Showing 66001 words to 69000 words out of 83501 words

Chapter 23 - DUHU DA HASKE Hausa Novels by Jiddah S Mapi.docx

19 Sep 2025

2250

unguwa da baƙina suka sauka, motata tsaya na fito domin duba meya samu motan kin san yaran wai me suka cemin?"

girgiza kai tayi tana kura mata ido a tsorace, tace "wai balarabiyan mahaukaciya"

tashi ammi tayi a firgice tace "ke kuma me kika ce musu?"

ganin yanayin ammin tace "relax mana ammi ban kulasu ba kawai na tafi"

ajiyan zuciya ta sauke tace "kimin alkawari ba zaki kara zuwa wancan unguwan ba"

tace "nayi alkwari"

tafiya zatayi manal tace "ammi saura wata nawa kenan na haihu?"

Abdool yace "yawwa dama inaso nima na sani amma kunyan tambaya nake"

tsaki taja a ranta wato duk basuda kunya shi wai a haka kunya yake, tace "saura wata shida"

tafiya tayi, Abdool ya rungumeta yace "me kama dake nakeso ki haifamin"

a ranshi yace "idan bakya raye ba za'a manta dake ba"

tace "ni dai nafi son na haifi me kama da kai"

shafa fuskanta yayi a hankali ta lumshe ido, matsowa yayi kusa da ita sosai yana jiyo numfashinta, bakinshi ya ɗaura akan nata, kafin yayi komai yaji ta fara kissing tongue nashi tareda haɗawa da pinkish lips nashi, hanunta a kanshi tana wasa da gashinshi dake a kwance, hanunta yaji ta fara ɓalle bottle na riganshi tana shafa suman dake kwance a kirjinshi, kwantar dashi tayi akan sofan ta bishi har yanzu bakinsu a haɗe, rufe ido yayi ya zame a hankali ganin tana neman ta fitar dashi hayyacinshi, yace "no ammi zata iya fitowa"

girgiza kai tayi kamar zatayi kuka tace "ba kai ka fara ba?"

zaiyi magana ta rufe bakinshi da nata, zamewa yake yana dariya, wayarta yayi kara alaman message, ɗauka tayi tana rungume dashi baya ganinta ta buɗe tana karanta sakon, driver ne yayi mata text "yarinyar da kika nunamin hotonta gata nan tazo amma na hanata shiga ciki tana nan wajen compound"

gabanta ya faɗi ko da me ameesha tazo? tsaki taja a ranta tace koma menene abinda na sani shine babu wanda ya isa ya rabani da Abdool, da sauri tace "uhm ni kam yau exercise zanyi tunda kaki muyi"

yace "good girl exercise nada kyau ga me ciki, jeki zan biyoki bari nasa jallabiya"

tashi tayi tana tura baki ta fita, haɗe rai tayi ganin ameesha tana turesu tana cewa "ku barni man nakeson gani"

cikin takun isa ta karasa inda take tace "duk kuje ku barmu anan"

tafiya sukayi ta rike hanun Ameesha ta jata kusa da wani babban dutse dake cikin gidan tsayawa tayi tace "meya kawoki?"

tace "nazo wajen man ne"

murmushi tayi tace "man yau kaɗai yake dashi gobe ze tafi paris kuma zai jima acan har sai na haihu zai dawo me zakiyi mishi?"

tace "ummanshi ce babu lafiya jikinta yayi tsanani shine nake so na faɗa mishi"

tace "okay zan faɗa mishi jeki"

girgiza kai tayi tace "nafi son na faɗa mishi da kaina ki mishi magana please"

cikin kallonta na tsananin ɓacin rai tace "nace miki zan faɗa mishi fita"

girgiza kai tayi tace "ba zan fita ba ko kasheni zakuyi saina sanar mishi domin alkawari na yiwa umma"

hanunta ta rike da karfi tana janta tace "fita ki bar gidannan"

tirjewa ameesha take, Abdool ne ya buɗe kofan ya canja kaya zuwa jallabiya fari me taushi, kallonsu yayi da mamakin ganin ameesha a wannan lokacin, ganin haka manal tace "ki sakemin hanuna ameesha inada ciki ki sakeni kada naji ciwo"

cikin tsananin mamakin sharrin da take shirin yi mata tace "kece kika rikemin hanu ai kece zaki sakeni"

da karfi tace "Abdool kace ta sakeni"

Abdool zaiyi magana kawai ta saki hanun Ameesha tayi juyi ameesha kuma tana shirin riketa kawai ta zube akan babban dutsen dake wajen, zaro ido man yayi itama ameesha ta zaro ido tareda ɗaura hanu a baki, manal cikin azaba taji jini ya fara zuba daga jikinta a take jinin ya fara sauka har zuwa kasa, da kyar ta buɗe baki tace "man cikina"

cikin gudun da bai taɓa yiba yazo ya ɗagata yana cewa "manal?"

ameesha cikin tsoro tasa hanu zata taɓata ya tureta saida ta kusan faɗuwa, jijiyoyin kanshi suka tashi, yana zufa ya nunata da yatsa yace "stay away from my wife"

tace "man ka fahimta banyi mata komai ba"

yace "ina gani kika tureta kice baki mata komai ba? ameesha yaushe kika zama muguwa haka? ko dama kin ɓoye muguntanki ne lokacin da muke tare?"

zatayi magana yace "stay away!!!"

shiru tayi, yana rike da manal jini yana zuba ya kira waya yace "kizo gida yanzu yanzu"

lokacin da zasu shiga falon manal ta buɗe ido tana yiwa Ameesha kallo sannan tayi murmushi ta kashe mata ido ɗaya, shiga ciki yayi da ita ammi jikinta yana rawa tace "ina jinku na kasa fita abdoo"

kwantar da ita yayi ya fara safa da marwa a ɗakin, dr A'isha ce tazo gidan ameesha tana tsaye a inda suka barta har ta shiga, duba manal ta fara, jikinta a mace tace "tayi miscarriage"

Abdool cikin tashin hankali yace "dan Allah ki kara dubata inason cikin sosai dan Allah, kunsan inason cikin"

kuka ya fashe dashi, manal tasan yadda yake son cikin sabida Abdool yana matukar son yara, cikin kuka tace "ɗanaaaaa wayyo ammi ɗana"

kuka take yi sosai, Dr A'isha tace "saide hakuri dan cikin ya gama sauka tayi ɓari amma garin ya haka ta faru? accident tayi ne?"

manal kuka take yi Allah ya sani tana son cikinta amma a halin yanzu babu abinda take so kamar man ba zata yadda kowa ya shiga tsakaninsu ba, ya girgiza kai kawai yana kallon kofa inda ameesha take tsaye yana aika mata wani irin mugun kallo me cike da tsana, zatayi magana yace "shikenan kin zubar da cikin kin samu kwanciyan hankali? shikenan?"

girgiza kai take zatayi magana yace "fita kibar gidannan ameesha, ban taɓa zaton akwai mugunta koda kwayan zarra a zuciyarki ba, yau kawai sai naji na tsaneki, ki fita a rayuwata ki barni mana, ki barni dan Allah wallahi na tsanaki yanzu"

hawaye ta share ganin yadda yake magana cike da ɓacin rai a tsawace kamar ba man ba

tace "to shikenan tunda ka tsaneni amma nima inaso ka sani a yau naji na tsaneka kuma zan fita a rayuwarka"

hanunta ya rike da karfi ya fara janta yace "fita banson ganinki"

ammi tace "Abdool ka saketa"

cikin zafin da takeji tace "ka sakeni man"

janta kawai yake ammi tana binsu har bakin kofa taga ya buɗe kofan yayi wurgi da ita, faɗuwa tayi kasa cikin azaban daya ziyarci hanunta tace "wayyo hanuna"

ɗauke kai yayi ganin tana kallon hanun har ya fara jini tana kuka

yace "ko me kama dake banason gani, idan kika kara shiga rayuwata zan miki abinda harki mutu ba zaki manta ba"

da alama man yaji ciwon zubewan cikinnan, yana matukar son cikin, tashi tayi da kyar tana ciza baki, ta share hawaye a hankali ta tako zuwa gabanshi ta tsaya kusa dashi tana kallon cikin idonshi, zuciyanta a bushe ta fara magaan cikin rashin tsoro tace "In dai sunana Ameesha Ibrahim ƴar halak aka haifeni ba zina akayi aka samu ciki na ba, zan fita a harkanka Abdulrahman haruna lamiɗo, amma kafinnan inaso ka sani ba nice na zubar da cikin matarka ba, banzo gidannan sabida na ganka ko naga matarka ba, sannan ban san da wannan cikin da kuke magana akai ba, idan kuma ka ɗauka cewar nice na zubar to kayi duk abinda kaga zaka iya ka idan kaso ka kaini inda ba'a dawowa, sannan zan isar maka da sakon daya sa ameesha tasa kafarta ta shigo wannan gidan, ummanka ina nufin wacce ta ɗauki cikinka na tsawon wata tara ta haifeka ta raineka har ka zama mutum batada lafiya, idan kaga dama kazo idan kaga dama karka zo, ni na isa na kula da ita sabida kafi kowa sanin wacece ameesha banida raunin zuciya ko da kai ko babu kai zan iya komai"

juyawa tayi zata tafi a hankali ta juyo ta share hawayen daya wanke mata fuska tace "butulu"

tafiya tayi shima ya shiga gidan tareda rufe kofan, bata kara juyowa ba, zama yayi a jikin kofan ya haɗa kai da gwiwa a hankali ya fara raira kuka me sauti, baba megadi dake rike da sanda yazo wajenshi yace "Abdool ba kuka zakayi ba duk abinda ya faru da kai a rayuwa addu'a zakayi kaji?"

a hankali yace "to baba ya zanyi?"

a hankali baba yace "kayi hakuri duk abinda kaga ya faru to an rubuta zai faru babu wani wanda ya isa ya goge domin takaddan ba a hanun ɗan Adam yake ba yana hanun ubangijin mu, saide karfin addu'a yana iya canja ƙaddara"

cikin kuka ya tashi jikinshi a sanyaye yace "to baba na gode" shiga ciki yayi, manal ta rike ammi tana kuka kamar ranta zai fita, kukan azaban ciwon cikin dake addabanta a halin yanzu take da kuma soyayyan da take yiwa cikin, cikin azaba tace "man shikenan na rabu da cikina?"

zama yayi kusa da inda take kwance a kasa ya ɗaura kanshi a cikinta yayi shiru yana hawaye, ammi tace "kuyi hakuri duk abinda ya faru a ƙaddaran ɗan adam an rubuta zai faru ne babu wanda ya isa ya hana, amma duk wanda yayi kokarin canja ƙaddaran wasu to Allah ba zai barshi ba kuma ba zaiyi karshe me kyau ba, ba zai taɓa samun farin ciki ba a rayuwa ko kuma Allah ya haɗashi da ciwon da babu magani"

ɗip hawayen manal suka tsaya jin abinda ammi ta faɗa, a hankali ta ɗago dara daran idanunta da eyelashes ɗin suka jiƙe da hawaye, itama ammi kallonta tayi, da sauri ta ɗauke kai, man ya kalleta yaga jikinta yana rawa, idonta ya gama rikiɗewa yayi jajur a hankali ya ɗagata ya kaita ɗakinta, akan gado ya kwantar da ita, tayi shiru ta rufe ido, tashi yayi zai tafi ta rike hanunshi cikin wani irin raunataccen murya haɗe da ciwon data ji tace "ina zakaje ka barni Abdool?"

so yake yace wajen umma, sai yaji tace "zan mutu Abdool ni nasan ba zan jima a duniya ba, duk wanda na tarewa jin daɗi ko kuma na kuntata mishi nasan zan mutu na barshi, haka Allah ya rubuta abdool haka Allah ya yini, abdool ni nasan me nakeji a jikina, ba zan jima a duniya ba"

dawowa yayi ya rungumeta kawai zuciyanshi yana kara karaya

itama manal ita kaɗai tasan ciwon da takeji a jikinta da zuciyarta ko kaɗan ba pretending take da ciwon da take dashi ba

ciwonta na gaskiya ne babu karya a cikinta, wasu zafafan hawaye suna wanke kyakkyawan fuskanta tana kallon bayan abdool wanda shima hawaye masu raɗaɗi suke sauka a idonshi

a cikin ranta tace "Abdool kayi hakuri abdool ka yafeni nayi sanadin cikin dake jikina badan komai ba sai dan banso a rabani da kai, naraunata kaina, na tuba Allah, na tuba bazan iya rabuwa da kai ba zan iya yin komai dan na zauna da kai, manal meyasa kikazo duniya kika zama wa mutane masifa? kina yin abu kamar ba ƴar mutane ba, kamar aljani ne yayi cikinki, a hankali yake shafa bayanta jin sautin kukanta yana karuwa, sun jima a haka kafin taji ya saketa ya kwanta a gefe, rufe ido yayi bacci ya ɗaukeshi sabida zazzaɓi ne ya rufeshi, murmushi tayi tana kallon kyakkyawan fuskanshi, a hankali ta janyo blanket ta rufashi dashi, kiss tayi mishi a goshi sannan ta sauka akan gadon, gaban mirror taje ta ɗauko stool ta zauna tana kallon kanta a madubi, wasu zafafan hawaye suna zubo mata suna wanke kyakkyawan fuskanta, cikin rawan murya ta motsa ɗan karamin bakinta tace "manal anya ke mutum ce?"

kara kallon kanta tayi ta kasa koda kyafta ido ta cikin madubin tace "manal meyasa?"

wani irin mari ta wanke fuskanta dashi, kallon shatin hanunta daya fito akan fuskanta take fuskan ya koma jajur, kara marin kanta tayi daga nan ta fara bawa kanta kyawawan maruka tana kuka, saida taga fuskanta ya kumbura yayi jajur sannan ta kalli bakinta da gefen yake jini tace "ba zan iya ranuwa da Abdool ba, wallahi ba zan iya ba, zan iya yin komai akanshi kuma a shirye nake nayi komai akanshi koda kuwa kowa zai mutu koda nice zan mutu"

a hankali ta mike daga kan stool ɗin ta koma kan gadon ta kwanta ta rungumeshi ta rufe ido.

*You can start making your payment, our free pages is about to finish, duhu da haske complete is 400 via 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, send your evidence of payment via 08144818849 may Allah bless you and ease your payment Ameen*

_Jiddah Ce....✍️_

[09/04 à 08:06] JIDDA MAPI: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*DUHU DA HASKE*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Na

*Jiddah S mapi*

*Chapter 18*

~Ameesha a kofan asibitin aka ajeta a hankali take tafiya jikinta babu kwari, murmushi tayi lokacin da suka haɗa ido dasu imran ya tashi da sauri yace "ina yake?"

tace "ban sameshi ba"

Anty tace "karya kike ameesha akwai abinda kike ɓoyewa"

murmushi tayi me sauti tana leƙa ɗakin da umma take tace "me zaisa nayi karya Anty? ban sameshi ba"

Imran ya tsaya a gabanta ta sunkuyar da kai tana rike yatsanta da yake zafi harma duka hanun zafi yake, yace "ki kalli idona ki faɗa mana baki sameshi ba"

kallon cikin idonshi tayi tace "ban...ban...ban"

faɗawa jikinshi tayi ta fashe da wani irin ɗan marayan kuka, Anty jingina kai kawai tayi da jikin bango, Imran a hankali yace "shiiii ki daina kuka"

dr ne ya bude kofa ya fito, jikinshi a mace yace "sai hakuri Allah ya mata rasuwa, amma wacece ameesha da Abdulrahman?"

Ameesha sakin Imran tayi a kiɗime tace "nice"

yace "ta mutu tana cewa ki kula da Imran ta bar miki amananshi tasan kece zaki kula dashi kamar wacce ta haifeshi, tace shima kaninki ne kamar fahad, shi kuma Abdulrahman tace tana son ganinshi sannan tace idan yazo kuce mishi ta yafe mishi komai ta yafe mishi domin tasan ba laifinshi bane"

Imran yace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un"

Ameesha silalewa tayi kasa ta faɗi, anty hanu ta ɗaura akanta ta ƙwala ihu, fahad da Imran ne kaɗai suka tsaya suna hawaye, hakuri aka taru ana basu mutane suka taimaka musu suka fitar da gawan a mashin suka sata, ameesha da kyar suka samu ta farfaɗo daga suman da tayi, tafiya sukayi gida, suna shiga ameesha ta kara zubewa kasa, har aka gama jana'iza bata farfaɗo ba, saida zasu tafi ta farfaɗo, rike makaran tayi ta hanasu fita dashi, Imran ne yazo ya riketa da kyar aka fita da umma, sannan ya saketa ya bisu domin kai umma gidan gaskiya gidan da kowa sai yaje, kwanciya tayi Anty tana bata hakuri itama tana kuka, da haka su imran suka dawo, time ɗin Ameesha tana zaune kusa da kujera tayi shiru idonta a kumbure, kwanciya yayi a kasa ya ɗaura kanshi a cinyarta yayi shiru yana jin zazzaɓi me zafi yana ratsa jikinshi, hanunta kawai ta ɗaura akanshi, duk wajen babu wanda yayi magana, haka har dare, mutanen unguwa da suka shigo duk suka tafi ganin dare yayi aka barsu su kaɗai.

cikin daren sai juye juye yake ya kasa bacci yanda yaga rana haka yake ganin daren, ta cikin dim light take kallonshi, a hankali ta matso kusa dashi sosai ta harɗe kafafunta a cikin nashi, rabin jikinta a kanshi tayi shiru tana kallon kyakkyawan fuskanshi, shafa sajenshi dake da matukar ɗaukan hankali tayi, cikin sanyin murya tace "me yasa bakayi bacci ba?"

muryanshi yana crack yace "ina cikin wani hali manal ban san me nakeji ba na kasa nutsuwa ina cikin tashin hankali"

a hankali ta rufe bakinshi, bakinta ta kai kunnenshi tace "relax babu komai karka damu Indai ciki ne Allah zai bamu wani"

zaiyi magana tace "please abdool banson kana shiga damuwa" cikin rashin nutsuwan da yake ciki ya janye zip ɗin rigan baccinta ya sauke kasa"

hanunshi ta rike tana girgiza kai

a hankali yace "me yasa?"

tace "an bani bed rest ka manta?"

girgiza kai yayi ya janye hanunta, saida ya tabbatar ya ɗan samu nutsuwa kafin ya koma ya kwanta, kwanciya tayi a jikinshi bacci ya ɗauketa, sam bacci yaki zuwa har yanzu, kwantar da ita yayi a gefe yaci gaba da juye juye ya rasa tunanin me ma zai fara, yadda sukayi da ameesha yafi komai tsaya mishi arai, a hankali ya ɗau wayarshi sabo yasa numbern Imran ya latsa call, kusan sau biyar yana kira bai ɗauka ba, Imran wayarshi a hanun Ameesha tana ganin sabon number ya damu da kira ta kashe wayan gaba ɗaya kawai ta aje a gefe, yadda sukaga rana haka sukaga dare, gara fahad ya ɗanyi bacci kaɗan, amma ita da Imran da Anty ko runtsawa basu yi ba.

ganin Imran bai ɗau wayan ba jikinshi ya kara sanyi, yar da wayarshi yayi a hankali yana kallon manal wacce take bacci cikin nutsuwa, shafa innocent face nata yayi yana tuna maganganun dr, cikin bacci ta rike hanunshi taci gaba da bacci.

sunyi kwana uku a gidan basa cikin hankalinsu sun rame sabida rashin cin abinci, sai Anty tayi da gaske suke shan tea itada imran, wa'azi take musu tana basu hakuri da shawaran su karɓi ƙaddara, da kyar ta samu suka fara warwarewa, Imran da fahad sukaci gaba da zuwa school, ita kuma kullum suna gida da Anty har yau ta kasa faɗa musu abinda ya faru tsakaninta da man, tana kokarin manta komai amma ta kasa, dole ta fito da mashin nata ta fara kaisu school saboda babu kuɗin transport, yauma kamar kullum ta dawo daga kaisu school umma tayi wata biyu da mutuwa yanzu, Imran kuma ya gama zana jarabawanshi na gama secondary yau zasu basu certificate, fuskanta da fara'a ta shiga tayi wanka, fitowa tayi taga Anty da sabon kayanta tace "Ameesha kisa wannan atamfan yau bakya sa atamfa kullum cikin riga da wando"

murmushi tayi tace "to"

karɓa tayi tasa riga da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login