Showing 81001 words to 83501 words out of 83501 words

Chapter 28 - DUHU DA HASKE Hausa Novels by Jiddah S Mapi.docx

19 Sep 2025

2241

dashi a jikinta, hanunta da babu drip ɗin tasa a gashin kanshi, matso dashi tayi kusa da ita ta manna bakinta akan nashi tayi shiru tana kallon cikin idonshi shima yana kallonta, zamewa tayi a hankali cikin kunnenshi muryanta kasa tace "i love you too my abdool"

hanun fahad ta rike tana tafiya a hankali kamar babu jini a jikinta, wani zazzafan mota ta buɗe mishi tace "shiga muje"

zaiyi magana tace "shiga mana"

shiga yayi itama ta shiga, da mugun gudu ta bar kotun, gani yayi ta nufi hanyan wani gida ba nasu ba, sunyi tafiya da nisa kafin suka isa wani unguwa me kyawun gaske, a kofan wani maƙeƙen tsararren gate suka tsaya tana hon, buɗe musu gate ɗin akayi da mamaki fahad yake kallonta yana kallon gidan, a babban compound ɗin tayi parking me ɗauke da wasu zafafan motoci sannan ta fito ta buɗe mishi marfin motan tana tafiya da hanunshi a sarƙe cikin nata, sunyi tafiya me nisa da mamakinshi yaga kowa idan sun haɗu masu aikin sai sun durkusa kasa sun gaisheta, da sauri take cewa su tashi kada su durkusa mata, a kofan dake ɗauke da glass suka tsaya knocking tayi kafin ta buɗe, hanan dake zaune akan sofa tayi kyau cikin riga da wando fatar jikinta kaɗai ya isa ya nuna dukiyan da take ciki, da sauri tazo ta rungume ameesha tace "my sweet sis anyi nasara?"

girgiza kai tayi tace "ba'ayi ba amma za'ayi"

kallon fahad tayi ta buɗe mishi hanu alaman ya rungumeta, shiru yayi ya tsaya yana kallonta, ameesha tace "itama yayarka ce"

a hankali ya rungumeta, tace "welcome home my handsome bro"

rike hanunsu tayi suka shiga tare, a hankali ameesha ta zauna tace "akwai wani abu da yake raina"

hanan tace "menene faɗamin?"

ganin ba zatayi magana ba tazo ta zauna a gefenta ta rungume ta tana turo baki a shagwaɓe tace "me kuma sis? ba zaki rabu da damuwa ba kullum?"

tace "hanan ina ganin tsananin kama tsakanin manal da momy"

dafe kirji tayi tace "subhanallah dan Allah ki raba momy da wannan muguwar yarinyar momy babu ruwanta yanzu ma ta kirani tana tambayata ya aka kare da case ɗin kinyi nasara ne? nace mata kin hanani zuwa kince sai zama na biyu zanje, momy tace Allah ya baki nasara yasa kici galaba akan manal, kuma kin san me? yau ma ya yazeed zai zo yana hanya, jirginsu ya kusa landing kuma ta nan zai biyo sabida yasan Abba yana nan"

murmushi tayi ta kalli fahad tace "nasan kanada tarin tambayoyi a ranka amma yanzu zan amsa mata"

tashi tayi ta shiga cikin tsararren ɗakinsu da hanan ta ɗauko wani hoto tazo ta zauna kusa dashi tace "wannan shine Alhaji Abdullahi wato mahaifin hanan shine me gidan marayun da wata mata tamin kwatance a lokacin dana tafi abuja, bayan naje gidan na haɗu da kawa itace hanan, komai tare muke yi da hanan mun shaƙu sosai, kullum hanan tana tambayata me yasa nake yawan kuka ina damuwa? sai na faɗa mata duk abinda ya faru na bata labari, nan take naga ta shiga damuwa, abinda ban sani ba shine hanan itace ƴar me wannan gidan marayun tazo hutu ne tace ita a gidan zatayi hutu sabida babu wanda suke zama dashi a gida sai yayanta yazeed shi kuma a yadda tace baya magana baya shiga harkan kowa, nayi mamaki sosai da naji haka, koda zata koma gida sai tace sai mun koma tare, da kyar na yadda ina tunanin ko abbanta zaiki karɓana sai kuma nayi mamaki naga ya karɓeni hanu bibbiyu bayan ta bashi labarin duk abinda ya faru.

abba yace me nakeso yamin a rayuwa tunda ƴarshi take sona haka? nace Inaso ya sani a makaranta zan karanci law, hakan kuwa akayi na karanci law ita kuma hanan tana karantan theatre art, na samu rayuwa me kyau a gidansu mahaifiyarsu hanan ta mutu tun lokacin da hanan take karama, son da abba yake yiwa momynsu hanan ya hanashi kara aure, da kyar suka sashi yayi aure saide bai dace ba ya auro wata wacce take neman ta kasheshi ta kwashe dukiyanshi ta gudu, bayan ya gano haka ya saketa, ya kara wani aure nan ma ya auro muguwa hakan yasa ya hakura da aure suna zaune haka, watarana muna zaune muna karatu a cikin laptop ɗin da Abba ya siya mana saiga abba ya shigo da wata mahaukaciya amma balarabiya, duk muka tashi zamu gudu saide mukaji tace karku gudu ku tsaya da hankalina yanzu, abin ya bamu mamaki hanan tace Abba ina ka samo mahaukaciya? Abba ya bamu amsa da cewar yaga wasu mutane suna niyan cutar da ita shiyasa ya taimaketa ya zaci tanada haukan ya bata kuɗi sai yaji tace mishi lafiya ƙalau take yanzu abinci takeso"

cikin tausayi ya ɗauketa ya kawota gidan, dani da hanan muka riketa muka kaita ciki saide har yanzu a tsoracen muke, toilet muka fara kaita tayi wanka kafin na kwashe kayan dattin na kai waje na bata sabon kaya tasa sannan nida hanan muka kawo mata abinci taci, bayan ta nutsu muka tambayeta daga ina take?

tace mana itama bata sani ba domin tun tana karama mamanta ta mutu, babanta balarabe ne ya auri bakar fata yaje can yana wulakanta da kyar mamanta ta gudu daga gidan da ita, koda sukazo nigeria mamanta ta wurgar da ita sabida yunwa da bakar azaba, tazo taga gawan mamanta a gefen titi, tace a haka take rayuwa har watarana ta haɗu da wani mutum ya ɗauketa ya kaita gidanshi amma bai aureta ba, ya girmar da ita ya fara zina da ita yana bata manyan kuɗaɗe da kuma duk abinda take so a rayuwa, a ranan da tace ya aureta yace ya rabu da ita ba zai iya aurenta ba, ita kuma da ranta ya ɓaci tace saita tona mishi asiri ganin haka yasa ya fara dukanta har saida ya taɓa mata ƙwaƙwalwa ta zama mahaukaciya, tace batasan shekara nawa tayi da hauka ba amma na kamu da haukan tanada shekara 20, ranan data fara gane hankalinta shine ranan da wasu mutane suka bigeta suka kaita asibiti, bayan an kwantar da ita ta tashi taga inda take kawai ta gudu, daga nan saita shiga mota batasan ina za'aje ba, tsintsan kanta tayi a wannan garin har suka haɗu da Abba, bayan ta gama bamu labari tace zata tafi, nida hanan muna kuka mukace ta zauna damu, ganin babu inda zataje yasa ta zauna, muka fara kulawa da ita muna bata duk abinda take so, wani lokaci ina iya fasa zuwa school sabida naga tana zama tayi tagumi tana yawan tunani da kuka, hakan yasa nake yawan zama kusa da ita ina bata labari, dani da hanan muka roki Abba ya aureta, Abba ya amince sabida labarinta da yaji, ranan aure muka yi mata kwalliya ba dan taso ba tasa sabbin kaya, nayi iya kokarina dan ganin ta samu rayuwa me kyau ta sake tana rayuwa kamar kowa, to amma bayan na zauna da momy sai naga tana min kama ko yanayi da wata, na rasa dawa take min kaman saida na dawo nan naga tana kama da manal"

hanan a shagwaɓe tace "haba mana sweet meyasa kike haka ki daina wannan maganan manal fa na gaya miki muguwa ce ta karshe, na baki labarin lokacin da Abba ya kawoni karatu a wajen kakata a kafuna kafin ta rasu, munyi class ɗaya ta kona min teddy ɗina tace data rasa saide kowa ya rasa, wannan abin da tamin har yau yana raina, tun tana karama take mugunta bata dariya bata magana, gata da kyau kamar aljana, amma kin fita kyau"

kwaɓe fuska ameesha tayi tace "banfi manal kyau ba, nasan inada kyau amma manal ta fini shiyasa man yaje wajenta ya barni"

kallon fahad tayi tace "karka damu zamu samu mama insha Allah zamu fara nemanta daga yanzu, sannan Imran zai fito daga prison komai zaiyi daidai kaji?"

yace "to"

wayan hanan yayi ringing ta ɗauka da sauri tace "ya yazeed"

cikin rashin son magana a takaice yace "na iso"

tsalle tayi ta fita daga ɗakin taje cikin gida inda mota ya tsaya, da gudu taje ganin ya fito sanye da baƙin suit, subhanallah wani irin kyau ne dashi tsaban farin fatarshi har ya koma yellow, skin nashi kamar na mace yana glowing, hancinshi me tsayi bakinshi ɗan karami, yana sanye da baƙin glass a idonshi hanunshi rike da jaka saide fuskanshi a murtuƙe babu dariya, da gudu ta faɗa jikinshi tace "oyoyo ya yazeed"

a hankali ya rungumeta baiyi magana ba, kuka ta fashe dashi, yana shafa bayanta cikin muryanshi me sanyi da daɗin sauraro yace "kukan me?"

shiru tayi tace "shekara ishirin saide video call da waya? yau naga yayana wanda tunda momynmu ta mutu ya tafi ya barni ya koma kasar india da zama ba dole nayi kuka ba?"

janyeta yayi daga jikinshi ganin tana nema ta sashi kuka yaja karan hancinta yace "to aku sarkin surutu"

murmushi tayi ya rike hanunta yace "Abba yace sai dare zai dawo"

suna tafiya tace "eh haka yace"

shiga ciki sukayi ameesha tana ganinshi tayi kasa tace "ina wuni"

a takaice yace "fine"

shima fahad yace "ina wuni?"

yace "fine"

hanan tace "itace ameesha wacce kullum nake tura maka hotonta da nawa"

yace "okay"

shiga ciki yayi ameesha bata damu ba dan hanan ta gama faɗa mata halinshi mugun miskili ne na karshe, ɗakinshi ta kaishi ya shiga ya zauna yana kallon ɗakin, zama tayi zata fara zuba mishi surutu yace "jeki banson surutu na gaji"

turo baki tayi tace "to ina tsaraba?"

yace "sai anjima jeki zan canja kaya"

tashi tayi ta fita, ya tashi ya cire suit na jikinshi yasa vest da gajeren wando, hawa gado yayi domin ya kwanta ya huta, wayanshi yayi kara a gajiye ya ɗauka yana kara kwanciya rub da ciki, ganin sunan ROHI yana yawo ya ɗaga a hankali cikin muryan bacci yace "Baby"

cikin harshen turanci yace "i missed you"

tace "let's do video call"

yace "okay"

buɗe video call call, ya ganta kwance akan gado rohi wata kyakkyawar budurwashi ce ita kaɗai yake kulawa baya kula kowace mace, ko ita ɗinma wata rana baya kulata, zatazo tayi ta kuka yaki kulata har sai yaga dama amma yana sonta sosai da sosai, hot ce domin ko yanzu wando ne ɗan karami a jikinta na jinx, da riga fari transparent, yana iya ganin shatin nipples nata ta cikin rigan, gashinta a kame da ribbon tanada wani irin masifaffen kyau, murmushi yayi ganin tana rungume pillow cikin harshen turanci suke magana amma ta iya hausa kaɗan kaɗan ya koya mata, yace "you miss me?"

idonta cike da hawaye muryanta yana rawa tace "so much, ba nace ka tafi dani ba kaki"

yace "sorry baby zakizo watarana"

shiru tayi tana kallonshi

lumshe ido yayi ya buɗe yana kallonta da tsumammun idanunshi yace "shirt up"

kallonshi tayi tana dariya tace "i can't"

turo baki yayi yace "i miss them Inaso na gansu"

ɓoye kirjinta tayi da pillow tace "nooo"

da alama tana matukar sanshi, yace "shikenan tunda ba zaki ɗaga ba"

ganin yayi fushi tace "okay"

ya zuba mata ido, tashi tayi ta zauna tana kallonshi, zata ɗaga rigan yace "it's okay"

murmushi tayi ganin shima yana murmushi tace "you sure?"

gyaɗa kai yayi yace "yes, I love you bye"

a hankali tace "love you too bye"

kashe wayan yayi a ranshi yana jin sonta idan har Abba ya amince mishi zai auri rohi idan bai amince bama zai aureta a ɓoye domin ba zai taɓa samun macen da zai rinƙa samun hundred percent pleasure idan yana tare da ita kamar rohi ba, ko muryanta yaji yana iya fara kuncewa bale ya ganta.

Ameesha shiru tayi tana kallon fahad dake cin abinci idonta cike da hawaye, tana tuna yadda man ya shaƙe wuyanta har yanzu tana jin zafi ɓoyewa tayi sabida kar hankalin fahad ya tashi, ga kuma tashin hankalin rashin mama da take ɓoyewa kada ta ɗaga musu hankali, ji take kamar ta aza hanu aka ta ƙwala ihu ko zataji sauƙin abinda yake damunta, ganin idon manal take a cikin nata, da alama zata iya yin komai akan man, dan tana iya hango tsananin soyayyan da take mishi, runtse ido tayi a ranta tace "ya Allah na rasa me nake ciki, ya zanyi?"

hanan tace "dan Allah ki daina wannan damuwan kada ki sawa kanki ciwo"

kukan da take ɓoyewa ta faɗa jikin hanan ta fara yi, hanan sai bubbuga bayanta take tana cewa "ya isa darling sis"

har dare bata samu natsuwa ba, fahad a wani ɗaki me kyau ya kwanta yayi wanka ya canja kaya sabo, har bacci ya ɗaukeshi, hanan tana kwance kusa da ameesha ta rungumeta tana bacci, ameesha kuma idonta biyu ta kasa koda rintsawa, juyi tayi akan runtse ido tayi zuciyanta yana tafasa, komai yana dawo mata sabo tana tuna Imran daya fita daga hayyacinshi ya koma kamar wani mahaukaci, fahad ya rame yayi baƙi ƙirin, gashi babu mama an saceta, toshe baki tayi tana kuka, batasan time ɗin da kukan ya suɓuce mata ba ta fara yi da karfi zuciyanta yana zafi tace "wallahi koda zan rasa raina saina rama duk abinda kikayi manal saina fito da Imran daga wannan kuncin

wsyarta ne ya fara ringing ɗauka tayi tana duba sunan dake yawo a gaban tsadadden screen na wayar, gani tayi SWEET MOM yana yawo a gaban wayar, murmushi tayi ta amsa call ɗin tace "momy na?"

momy wacce take zaune akan sallaya cikin wani tsararren ɗaki ta mike tana ninke sallayan sannan ta cire hijabin jikinta, subhanallah wannan itace asalin balarabiya, tssyawa faɗan kyawun wannan balarabiyan ɓata lokaci ne, cikin sanyin muryanta tace "ƴata Ameesha kada ki karaya a kullum kece kike bani karfin gwiwa kece kike cewa na daina shiga a damuwa, idan yau bakiyi nasara ba gobe zakiyi haka rayuwa take, ina nan ina tayaki da addu'a a matsayina na uwa, da yaddan Allah zakiyi nasara akan wannan manal ɗin, ba zatayi albarka ba ban ganta ba amma na tsaneta, idan har kinga wannan case ɗin zaifi karfinki ni nayi alkawarin shiga kuma zan tabbatar na taimakeki koda mutuwa zanyi, ina tare dake ƴata Ameesha"

cikin muryanta daya dishe tace "momy na gode ki kwanta kiyi bacci zuwa gobe zamuyi waya"

tace "ameesha na saba dake ba zan iya baccin ba idan bana ganinki"

tace "momy ki kwanta mana ko sai nayi fushi?"

da sauri tace "A,a zan kwanta"

murmushi tayi momy ta kwanta, ameesha tace "good night momy"

tace "good night I love you"

tace "love you too momy"

katse wayan tayi ta kwanta tana kallon saman ɗakin ta rasa tunanin mema zata fara tsaban yadda lissafinta ya dagule.

*Laifin daɗi karewa Anan na kawo karshen free pages, duhu da haske is ₦400 ta account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, make your payment for complete sai a turo katin shaidan biya ta nan 08144818849 please idan kinsan baki shirya ba kada kimin magana receipt kawai zaki turamin*

_Jiddah Ce...✍️_

08144818849

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login