Showing 78001 words to 81000 words out of 83501 words
gashi ne ya cika har ya sauka wuyanshi, hanunshi da kafanshi ɗaure da kaca sun sashi a gaba suna biye dashi a baya, yana ganin fahad yace "ina mama?"
bakinshi ya fara rawa ya kasa magana, hawaye masu zafi suka zubo yace "tunda taje neman lauya kwana uku da suka wuce wanda zai kareka, ta tafi da kuɗi masu yawa domin ta biya lauya ta siyar da gidanmu har yau bata dawo ba, ni kaɗai nake kwana a gidan mama bata dawo ba..."
ya karasa maganan yana kuka, shiru Imran yayi suka rikeshi suna tafiya dashi, shima fahad ya tashi yana binsu a baya har aka fita dashi aka sashi a mota zuwa kotu, fahad ya hau mashin ya bisu a baya,
man yana gyarawa ammi hijabinta tana zaune akan wheelchair yayi murmushi ya rike fuskanta da hanu biyu yace "yau za'a yankewa wanda ya saki a wannan halin hukunci kinji ammi?"
tana iya ganin yadda yake jin ɗaci a kasan ranshi, tana iya ganin tashin hankalin da yake ɓoyewa a kullum, hawaye masu zafi suka fara wanke mata fuska inama tanada baki da tace mishi ya ɗauketa su gudu su bar gidannan, data faɗa mishi gaskiya, tun daga kan mutuwan dady har zuwa yanzu ta gama gane komai akan manal saide bakinta ba zai iya magana ba, kallonta yayi duk yadda yaso ya daure ya kasa kifa kanshi yayi a cinyarta ya fashe da wani ɗan marayan kuka, a hankali take shafa bayanshi alaman lallashi, karan takalmin manal yasashi tashi da sauri ya share hawayen sannan ya sharewa ammi, cikin rashin dariya na asalinta manal ta fito sanye da abaya baƙi tasa siririn mayafi a kanta, idonta ta rufe da baƙin glass sannan tasa flat shoe hanunta rike da waya, kallon Abdool tayi wanda yake kallonta yana murmushi, karasowa tayi ta zuba hannayenta akan wuyanshi tana kallon cikin idonshi bayan ta ɗaga glass ɗin tasa a saman mayafin tace "my abdool na yafewa Imran ina ganin mu janye wannan case ɗin sabida yana cikin wani hali"
waya ta ɗaga zatayi kira ya rike wayan, yace "idan kin yafe ammi bata yafe ba, ki duba kiga ba zata kara tafiya ba har karshen rayuwarta, duk wanda ya saka a wannan halin dolene a kullum sai kaji ka tsaneshi a cikin ranka, koda kin yafe dole a yiwa ammi adalci"
tace "nasan ammi zata ya..."
yatsanta yasa a bakinta hakan yasa tayi shiru, cikin son kawar da maganan yace "sha"
tsotsan yatsan tayi tana kallonshi, murmushi yayi yace "to ya isa"
tsayawa tayi ya cire yatsan daga bakinta yace "haka nakeso a kullum idan na faɗa miki abu kiji"
har cikin ranshi yana jin daɗin yadda idan ya faɗa mata abu bata musu zatabi umarninshi yasan tana yin hakan ne sabida tsananin sonshi da take, a hankali tace "my abdool ina sanka zan iya mutuwa a kanka"
idonta cike da hawaye tayi maganan, yana kokarin fara tura ammi yace "na sani, manal soyayyan da kikemin yayi yawa ya kamata ki ɗan rage"
tsayawa tayi tace "kalleni my abdool"
kallonta yayi, ta rufe ido tace "na rantse da ubangijin daya halicci rana kuma ya halicci wata, ubangijin da yayi mutum kuma yayi aljani, ubangijin da yake bawa wanda yaso ya kuma hana wanda yaso, na rantse da ubangijin Annabi muhammad s.a.w bazan daina sonka ko kuma na rage sonka ba till the end of time"
da sauri yazo ya rike ta yace "dan Allah manal ki daina wannan maganan"
zatayi magana yace "karfe ɗaya da minti goma yanzu karfe biyu za'a shiga kotu"
tura ammi yayi har zuwa wajen mota, shi ya ɗagata ya sata a motan sannan ya shiga itama manal ta shiga, driving zai fara ammi ta ɗan taɓashi, juyowa yayi yace "na'am ammi akwai abinda kikeso ne?"
kallonshi takeyi sosai da alama akwai abinda take so ta faɗa mishi, yace "kina buƙatan wani abu?"
ta cikin madubi ta kalli manal wacce take aika mata kallo da idanunta masu rikita mutum, a hankali ta girgiza kai alaman babu, killer smile manal tayi, yaja motan suka tafi.
a cikin kotu sukayi parking da kanshi ya cire ammi yana turata ita kuma manal ta rufe idonta da glass ɗin suka jera tare suna tafiya, a daidai lokacin aka shigo da Imran cikin kotun, shima fahad ya karaso ya aje mashin nashi a gefe, yana gaba suna biye dashi an ɗaure hanunshi an kwance na kafanshi domin yayi tafiya, ido huɗu sukayi da man wanda hanunshi yake kan keken ammi, ɗauke kai yayi yaci gaba da kallon gabanshi, fahad kallo ɗaya ya yiwa su man ya wuce yana binsu Imran, man jikinshi ya fara rawa ganin yadda Imran ya koma, da kuma fahad kuma baiga mama ba baiga ameesha ba, yasan ita bata nan tunda ta tafi yau shekara huɗu kenan bai kara ganinta koda a hanya bane, ammi ta ɗaura hanunta akan nashi cikin tausayi, murmushi yayi mata ya turata suka shiga ciki, dashi da manal da ammi suna gaba gaba, fahad yana nesa dasu shima layin gaba ya sunkuyar da kanshi yaki kallon Imran dake tsaye a gaban kotu, yau kam kotu har yafi na koda yaushe cika, fal yake da mutane har wasu suna tsaye akan kafarsu, alkali ya shigo kowa ya tashi domin bashi girma saida ya zauna kowa ya zauna akayi shiru, alkali yace "ina lauyan wanda yake kara da wanda ake kara"
lauyan manal ne ya tashi yace "sunana barrister fadeel lauyan wanda yake kara"
komawa yayi ya zauna, Alkali yace "ina lauyan wanda ake kara?"
shiru babu amsa, ya kara maimaitawa, har yanzu shiru babu amsa, alkali yace "za'a fara gudanar da shari'a yaune karshe yau za'a yanke hukunci, barrister fadeel bismilla"
fitowa barrister fadeel yayi ya tsaya a gaban Imran ya fara mishi tambayoyi amsawa yake a hankali cikin karaya, barrister fadeel yace "ina neman kotu nan me alfarma ta taimaka ta yiwa waɗanda aka zalinta adalci tunda ya fara karaya da alama zai amsa laifinshi"
alkali ya kalli Imran wanda ya sunkuyar da kai yace "malam Imran shin ka amsa laifin da ake tuhumanka dashi?"
a hankali yace "eh na amsa"
a firgice Abdool ya kalleshi jin abinda ya faɗa, Alkali ya kara cewa "shin ka amsa laifin da ake zarginka dashi?"
yace "kwarai na amsa"
yace "kaine ka yiwa matar yayanka fyaɗe kayi niyan kashe mahaifiyarta har ta samu rauni me muni?"
a hankali yace "eh nine"
kanshi a kasa yake amsawa, alkali yace "ɗago kai ka kalli kotu ka faɗa laifinka a gaban kowa"
a hankali ya ɗago kai ya kalli duk mutanen ciki kafin yace "na amsa laifina na zuwa gidan yayana wanda muke uwa ɗaya uba ɗaya na yiwa matarshi fyaɗe sannan da zan gudu mahaifiyarta tana kokarin hanani gudun na tureta daga stair ta faɗi taji ciwo"
duk kotu yayi shiru harda alkali, sautin kukan fahad kawai akeji, alkali ya kalli mutanen kotu yace "bayan Imran ya amsa laifukan daya aikata da kanshi kotu ta yanke mishi hukuncin kisa sabida yayi niyan yin kisa sannan ya aikata mummunan laifi wato fyaɗe"
fahad yace "dan girman Allah alkali kuyi hakuri wallahi bashi ya aikata ba, na rantse da Allah bashi bane"
manal kanta a kasa man yaki yadda ya kalli inda Imran yake, ammi banda hawaye babu abinda take yi, alkali yace "yaro shifa da bakinshi ya amsa laifinshi kuma ya maimaita a gaban kotu, idan kana ganin anyi mishi rashin adalci yanada lauya ne?"
shiru yayi, alkali yace "yanada lauya?"
"Eh yana dashi"
muryan ameesha ne ya karaɗe cikin kotun, daga bakin kofa take tsaye, duk suka juyo atare harda manal, murmushi ne ya suɓucewa Imran da fahad ganin ameesha tsaye a bakin kofa cikin uniform na lauya baƙi da hula akanta, tasa bakin takalmi me tsayi tayi parking na tulin gashinta tasa ribbon baƙi kafin ta ɗaura hulan lawyer a sama, tayi wani irin masifan kyau ta kara zama fara fatarta yana wani glowing ta zama kamar balarabiya, saide babu murmushi akan fuskanta ko kaɗan, tayi wani kwarjini na musamman, cikin takun nutsuwa da class kamar ba ameesha ba ta fara takowa duk mutanen kotu suna kallonta, manal idanunta a waje take kallon ameesha, a gaban Imran ta tsaya sannan tace "sunana barrister ameeesha Ibrahim lauya me kare wanda ake kara"
a hankali taje gaban alkali ta mika mishi takaddunta tace "ina rokon kotu tamin alfarma sabida late ɗin da nayi banzo da wuri ba, amma inada kwakkwaran uzuri"
alkali ya duba takaddunta yaga eh tabbas successful lawyer ce sannan lawyer ce me kokari domin da first class ta fito, gyaɗa kai yayi, tace "idan ba damuwa zanso a maida wannan case ɗin baya sannan idan har case ɗin baimin ba zan ɗaukaka kara"
alkali duba da matsayin da take dashi a fannin karatu yace "na baki dama wannan case ya zama sabo"
kallon mutanen kotu yayi sannan yace "lauyan wanda suke kara zai iya fitowa sannan an baku dama kowane challenge fa zaku kare wanda kuke karewa ku yishi amma banda zagi banda cin mutunci"
cikin girmamawa ta karɓi takaddunta daga hanun alkalli ta rungume a kirjinta, dr fadeel ya fito,
Alkali yace abasu kur'ani suyi rantsuwa zasu faɗi gaskiya, dr fadeel yayi sabon rantsuwa sannan ameesha ta karbi kur'ani tace "na rantse da ubangijin daya aiko mala'ika jibril a cikin kogo ya cewa Annabi muhammad s.a.w kayi karatu da sunan ubangijinka wanda ya halicceka (ikra bismi rabbikallazi khalaka)
ba zan kare me laifi ba, mika kur'ani tayi cikin girmamawa alkali ya karɓa ya aje, kallon manal tayi tace "zanso abani dama na kira wacce ta kawo kara domin akwai wasu tambayoyi da nakeso nayi mata"
alkali yace "an baki dama, wacce tayi kara bismilla"
a hankali manal ta tashi daga inda take taje ta tsaya tana kallon kotu, zuciyanta yana dukan ɗari ɗari.
cikin confidence Ameesha ta tako zuwa gabanta tace "manal umar maidawa"
kallonta manal tayi tace "manal Abdulrahman lamiɗo kamar kin manta inada aure"
murmushi tayi me sauti sannan tace "sanin darajan mahaifi yasa na kiraki da sunan mahaifinki, ko dai bakisan darajan naki bane?
sannan ko a addini babu inda akace ki cire sunan mahaifi kisa sunan miji ko dai bakije islamiya bane? okay na manta mahaifinki ya mutu oh sorry an kashe shi ina nufin wata ta tura motarta ta bige motarshi tana gani yana ɗaga hanu a cikin motar yana neman taimako bata taimaka mishi ba har saida ya zama toka, sannan tabi wacce suke tare a hotel ta sata rataye kanta sabida kada ma zargi ya hau kanta"
kallonta manal tayi jikinta ya fara rawa, itama ameesha kallonta take tana wani irin smiling da alama a shirye tazo.
ameesha tace "koda shike ba case nashi muke yi ba kawai ina tayaki alhinin mutuwan mahaifinki ne"
kallon mutanen kotu tayi sannan ta kara maida hankali kan manal tace "manal zanso na faɗawa kotu wani abinda kika taɓa yinshi lokacin da kike yarinya hakan zaisa kowa ya fahimci abinda zaki iya aikatawa da wanda ba zaki iya ba, a lokacin da kike school kin taɓa kwace teddy ɗin wata yarinya me suna hanan kika kona a cewarki duk abinda kikeso daki rasashi gara kowa ya rasa"
da mugun mamaki manal ta kalleta aina tasan wannan labarin?"
murmushi tayi tace "kin girma da wannan abin a ranki hakan yasa a lokacin da kika haɗu da abdool ko kuma ince kika kwace Abdool kinga cewar mahaifiyarshi da kaninshi basa sanki hakan yasa kika fara kulla sharruka har saida kika janye Abdool zuwa gidanku, sannan bayan kunje gidanku bakyaso kowa ya raɓeshi kika yiwa kaninshi sharri, ta yaya akayi Imran yasan inda makullin ɗakinki yake?"
tana mata wani irin kallo tace "makullin yana jikin kofa"
girgiza kai tayi tace "gidanku basa barin makulli a jikin kofa kuma kece kika hana hakan, idan baki yadda ba inada shaida"
buɗe murya tayi tace "Atika"
wata me aikin gidansu manal me suna Atika ce ta shigo, ameesha ta nuna mata waje ta tsaya tace "sannunki"
a hankali tace "yawwa"
tace "zaki iya gayawa kotu wacece ke?"
tace "sunana Atika nice me kula da shara da goge na gidansu manal"
tace "sannu malam Atika shin zaki iya faɗa mana yaushe rabon da abar makulli a jikin kofan gidansu manal?"
tace "gaskiya ya jima domin manal ta hana hakan"
murmushi tayi tace "mun gode zaki iya tafiya"
fita tayi, ameesha tace "to manal ta yaya akayi Imran yaga makulli shida ba shiga gidan yake ba har ya rufe ɗaki?"
tayi shiru, ameesha tace "tambaya na gaba, shin Imran ne ya yaga rigan jikinki ko kece kika yaga nashi?"
tana huci kanta a kasa tace "shine"
girgiza kai ameesha tayi tace "no kece kika yaga riganshi dogon domin yagun ta gaba ne, da ace fyaɗe zaiyi miki da ta baya zaki yaga riganshi domin ceton kanki, amma ta gaba ya nuna kinason abinda zai yi miki"
dunƙule hanu manal tayi, ameesha tace "sai tambaya ta gaba shin minti nawa yayi yana amfani dake?"
a fusace ta kalleta tace "taya za'ayi nasan minti nawa ne?"
tace "ta yadda akayi kikasan fyaɗe ya miki, a ganina duk macen da miji ya kusanceta dole tasan daɗewanshi ko akasin haka a yadda nasan Imran ko s*x bai sani ba, baisan yadda ake yinshi ba ta yaya wanda baisan komai ba akan abu zai aikata?"
manal tace "ta yaya kikasan bai sani ba?"
tace "na tashi tare dashi tun muna yara kanana, Imran tun yana ɗan kankanin yaro nake tare dashi ki sani duk wanda na zauna dashi nasan abinda zai iya kuma nasan wanda ba zai iya ba, sabida ni ba dabba bace me manta komai"
manal tace "to waye dabba?"
ameesha tace "duk me manta Alkhairi dabba ne kamar mijinki"
kukan kura manal tayi ta fito daga inda take tsaye ta shaƙe wuyan ameesha, murmushi ameesha tayi dama haka takeso shiyasa tayi hakan sabida tanaso asalin halin manal ya bayyana a gaban alkali sannan hakan zaisa a ɗaga kara zuwa gaba daga nan zatayi duk yadda zatayi ta fitar da Imran daga wannan zargin, rike manal aka fara, man ne yazo da gudu yana janta, manal tace "saina kasheki"
murmushi tayi tace "dama kin iya kisa ne?"
da kyar man ya janyeta, tsayawa tayi da faɗan, idonta ya gani yana rufewa atake ta fara aman jini a cikin kotun, zaro ido man yayi yana kallonta yace "manal manal open your eye's manal"
alkali yace "an ɗaga wannan case ɗin zuwa nan da sati ɗaya"
duk mutane suka fara fita, man ya kalli ameesha wacce Imran yazo da gudu ya kankameta yana kuka, itama hawaye take, cikin kuka yace "baki karya alkawari ba kinzo banyi zaton zaki dawo ba"
tana rungume dashi tace "sai butulu ne yake manta baya Imran koda me na zama a rayuwa ba zan taɓa mantawa daku ba"
police sukazo suna janyeshi zasu tafi dashi yace "Ameesha zasu koma dani wajen babu daɗi babu komai sai soro da sanyi, nayi kewarki unty ameesha"
juya baya tayi da zasu fita dashi tace "Imran nayi alkawarin kota wuya kota daɗi saina fitar da kai"
man ya kwantar da manal wacce idonta ya juya ta bushe a wajen, cikin wani irin zafin rai ya fuskanci ameesha ya nunata da yatsa yace "meesha"
tana kallon cikin idonshi tazo dab dashi tana wani irin smiling na rainin hankali tace "barrister Ameesha Ibrahim zakace"
yace "idan wani abu ya samu manal"
cikin bushewan zuciya tace "me zakayi? kasheni zakayi? ko nima sharri zakumin a kulleni kamar yadda kuka yiwa kaninka? to amma Inaso ka sani malam Abdulrahman ameesha tafi ƙarfin ɗauri, da wannan maganan da tada jijiyan wuya da kake da matarka ka ɗauka ka kai asibiti watakila yau ta cika shekara huɗu daya rage mata a duniya ko ka manta shekara huɗu dr yace zatayi? ko dai har yanzu ƙwaƙwalwan naka irin na dabbobi ne baka daina mantuwa ba?"
cikin wani irin yanayi yake kallonta yace "idan wani abu ya sameta ba zan kyaleki ba"
tace "idan ka fasa Abdulrahman"
hannu ya ɗaga zai mareta sai kuma ya dunƙule hanun yana huci yana kallonta, murmushin gefen baki tayi tana kallon hanunshi tace "zanso kayi wannan kuskuren koda sau ɗaya ne na marina"
bai kara kulata ba ya juya manal ya ɗaga tana tari yasa hanu a bayan wheelchair ɗin ammi wacce idanunta akan ameesha tana murmushi ya fara tafiya dasu, fahad yace "anty ameesha mama yau kwana uku kenan da ɓatanta babu ita bata kara dawowa ba"
a ruɗe tace "ina taje?"
yace "tunda taje nemawa Imran lauya har yau babu ita, kuma ta siyar da gidanmu"
shafa kanshi tayi tace "karka damu"
man yana jinsu har suka fita, asibiti ya kai manal aka kaita emergency, zama yayi kusa da ammi yayi shiru, jim kaɗan aka fito da ita, shi ya kaita gadon asibitin ya kwantar da ita, juyawa yayi zai fita manal ta buɗe ido, murmushi tayi a hankali ta rike hanunshi, juyowa yayi ya zauna akan kujera yana facing nata, lumshe ido tayi ta buɗe kana cikin muryanta da baya fita sosai tace "ina sanka my abdool"
shiru yayi ya sunkuyar da kai, a hankali tace "ko sau ɗaya ban taɓa ji kace kana sona ba, yau zanso naji wannan kalman daga bakinka"
a hankali ya kalleta, tausayi take bashi, a yadda dr ya faɗa zata mutu nan bada jimawa ba, kuma duk wani sign ɗin da dr ya faɗa na cutan idan ya gama cin karfinta duk ya bayyana domin yaga idanunta suna canja kala suna komawa ɗan jaja, hanunta ya rike a cikin nashi yana murzawa, ta kalli karamin bakinshi tace "ka faɗamin"
a hankali ya matso sosai ya manna fuskanshi a nata yace "i love you manal"
murmushi tayi zatayi magana jini ya fara fita daga bakinta, da sauri ya ɗauko tissue ya goge mata, hanunta cikin nashi tace "kiss"
murmushi tayi dan ya lura tana son kiss koda yaushe idan suna zaune bata rabo dayi mishi, bakinshi ya manna a kumatunta, a hankali ya zame ya fara manna mata kiss a duk inda yaci karo