Showing 24001 words to 27000 words out of 83501 words

Chapter 9 - DUHU DA HASKE Hausa Novels by Jiddah S Mapi.docx

19 Sep 2025

2233

waya akan dadynki sunce sunason yin meeting da matarshi ko kuma ƴarshi domin akwai kuɗin daya zuba hanun jari suna so su mayar kishi"

tace "okay aina za'ayi meeting?"

tace "zan tura miki address"

tace "okay ammi"

tana kashe wayan ta turo mata address, kallo tayi sannan taje wajen mota ta shiga, ammi ta kirata tace "sunce suna jiranki na basu number ɗinki da kinje kin kirasu zasu ganeki"

tace "okay"

fita tayi tana driving a hankali tana duba address ɗin, tayi tafiya da ɗan nisa kafin ta isa wajen, kamar company ne domin yanada girma sosai gashi da kyau kamar a turai, fita tayi ta rufe mota tana taunan cingum tana tafiya harta isa ciki, me gadi zaiyi magana ta nuna mishi ID card nata na m.u.m yana gani ya bata hanya, shiga tayi har zuwa wajen data tabbatar anan ne ake taro domin taga alaman takalman mutane na mata a bakin kofa, bata cire takalminta ba tayi knocking suka amsa mata da "yes"

shiga tayi duk suka kalleta suna zaune akan kujera sunsa manyan kaya da ganinsu masu kuɗi ne kuma masu muƙami, akan kujera itama ta zauna sannan ta cire glass na idonta ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya ta zuba hannayenta akan table na gabanta tace "gani"

duk suka kalli juna kafin ɗaya daga cikinsu da alama shine babba yace "kece manal?"

tace "umar maidawa nice"

ya jijjiga kai yace "okay"

takaddu ya tura gabanta yace "wannan takaddun Alhaji umar yayi sign kafin ya mutu, makudan kuɗaɗe ya zuba hannun jari saide ya mutu kafin ayi harkallan, ina fatan zaki bamu goyon baya kiyi sign sabida kada a dakatar da abinda ya fara"

murmushi tayi sannan tace "nawa ya zuba a ciki?"

mutumin yace "biliyan 20"

murmushi tayi tace "ba zanyi sign ba saida sharaɗi guda biyu"

kallon juna sukayi sannan suka ce "menene sharaɗin"

tace "sharaɗin farko shine ku tabbatar koda ciwon kai ba zai samu naira biyar a cikin kuɗinnan ba, idan abu ya samu kuɗinnan manal umar maidawa ba zata bar kowa a cikinku ya zauna lafiya ba"

shiru sukayi, tasa glass nata ta tashi daga zaunen tace "sharaɗi na biyu shine ba zanyi sign ba har sai kowa ya nuna min abinda ya mallaka wanda ya kai naira biliyan ɗaya ta yadda koda abu ya samu kuɗin inada right ɗin da zan nuna abin a matsayin jingina"

duk suka kalleta, murmushi tayi musu ta juya zata tafi, sukace "dakata"

tsayawa tayi tana murmushi tace "kun amince?"

duk sukace "eh"

zuwa tayi duk suka nuna mata kadaran da suke dashi a waya da address ɗinsu da kuma numbern wayarsu dana ƴaƴansu manya, murmushi tayi ta janyo takaddun tayi sign sannan ta mika musu, tafiya tayi, har ta fita sai kuma ta dawo, wayarta ta buɗe ta fara nuna musu video daga lokacin data shigo har lokacin da zata fita duk abinda sukayi tayi video basu sani ba, murmushin gefen baki tayi kana tace "bani kaɗai keda wannan video ba a yanzu harna turawa mutane biyu wanda nasan koda wani abu ya sameni zasu baza video a lungu da sako har sai an gano menene dalilin faruwan na barku lafiya"

fita tayi ta shiga motarta cikin kwarewa a tuƙi ta har wajen, shiru sukayi babu wanda ya kara magana, ɗaya daga cikinsu yace "Alhaji lawal wannan yarinyar ta fimu taurin kai"

wanda aka kira da Alhaji lawal ya share zufa yace "Innalillahi ashe duk taurin kanka akwai wanda ya fita kuma duk wayonka akwai wanda ya fika, wallahi na gama sawa a raina tana gama yin sign zamu sa a gama da ita mu raba kuɗin a tsakaninmu"

ɗayan yace "kut akwai aiki wato sunanta mukeji yau mukaga asalin wacece manal, ni dama cewa nayi idan mun raba kuɗin saina lallaɓa na aure kyakkyawar matar Alhaji umar daya bari ashe da sauran aiki"

ɗayan da yayi shiru sukace "Alhaji sani kayi shiru fa bakace komai ba"

yace "ta gogemin hadda ne, saifa mun san takun mu domin babu tsoro a idonta kuma babu shaƙƙa"

duk sukace "tabbas hakane akwai dakakken zuciya a wajen".

Ameesha parking na mashin nata tayi bata cire hulan tukin daga kanta ba ta fara tafiya a hankali zuwa cikin gidansu man, hanunta rike da wayarta ta buɗe kofan a hankali ta shiga, ɗaga hulan tayi, kyakkyawan fuskanta ya bayyana amma babu walwala kamar yadda ta saba, da alama yau akwai abinda yake damunta, kamar kullum riga ne da wando a jikinta wandon a buɗe sosai rigan kuma ya kamata kaɗan pink wandon fari, cikin sanyin murya tace "umma ina wuni"

umma da mamaki tace "lafiya ameesha"

wucewa tayi ɗakin man tayi sallama a hankali ta shiga, yana zaune a kasa yana zane, ɗauke kai tayi cikin jin haushin zanen da yake yi kullum gashi zanen bai taimaka musu da komai ba, kallonta yayi har ta karaso ta zauna a bakin gado kafafunta kusa dashi tayi shiru tayi tagumi, yana cigaba da zanen hotonta da nashi yace "meya samu princess ɗina yau?"

tsaki taja kaɗan sannan ta ɗauke hoton daga gabanshi ta nuna hoton tace "mutane suna samun cigaba a kullum cikin rayuwarsu, mu saide abu ya koma baya bama samun cigaba, kullum ina cemaka muje mu nemi aiki koda kai ka samu babu damuwa amma kaki saide ka zauna kayi ta zana hoton da babu amfaninshi, bana bacci kullum ina searching a social media ta yadda zaka samu aiki amma bamu samu ba"

tashi tayi ta ciro hotonsu dake kasan gadonshi ya zana da wanda aka ɗaukesu tun suna yara da wanda suke tareda su abba da kuma su umma sai wanda suka rungume juna suna dariya ita dashi, zanen yafi yawa akan asalin hoto, tace "kullum sai kayi wannan zanen kwarewanka a zane bai kawo mana komai ba"

tana magana tana hawaye, ya zuba mata ido ko kyaftawa babu, ta ɗago manyan idanunta sexy tace "ko dai zamu bar garinnan ne man?"

gyara zama yayi yana kallonta ya lumshe mata kyawawan idanunshi yace "meesha kin san matsala dake?"

shiru tayi yace "gaggawa"

magana zatayi yace "shiiiii a kullum kin manta kina min addu'a Allah ya bani aikin yi? to meyasa ba zakisa a ranki watarana Allah zai bamu aiki ba?"

a hankali tace "to ai..."

rufe mata baki yayi da hanunshi, kallonshi take shima yana kallonta yace "please nasan kin gaji, amma mu kara hakuri muci gaba da addu'a, ba gashi duk da babu aiki bamu bar kannemu suna zama ba karatu ba? kinga fahad ya gama primary ya shiga jss 1 shi kuma Imran zai gama secondary nan bada jimawa ba"

tace "to idan ya gama karin karatu....."

yace "karki damu da wannan zamu saki aiki kafin hakan ya faru"

shiru tayi ta ɗaura kanta a gwiwa tana kallonshi yana zanen yana murmushi, saida yayi nisa ya ɗago kai ya kalleta, murmushi yayi mata tace "kanada kyau"

fentin da yake zanen dashi ya lakata mata a karan hancinta yace "kin fini kyau"

turo baki tayi tace "shine zaka shafamin fenti?"

yace "sorry baby"

tace "tashi ka rakani"

yana kan zanen yace "ina?"

tace "zanje kasuwa"

yace "siyan me?"

tace "pant Anti ta bani kuɗi na siyo"

murmushi kawai yayi a ranshi yace "ta riga ta saba faɗamin tun muna yara ba zata iya dainawa ba hasalima bata ɗauki hakan wani abu ba"

a fili kuma yace "bari na gama"

saida ya gama zanen ya nuna mata, dariya tayi ta karɓa tana kallo tace "Ameesha da Abdulrahman"

yace "munyi kyau?"

tace "yes amma nice zan tafi da wannan hoton"

taɓe baki yayi yace "normal"

ɗauka tayi ya tashi ya wanke hanunshi suka fita tare, akan mashi suka tafi kamar ko yaushe itace take driving, har sukaje kasuwa ta siyo sannan ta juya kan mashin zasu tafi gida yace "no rakani gidan abokina bilal"

tace "okay"

juya mashin tayi suna tafiya suna hira har suka isa gidansu bilal, tare suka fito dashi tace "tunda kuka gama school baku haɗu ba sai yau"

yace "yes"

sallama yayi bilal ya amsa tareda cewa "ina zuwa"

jim kaɗan ya fito masha Allah yanada kyau amma baƙi ne irin me glowing ɗinnan, yana ganinsu yace "su waye wannan?"

Abdul yace "mu ne"

yace "mu shiga ciki"

hanu Abdul ya mika mishi suka gaisa yace "kana nan?"

yace "ina nan ka shareni"

kallon ameesha yayi wacce bata rabo da murmushi yace "hi ameesha"

hanu ta mika mishi alaman su gaisa, da sauri man ya rike hanunta ya hana gaisuwan, murmushi bilal yayi yace "mu shiga ciki mana"

Abdul yace "no ba zamu shiga ba dama nace kawai nazo na dubaka mun jima bamu haɗu ba"

yace "gaskiya kun kyauta Allah ya bar zumunci nima rasa number ɗinka nayi ai da kullum ina kai muku ziyara"

numbern shi ya bashi yace "muna jiranka"

sunyi hira kaɗan kafin yace "hajiya ameesha ki gaida gida sosai"

tace "to insha Allah"

har suka hau mashin bilal yace "wai har yanzu baka daina hawa baya idan zaku fita ba? mace ke janka a mashin?"

taɓe baki yayi yace "ba itace taki ba"

dariya ameesha tayi taja mashin ɗin tace "bye"

har sukayi nisa yana ɗaga musu hanu, a rayuwa bai taɓa ganin amintattu irin ameesha da Abdul ba yace "Allah ya barku tare"

wajen gyaran motarshi sukaje akace musu mota ya gyaru, amma sai sun cika kuɗin gyara kafin a basu, kallanshi tayi kamar zatayi kuka tace "wannan motan naka shine ya kara talautamu ka siyar kawai mu cinye kuɗin tunda muna tafiya a mashin ɗina"

girgiza kai yayi shima kamar zaiyi kukan yace "no inason motata ai kema kina hutawa idan tana gyare"

ɓata rai tayi tace "sai muga inda zamu samu kuɗi mu ɗauka"

yace "eh dai a barmin abuna"

hawa mashin ɗin yayi suka tafi gida, a fusace ta juya bayan ta ajeshi a kofa ta tafi, shima a fusace ya shiga gida, tana shiga gida tayi wurgi da hulan tuƙin sannan ta wuce zata shiga ɗaki taji fahad yana cewa "to daka Anty ai da ya Abdul sukayi faɗa shiyasa take fushi kuma anjima kaɗan zaki ga sun shirya"

cikin fusata tace "ba zan shirya dashi ba wannan karon na daina mishi magana"

shiga ciki tayi ta kwanta akan gado ta ɓata rai, meyasa ba zai yadda su saida motan daya gama talautasu ba?

tana fushin har dare basu ga juna ba, ta taƙura sosai kamar yadda shima man yake a taƙure sai juyi yake a gado ya kasa samun nutsuwa, ya saba suna waya da dare har suyi bacci amma yau tunda suka dawo bata kara zuwa ba shima kuma baije ba, Imran dake shirin bacci yace "ya man ba zaka iya fushi da Ameesha bafa gara kawai ka kirata"

cikin tsawa yace "kamin shiru zanga me kiranta"

taɓe baki Imran yayi ya saba ganin haka kuma da kansu suke kara shiryawa ya ɗale gado yaja bargo ya rufe har kanshi ya fara bacci, ameesha tana kwance akan gado cikin rigan baccinta ta rufu da blanket sai juye juye take tana kallon wayarta ko zai kira, shiru taga bai kira ba, fahad dake kwance yana rubuta home work nashi yace "Anty meesha ki kirashi kawai nasan ba zaki iya fushi dashi ba"

cikin tsawa tace "kamin shiru zanga me kiranshi yau koya kira zanga me ɗauka"

ɓata rai tayi, har ya gama home work yaja bargo kamar me bacci ya rufe ido, lekawa tayi tana son ganin ko yayi bacci ganin idonshi a rufe ta ɗauka wayan a hankali zata latsa mishi call, shima man leka fuskan Imran yayi ganin yayi bacci ya danna mata call, gani tayi ya rigata kira da sauri ta ɗauka ta kara a kunne, cikin kasa da murya tace "hello?"

shima kasa yayi da murya yace "na kasa bacci"

tace "nima haka"

yace "kiyi hakuri"

itama tace "kayi hakuri kaima bazan iya fushi da kai ba"

shima yace "nima bazan iya ba"

hira suka fara tace "bye good night"

shima yace "good night"

kashe wayan tayi cikin sanɗa ta tashi tasa a caji komawa tayi ta kwanta tana hamdala da fahad bai tashi ba, tana kwanciya yace "ai dama na gaya miki"

waro ido tayi alaman meyasa yaji, sai kuma taja tsaki ta shareshi ta kwanta.

leka Imran yayi ganin yana bacci yace "alhmdllh bai jini ba"

Imran yace "na jika tsaf"

ɓata rai yayi kamar bai taɓa dariya ba, Imran a ranshi yace "cin maganin banza"

washe gari meesha tana tashi da gajeren wandon baccin dake jikinta ta shiga toilet tayi brush kasancewar bata salla yasa batayi alwala ba kawai wanka tayi ta fita, wandon da man ya siya musu kala ɗaya tasa kamar na ƴan ball tasa riga me dogon hanu tayi parking gashinta sannan ta ɗale gadonta zata koma bacci wani abu yace ta hau online, facebook ta hau ta fara searching masu neman ma'aikata, tsaki taja harta gaji zata sauka can taga anyi tagging wata daga cikin friend ɗinta a wani post, bi tayi taga wani post ne, gani tayi an rubuta M.U.M designing company is currently for an exceptionally talented artist to join our design team"

tsalle ta daka akan gadon ta fara tsalle, kallon address ɗin tayi sannan tayi screenshot, numbern wayarsu ta ɗauka atake ta kira, ɗauka akayi "kina magana dame kula da harkokin m.u.m fashion designing dame zamu taimaka miki?"

da sauri tace "naji kuna neman ƙwararren me zane?"

da sauri yace "kwarai kuwa muna nema kuma muna maraba dake idan kin kware"

hawaye taji na farin ciki ya cika mata ido tace "yaushe zaku fara interview?"

yace "yau zamu fara zuwa gobe zamu rufe"

tace "to na gode sosai"

rigan sanyi kawai ta ɗaura akan kayan jikinta ta ɗau makullin mashin da gudu ta fita kamar zata faɗi kasa, Anty tace "ina zajije?"

tana gudu tana sa hulan mashin tace "Man zai samu aiki yau"

fita tayi daga gidan kamar zata kife akan mashin ɗin harta isa gidansu, wurgar da mashin ɗin tayi da mugun karfi take bubbuga kofan gidansu, umma tazo ta buɗe tasan ameesha ce da wannan bugun kawai ta juya ta koma gida, rungumeta ameesha tayi ta baya tana tsalle tace "man zai samu aiki umma"

cikin kwaɓa fuska da gajiyan maganan aikin tace "to Allah yasa"

sakinta tayi ta ruga da gudu zuwa ɗakinsu, knocking take yi da karfi suna bacci su duka da Imran, cikin bacci Imran yayi tsaki yace "wallahi ameesha zata kashemu lokacin mu baiyi ba"

yana buɗe kofan ta rungumeshi kam tana juyi dashi, cikin mamaki yace "meya faru?"

tace "man zai samu aiki yau"

sakinshi tayi yaja tsaki a ranshi sabida yasan rashin sa'ansu a fili kuma yayi murmushi yace "to Allah dai yasa"

kallon man wanda yake bacci peacefully tayi, da gudu ta faɗa kanshi buɗe ido yayi da sauri yana kallonta, dariya take yi cikin farin ciki tana rungumeshi kamar zata shiga jikinshi, cikin baccin da ba isheshi ba ya motsa karamin bakinshi yace "what?"

kiss yaji tayi mishi a baki abinda bata taɓa yimishi ba saide a gefen kumatu ko kuma a goshi, Imran ya rufe ido, zamewa tayi cikin murna tace "yau zaka samu aiki"

runtse ido yayi jin yauma maganan aiki ne kamar kullum, tashi yayi yana sauketa yace "sauka"

sauka tayi amma bata zame kafafunta daga jikinshi ba tana kusa dashi sosai ta buɗe wayarta ta nuna mishi, wani irin smiling yayi ganin da gaske ne, rungumeta yayi ya ɗagata sama yana juyi da ita a cikin ɗakin, dariya takeyi, ajeta yayi a kasa yace "thank god"

umma dake tsaye a bakin kofa tace "wai kunje kun samu aikin ne kuke wannan murnan?"

ameesha tace "no amma zai samu sabida nasan ya kware"

man ya shiga toilet da sauri yayi wanka ya fito, ameesha ce ta ɗauko rigan yana shafa mai tana sa mishi, Imran yace "to Allah yasa a samu wannan aikin ko zamu fara baccin safe cikin nutsuwa"

yana gama shiri suka rike hanu atare suka fita, akan mashin nata suka tafi ta fara gudun da bata taɓa yi dasu ba sabida kada suyi late, sunyi sa'a suna zuwa mutane sun gama taruwa amma basu fara Interview ba, gefe taje zatayi parking mashin shi kuma Man ya fara tafiya a hankali yana jiran ta iso, ji yayi an kusa bigeshi da mota da ihu ameesha ta dafa kirji tareda waro manyan idanunta tace "maaaaan!!!!"

rufe ido tayi shima ya rufe ido, da kyar ta tsayar da motan bata bigeshi ba, parking tayi a hankali tasa kafanta dake sanye da high hill red, fitowa tayi tana fito kamar kullum tana taku cikin isa da gadara, jan dogon riga ne a jikinta yana da tsayi yana sharan kasa bayan gaban kuma guntu tasa mayafi akan gashinta daya bayyana har hips nata, Ameesha bakinta a buɗe tana kallonta dan ba karamin kyau tayi ba gashi tana tafiya cike da class, a gaban man ta tsaya tana cigaba da yin fito ta kalleshi from head to toe sannan ta buɗe baki kamar batason magana tace "kai makaho ne ko kurma?"

shiru yayi yana kallon cikin idonta kamar yadda itama take kallon nashi, tace "useless ka rinƙa kallon hanya idan kana tafiya kada watarana na bigeka"

wucewa tayi tana fito tana tafiya kamar ɗawisu, shima fito yayi sau ɗaya, juyowa tayi tana kallonshi, signal yayi mata sannan ya fara karkaɗa makullinta dake hanunshi, da mamaki ta kalleshi "ya akayi makullinta yaje hanunshi?"

zuwa yayi gabanta ya tsaya yana kallon cikin idonta yace "ke makauniya ce ko kurma?"

matsawa tayi baya ganin yadda yake kallonta, wurga mata makullin yayi a sama, cafkewa tayi yace "ki rinƙa kula da kanki idan kina tafiya domin kada watarana nayi miki sata"

a fusace ta juya bata mishi magana ba ta shiga ciki kamar zata tashi sama tsaban ɓacin rai, duk suna ganinta suka tashi, sai a lokacin Ameesha tayi hamdala tace "ya Allah har raina ya tsinke"

zuwa tayi ta rikeshi tace "ka rinƙa kula raina ya tsinke wallahi"

yana rike da ita yana fito shima suka shiga ciki, aka kujeran da taga an bawa mutane suka zauna, hanunta a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login