata kara kwanaki may be a duniya"
manal ta ɗaura hanu aka zatayi ihu Abdool ya rufe mata baki da nashi, shima baisan abinyi ba shiyasa ya fara kissing nata, dr habib da mamaki ya kallesu sai kuma ya kalli dr jamal daya ɗauke kai yana cigaba da dubata, dr habib zaiyi musu magana yace "daka kyalesu sabida wani lokaci idan zuciyar mutum zata buga ana buƙatan ya samu wani kusa dashi hakan zaisa bugun zuciyan ya daidaita"
saida man yaga sun ɗan dawo hayyacinsu kafin ya saketa, kanshi ya ɗaura akan sofa yayi shiru, itama manal haɗa kai tayi da gwiwa tayi shiru duk ta raunata kanta, dr jamal ya basu magani yace "wannan ku tabbatar kullum ta haɗiye zai taimaka mata ta daina jin raɗaɗi nan take, sannan ku rinƙa kula da ita sabida kada wani ciwon ya kara samunta"
har ya gama magana babu wanda ya amsa mishi a cikinsu, tashi yayi yace "Allah ya bata lafiya zan bawa dr habib wheelchair ya kawo mata, akwai remote a jikin wheelchair idan tana buƙatan abu tana danna remote ɗin zaiyi kara hakan zaisa me kula da ita yazo da sauri"
allura yayi mata sannan suka tafi da habib, jim kaɗan dr habib ya dawo hanunshi rike da sabon wheelchair wanda zata rinƙa amfani dashi, yace "Allah ya bata lafiya"
tafiya yayi shima, manal da abdool babu wanda ya kara magana cikinsu.
Imran a kofa ya wurgar da mashin ɗin ya shiga gidan da gudu, ameesha tana juye ruwan wanka a kitchen taji yana kiran sunanta, tace "gani anan"
shigowa yayi a gigice, kallonshi tayi yadda jikinshi yake rawa gaba ɗaya a firgice yake, roban ruwan ya faɗi tace "me?"
riketa yayi ya rungumeta kamar zai shige jikinta yace "banyi komai ba, wallahi tallahi ban aikata komai ba, manal ce tayi duk abinda ya faru, ki taimakeni banyi komai ba, unty ameesha kinfi kowa sanin ban san komai ba...."
cikin rashin gane inda ya dosa tace "wai menene Imran?"
a haukace ya fara faɗa mata abinda ya faru, dafa kirji tayi tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, Imran meya kaika? Imran meyasa kaje gidansu bayan kasan babu abinda ba zata iya ba akan man?"
kuka yake yi yana daɗa riketa yace "wallahi banyi komai ba, ki taimaka min"
hanunshi ta rike suka tafi ɗakinsu, kayanshi ta kwaso ta fara zubawa a cikin akwati tace "ya zama dole kayi nisa da nan kaje ko gidan abokanka ne a wani wajen me nisa har sai komai ya lafa zan kiraka ka dawo"
yace "to amma bazan iya tafiya na barki ba, bazan iya barin fahad da unty ba"
tace "ya zama dolene Imran kayi nesa da nan domin nasan manal akwai abinda ta shirya"
yana kuka yace "zaki rinƙa kirana ina kallonku a video call?"
cikin sauri take yin komai share hawaye tayi tace "insha Allah"
takalmi ta durkusa tana sa mishi, sannan ta tashi tasa mishi facemask ta rike hanunshi tace "tashi maza babu lokaci"
hijabi tasa da niyan rakashi tana rike da hanunshi bata bari ko sallama yayi dasu mama ba, yace "zan yiwa unty da fahad sallama"
tana hango gagarumin matsalan da za'a samu tace "muje kawai Imran ba lokaci"
buɗe kofan tayi