Showing 39001 words to 42000 words out of 83501 words

Chapter 14 - DUHU DA HASKE Hausa Novels by Jiddah S Mapi.docx

19 Sep 2025

2227

ta gayawa su Imran haka ta gayawa umma, saida sukaci abinci kafin suka koma gidansu, basuci abincin ammi ba suka zauna dan sun san man ta gidansu zai fara dawowa, wasa wasa har dare bai dawo ba kuma bai ɗauki wayanta ba, duk sun shiga damuwa ta koma gidansu ko ya dawo umma tace bai dawo ba, ta zauna tayi shiru.

saida ta farka tana buɗe ido ya mata murmushi, a hankali ta kalli gefenta tace "ammi?"

cikin sanyin murya tayi maganan, yace "kin san me madam?"

shiru tayi tana kallonshi yace "yau na sata drinks a frij naki"

murmushi tayi sai yaga tayi dariya kaɗan bata kara kulashi ba, ganin haka ya tashi yace "saida safe"

ammi wacce take kusa da ita tana rike da ita tace "mun gode ya sunanka?"

yace "Abdulrahman ana cemin Abdool"

tace "mun gode Abdool"

yace "ba komai"

fita yayi daga gidan da sauri ya shiga mota yana kallon agogo, sai yanzu yaga miss calls na ameesha yafi sau a irga, gudu yake akan titi har ya isa gida, da sallama ya shiga dan yasan suna gidansu shiyasa bai wuce gidansu ameesha ba, duk suka tashi suna cewa "kana lafiya?"

yace "ina lafiya ba komai"

hamadala umma sukayi dasu Anty wanda hankalinsu ya gama tashi, ameesha tace "ina kaje?"

yace "ina gidansu manal"

kirjinta ya bada sauti dum, tace "manal boss taka ta wajen aiki?"

jijjiga kai yayi yace "yes"

tace "tun ɗazu da kuka fita a gidansu kake?"

yana shiga ɗaki yace "yes a gidansu nake batada lafiya ne, bari nayi wanka na gaji zan kwanta idan nayi wanka good night love you"

da ido Ameesha ta bishi, Imran ne yazo da dafata yace "karki damu"

murmushi tayi tace "ba komai"

ta kalli Anty da Imran tace "muje dare yayi"

umma tace "muje mu raka su"

rakasu sukayi har gida kafin suka koma, yana yin wanka ya kwanta kan gado ya fara bacci.

*Jiddah Ce....*

08144818849

[09/04 à 08:06] JIDDA MAPI: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*DUHU DA HASKE*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Na

*Jiddah S mapi*

*Chapter 11*

~Ameesha itama kwanciya tayi akan gado bayan tasa kayan bacci, juyi take akan gadon tana kallon wayarta ko zai kira, a hankali ta lumshe ido ganin bai kira ba, da kyar ta samu bacci ya ɗauketa, sai washe gari ta shirya taji yana hon a kofar gidansu, fitowa tayi tareda fahad ta zauna a gaba tace "good morning"

cikin son ganin ta kalleshi yace "morning princess ya kika tashi?"

a hankali tace "lafiya ƙalau"

Imran yace "good morning"

tace "ya kake"

tafiya suka fara fahad ya gaishesu, a school ya ajesu fahad sannan suka tafi, a hankali tace "akwai maganan da nakeso muyi"

yace "okay"

tace "dama inaso na faɗa maka wani abu"

yace "okay menene abin"

tana wasa da yatsunta ta rasa ta inda zata fara tace "man ina s..."

wayarshi aka kira ya ɗauka, gani yayi sunan boss yana yawo da sauri ya ɗauka yace "good morning boss"

muryanta kasa tace "ya kake?"

yace "ina lafiya ya jiki"

"da sauki yau ba zanje aiki ba inaso ka kula da komai na company duk wani abinda kasan inayi to kayi yau ko ɗaya banson ayi ɓarna ko wani abinda ba daidai ba"

da sauri yace "okay madam"

kashe wayan yayi ya kalli ameesha ya mata signal tareda cewa "guess what?"

girgiza kai tayi ya mika mata hanu suka tafa yace "yau madam ba zata zo wajen aiki na tace ta bar komai a hanuna zamu tafe tare dake yau tare zamuyi aiki saiki tayani ko?"

gyaɗa kai tayi tana murmushi tace "to ya zanyi da ɗan lukutin wajen akinmu?"

yace "zanji dashi"

a kofan wajen aikinsu ya tsaya yace ta ɓuya a motan, ɓuya tayi ta ya shiga yayi fuskan tausayi ya gaishe da mutumin da yake ta hararanshi, mutumin ya amsa yace "yau ameesha ba zata samu zuwa wajen aiki ba cikinta kanta kafanta na ciwo sai gobe zata zo, bayan wannan sai me zaka kara akan maganan da zakayi?"

shiru yayi jin mutumin ya faɗi duk abinda zai faɗa, a hankali yace "eh sai gobe zata zo"

tsaki yaja yace "kullum magana ɗaya kaima kamar ita kake baku girma kamar yara fitamin da gani"

da sauri ya fita ya koma motan yace "muje muje"

saida sukayi nisa ta ɗago kai tace "ya yadda?"

gyaɗa kai yayi yace "yes"

har cikin company ya shiga da ita suka fita ya rike hanunta da jakanta data rataya, tayi kyau cikin riga da wando kamar kullum palazoo da top sai hula me faɗi akanta da takalmi canvas, shiga yayi duk masu aikin suka zuba mishi ido yace "yau kun san me?"

sukace "no"

yace "madam ba zata zo ba zamuyi shagalin birthday ɗin Ameesha ta cika shekara 21"

murna suka fara da shike duk sun san ameesha kullum tana zuwa kofan jiranshi kuma tare suka fara ganinsu, ameesha cikin murna tasa hanu a baki ta manta yau birthday ɗinta, yaje frij na manal ya kwaso musu sauran drinks ɗin ya fita ya siyo musu snacks dasu cake da yayi order tun a gida a rubuta happy birthday meesha, yazo ya fara haɗa musu party da taimakon ameesha, akan kujeranshi ya zaunar da ita yace "kema gobe zaki zo neman aiki anan kuma zaki samu by god grace kullum saiya zama muna tare"

murmushi tayi tace "to bani jakan na rike domin takadduna suna ciki"

bata yayi ta rataya,

shagali suke yi sun maida company yau kamar wajen party.

kwance take akan gado tayi shiru cikin blanket, ba wani rashin lafiya take ba amma tana jin jikinta so weak, a hankali ta yaye bargon ta tashi domin shiga toilet, rigan bacci daidai gwiwa ne a jikinta fari sal, gashinta tayi kitso biyu yayi kyau sosai, tasa hanu akan handle ɗin sai kuma ta tsaya, ji tayi tanason ganin yadda suke gudanar da aiki a company, komawa tayi bakin gado ta janyo laptop ta ɗaura akan cinyarta, buɗewa tayi ta shiga vootage ɗin data saita da cctv dake company, zaro ido tayi ganin Abdool yana yanka cake da wannan yarinyar a cikin company ɗinta, ɗauko cake ɗin yayi yasa mata a baki tana dariya ta rike hanunshi tana ci, sauran suna tafi suna mata waƙan happy birthday to you, murnan da yake kan face nata zai nuna maka yadda taji daɗin birthday da Abdool ya haɗa mata wannan shi ake kira surprise, fita yayi daga wajen ita kuma tana bawa kowa cake a baki tana murmushinta me kyau, shigowa yayi da manyan kwalaye ya durkusa kasa a gabanta yace "your birthday gift"

karɓa tayi ta buɗe ganin sabon waya babba me kyau da kuma sabon agogo da takalmi snicker ta aje a gefe ta durkusa a kasa itama ta rungumeshi, murmushi yayi yana kallon bayanta ganin sun fara zama too emotional faruk yace "let's continue with the party"

tashi sukayi suka fara shagali.

manal huci take yi tana kallonshi ya ɗau crown me kyau a cikin ɗayan kwalin golding ya sawa Ameesha, dariya take yi sosai tana jin daɗi tace "thank y..."

rufe mata baki yayi yace "kin manta? babu godiya tsakaninmu"

tana huci da sauri ta tashi ta cire rigan jikinta tasa dogon riga bata tsaya yin komai ba ta yafa mayafi kawai tasa dogon takalmi domin bata iya tafiya da flat shoe, fita tayi daga gidan a fusace ammi tana kiranta ko kallonta batayi ba, gateman yana ganin haka ya buɗe mata gate, sharara gudu ta fara tana huci kamar ta tashi a iska, da wani irin gudu ta shiga company tayi parking wani dake aiki a waje ya shiga da gudu yace musu ga madam tazo, man da ameesha suka fara tattara wajen cikin sauri da taimakon sauran mutanen suka tattara, hanun meesha ya rike ya ɓoye kwakayen ya zaunar da ita a kujeran masu neman aiki ta rungume jakanta saide bata cire crown ɗin ba, da sauri ya koma wajen zamanshi ya fara latsa laptop, kowa yana kallon laptop kamar ba abinda sukayi, karan takalminta sukaji babu wanda ya ɗago, a bakin kofa ta tsaya tana kare musu kallo, da mamakinta taga sun gyara ko ina sun nutsu, wani kallo ta aikawa ameesha take taji cikinta ya ɗibi ruwa, kallon Abdool tayi tace sannan ta kara kallon sauran tayi gyaran murya, duk suka tashi suna mata sannu da zuwa da gaisuwa, bata amsa ba ta shiga office ta nuna batasan komai ba, tana shiga ta aika a kira masu neman aiki, saida mutane biyu suka shiga kafin akazo kan ameesha, a tsorace ta kalli abdool yayi mata alaman taje kada taji tsoro, jijjiga kai tayi a hankali ta fara tafiya ta rike takaddunta gam, ta cikin computer take kallon duk abinda sukeyi har zuwa lokacin data fara knocking, bata amsa da wuri ba saida ta jima a wajen tana knocking kafin tace "yes"

juya baya tayi akan kujeran har ameesha ta shigo ta zauna tace "sannu madam gani"

juyowa tayi a hankali tana kallonta daga kasa har zuwa sama, takaddan data rungume ta kalla sannan tace "suna"

da sauri tace "Ameesha"

tace "bakida baba ne?"

da sauri tace "Ameesha Ibrahim"

tace "matakin karatu"

tace "secondary"

kara kallonta tayi a wulaƙance sannan ta jijjiga kai a hankali, tace "me kika karanta?"

da sauri tace "Art"

hanu ta mika tace "takaddu"

mika mata tayi da sauri cikin girmamawa, karɓa tayi tana kallo a hankali, ta jima kafin ta ɗago kai, tashi tayi tazo gabanta, tana kallon cikin idonta tace "takaddunki yayi kyau amma kin san me zaisa ba zan ɗaukeki aiki ba?"

girgiza kai tayi, murmushin gefen baki tayi tace "sabida gaba ɗaya bakiyi kama da mata ba, kinfi kama da maza domin kullum cikin dressing nasu kike kuma kina tare dasu, meyasa ba zakiyi rayuwarki ke kaɗai ba saikin shiga harkan maza?"

shiru tayi, gani tayi ta matso da takaddun daidai fuskanta, zaro manya manyan idanunta tayi ganin ta yaga takaddun tayi pieces dasu ta watsa mata a fuska tace "fita ba zan ɗaukeki aiki ba"

idanunta cike da hawaye tabi takaddun da kallo, cire crown ɗin kanta tayi tace "sam baki dace da wannan crown ɗinba, bakya kama da sarauniya kinfi kama da ɓarauniya me sata abin company tayi birthday dashi"

kallonta tayi zuwa yanzu hawaye sun gama wanke mata fuska har zuwa gaban riganta, karɓan crown ɗin tayi ta maida kanta cikin hawaye tace "ban damu ba dan duniya sunce banyi kama da sarauniya ba, na yadda ni middle class ce, tunda Abokina ya bani sarautar na karɓa hanu bibbiyu nasan ya tsallaka mata high class dayawa ya bani sarautar sabida a wajenshi na fisu"

durkusawa tayi kasa ta kwashe takaddun data yayyaga cikin kuka ta fita, tana ganin Abdool ta share hawayen tana kakalo murmushi ta ɗaga mishi hanu tace "saika dawo na tafi"

da sauri ya tashi yaje gabanta ya tsaya ganin tana sunkuyar da kai ya ɗago fuskanta yana kallonta baice komai ba, da sauri ta kawar da kai tana maida hawaye tace "bari naje"

rike hanunta yayi ya kalli takaddun da suke a yage yace "me tayi miki?"

da sauri tace "ba kom..."

kuka ne yaci karfinta ta zare hanunta ta fita da gudu, binta yayi da kallo yana ganin tana share hawaye tana gudu, cikin zafin nama ya nufi office na manal babu ko knocking da kafa ya hankaɗa kofan ya shiga, turawa yayi gau, a firgice ta ɗago kai daga zaunen da take akan kujeranta me juyawa ta kalleshi, gabanta ya faɗi ganin wani irin kallo da yake aika mata sannan yana nufota gadan gadan cikin tsananin ɓacin ran da tunda ya fara aiki anan bata taɓa ganin koda rabinshi a tare dashi ba, cikin in ina tace "me..me..ya faru?"

akan kujeran da take ya dira hannayenshi duka biyu ya sata a tsakiya fuskanshi kusa da nata sosai, idanunshi sunyi jajur alaman yana cikin ɓacin rai, cikin kakkausan murya yace "me kike tambaya? me?"

a tsawace yayi maganan, zatayi magana ya nunata da yatsa ya girgiza ta akan kujeran a firgice tasa hanu biyu ta rike hanun kujeran tana kallonshi da dara daran idanunta, yace "kin san waye kika taɓa kin san ita ɗin wacece a rayuwata? me kika gaya mata!!!!?"

a tsorace tace "ban..ban..."

ya daka mata tsawan da yasa jikinta ya fara rawa yace "kin san wacece ita? akanta zan iya barin aikina koda biliyan ɗaya nake karɓa a kowane sati, kuskuren da zaki tafka a rayuwa shine ki kara taɓa ameesha a ranan zan nuna miki ke karamar ƴar iska ce, kin san wahalan da tasha kafin ta samu takaddunta?"

ya kara girgiza kujeran kamar zai kifar da ita, yace "kin sani?"

watsi yayi da kayan dake gaban table nata,

batayi magana ba ya riko hanunta da mugun karfi yace "kin sani?"

kara tayi cikin jin zafi tace "ash abdool ka sakeni da zafi"

yace "ki bani amsa"

girgiza kai tayi tace "A,a"

sakinta yayi yace "ba zaki sani ba sabida baki taso cikin wahala ba kin taso cikin wulaƙanta mutane kina ganin hakan shine jin daɗi, to bari na gaya miki wani magana idan baki sani ba, Ameesha macece da ko namiji ba zai iya jarumtar da tayi ba a cikin rayuwar family ɗinta da kuma nawa, da ni kika kira kika yayyaga takadduna kika min duk wulaƙancin da kikaga dama zan ɗauka amma banda Ameesha tafi ƙarfin wannan matukar ina wajen, kin fahimta?"

a tsorace jikinta yana rawa tace "eh"

sakin kujeran yayi ya fita daga office ɗin ya rufe kofan "gauuuu"

toshe kunne tayi domin kamar zai ɓalla kofan, a tsorace ta kalli kofan lokacin daya fita, da sauri taje ta ɗauko ruwan sanyi a frij tazo ta zauna tasha, rufe ido tayi tana sauke ajiyan zuciya kamar wacce tayi gudun minti talatin.

yana fita ya shiga motarshi yabi bayanta, har ta shiga napep ta tafi gida, duk wani gift daya siya mata saida ya ɗauko mata, gidansu yaje yayi sallama ya shiga, anty dake zaune akan sallaya taga ameesha ta shigo da gudu tana kuka sai kuma ga man, tana gani ya wuce da kwali baiyi magana ba, ɗakinta ya shiga ya kalleta ta kwanta tana kuka akan gado, zuwa yayi ya zauna kusa da ita, jin kukan yana yawa yace "idan kinaso zuciyata ta buga kici gaba da wannan kukan"

a hankali ta tashi ta share hawayen, murmushi tayi tace "raina bai ɓaci ba kawai de ina kuka ne"

rungumeta yayi domin tanada son ɓoye damuwa bada garaje take bari asan tana cikin damuwa ba, yace "karki damu ba zan kara kiranki inda za'a wulaƙantaki ba nima na aje aikin"

da sauri ta janye tace "ka aje aiki kuma? sabida me?"

ganin hankalinta ya tashi yace "bance na aje ba so nake na kwantar miki da hankali kiyi hakuri haka boss namu take muma hakuri muke da ita"

karɓan kwalin hanunshi tayi tace "gaskiya na tsorata na zaci zata kamamu muna shagali fa Allah ne ya taimakemu"

yace "hmm dako saita samu tsallen kwaɗo mu duka harda ke"

dariya tayi tace "zan gudu na barka"

sauka yayi yana ɗaga kafanta ya ɗaura akan cinyarshi yana sa mata takalmin, ganin ya mata daidai kuma ya mata kyau yace "wow ya kika gani?"

tace "gobe dashi zanje aiki"

yace "nima zan siya kalanshi muyi anko"

hanu ta mika mishi suka tafa, hira suka fara kamar ba abinda ya faru, manal da kyar ta saisaita kanta ta koma gida, koda taje ɗaki ta shiga bata yiwa ammi magana ba, toshe kunne tayi tana tuna tsawan da yayi mata, a ranan da kyar ta samu bacci, washe gari man daya kai ameesha wajen aiki komawa yayi gida baije aiki ba, manal da tazo bata ganshi ba sai taji jikinta yayi sanyi, wasa wasa har kwana biyar baizo aiki ba, ameesha idan an tashi saide ta ganshi a kofa yana jiranta yace mata yana tashi da wuri yanzu, ya hana kowa faɗa mata baya zuwa aiki, manal wacce take zaune akan kujeranta tana juyi hanunta ta dafa kai tana kallon pop ɗin saman ɗakin, idonta akan computer tana kallon duk masu aikin kujeranshi take kallo yau sati ɗaya kenan baizo ba, sai taji company ɗin yayi shiru babu wani abin cigaba ko walwala, duk da bata saba walwala ba amma taji wani kala, cikin sanyin jiki ta koma gida, da dare sai juyi take akan gado kusa da Ammi bacci yaki ɗaukanta, cikin juyin da yafi sau a irga ta rungume ammi tayi shiru kamar me bacci, Ammi wacce rabonta da samun isasshen bacci tun mutuwan Dady tace "manal?"

cikin sanyinta tace "na'am"

ammi tace "me yake damunki a cikin kwanakinnan bakya bacci?"

shiru tayi kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace "ammi meyasa ake damuwa da mutum idan ba'a ganshi ba?"

tace "so"

shiru tayi, smmi ta kunna wutan ta juyo ta kalleta tace "soyayya ne zaisa ki kasa bacci akan wani, idan kuma baki yadda ba ki gwada zuwa ki ganshi koda sau ɗaya ne, idan kinji farin ciki kinyi bacci to kin kamu da so"

a hankali ta rufe ido bata amsa mata ba, murmushi kawai Ammi tayi dan ta lura tana yawan tunani, washe gari tasa dogon riga dubai ta yafa mayafi siriri sannan tasa glass a idonta tasa dogon takalmi, ammi tace "ga breakfast"

girgiza kai tayi tace "banjin yunwa"

fita tayi bata jira taji me zata ce ba, cikin class take tafiya harta buɗe mota ta shiga, fita tayi ta nufi company ta kalli wajen zamanshi yauma baizo ba, shiga ciki tayi ta dafa kanta, waya aka kira na company ta ɗauka ta kara a kunne, cikin sanyin muryanta tace "yes nice"

shiru tayi tana sauraran abinda ake cewa, sannan tace "okay deal"

aje wayan tayi ta buga jikin table na gabanta tace "ta ina zan fara nemanka? gashi ana buƙatan zane kala ɗari biyu"

dafa kai tayi kamar tayi kuka sai wani tunani ya faɗo mata, da sauri ta kira numbern faruk tace "shigo"

bs jimawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login