Showing 42001 words to 45000 words out of 83501 words

Chapter 15 - DUHU DA HASKE Hausa Novels by Jiddah S Mapi.docx

19 Sep 2025

2251

ya shigo yace "gani madam"

cikin rashin fara'anta tace "kasan gidansu Abdool?"

yace "eh na sani"

ta bashi takadda da biro tace "rubutamin address"

rubuta mata yayi sannan yace "sune a farko"

ta karɓi tskaddan kawai ta tashi, tsintsan kanta tayi da gyara fuskanta a madubi sai kuma ta fesa turare tayi murmushi, fita tayi tana kaɗa makullin mota a hanu har ta shiga, fita tayi tana driving cikin kwarewa tana duba address ɗin.

Ameesha ta kalli agogo yau an tashi musu da wuri tace "ya zanyi da man? ko dai zanje na sameshi nace yau shi kaɗai zai tafi nikam na wuce ne?"

sai kuma tace "gaskiya gara naje"

sauri ta fara akan titi ta saba da tafiyan sauri bata damuwa har taje company ta shiga ciki domin nemanshi, wani ta samu tace "please ina neman Abdool"

yace "Abdul ai yayi sati baya zuwa aiki"

tace "amma kasan wani abdool nake nema?"

hotonshi ta nuna mishi tace "wannan fa"

yace "na sani mana yayi sati baya zuwa aiki tun ranan da akayi birthday ɗinki anan bai kara zuwa ba"

da sauri tace "na gode"

fita tayi ta kira wayanshi ya ɗauka cikin nauyin bacci yace "darling"

a hankali tace "meyasa bakazo aiki ba?"

yace "banda lafiya"

kafin tayi magana ya kashe wayan, napep ta shiga zuwa gidansu.

manal cikin kankanin lokaci ta isa gidan da aka tabbatar mata shine nasu, kallon gidan tayi na talakawa ne a hankali tayi knocking, ba'a buɗe ba, ta kara yin knocking, Imran dake kwance cikin busy ɗin falonsu ya ɗaura kai a ƙafan umma yana karatu yaji ana knocking kallon umma yayi yace "nasan ba Ameesha bace dan tana wajen aiki"

umma tace "to jeka duba mana"

tashi yayi, gajeren wando ne a jikinshi ya buɗe kofan, manal ce tsaye tana ganinshi tayi mishi murmushi, waro ido yayi cike da mamaki yake kallonta, umma dake ɗinka safan sanyi wa ameesha tace "imran waye ne?"

baiyi magana ba ta tashi zuwa wajen domin ganin ko waye, ido huɗu sukayi da manal wacce take tsaye tana murmushi, a hankali tace "sannu da zuwa"

cikin murmushi tace "yawwa"

ganin sun tsaya basu bata hanya ba kuma basu ce ta shigo ba Imran sai leƙa abdool yake, tace "zan iya shigowa?"

a hankali umma ta matsa mata, Abdool daya tashi a bacci yanzu ya ɗau brush ya fito dashi a bakinshi, wando three quarter da riga armless a jikinshi, gashinshi kamar na mace ya barbaza sabida bacci, idonshi a lumshe yace "Imran waye yazo?"

Imran ya juyo yana mishi alama ya tattara ɗakin kafin ta shigo, waro ido yayi ganinta a tsaye bakin kofa tana murmushin da yake kara mata kyau sosai, da sauri ya juya ganin wandon dake jikinshi ya koma ciki domin sa jallabiya, umma tace "shigo"

ƙafan hagu tasa zata shiga sai kuma sukaga ta koma da baya tasa ƙafan dama tace "salam"

umma ta nuna mata wajen zama tace "zauna"

a hankali ta zauna tayi shiru tana kallon Imran dake tattare kayan ɗakin, da gani kanin abdool ne domin suna kama sosai,

umma ta kawo mata ruwa tace "ga ruwa"

karɓa tayi tasha sannan tace "na gode"

ajewa tayi tace "ina wuni"

umma tace "lafiya amma saide ban ganeki ba"

a hankali tace "sunana manal daga wajen aikin Abdoool"

tace "laaaa kece? dan Allah kiyi hakuri bari na kawo miki abinci"

shiru tayi umma ta shiga kitchen tareda Imran ta zuba mata shinkafa da waken data dafa tun na safe Abdool baici ba, Imran ne ya kawo mata lokacin abdool ya fito daga ɗaki sanye da jallabiya brown, yayi kyau sosai musamman da gashinshi ke harharɗe, a nesa da ita ya zauna yace "sannu da zuwa"

tace "kayi mamakin zuwana ko?"

yace "eh"

kallonshi tayi sai taji duk wani damuwan da take ciki ya kau, tace "nazo na baka hakuri akan abinda ya faru kuma ina rokonka ka dawo aiki"

yace "bani zaki bawa hakuri ba wacce kika yiwa zaki bawa hakuri"

zatayi magana ameesha ta ɗaga murya tun daga bakin kofa ta fara ƙwala mishi kira "maaaaaaaan maaaaan ina kake? yau saika......"

turus ta tsaya a bakin kofa ganin manal ta sauko kasa wajen abincin ta fara zubawa, ɗago manyan idanunta tayi tace "Imran zan samu tumatir da attarugu?"

Imran yace "eh"

da sauri yaje kitchen ya ɗauko mata tumatir da attarugu ya aje mata da karamin wuƙa, murmushi tayi tace "thanks"

wani kallo ta aikawa ameesha tace "shigo mana ko bakiyi farin cikin zuwana bane?"

a hankali ta shigo ta zauna kusa da man, kafin tayi magana manal ta kalli man tace "zan samu ruwa?"

gyaɗa kai yayi ya tashi domin kawo mata ruwa, umma da Imran sun tafi ɗaki domin bata waje taci abinci, a hankali ta ɗauki wuƙan ta fara caccakawa akan attaruhun kanta a kasa, a tsorace Ameesha take kallonta, ɗago ido tayi ta ɗau Attaruhun ta fara ci, babu ko alaman jin zafi a tare da ita saide idonta yayi jajur tana kallon ameesha dasu, cikin tsoro ameesha take waro ido, saida ta cinye duk attaruhun batasa komai a bakinta ba, Abdool yazo da ruwan ya mika mata, karɓa tayi da mugun mamaki ameesha take kallonta ganin ta aje ruwan bata sha ba, cikin kakkausan murya da jajayen idanunta tace "kiyi hakuri"

ameesha a tsorace ta kalli man zata tashi yace "tana baki hakuri"

manal ta dunkule hanu da karamin wuƙan a hanunta tace "kiyi hakuri da abinda ya faru"

gani ameesha tayi hanunta yana jini, a firgice tace "hanunki?"

ɗaga mata ɗayan hanun tayi tace "ina baki hakuri ki maida hankali akan hakurin ba jikina ba"

man bai kula da abinda take yiba, ameesha tace "ba komai ya wuce"

tashi tayi tana murmushi ta ɓoye hanunta dan kada yaga jinin tace "na gode zan tafi office amma zaka dawo bakin aiki?"

murmushi yayi ganin ta bawa ameesha hakuri yace "yanzu ma zan tafi ki jirani zan fito"

a hankali tace "ina mota"

shiga ɗaki yayi ita kuma ta kalli ameesha kallon dako ita bata san name bane, sannan tayi murmushin gefen baki ta kalli umma data fito yanzu ta ciro kuɗi daga aljihunta na rigan, dubu ɗaɗɗaya ne sabbi dal bunch biyu ta aje a kusa da umma tace "to umma ga wannan ba yawa, na gode na tafi"

umma tace "a,a bamason haka dan Allah kada kiyi haka"

murmushi kawai ta fita bata jira umma ta karasa maganan ba, a hankali tace "mun gode"

ficew tayi daga ɗakin, motarta ta shiga ta ɗauko ruwan dake cikin gora cikin azaban da harshenta yake ta fito dashi waje ta fara zuba ruwan, babu sanyi ta kama gefen riganta tana gogewa wasu zafafan hawayen azaba suna zubowa.

Ameesha ganin ta fita kalli kuɗin sannan ta kalli umma wacce itama take kallon kuɗin da mamaki, bin man tayi da gudu zuwa ɗaki, ya cire jallabiyan yana shirin sa kaya me kyau ameesha tace "man wannan matar fa hankalina baya kwanciya da ita kamar fa muguwa ce da wuya idan tanada imani...."

sa rigan yayi ya rufe mata baki yace "koma menene tunda ta sauke kai tazo har gida ta baki hakuri ai shikenan saimu kalli kirkin da tayi mu zubar da rashin kirkinta ko?"

girgiza kai tayi ya cire hanunshi a bakinta yana sa takalmi tareda ɗaukan wayarshi tace "ba hakurin zaka duba ba abinda yasa ta bada hakurin zaka...."

yace "kai princess kada ki zama me korafi mana ban sanki dashi ba"

zatayi magana yace "na tafi"

fita yayi ta bishi har waje tana kokarin fahimtar dashi har ya buɗe motan ya shiga, kallo manal ta bita dashi sannan tayi mata murmushin gefen baki ta kuma haɗa fuska taja motan suka tafi, ameesha cikin damuwa da jin haushin man da ya kasa fahimta ta juya zata tafi Imran yace "nima hankalina bai kwanta da ita ba"

da sauri tace "kaima ka gani ko? kaga me na gani a tare da ita? amma shi man ya kasa ganewa"

yace "ba komai bata isa tayi komai ba sai abinda Allah yayi"

tace "hakane amma mu kare kafin wani abin ya faru"

yace "addu'a"

tace "ys gama komai"

tafa hanu sukayi yadda suka saba.

a mota yaga tayi shiru yace "ya jikinki?"

a hankali tace "ba sauki"

yace "me yasa?"

tace "aini kullum cikin rashin lafiya nake kwana ban taɓa kwana ɗaya cikin jin daɗi ba"

shiru yayi, sannan yace "amma meyasa?"

tace "banida kowa sai ammi idan kaga na ɗaga waya to da masu aikina ko wanda nake aiki tare dasu nake magana ko kuma Ammi haka nake rayuwa babu kawa babu kowa"

kallonta yayi yaji tana bashi tausayi domin innocent face gareta bata magana sosai, yace "to kiyi kawaye mana"

tana kallon titi yana kallonta tace "ban iya ba saide idan zaka koyamin"

yace "shikenan zan koya miki domin Dr a gabana yace idan baki samun farin ciki za'a iya rasa ki"

murmushi tayi tasan hakan zai iya faruwa domin ko ita kanta tana jin hakan a ranta, tace "amma da sharaɗi"

gyara zama yayi yace "ina jinki"

tace "da kai kaɗai zanyi abota sannan duk wani damuwata zan rinƙa faɗa maka, kuma zanso nima na fara yin waya kamar kowa naji yadda akeji nima inaso nayi dariya a rayuwata banson zama irin na gidanmu da nakeyi kullum cikin ɗacin rai"

yana iya hango damuwa a tare da ita, a hankali yace "na amince"

badan komai ba sai dan ya ceto rayuwarta daga shiga matsala.

murmushi tayi ta mika mishi hanu irin na yara a tv idan zasuyi alkawari haka taga sunayi tace "promise"

yasa hanun a nata ya sarke sannan yace "promise"

a takaice tayi murmushi tace "thanks"

daga nan har suka isa company bata kara cewa komai ba, rashin magana a jininta yake, koda suka fito fuskanta kamar kullum ta mayar kamar bada ita suka gama hira ba, kallonta yayi yace "idan kina dariya kinfi kyau"

murmushi tayi tace "ban saba ba kullum haka ammi take cewa"

a tare suka shiga ciki suna ganinta suka tashi tayi musu alama su koma su zauna, office ta wuce man kuma yayi musu gaisuwa sannan ya zauna a mazauninshi yana buɗe laptop ɗinshi daya jima be buɗe ba, zama tayi akan kujera tana kallonshi ta cikin computer ko kyafta ido batayi, yau cikin farin ciki ta wuni.

*Jiddah Ce....✍🏻*

08144818849

[09/04 à 08:06] JIDDA MAPI: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*DUHU DA HASKE*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Na

*Jiddah S mapi*

*Chapter 12*

~Bayan an tashi tafiya take kamar hawainiya tana taku a nitse cike da class, Abdool ya rataya jakanshi yana waya da ameesha sai dariya yake suna haɗa ido yayi mata murmushi yaci gaba da wayanshi yana makalewa a kafaɗa ta yadda wayar ba zai faɗi ya fara rufe laptop nashi, a hankali take tafiya har ta iso kusa dashi, yace "my meesha saina dawo"

ji tayi wani abu ya tokare mata kirji sunan daya kira sai taji kamar ansa wuta a kirjinta, sa wayan yayi a aljihu yace "madam kema kin fito?"

harɗe hanu tayi a kirji tana kallonshi, yanada matukar kyau yafi kama da indiyawa, cikin alaman respect yace "madam na tafi"

murmushi tayi tace "mahaifinka ɗan wani kasa ne?"

yace "nigeria"

jijjiga kai tayi tace "amma da naje ban ganshi ba"

yace "ya mutu da jimawa tare suka mutu da mahaifin ameesha sabida abokaine tun suna yara sunyi accident rana ɗaya suka mutu"

shiru tayi jikinta a sanyaye tace "Ayya sorry Allah yaji kanshi"

kallonta yayi yana gyara jakan yace "Allah yaji kansu dai"

a takaice tace "Allah yaji kansu"

yace "ameen madam"

tace "ba madam ba sunana manal"

murmushi yayi yace "ameen manal"

tafiya suka fara tana harɗe da hanu a kirji har suka fito daga, wajen motarta ya rakata zata buɗe marfin yayi saurin buɗe mata, ɗan ranƙwafawa yayi hannaye a baya kamar wata soja yake gabanta yace "to ranki daɗe allah tsare hanya"

shiga tayi ta zauna tana kallonshi har ta tada motan, wucewa yayi wajen motarshi ya shiga hanu ta ɗaga mishi shima ya ɗaga mata hanu, itace ta fara tafiya kafin shima ya tafi, ita kaɗai sai murmushi take harta isa gida, gateman daya buɗe mata yaga ta sauke glass fuskanta ɗauke da murmushi a fili yace "lalle yau za'ayi ruwa da ƙanƙara wannan ce take dariya?"

a babban tsararren compound ɗinsu tayi parking kana ta fito ta rufe motan, tana tafiya tana ɗan haɗawa da tsalle ita kaɗai tana dariya, tura kofan falon tayi cikin tsallenta da dariya ta shiga, ammi tana tsaye a kusa da showglass tana da turare juyowa tayi taga manal tana tsalle tana juyi a ɗakin tana dariya, haka kawai taji gabanta ya faɗi, tasan idan manal tana dariya haka da farin ciki to wani abin ne ya faru mara daɗi, da gudu taje ta rungume ammi ta ɗagata sama tana juyi da ita, ajeta tayi ammi tana kallonta da mamakin farin cikin da take ciki tace "manal me?"

hanun ammi taja ta zaunar da ita akan sofa, zama tayi akan cinyarta ta zagaye hannayenta a wuyanta, kwantar da kai tayi a kirjinta cikin farin ciki tace "Ammi am in love"

da sauri tace "love?"

jijjiga kai tayi tace "ammi na kamu da soyayya"

murmushi ammi tayi me kama da dariya tace "ƴata ta girma, amma wani me sa'an ne wannan?"

wsyarta ta ciro ta nuna mata hoton abdool wanda ta ɗaukeshi yau ba tareda ya sani ba, tace "Abdool"

kallonshi ammi tayi tace "ba shine yazo gida rannan ba?"

jijjiga kai tayi tace "shine ammi shi nakeso"

cikin jin daɗi ammi tace "shima yana sanki?"

shiru tayi take yanayinta ya canza, da sauri ammi tace "kin tambayeshi ko yanada budurwa?"

a hankali ta fara canja fuska daga dariya zuwa asalin kalanta, tace "sabida me zan tambayeshi?"

ammi tace "sabida kada ki shiga tsakanin masoya akwai ciwo"

kallon ammi tayi ido cikin ido, da sauri ta tashi daga kan cinyarta ta goya hanu a baya ta fara zagaye falon, can tace "ban tambaya ba kuma koda yanada budurwa bai dameni ba abinda na sani shine ina sanshi"

ammi zatayi magana ta juya tana cigaba da tsallen jin daɗi ta haura sama, rufe ido ammi tayi tace "ya Allah nasan halin ƴata idan tana son abu bata damu da ko abin ya dace da ita ko akasin haka ba, hasalima kwata take ta karfi da yaji, ina rokonka kasa baida budurwa"

tana shiga ɗakinta ta janyo kayan zanenta ta wurgar da mayafin jikinta ta ciro kaya marar nauyi riga da wando fari sal tasa, stool ta aje kusa da black boat ta ɗauko zanen ta fara zana hoton abdool, sauka tayi daga kan stool ɗin cikin kwarewa ta zauna a kasa duk fentin ya ɓata mata fuska da jiki, murmushi kawai take tana ciza leɓenta na kasa ganin zanen yana fita, ita kaɗai tana dariya, wayarta aka kira ta ɗaga bata duba suna ba ta kara a kunne, cikin farin cikin da take ciki tace "hello"

aka amsa tareda cewa "mune muka kiraki akan taimakon yara mata da aka yiwa fyaɗe kikace bakida time a lokacin shine muka kiraki yanzu"

cikin yanayin da take ciki tace "na basu kyautan biliyan ɗaya"

da sauri ya kalli wayan yace "amma muna magana ne da manal umar maidawa?"

tace "kwarai nice yau ina cikin farin ciki ku turo account number"

kashe wayan tayi ya turo account number, a wajen ta tura mishi, cigaba tayi da zanenta yana kiranta tana ji bata amsa ba, ammi ganin ta jima sosai bata fito ba ta shigo mata ɗaki da abinci bakinta ɗauke da sallama ta shigo tace "manal me kike tun ɗazu baki fito ba?"

turus ta tsaya ganin ta zama kamar sabuwar kamu a hauka duk jikinta ta ɓata da fenti gaba ɗaya ta maida hankali akan zanen hoton da take yi, bata juyo ba kuma bata amsa ammi ba, aje plate ɗin tayi tace "manal me haka kikeyi?"

sai a yanzu ta juyo, fuskanta duk ya ɓaci da fenti baƙi da blue da sauran kaloli, juyawa tayi taci gaba da zanen saida ta gama tas sannan ta kalli ammi dake zaune a bakin gado tayi tagumi tana kallonta, murmushinta me kyau tayi sannan tace "ammi wani kala ne kike ganin babu kuma ya dace asa a jikin hoton masoyi?"

ammi cikin tsorata da yanayin manal tace "duk kala ansa manal yayi kyau ki bari kici abinci tunfa da safe bakici komai ba"

murmushi tayi ta kara kallon hoton kana tayi kamar tana tunani, can tace "RED"

kallon kalolin ta fara bataga red ba, tashi tayi taje ta buɗe drower ɗin da take zuba kaloli ta fara dubawa bata gani ba, haukacewa tayi s ɗakin tana watsi da kayan cikin wardrobe nata, da sauri ammi ta tashi tana riketa tace "manal ki dawo hankalinki mana me kikeyi haka?"

tace "red color nake nema"

ta duba ko ina bata gani ba, fita tayi daga ɗakin taje ɗakin ammi ta ɗauko reza tazo ta tsaya a wajen hoton, ta zanashi yana dariya kamar yadda ya saba a koda yaushe, ammi a firgice tace "me zakiyi da reza manal?"

batayi magana ba ta rufe ido ta tsaga hanunta, rufe ido Ammi tayi sai kuma ta buɗe tana ganin jini da yake zuba har kasa, da gudu ta tashi tana rike hanun tace "kinyi hauka ne manal?"

murmushi tayi fararen haƙoranta masu matukar kyau suka bayyana, gefen kumatunta ya lotsa, tace "ammi na INA SON ABDOOL"

zama tayi kasa daram jinin ya fara ɓata tiles na ɗakin har jikinta a ɓace yake, da hanunta da yake malalar da jinin ta fara shafa duk inda yake buƙatan jan kala a jikin hoton, saida ta tabbatar ya zama perfect sannan ta juyo da dara daran idanunta masu shape ɗin kwai farare sal kamar madara, tana murmushin da yake kara mata kyau tace "wow ammi ya kika gani?"

ammi jikinta yana rawa ta rasa me ma zatayi, shagwaɓe fuska manal tayi kamar karamar yarinya tace "ammi na magana fa nake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login