Showing 3001 words to 6000 words out of 83501 words
nan ta ɗauke kai daga kallonshi, jikin Ammi ne yayi sanyi domin halin manal bata gaishe da mutum saide idan ra'ayinta ne ya so, sannan bata kula kowa koda zatayi awa shida ne a wajen mutane ba zata yiwa kowa magana ba sai idan taga dama, kuma idan ranta ya ɓaci bata yadda taci komai harma tana iya kai kwana uku bataci abinci ba, wannan abin yana tsorata Ammi sosai, dady ganin haka ya katsar mata da tunanin yace "ki maida hankali kinsan register wa ƴarmu mukazo ba tunani ba"
murmushi tayi ta maida hankali a kansu, headmaster yace "what is your name?"
a takaice tace "manal"
sai kuma ta sunkuyar da kai taci gaba da wasa da wayar dady dake hanunta, karɓan wayan yayi ganin headmaster ya fara mata wani kallo, yace "maida hankali akan abinda ake tambayarki"
kallon cikin idon headmaster tayi abin mamaki ko kyafta idon batayi tana jira ya kara yin magana tunda dady yayi magana, yace "how old are you?"
taɓe baki tayi alaman itama bata sani ba, dady a ɗan tsawace yace "open your mouth kiyi magana"
a hankali tace "ban sani ba"
yace "4years"
ammi tayi shiru tana kara kallon manal babu abinda yake bata tsoro kamar yadda taga idon yarinyar a bushe babu tsoro a ciki, yace "okay full name nata fa?"
dady yace "MANAL UMAR MAIDAWA"
kallonshi headmaster yayi cikin girmamawa yace "yallaɓai dama kaine?"
murmushi Dady yayi yace "nine"
cikin girmamawa yace "sannu yallaɓai ayi hakuri ban san kai bane da ko tambayoyi ba zanyi ba zan bata class insha Allah za'a kula da ita sosai, munji daɗi daka kawo ƴarka school namu, wannan cigaba ne muka samu"
murmushi dady yayi sannan ya ciro kuɗi me yawa ya aje akan table ɗin yace "ga wannan ayi duk abinda ya dace sannan a bata uniform yanzu ta fara zama a cikin class kamar sauran yara"
da sauri ya tashi yace "an gama sir"
fita yayi, jim kaɗan ya dawo da uniform me kyau a hanunshi riga da wando green, yace "gashi"
karɓa tayi tana kallon uniform ɗin, ɗago kai tayi tace "dady wannan uniform is too local"
dariya sosai yayi yace "manal kenan wannan uniform ɗin duk garinnan ba kowa yake samun yasa shi ba, uniform ne da kowa ya ganki yasan kina school me tsada"
murmushinta dake lotsar da gefen kumatunta tayi sannan tace "okay dady"
Ammi tace "zo nasa miki"
zuwa tayi ammi ta canja mata, kame mata gashinta take a baya tace "manal kada ki zama me ware kai a cikin ƴan class naku ki ɗauki rayuwa da sauki kamar dadynki kinji?"
tace "to Ammi"
sa mata hulan tayi sannan ta rataya mata jakan da aka bata books tace "yawwa ƴar dady gashi kinyi kyau sosai kamar na saceki mu gudu"
dariya tayi sosai tace "ammi chocolate ɗina fa"
tace "nasa miki a zip ɗin bayan jakan"
murmushi tayi, kiss ta yiwa ammi da dady a gefen kumatu sannan tace "bye"
tana tafiya headmaster yana gaba tana biye dashi, fuskanta babu alaman dariya ta haɗe rai kamar ba itace ta gama dariya dasu ammi ba, kallonta yayi ya nuna mata class yace "ga class naki daga yau idan kinzo anan zaki zau...."
kafin ya karasa ta shiga ta barshi tsaye a wajen baki buɗe yana binta da kallon mamaki, wajen zaman da taga babu kowa akai kuma nesa da sauran student na class ɗin taje ta zauna tayi shiru tana kallon black boat, kallonta yayi sai kuma ya juya ya koma office domin ya sallamesu, wata kyakkyawar yarinya ƴar karama kamar ita tazo wajenta tace "kin zauna a wajena"
ko kallon yarinyar batayi ba tana cigaba da kallon black boat, yarinyar ta kara cewa "kin zauna a wajena"
wannan karon idonta cike da hawaye tayi maganan, hankalin malamar dake teaching ya dawo kansu, zuwa tayi tace "meya faru hanan?"
nunata tayi tace "wannan ce ta zauna a wajen zamana ina mata magana bata kulani ba"
kallon manal tayi tace "ke sabuwar zuwa ce?"
kai kawai ta ɗaga alaman eh, malamar tace "ya sunanki?"
a hankali tace "manal"
daga nan ta ɗauke kai, cike da mamaki yarinya karama da wannan halin malamar tace "manal wa?"
a takaice tace "umar maidawa"
jin sunan yasa ta kara kallonta, zuwa yanzu ta ɗauke kai taki kallon inda suke, malamar fuskanta ɗauke da mamaki tace "nan wajen zaman hanan ne tashi ki koma can"
bata nuna taji me tace bama, malamar tace "tashi nace"
ko gezau batayi ba bale ta tashi, bulalan hanunta ta ɗaga tace "da alama kinada rashin kunya to bari ki gani zaki tashi ko saina watsa miki?"
kanta ta dukar kasa bata ko ɗago ba bale tasan malamar tana magana, watsa mata bulalan tayi domin ba karamin haushi ta bata ba, tayi karama da wannan taurin ran, ko sanin an zuba mata bulala batayi ba, kara watsa mata tayi ko gezau batayi harta gama dukanta ta kalli hanan tace "hanan zauna acan"
hanan ɗin ta ɗau jakanta dake cikin drower ɗin ta koma wani waje, fita malamar tayi direct ta wuce office na headmaster ta shiga da excuse, zama tayi akan chair tayi shiru tama kasa magana, yace "Anty fatima menene?"
ɗagowa tayi ta kalleshi da fuskanta cike da mamaki tace "manal umar maidawa..."
murmushi yayi yace "nasan za'ayi haka"
da sauri tace "kasan abinda ya faru ne?"
yace "naga yarinyar da alama tanada taurin zuciya, kuma batada tsoro, wanda sam ba'aso mace ta kasance da irin wannan zuciyar da farko nayi niyan ba zan karɓeta ba a wannan school ɗin sai kuma naji sunan mahaifin nata wato umar maidawa, dukkanmu mun san waye umar maidawa wajen taimako a wannan garin, wannan mutumin ba karamin hamshaƙin ɗan kasuwa bane ya kasance yana iya karya farashin abu a kaso ɗari ya zubar da saba'in ya siyar da talatin kowa ya samu sabida a samu sauƙin rayuwa, marayun da yake taimako da gidajen marayun daya buɗe ba zasu irgu ba, pompo da asibiti daya buɗewa talakawa ba zasu irgu ba, ina ganin wannan dalilin kaɗai ya isa mu ɗauki ɗiyarshi a wannan school ɗin, koda me zatayi saide muyi mata addu'a"
shiru tayi tace "amma anya zan iya handling wannan yarinyar?"
yace "kokari zakiyi fatima ki danne zuciyarki"
a hankali tace "to Allah ya bani iko".
Ammi a hanya tayi shiru tayi tagumi, kallonta dady yayi sannan ya kyasta hanu ta yadda zata dawo daga duniyar tunanin da take ciki yace "my love tunanin me kike?"
numfashi taja tace "honey kasan wani abu da yake ɗauremin kai da manal?"
girgiza kai yayi
tace "idan tanason abu ko me za'ayi saita mallaki abin, wannan halin nata yana bani tsoro kada fa ya zama matsala a rayuwar wasu...?"
da sauri ya rufe mata baki, kallonshi take da kyawawan idanunta, yayi mata murmushi me sanyi yace "nima na kula da hakan amma kada ki rinƙa ambato matsala akan ƴarmu kinsan bakin uwa yana iya bin ƴarta"
jijjiga kai tayi, a hankali ya zame hanun daga bakinta, tace "kuma bata shiga cikin mutane sannan koda laifi akayi mata saita rufe kai a ɗaki taki kula kowa taki cin abinci ka manta har kwana biyar ta taɓa yi bataci komai ba sabida na kyautar da biscuit nata? wannan abin yana damuna"
yace "ba komai dama wani yaron haka yake idan ya girma saiya daina"
a hankali tace "to Allah yasa, amma kasan inason manal sosai na fika santa"
yace "no no no baki fini son manal ba, jinta nake kamar ƴar cikina"
musu suka fara har suka isa gida,
manal na zaune a inda take kowa a class ɗin sai kallonta suke saboda tsananin kyawunta, bata damu ba duk wanda ya kalleta itama kallon cikin idonshi take.
Bayan an tashi a school Ammi ce tazo ɗaukanta dan dady ya tafi aiki, zama tayi a motan ta aje jakanta akan cinyarta, Ammi wacce tayi kyau cikin hijabi tace "ya school ɗin dai my dear?"
a hankali tace "fine"
daga haka bata kara magana ba sai ruwan ammi data ɗauka na cikin gora ta buɗe tana sha a hankali, aje goran tayi tana lumshe ido, a check point suka tsaya suna jiran a basu hanya, Ammi ta kalli gefe wani mutum maƙaho yana rike da wuyan ɗanshi suna tafiya a yunwace suna bata taga kafarshi babu takalmi, kallon manal tayi tace "Allah sarki kiga wannan manal ko takalmi babu a kafarshi ga zafin rana"
kallonshi tayi sai kuma ta ɗauke kai tana kallon titin dake cike da manyan motoci, shiru ammi tayi, sai kuma ta buɗe jakanta ta ciro kuɗi dayawa tace "manal gashi kai musu kafin a bamu hanya"
karɓa tayi ta fita a motan, tafiya ta fara zuwa wajensu, kallon ammi tayi time ɗin data iso dab dasu, gani tayi hankalin ammi ya koma wani wajen, watsar da kuɗin tayi a gefen titi yaron yana kallonta sannan ta juya ta koma cikin motan ta rufe, ido ta zubawa yaron har mutane sun kwashe kuɗin bai samu ko naira a ciki ba, murmushi tayi ganin yana hararanta, Ammi taja motar tace "yawwa manal ɗin dady kinga kullum idan kina tafiya kikaga mabuƙata haka ki rinƙa tsayawa kina basu sadaka idan da kudi a hanunki, koda shine iyaka abinda ya rage a hanunki ki rinƙa bawa masu buƙata kinji?"
gyaɗa kai kawai tayi tana cigaba da kallon kyawawan gine ginen dake gefen titin, da haka har suka isa gida, a compound Ammi tayi parking fitowa tayi ta rataya jakanta a baya tana tafiya a hankali, da haka har ta shiga falonsu ne kyau da girma, kwanciya tayi akan sofa ta dau remote ta kunna tv, cartoon tasa tana kallo, Ammi tazo ta zauna a gefenta ta ɗan ɗaga murya tace "Atika!!! Atika!!!"
da sauri me aiki tazo sanye da uniform irin na masu aikin gidan tace "gani hajiya"
tace "bani youghurt a frij"
ɗauko mata youghurt ɗin tayi da cup guda ɗaya, Atika ta kalli manal tace "kema a kawo miki?"
bata kalleta ba bata amsa ba, kusan sau uku tana tambaya, ammi tace "magana ake miki manal"
sai yanzu ta juyo tace "no"
cigaba tayi da kallo, Ammi tayi murmushi kawai tace "Allah ya shiryamin ke"
Kullum tana zuwa school sai ranan weekend take samun hutu, har zuwa yanzu babu wanda take magana dashi a class kullum ita kaɗai take zama, yauma kamar kullum tana zaune ta harɗe hanu a kirji tana kallon yaran dake safa da marwa sabida break time ne, fuskanta kamar kullum babu fara'a, hanan wacce take zaune itama hanunta rike da wani teddy me kyau pink tana wasa dashi, murmushin gefen baki manal tayi sannan ta tashi taje inda manal take, zama tayi akan desk tace "ki siyarmin teddy ɗinki inaso"
make kafaɗa tayi tace "dadyna ne ya siyamin ba zan siyar ba nima ina so"
manal tace "to ai idan inason abu bana haɗawa da wani ni kaɗai nakeso na mallaka ki siyarmin"
yarinyar tace "A,a nikam bazan siyar ba"
fizgewa tayi ta rike a hanunta tace "to tunda ba zaki siyar ba na kwace ya zama nawa domin banason abu na rasa shi koma menene"
kuka yarinyar ta fara tana cewa "ki bani teddy ɗina, nikam ki bani abu na"
yaron dake gefensu me suna sadik yace "ki bata abinta kullum tana zuwa dashi tanason teddyn nan sosai ki bata abinta"
murmushi tayi wanda basu taɓa ganin tanayi ba tace "to ai nafison abinda mutum yafi so ya zama nawa, kuma inada kuɗin da zan iya bata harma ta siyi kantin teddyn ɗin idan tanaso"
sadik ya tashi ya fara kwace teddy a hanunta damke hanunshi tayi da iya karfin da Allah ya bata ta zuba mishi manyan sexy eye's nata masu ɗauke da zara zaran eyelashes, kara yayi yace "ki sakemin hannu"
bata sakeshi ba kuma bata daina kallonshi yana kuka ba, duk da yadda hanan take bugunta tana nema ta kwace hanunshi ta kasa, kukan azaba yake domin har hanunshi ya koma jajur, hanan jakanta ta ɗauka tana bugunta dashi amma ko gezau manal batayi ba, sauran yaran class sunfi sabawa da sadik hakan yasa sukazo suna kwatan hanunshi daga na manal, sun kasa sai kallonshi take tana murmushin gefen baki, da gudu hanan ta fita tana kuka taje ta kira headmaster, tareda Anty fatima sukazo suma a guje, har lokacin tana rike da hanunshi zuwa yanzu ya fara kuka yana rokonta ta sakeshi, anty ce ta daka mata tsawa "manal sakeshi"
ko gezau batayi ba, kallon headmaster tayi tace "kana gani?"
matsowa yayi shima ranshi a ɓace ganin yadda yaron yake kukan azaba yace "sakeshi"
kin sakinshi tayi kuma ɗayan hanunta rike da teddy, mari ya ɗauketa dashi, bata damu ba amma taji zafi sosai, kara marinta yayi sannan suka haɗu da anty fatima suka kwace hanun yaron, hanunshi ya koma jajur itama gefen fuskanta yayi jajur, jan hanunta Anty fatima tayi suka fito waje a tsakiyan makarantar ta durkusar da ita, bulala ta ɗauko ta fara dukanta dashi, headmaster ya karɓi bulalan da kanshi shima yayi mata bulala goma, har suka gama bata motsa ba, waya ya ciro ya kira layin dadynta rai a ɓace yace "idan zaku samu time kuzo kaida mahaifiyar manal"
yana faɗan haka ya kashe wayan ba tareda ya amsa tambayoyin da dady yake mishi ba, janta sukayi zuwa office da hanan da kuma sadik duk suka zauna a kasa su kuma kan kujera, ta sunkuyar da kai taki yadda ta kalli kowa sannan taki sakin teddy, Dady dake cin abinci ya kalli Ammi wacce take kallonshi tace "lafiya?"
yace "sa hijabi muje school nasu manal akwai matsala"
tashi tayi har tana tuntuɓe, da gudu ta fito da hijabin a hanu tace "idan wani abu ne ya samu manal ɗina ya zanyi? na saba da ita na shaƙu da ita bazan iya rabuwa da ita ba, na shiga uku"
karɓan hijabin yayi ganin yadda ta birkice ya rungumeta domin ta nutsu yace "relax babu abinda zai sameta"
rufe ido tayi tana sauke ajiyan zuciya, janyeta yayi daga jikinshi yasa mata hijabin yace "let's go"
tun a compound ya fara hon gateman da yake ɗingishi sakamakon ciwon ƙafan ya tashi ya buɗe, fita sukayi da gudu yake driving har suka isa school ɗin Ammi na addu'a a fili "ya Allah kada ka jarabceni da abinda ba zan iya ba, ya Allah ina tsoron wani abu ya samu ɗiyata itace ka bani kyauta..."
hanunta ya rike suka shiga ciki, hamdala sukayi ganin tana durkushe a kasa kanta kasa bata ɗago ba, dady yace "meya faru?"
headmaster yace "bismilla ku zauna"
zama sukayi duk suna kallonshi suna jiran bayani, yace "banyi niyan kiranku ba amma abin ya zama min dole ne"
kallon sadik yayi yace "nuna hanuka"
nuna musu hanun yayi ammi ta runtse ido ganin har fatan hanun ya fara ɗayewa, dady yace "meya sameshi?"
nuna manal yayi yace "itace tayi mishi hakan, a gaskiya ƴarku tanada tsautsaran ra'ayi wanda idan ba'ayi hankali ba a gaba za'a iya samun gagarumin matsala...."
Ammi da sauri tace "ka iya bakinka kasan me zaka faɗa kada ka yiwa ƴata baki"
dady yace "kayi hakuri sannan a haɗani da iyayen yaron zan basu hakuri dan Allah kada ku koreta a school nayi alkawarin zanja mata kunne sosai sannan ba zata kara ba"
headmaster yace "ba komai dama na kira ne domin kusan me ake ciki amma munyi mata hukunci, munaso ta basu hakuri sannan ta mayarwa yarinyar abinta"
ya kalli manal yace "ki basu hakuri"
shiru tayi bata amsa ba kanta har yanzu a kasa, cikin tsawa yace "ki basu hakuri nace"
ko sanin ana mata magana batayi ba, dady ya lura da murza yatsun hanunta da take yi, cikin tsawa yace "wai manal ba magana ake miki ba?"
a hankali ta buɗe baki tace "kuyi hakuri"
Dady shima ranshi a ɓace yace "ɗago kai ki basu hakuri"
sai yanzu ta ɗago kanta, idanunta sun koma jajur fuskanta yayi zufa sosai cikin tsananin ɓacin rai tace "kuyi hakuri"
Ammi kallonta take bata taɓa ganinta haka cikin ɓacin rai ba, dady yace "dan Allah ayi hakuri shima yaron zan karɓi numbern babanshi na bashi hakuri"
headmaster yace "ba komai ya wuce, amma ta bata teddy ɗinta"
dady yace "oya bata teddy ɗin"
mikawa hanan tayi tana aika mata wani irin kallo me tsananin rikitarwa, headmaster yace "dama an tashi zaku iya tafi tunda kowa ya fara fitowa sabida kona takaddu marasa amfani ne ma da mukeyi yasa bamu tashi da wuri ba yau"
dady yace "to mun gode"
fita sukayi su duka hanan tana rike da teddy ɗinta tana murna an bata abinta, manal tana rike da hanun Ammi har zuwa wajen wutan dake ci ana kona takaddun, a hankali ta zame hanunta ba tareda ta bari sun ganta ba, kallon teddy ɗin hanun hanan tayi sannan ta fizge da sauri ta jefa a cikin wutan, ihu hanan tayi kafin su ankara teddy har yayi rabi yana ci da wuta, duk suka waro ido harda dady da Ammi ganin abinda ta aikata, har teddy ɗin ya gama konewa tana kallo, sai yanzu murmushi ya suɓuta akan fuskanta, kallon dady ammi tayi shima ya kalleta, duk sun kasa magana, hanan tana kuka tace "ta konamin teddy ɗina"
sai yanzu tace "ai dama na faɗa miki duk abinda nakeso bana haɗashi da wani, sannan da in rasa gwara mu duka mu rasa"
jikin Ammi har rawa yake ta buɗe baki tanaso tayi magana, maganan yaki fitowa, dady da kyar ya harhaɗa magana yace "manal me kika yi?"
a hankali tace "dady am sorry"
hanu yasa ya kira hanan yana shafa kanta ya ciro kuɗi dayawa a aljihu ya bawa headmaster yace "dan girman Allah kuyi hakuri, a siya mata irinshi sak"
karɓa yayi yace "insha Allah za'a siya mata karka damu"
hanunta manal ya rike da karfi yana janta har zuwa cikin mota, ammi cike da mamaki ta shiga motan, bulala ya ɗauko ya fara zaneta, abin mamaki banda hakuri babu abinda take bashi babu hawaye kuma, sabida ɓacin ran da taga yana ciki yasa take bashi hakuri, kara dukanta yake