Showing 36001 words to 39000 words out of 83501 words
ammi tayi, ta kamo hanunta tana dariya haɗe da hawaye tace "zan iya siyan soyayya koda a hannun waye ne ko ammi?"
jijjiga kai ammi tayi cikin son kwantar mata da hankali, tace "karna damu ko? na kwantar da hankalina ko?"
ammi tace "eh"
kwantar da kanta tayi a hankali ta fara bacci, busashen hawaye akan fuskanta.
*Jiddah Ce....✍️*
08144818849
[09/04 à 08:06] JIDDA MAPI: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*DUHU DA HASKE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 10*
~Ranan lahadi babu aiki duk suna gida man yayi shiru yana jin ameesha tana karanta mishi labarin Amina da pampered girl book2, ya gaji amma ta hanashi tashi wayarshi tayi kara alaman saƙo ya shigo yana dubawa yaga alart, rungume ameesha yayi tace "what?"
ya saketa ya nuna mata, cikin jin daɗi tace "yeeee"
ya faɗawa umma dasu Anty shida Ameesha sukaje suka cire farko kayan abinci duka siya sannan ya biyawa Imran da fahad kuɗin school fees nasu ya siyawa umma da Anty kaya, yace "muje saura naki"
girgiza kai tayi tace "nikam kada ka damu next time saika siyamin kaga abubuwa dayawa a kanka zan karɓi 15k ɗina ranan monday zan siya komai dashi ka aje sauran a account sabida akwai abu dayawa kuma rashin lafiya baya sallama"
yace "no saina siya miki abu kinsan 200k dayawa yake"
duk yadda tayi dashi yaki saida ya siya musu kaya yasan tafi son riga da wando hakan yasa ya siya mata da ɗan yawa shima ya siya kafin suka koma gida, Imran da fahad sunyi farin ciki sosai, umma saida tayi hawaye Anty ta rinƙa da mishi albarka, washe gari monday suka tafi aiki, ya zage sosai yana aiki da zuciya ɗaya domin yasa shine babba a family kamar yadda ameesha take faɗa mishi, yauma tayi kyau sosai cikin abaya tasa glass baƙi ta shigo, tashi sukayi da mamaki sukaga tayi musu alaman su zauna, duk suka zauna gani sukayi tana murmushi kowa ya kalli juna harta wuce, aiki ta fara data shiga ciki tana kallon duk abinda yake faruwa a company ɗin ta cikin computer basu san tana kallonsu ba, abinda ke sata murmushi shine cigaban da take samu a kullum, a yau tafi samun cigaba domin kuwa ta haɗa hannu da manyan masu zane na duniya yanzu ta zama na hanun damansu a yau suka sanar mata hakan kafin ta shigo company, har aka tashi bata hantari kowa kamar yadda ta saba ba, Ameesha tayi kyau cikin kayan pakistan daya siya mata tana goye da jakan baya tana ganinshi tayi murmushi, manal ce ta fito tana kallon agogo da alama sauri take ta tafi, motarta ta shiga da sauri ta tada zata tafi taji motan ya tsaya, kunnawa tayi taji yaki kunnuwa, kallon agogon ta kuma yi, ɗago kai tayi taga Abdool yana shirin buɗe motarshi, fitowa tayi da sauri tace "please kaini gida ina sauri motata ta ɓaci"
yace "okay muje"
jerawa sukayi suna tafiya ameesha tana ganinsu taji zuciyanta ya tsinke, gaban motan ta buɗe ta shiga ta zauna, kallon ameesha yayi wacce take tsaye a gefe, da hanu yayi mata alaman tazo, zuwa tayi ya buɗe mata gidan baya ta shiga ta zauna, a mazaunin driver ya zauna ya tada motan suka tafi, shiru motan yayi manal ta ɗago dara daran idanunta tana kallon ameesha ta madubi, ameesha kuma tayi shiru a baya tana murza hanunta a duk lokacin da take cikin tsoro haka take yi, a hankali ta ɗago dan ta kalli man ganin manal na kallonta ta cikin madubi tayi saurin janye idonta a tsorace, man ya juyo yace "my meesha kinyi shiru me yake damunki?"
girgiza kai tayi a hankali tace "ba komai"
yace "kinason chocolate?"
shiru tayi tana gyaɗa kai kamar kurma, cirowa yayi a aljihu ya mika mata, karɓa tayi tace "thank you"
ɓata rai yayi cike da sakalci da shagwaɓa ya kwaɓe kyakkyawan fuskanshi yace "ni dai banson naga kinyi shiru bana jin daɗi sai naga kamar baki akwai abinda ke damunki"
murmushi tayi tace "ba komai fa"
tana rike da chocolate ɗin yace "to kimin murmushi na gani"
a hankali tayi murmushi, yace "sosai nake so ba kaɗan ba"
murmushi ta kuma yi yace "ni dai ba haka ba"
ganin yadda yayi da fuskarshi ta fara dariya tana sa yatsu a baki tana rufewa, wani smiling yayi yace "ko kefa"
manal tana jinsu kuma tana ganinsu, wayanta kawai ta amsa tace "ina hanya"
da mamaki taga man ya kaita har kofa, buɗe marfin tayi zata fita yace "bakice ya akayi nasan gidanku ba"
a takaice tace "banda wannan lokacin"
zata fita yace "a jikin file naki naga address"
rufe marfin tayi ta fara tafiya, ɗaga murya yayi yace "ba godiya?"
ko kallonshi batayi ba tayi knocking aka buɗe mata kofa ta shiga, ya kalli ameesha ya nuna mata gaba yace "boss ta tashi dawo wajen zaman ki"
dawowa tayi ta zauna yace "wai menene duk kin taƙura?"
tace "ba komai"
manal tana shiga gida ta samu ammi dake zaune tace "kin tsinkamin rai wai meke faruwa kikace na dawo yanzu?"
ammi cikin murmushi tasa hanu a haɓanta tace "ƴata nasan zaki so duk abinda zanso, ba komai yasa na kiraki ba sai dan ɗan gidan ƙawata miniter tace zatazo su ganki kiga ɗanta domin tanaso a haɗaku aure"
shiru tayi ganin ammi tayi kalan tausayi tace "okay"
cikin jin dadi tace "Allah miki albarka"
a hankali tace "ameen"
badan taso ba ta shiga ciki ta canja kaya tana cikin shafa lipstick amminta shigo tace "sunzo ki sauko ku gaisa"
"okay"
fita ammi tayi ta samesu zaune akan sofa suna shan ruwan sanyin daya kawo musu, kyakkyawan saurayi ne da mamanshi itama kyakkyawa sanye da tsadadden leshi da siririn glass a ido, hira suka fara manal cikin rashin fara'anta take saukowa tana kallonsu, akan sofa ta zauna bayan tayi musu sannu da zuwa, kallonshi tayi shima ya kalleta ta gaida mamanshi sannan ta ɗauke kai tana latsa waya, ammi taja mamanshi ciki domin su basu waje, koda suka tafi ya dawo kusa da ita ya zauna, shiru sukayi tana latsa waya yace "sannu"
a takaice tace "sannu"
shiru yayi suna zaune haka har ammi ta rako mamanshi zasu tafi, har mota ta kaisu, manal ta tashi ta koma ɗakinta ta cire kayan tasa na shan iska ta fito ta wuce garden domin shan iska, sai yamma likis ta dawo tana cin apple taga ammi tayi tagumi, tazo ta zauna a gefenta ta gutsiri apple tace "ammi kina lafiya?"
girgiza kai tayi tace "gaskiya manal ba lafiya ba, wannan yaron yace baki mishi ba, yace baya sonki"
dunƙule hanu tayi cikin ɓacin rai tace "to miye abin damuwa?"
Ammi tace "abin ya fara damuna manal"
tashi tayi ta bar wajen, bata kara kula ammi ba har dare tayi shirin bacci ta kashe wuta ta kwanta, a hankali ta rufe ido ta fara bacci, kamar a mafarki taji an kira sunanta "MANAL"
cigaba tayi da bacci ta kuma jin ana kiran sunanta "manal"
a mugun firgice ta buɗe ido jin muryan dady, ji tayi ana kara kiranta, makunnin wuta ta fara nema da sauri kasa kunna wutan tsaban rawan da jikinta yake, rufe ido tayi jin kunnuwanta suna jin sunanta da ake kara kira, ihu tayi da karfi tace "Ammiiiiiiiii"
a cikin duhun ta sauko daga gadon ta fara laluben kofa, ji tayi kamar an sake cewa "manal"
wani ihun ta kuma yi tace "ammiiiii"
smmi dake bacci akan gadonta taji ihun manal da sauri ta buɗe ido ta kunna wuta ta fita, ɗakinta taje tana knocking, tsaye take a tsakar ɗakin tana laluben kofa tana kiran sunan ammi, da kyar ammi tace "manal gani nan ki buɗe kofa"
laluba bangon da taci karo dashi ta fara da kyar ta samu kofa, jikinta yana rawa ta buɗe, tana ganin ammi ta faɗa jikinta ta kankameta kamar zata maidata jikinta tace "ammi dady, dady ne yanata kiran sunana ammi ki tafi dani daga nan"
kunna wutan ammi tayi tace "manal babu kowa mafarki kikayi"
girgiza kai tayi kamar sabon kamu a hauka jikinta yana rawa tace "wallahi shine dady ne yanata kiran sunana ki tafi dani ɗakinki"
taki sakinta ko rufe kofan tayi da haka har sukaje ɗakin ammin akan gadon ta kwanta bata yadda ta saketa ba, kankameta tayi ta yadda zata iya barinta ba koda sunyi bacci, addu'a ta fara tofa mata tana share mata zufan daya tsatsafo a goshinta, da kyar ta samu tayi bacci, addu'a anmi ta fara tana kuka tareda rokon Allah ya takaita mata.
washe gari ta tashi a hankali tayi alwala tayi salla kafin ta shirya ta yiwa ammi sallama kamar ba abinda ya faru da ita jiya, ammi ma ganin ta manta sai bata tuna mata ba ta bita da addu'a Allah ya kare, koda ta shiga office nata dafa kanta tayi tana tuna abinda ya faru jiya kamar mafarki kamar kuma a fili batayi bacci sosai ba hakan yasa take jin bacci sosai sabida ayyukan dake gabanta ne yasa bata zauna a gida ba, aiki take yi sosai tana tsaka da aikin hanunta rike da fenti bacci ya ɗauketa ta kwantar da kanta akan zanen da takeyi na kan table dake gabanta tana bacci cikin nutsuwa, tayi nisa sosai cikin baccin man yana zaune ya ɗago ya kalli ƴan uwanshi ma'aikatan yaga duk sunata hamma da alama yunwa sukeji kuma babu tashi sai sun gama, tashi yayi yayi knocking a office nata domin ya nemi excuse ya siya musu abu, jin tayi shiru ya buɗe ya shiga, gani yayi tana bacci akan table a fili yace "thank god"
cikin sanɗa yaje wajen frij nata ya buɗe, waro ido yayi ganin cike yake fam da drinks kala kala, ɗauka ya fara ya buɗe riganshi yana zubawa a ciki, saida ya ɗibi dayawa har yana gagara tafiya kafin ya fita cikin sanɗa ya rufe kofan, suna ganinshi suka waro ido ya mika musu duk sukace ba zasu sha ba suna tsoro, yace "madam ce ta bani na raba muku akwai saura ma a ciki"
zuwa yayi ya karo wasu dayawa saida ya raba musu biyar biyar ya tabbatar babu a frij sosai kafin ya ɗibi guda goma ya zuba a jaka domin kaiwa Ameesha, rufe kofan zaiyi cikin sanɗa yaji tace "dady"
shiru yayi bai rufe ba, faɗiwa tayi daga kan kujeran jikinta yana rawa ta fara cewa "dady please, please dady"
rawa jikinta yake sosai atake tayi zufa, da sauri ya shigo yana kiranta "madam? madam?"
tana girgiza kai tana hawaye tace "dady"
da karfi yace "madam?"
buɗe ido tayi a firgice duk ta sauya harta faɗa, ganinshi kusa da ita kawai ta faɗa jikinshi ta rikeshi kam tace "kaini wajen ammi"
shiru yayi yana jinta kamar zata shiga jikinshi ga rawan da jikinta yake, cikin rawan murya tace "dan Allah"
ji yayi ta bashi tausayi a hankali ya tashi da ita a jikinshi ya fara tafiya da ita, gani yayi idonta a rufe, fita yayi da ita kowa na kallonshi, motanshi ya shigar da ita sannan ya shiga shima tana rike dashi har ya fita a wajen, gani yayi ta haɗa kai da gwiwa wayanta yana hanunshi da jakanta dake kan table duk ya ɗauko mata, har kofan gidansu ya tsaya cikin rawan murya tace "shiga dani ciki dan Allah"
idan tace dan Allah ɗinnan sai yaji ta bashi tausayi a hankali yayi hon, gateman cikin ɗingishi da sanda a hanunshi ya buɗe gate shiga ciki yayi ya buɗe marfin ya fito, yazo ya buɗe mata, da mamakinshi yaga ta damke hanunshi tace "wajen ammi zaka kaini"
gani yayi har yanzu jikinta be daina rawa ba, ya rasa ta ina zaibi da ita, cikin gidan da girma yake, a hankali dai ya fara tafiya duk inda yasa kafa itama acan take sawa da haka har yaga wani kofa me kama da falo, knocking yayi yaji ance "ina zuwa"
jim kaɗan aka buɗe, kyakkyawar mata ya gani da alama itace ammin, tana ganinsu ta zuba mishi ido a hankali ta kalli manal tace "manal?"
sakinshi tayi jikinta ya kara fara sabon rawa tace "ammiii ki kaini ɗaki ammi dady"
a kiɗime ammi tace "manal wai menene haka dan Allah ki nutsu kada zuciyata ta buga kece kaɗai kika ragemin na rasa kowa nawa ba zanso komai ya sameki ba ki nutsu dan Allah"
riketa tayi man ya juya zai tafi yaji ta rike hanunshi, tsayawa yayi yana kallonta, tana rungume da ammi tana rike da hanunshi, ammi ta kalleshi cikin hawaye tace "ka taimakamin ina tsoro, banason wani abu ya samu manal kaga mu biyu kawai muka rage, itace take kula dani itace take kula da komai idan wani abu ya sameta ba zanji daɗi ba"
cikin kuka tace "na tabbata depression ne yake damun manal, batada kawaye batada masoyi a kullum sai tace ammi ni babu wanda suke sona ni kaɗai nake rayuwa tun ina yarinya, ammi babu wanda nake iya faɗawa damuwata ni kaɗai nake handling ɗin kaina, ni kaɗai nake bawa kaina shawara kuma na bawa kaina labari, ni kaɗai nake kuma ni kaɗai nake dariya, na tabbata wannan abin yake damunta har ta kamu da depression dan Allah ka taimakamin banason na rasa ta kaga dadynta ya tafi ya barni"
kukan da take yi kaɗai ya isa ya faɗa maka halin da take ciki, itama manal kanta akan kafaɗan ammi tana hawaye tana cewa "dadyyy ammi shine yake kirana"
ji yayi hawaye ya cika mishi ido, a hankali ya rike hanunta yace "manal?"
cikin hawaye tace "na'am"
cikin sanyin murya yace "muje ciki ba dady bane ga amminki kusa dake kinji?"
girgiza kai tayi tace "shine yake kirana tun jiya"
ammi kuka kawai take yi, rike hanunta yayi ya janyeta daga jikin ammin, ji yayi jijinta yayi zafi ga wani zufa da take yi sosai ga kuma rawan jiki, da taimakon ammi ya kaita ɗakin ammin ya nuna mata gado yace "kwanta ki huta"
kwanciya tayi ya juya zai tafi yaji ta rike hanunshi, a hankali ya juyo yaga tana kallonshi da manyan idanunta tana girgiza mishi kanta, ammi tace "tana nufin kada ka tafi"
jikinshi a mace ya zauna a kasa yana ganin hanunta dake cikin nashi tana lumshe ido tana buɗewa, ammi fita tayi ta kira dr har gida yazo ya fara dubata, saida ya gama ya kalleta tana bacci ammi tace "me yake damunta dr habib?"
shiru yayi kamar ba zai faɗa ba sai kuma yace "a gaskiya tana ɗauke da cutan damuwa akwai abinda yake damunta a zuciya, sannan wannan yarinyar tanada buƙatan farin ciki a rayuwarta kamar bata samun farin ciki kamar sauran mutane hakan yasa take dab da kamuwa da cutan damuwa wanda rashin shiga cikin mutane da kuma rashin sharing damuwanka da wani ko wata, da kuma rashin yin dariya koda sau ɗaya ne a wata wannan yasa tana gab da kamuwa da cutan da zai iya taɓa mata zuciya idan ya kai last stage nashi ma gaskiya zuciyarta zai iya bugawa ba fata ake ba za'a iya rasata, kiyi hakuri banso faɗa miki ba amma ɓoyewa zai iya zama matsala babba fiye da faɗan"
dafa kirji ammi tayi hawaye masu zafi suna zuba mata, kanta ta ɗaura akan cikin manal wacce take bacci a hankali.
cikin kuka marar sauti tace "manal me kikeso kiyi da rayuwarki? manal ki daure mana ki zama kamar kowa ki rinƙa walwala ni ai ina sonki koda kowa na duniya baya sonki, sannan dadynki ya riga ya mutu ya tafi ya barmu kada ki bari na rasa ki"
dr yace "ki daina kuka, ni na tafi"
ya kalli man dake zaune yana ganin duk abinda yake faruwa yace "ka lallasheta sannan idan ta farka so samu ta samu a fara bata labarin da zai sata farin ciki harma tayi dariya saɓanin haka zai karawa ciwonta zafi"
ammi tace "na gode"
tashi tayi ta bashi kuɗinshi tazo ta zauna akan sofan ɗakin ta ɗaura kanta a hanun sofan ta fara hawaye, shiru man yayi yana kallon fuskan manal ya kasa cewa komai, yana zaune a wajen har lokacin tashi a wajen aiki ya wuce.
cikin sauri ameesha take tsallaka kwalta, hamdala tayi bayan ta tsallaka lafiya sannan ta fara tafiya tana sauri kamar kullum, yauma rigan ne da wando a jikinta, wandon baki da zanen fari layi biyu a gefe gefen, sai riga babba kamar na sanyi da karamin hijabi, bayanta goye da jakan laptop nata hanunta kuma wayarta tana kara kiran numbern man tun ɗazu baya ɗauka, har ta isa wajen aikinsu ta zauna tana jiranshi har aka tashi taga kowa ya fito banda shi, ganin an watse ta tashi da sauri ta samu wanda yake fita karshe yana rufe kofa tace "sannu dan Allah Abdool fa?"
yace "ai Abdool sun tafi tun ɗazu"
da sauri tace "da wa?"
yace "da madam sun jima da tafiya kuma basu dawo ba"
shiru tayi sai kuma tace "na gode"
zama tayi a inda take zama tana kara kiranshi yana shiga baya ɗauka, jikinta a mace ta tashi gashi batada kuɗi a hanunta da kafa ta fara tafiya, ta gaji sosai harta isa school nasu Imran, ta iso sun tashi har sun gaji da jiransu, suna ganinta suka saki fuska itama daurewa tayi ta musu murmushi, Imran ne ya fara zuwa yace "ina ya Abdool? meyasa kikazo da kafa?"
tace "naje ance sun tafi amma nake wani aikin ne ya rikeshi mu tafi gida may be ya koma gida ko ya gaji"
Imran yace "koda ya gaji ai saiya kiraki ya gaya miki"
tace "eh may be ko yana busy bai samu daman kiran ba kasan fa aiki"
yace "okay yanzu da kafa zaku tafi?"
jijjiga kai tayi tace "yes"
hanunsu ta rike ta tsaya a tsakiyansu suna tafiya suna hira rana sosai yake haskasu ga zafi, ameesha gashi ta gaji sosai da haka har suka isa gida, gidansu Abdool sukaje umma tana ganinsu tace "ina Abdool?"
kamar yadda