Showing 51001 words to 54000 words out of 83501 words

Chapter 18 - DUHU DA HASKE Hausa Novels by Jiddah S Mapi.docx

19 Sep 2025

2252

a wajenta"

shiru sukayi ya fita ammi sai shesheƙan kuka take shi kuma yana girgiza kafa yayi shiru, sun jima sosai a haka kafin ta fara buɗe ido a hankali ta sauke akanshi, murmushin da yake lotsar da gefen kumatunta tayi, saide oxygen ya hana suga murmushin, hanu ta mika mishi cikin sanyin jiki ya mika mata nashi, gaisawa tayi dashi sai kuma ta lumshe ido ta kalli ammi, ɗayan hanun ta mikawa ammi, saida ta ɓuya ta share hawaye kafin ta mika mata hanun itama suka gaisa, hannayensu a cikin nata tana kallonsu tana girgiza kai alaman kada su bari hawayensu ya sauko

juya baya man yayi cikin yanayin da ko shi kanshi baisan me yake ji ba yace "will you marry me?"

hawaye masu zafi suka fara sauka daga idonshi, ammi kallonshi tayi sai kuma ta kalli manal wacce itama take kallonshi, ganin bai juyo ba taja hanunshi, juyowa yayi kanshi a kasa yace "zaki aureni manal?"

lumshe ido tayi ta buɗe, a hankali ta jijjiga kai, murmushi yayi tareda hawaye ya kalli ammi yace "zan auri manal yanzu idan kin amince"

ammi cike da mamaki tace "yanzu?"

yace "eh"

kallon manal tayi wacce idonta akanta, a hankali kuma ta kalleshi taga hawaye sai zuba yake, a hankali tace "na amince"

murmushi yayi mata ya zame hanunshi daga na manal yace "ki kira duk wanda kike ganin ya dace ya zama waliyyinta sannan mu samu shaidu nima zan kira wanda zai zama waliyyina"

a hankali tace "to Abdool amma kada kayi abinda zai zo ya zama maka ma..."

yace "ki kirasu yanzu"

fita yayi ya ɗaga wayarshi ameesha tayi mishi miss calls dayawa, kiran numbern faruk yayi yace "faruk taimako nakeso kamin ka siyomin goro da cingum dayawa kazo min da cash na dubu ɗari sannan kazo ka sameni a well care hospital ɗaki me number huɗu"

faruk ya fara jero mishi tambaya yace "kayi abinda nace ina jiranka yanzu"

kashe wayan yayi bai amsa mishi tambaya ko ɗaya ba, ammi baba megadi ta kira tace "kazo asibitin well care yanzu ɗaki me number 4 ina jiranka ka samu driver yanzu ku taho tare"

kashe wayan tayi tana zaune tana kallon manal itama manal tana kallonta babu bakin magana, saide tana lumshe ido kuma tana buɗewa akai akai, basu jima ba saiga faruk suma du baba megadi suka zo, duk suka shiga ɗakin Abdool ya karɓi goron da cingum da kuma dubu ɗarin ya aje a kusa da manal yace "wannan shine sadakinki 100k ne"

ya kalli faruk yace "kaine waliyyina"

Ammi cikin hawaye tace "baba kaine waliyyin manal"

duk suna kallonsu da mamaki, yace "mu kira sauran likitocin su zama shaida suma"

faruk cike da mamaki yaje ya kira duk nurse da dr ɗin asibitin, kowa ya taru a ɗakin suka shimfiɗa babban tabarma anan aka fara ɗaura auren Abdulrahman haruna lamiɗo da manal umar maidawa akan sadaki naira dubu ɗari, kowa ya shafa fatiha ciki harda ammi wacce take kuka sosai, hawaye ya gani a idon manal yana sauka, shima hawayen yake yi, faruk yace "wai meke faruwa ne Abdool?"

cikin sanyin jiki yace "babu komai"

cingum ɗin yasa tasa hanu ta ɗau guda ɗaya tana ɓarewa, shiru yayi yana kallonta, alama tayi mishi ya karɓa, a hankali ya matso yasa hanu zai karɓa ta janye, kallonta yayi ta kai kusa da bakinshi buɗewa yayi tasa mishi, a hankali yayi murmushi ya share hawaye, text yaji ya shigo wayarshi, dubawa yayi yaga ameesha ce ta turo sako kamar haka

"barka man kasan me? nayi kewarka sosai, jikin umma yayi sauki anyi mata allura harma taci abinci, nasan abu ne me muhimmanci ya hanaka zuwa ka karasa abinda kake kafin kazo nasan koma menene abinda zai gyara rayuwarmu kake yi, bye take care"

jikinshi yana rawa ya maida wayan aljihu, gani yayi manal tana kallonshi, ya kakalo murmushi yayi mata, lumshe mishi ido tayi.

_naji dayawa mutane suna tambaya wacece jaruma tsakanin ameesha da manal, to gaskiya jarumai biyu ne, amma asalin jarumar itace manal domin labarinta ne wannan, sannan naji wasu suna cewa basa karanta wajenta suna wucewa su karanta nasu ameesha, ya kamata ku nutsu ba lalle kowane labari yazo maka a yadda kake so ba, dole akwai lost story, dole akwai labari me taɓa zuciya, so ku karanta labarin manal ku kwantar da hankali a rayuwa akwai jarabawa kuma a rayuwa dole akwai nasara kuma akwai faɗuwa, wannan lost story ne sai kunyi hakuri sosai wajen karatu_

*Jiddah Ce....*

08144818849

[09/04 à 08:06] JIDDA MAPI: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*DUHU DA HASKE*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Na

*Jiddah S mapi*

*Chapter 13*

~Kwance take akan gado tana rawan sanyi hakoranta suna haɗuwa sai kankame jiki take tana kara jan bargon tana rufa har kanta, amai taji yana zuwa mata da sauri ta tashi zata sauka akan gadon kawai taji aman yazo, jini take amarwa akan farin bedsheet ɗin dake kwance me taushi akan gadon, ji tayi kirjinta yana zafi jikinta yana zufa, ammi wacce ta fita domin kawo mata maganinta ta buɗe kofan ta shigo hanunta rike da glass cup cike da ruwa da kuma maganin a ɗayan hanunta, faɗuwa glass cup ɗin yayi a wajen ya tarwatse, cikin ihu tace "manal"

da gudu ta watsar da maganin taje kan gadon tana tiketa, tayi aman jini sosai kafin ta ɗago tana haƙi tana kallon Ammi, cikin tashin hankali ammi tace "bari na kira dr habib"

bata musa ba ta koma ta kwanta tana cigaba da rawan ɗari, kiran wayan dr habib tayi tace "kazo yanzu jikin manal ya tashi kuma da alama yayi worst domin tana aman jini sosai, ka taimakeni dr ka taimakeni"

yace "okay ina zuwa"

kifa kanta tayi akan ƙafan manal ta fashe da kuka kamar zata shiɗe, manal dake cikin bargo ta miko hanu tasa hanunta cikin nata ta damke, man sai safa da marwa yake a cikin company ya rasa abinyi, manal tana yawan gaya musu batason abinda zai ɓata tsakaninta da wanda suke harka dasu na kasar china wato mr chang, sai kiran wayanta yake ba kakkautawa yana shiga amma bata ɗauka, yana tsaye ya rasa abinyi yaji an dafashi, da sauri ya juyo faruk yace "man mr chang fa yace idan ba'ayi wannan zaman yau ba zaiyi resign da company ɗin m.u.m kuma madam tace koda wasa bataso ta rabu dasu ina ganin sai kaje gida kaga ko meya hanata fitowa dan shima yanzu yanata kiranta bata ɗauka, kuma yace koda wakili ne ta tura suyi wannan zaman"

shiru yayi na ɗan lokaci, kallon faruk yayi yace "to muje gidan nasu mana mu duba ta tare"

faruk ya girgiza kai yace "no kaje ka dubata zanji dasu mr chang zan basu hakuri har tazo dan nasan idan taji shine babu abinda zai hanata fitowa koma menene"

da sauri yace "to shikenan kaje kaji dashi bari naje"

yace "saika dawo"

motarshi ya shiga da sauri ya fita, gudu yake akan titin yana kara gwada number ɗinta ko zata ɗauka bata ɗauka ba, cikin jin haushi ya aje wayan, a kofan gidansu yayi parking ya fito yana knocking, ammi wacce ta kasa zama ganin manal tana kara yin aman ta fito da gudu ta mayar Dr habib ne, da kanta ta buɗe gate ɗin a rikice tace "Dr kazo da sauri zata mutu..."

ganin Abdool tsaye yana shirin gaisheta taja hanunshi da sauri kamar ma bata cikin hayyacinta tace "yawwa gara da kazo ka taimakeni manal zata mutu"

Binta yake yana kallonta da mamaki, ɗakin manal ɗin ta kaishi suna shiga tana amai sosai ta ɓata gaban riganta, zaro ido yayi yace "madam?"

tare da ammi suka karasa wajenta, tana ganinshi ta mika mishi hanu riketa yayi yace "madam"

aman ne ya tsaya cikin galabaita tace "Abdool zan mutu"

da sauri yace "ba zaki mutu ba"

idonta cike da hawaye tace "koda banda lafiya babu me zuwa wajena sai ammi"

kuka take yi me taɓa zuciya, dr habib ne yayi sallama ammi tace "shigo"

shigowa yayi ya fara dubata, man ya cire bedsheet ɗin daya ɓaci da jinin ya fitar waje ya bawa me aikinsu, ammi ta juya hotonshi ta yadda ba zai gani ba, allura yayi mata sannan ya kalli ammi yace "ciwon manal yana karuwa ku rinƙa kula da ita ku daina barinta ita kaɗai akwai matsala babba idan ana barinta ita kaɗai tunani yayi mata yawa sannan wannan rashin dariyan nata shi yake kara ciwon idan so samu ne kuyi mata aure"

shiru ammi tayi sai sharan hawaye da take, shi kuma Abdool ya zauna a gefe yana kallonta tana bacci cikin nutsuwa, har Dr ya tafi babu wanda yayi magana, a cikin bacci tayi juyi ta turo baki sannan taci gaba da baccinta, sun ɗau lokaci kafin ya turawa faruk text "yana nan?"

faruk yayi reply da "eh"

baiyi magana ba ya tashi zai tafi cikin muryan ciwo tace "Abdool"

da sauri ya juyo yace "na'am madam"

da hanu tayi mishi alaman yazo, zuwa yayi ya tsaya yana sunkuyar da kai, ta mika mishi hanu tace "ɗagani"

ɗagata yayi ta zauna tana kallonshi tace "me yasa kazo?"

yace "dama mr chang ne yazo kuma yace idan bai haɗu dake ba wannan shine last chance, na kira wayarki kuma baki ɗauka ba shiyasa nazo"

a hankali tace "to yanzu idan ka tafi me zakace mishi?"

shiru yayi, tayi murmushi tace "zakace banda lafiya?"

gyaɗa kai yayi, ta nuna mishi gefenta tace "zauna"

zama yayi ta ɗau waya ta kira numbern mr chang, cikin sanyin muryan rashin lafiya tace "unfortunately I won't be able to attend but my manager will be representing me"

tana faɗan haka ta sauke wayan, man da mamaki yake kallon ta, a hankali ta sauka akan gadon cikin ciwo da rashin karfin jiki da jinin daya ɓata mata gaban riga taje cikin wardrobe nata ta buɗe, ciro wani kayan data ɓoye na dady tayi sannan tazo babanshi, tashi yayi dan ganin me take shirin yi, a hankali ta durkusa kasa ta mika mishi kayan tace "will you be my manager?"

da sauri ya kalleta sannan ya kalli jinin dake gaban riganta tunawa yayi da abinda Dr ya faɗa, a hankali yasa hanu akan kayan da take mika mishi ya haɗa da hanunta ya ɗagata, tissue dake gefe ya yaga ya goge mata bakinta duk inda jini ya ɓata a fuskanta a hankali ya jijjiga kai yace "not only your manager but also your caregiver"

murmushi ammi tayi cikin hawaye tace "zaka kula da ita da gaske?"

a hankali yace "insha Allah"

manal tayi dariya kaɗan sannan tace "wannan kayan mahaifina ne yanzu nake so kasa dashi zaka je kayi representing ɗina"

zai yi magana tace "no please Abdool"

tausayi take bashi a hankali ya karɓa, ta nuna mishi toilet tace "shiga ka canja"

shiga ciki yayi ta koma bakin gadon ta zauna tana rufe ido domin kirjinta ciwo yake mata, tana zaune a wajen ya fito cikin manyan kayan shadda ne me kyau maroon da hula maroon, yayi kyau sosai kasancewar bai saba sa manyan kaya ba yasa hulan bai zauna akanshi yadda yake so ba, murmushi akan fuskanta ta tashi zuwa wajenshi tayi mishi alaman yayi kyau, sunkuyar da kai yayi badan yaso ba yasa kayan, gyara mishi hulan tayi sannan ta lumshe ido ta buɗe akanshi, yace "zan tafi"

tace "Abdool"

tsayawa yayi, taje ta buɗe drower ɗinta ta ciro sabon makullin mota tazo gabanshi ta mika mishi hanunta tace "bani makullin motarka"

yace "me zakiyi da ita?"

tace "bani mana"

bata yayi ta rufe a hanunta, sabon makullin mota ta bashi sannan tace "wannan naka ne wa kai na siyawa sabida ka zama manager kasan komai ya dawo kanka na company, fitowa da wuri tashi bada wuri ba, sannan zaka iya yin tafiya zuwa kasashe da dama a koda yaushe ka zauna cikin shiri domin kaine zaka rike company ɗin m.u.m"

girgiza kai yayi yace "gaskiya ki barni da motata a matsayin da nake ma a company ina aiki ina samun kuɗina ya isheni"

girgiza kai tayi tace "Abdool kokarinka yasa na baka wannan matsayin ba wai sabida wani abu ba kuma ka cancanta"

girgiza kai yayi yace "gaskiya banaso ki bani makullina kawai."

bashi tayi ta juya tana sharan hawaye rike kirji tayi tace "kullum saina faɗa miki ammi harta kyautan da zan bawa mutane basason karɓa a hanuna"

jikinshi yayi sanyi sosai yace "zan karɓa"

murmushi tayi da sauri ta juyo tana share hawaye tace "da gaske zaka karɓa?"

jijjiga kai yayi ya mika mata hanu, danka mishi makullin tayi, yace "na tafi"

ammi tace "Abdool"

tsayawa yayi, tace "Allah ya maka albarka ya kareka da kariyanshi ya tsareka da sharrin kowane sharri"

ido manal ta zuba mata, shiru tayi yace "ameen"

fita yayi jikinshi a mace, duk abinda ya karɓa ba dan kanshi yaso ya karɓa ba sai dan mummunan rashin lafiyan da yaga tana dashi, motar ya kalla wanda tace shine nashi, mota ne me matukar tsada dallele fari jikinshi a mace ya shiga, da gudu yake tuka motar har ya isa company, da sauri ya shiga ciki, da mamakinshi tun daga bakin kofa yaga sunyi decoration yana shiga yaga an tsara wajen faruk ya kalla wanda yake mishi dariyan farin ciki, cake sukazo wajenshi dashi sukace "muna tayaka murnan zama manager sannan munji daɗi da kaine ka zama manager mun tabbatar zamuji daɗi mu samu walwala a company ɗinnan"

cak ya tsaya yana kallonsu faruk yazo yaja hanunshi sauran suna biye dasu ya kaishi tsararren office ɗinshi dake kusa dana manal a saman office an rubuta ABDOOL da manyan harufa buɗe mishi sukayi faruk yace "madam ta kiramu a waya ta faɗa mana komai"

shiga yayi yana kallonsu sunki barinshi yayi magana, kujeranshi faruk ya nuna mishi yace "wannan shine kujeran manager"

zaiyi magana faruk ya zaunar dashi, wata da suke kiranta da husna tazo da cake ɗin gabanshi da karamin wuƙa ta mika mishi, yace "wai me kukeyi haka ne?"

faruk yace "mu yanka cake"

sa mishi wuƙan yayi a hanu suka yanka cake duk sukayi tafi sukayi ihu, a hankali yace "nifa ban..."

faruk yace "dan Allah kada kaki matsayin da Allah ya baka idan kayi haka baka kyauta ba, Allah ne ya zaɓe ka a cikin mutane dayawa sabida yaga kyawawan halinka ya baka matsayi dan Allah kada kaki yadda da ƙaddara kaji?"

a hankali ya sunkuyar da kai yace "to amma faruk..."

husna tace "ya abdool yadda kake bawa kowa farin ciki a wannan company muma zamu so mu ganka cikin farin ciki kodan madam da take taƙura mana ka karɓi wannan matsayin ka rike hanu biyu sannan ka mana alkawarin ba zaka mayar ba"

a hankali ya kallesu duk sunyi kalan tausayi, murmushi yayi yace "na karɓa"

ihu sukayi suna tafi, faruk yace "mr chang zai shigo yanzu"

fita sukayi su duka faruk ne ya yiwa su mr chang ido, koda suka shigo Abdool ya nuna musu waje suka zauna su uku sanye da bakaken suit.

manal tana zaune a bakin gadonta tayi wanka ɗaure da towel a jikinta, computer ta janyo ta ɗaura akan cinyarta tana kallon duk abinda yake faruwa daga lokacin da suka fara shagalin har lokacin dasu mr chang suka shigo, cikin nutsuwa yake musu bayani banda murmushi babu abinda take yi, gyara zama tayi ta jingina bayanta da jikin gadon duk da tana jin ciwon amma taji sauki da take ganinshi,

Ameesha cikin wani irin gudu ta isa gidansu man kamar zata kife kasa ta shiga ɗakin umma Imran dasu Anty suna tsaye a kan umma dake kwance flat akan gado bata motsi, cikin tashin hankali tace "umma umma ki tashi mana na kira wayan man tun ɗazu baya ɗauka"

Imran idonshi cike da hawaye ya zauna akan stool na kusa da gadon ya dafa kanshi, Anty tace "kawai tana tsaye ta yanke jiki ta faɗi? meya ɗaga mata hawan jinin?"

Imran ya girgiza kai kawai ya kasa magana, Anty kiran man ta fara da wayarta yana shiga baya ɗauka, ameesha kara kira tayi kusan kira ishirin tayi mishi wurgar da wayan tayi tace "ya zamuyi? man bai ɗauki waya ba"

Imran yace "ko zamu je mu kirashi?"

tashi tayi ta share hawaye tace "ka zauna dasu Anty ni zanje na kirashi"

da gudu ta fita, napep ta tara ta mishi kwatance tace "dan Allah kayi gudu"

gudu yake da ita banda murza yatsun hanunta ba abinda take yi, a kofan company ya sauketa ta fita da sauri tana laluben kuɗi a aljihu.

manal dake kallonsu ta juyo da camera zuwa waje domin ganin abinda yake faruwa, huci ta fara lokacin da idonta ya sauka akan Ameesha wacce take laluben kuɗin da zata biya me mashin, wayarta ta ɗaga ta kira me gadi, cikin kakkausan murya tace "zan tura maka wani hoto kada ka barta ta shiga company je watsapp yanzu"

kashe wayan tayi atake ta tura mishi hoton yace "to madam"

tana bashi kuɗin bata tsaya jiran canji ba ta juya da gudu zata shiga cikin company me gadi ya tare kofa, da sauri tace "dan Allah nazo neman Abdool ka taimaka na shiga ko ka kiramin shi"

girgiza kai yayi yace "babu me shiga ki koma inda kika tashi"

da karfi tace "ka buɗemin kofa mahaifiyarshi ce batada lafiya"

kallonta yayi yaga tana huci kamar zata kai duka, yace "okay bari na shiga na kirashi ki tsaya anan"

tace "to kace mishi ameesha ce tazo umma babu lafiya yazo mu kaita asibiti"

yace "okay"

shiga ciki yayi ya rufe kofan ya barta a waje, safa da marwa take tana murza hanunta ta kasa nutsuwa, riga da wandon jinx ne a jikinta sai rigan sanyin data ɗaura a waist nata baƙi, tayi kyau kamar ka sace ta, manyan idanunta sun cika da hawaye ɗan karamin bakinta sai rawa yake, karan hancinta yayi jajur sabida sharan hawaye da take yi akai akai, tsayawa yayi ganin kiran madam yana shigowa, da sauri yace "madam tace....."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login